Showing 72001 words to 75000 words out of 182238 words

Chapter 25 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt

Advertisement

kansa ke da wuya yaga ashe bacci ne ya ɗauke shi. Saurin bacci ba ɗabi'ar Kamal bace. Kuma bai fi minti biyar da raka ƴan uwansa waje ba don ya tabbatar sun tafi. Ya yi tsammanin zai dawo su yi hira ma tunda yaga kamar jikin da sauƙi. Hankalinsa sai bai kwanta ba. Anya allergy ne kawai? To ko kuma allurar bacci aka yi masa? Shi kaɗai ya dinga saƙe saƙe a ransa har Mubina ta shigo.

Haɗuwar farko ta jinjinawa soyayyar dake tsakanin ƴan uwan biyu. Lokacin Kamal ya tashi har Taj ya bashi labarin yadda su ka yi a Abuja. Ya ɗora da mitar me yasa ya zama na ƙarshen sanin bashi da lafiya. Cacar bakinsu su ka yi aka daidaita. Sai ga Kamal kamar ba shi ba. Jikinsa ma yayi ƙwari sannan kumburin duk ya sauka.

"Zan sallameka amma akwai magunguna da zan sabunta maka. Don Allah kada kayi wasa dasu."

Tashi Taj ya yi ya ce "Idan akwai a pharmacy ɗinku ki bani na siyo kafin mu tafi."

"A'a ka barshi kawai" in ji Kamal

"Ba duka za a samu ba." Ita kuma ta ce da sauri.

Murmushi Taj ya yi, amma a zuciyarsa yaji rashin yarda dasu. Zargin nasa bai sami ɗorewa ba da yaga da gaske Mubina wata kulawa ta musamman take bawa Kamal. Daɗi ya kama shi. Wannan karon da alama za a dace, Kamal zai daina gudun matan da yaga yana yi.

"Bari na baku wuri ku ƙarasa maganan. Na san ba komai na patient ya kamata wasu su ji ba."

"Har akwai abin da ya shafeni wanda bai kamata kaji ba?" Kamal ya faɗi yana ɗauke kai daga hararar da Mubina take masa.

"In ta faɗa ka sanar dani. Bari na duba ko Bishir ya zo."

Ficewa ya yi ya barsu. Mubina ta sami sakewar ƙara sanar dashi dokokin da ya kamata ya kiyaye.

"Me yasa ya fita?"

"Ya zata akwai wani abu tsakaninmu. Bai san ni yanzu soyayya ko sadakarta aka bani zan mayarwa mai ita ba."

Murmushin zuci kawai Mubina tayi. In zai ɓoyewa kowa ita ba zai yaudareta ba. Tana da saurin karantar mutane. Tun farkon zuwan Kamal asibitin ta fahimci ya kamu da sonta. Sai dai bayan ya gama faɗa mata alamomin ciwonsa da aka yi gwaji ta sanar dashi lalurar shikenan komai nasa ya sauya. Soyayyar da take gani ƙuruƙuru ta koma yaƙin neman lafiya. Da ya gane da wuya lafiyar ta samu sai ya zama mai mugun sadaukarwa ga duk wanda yake mu'amala dasu. Musamman wannan ɗan uwan nasa Taj. A halin da ake ciki za ta cigaba da adana soyayyarta ta mayar da hankali wurin ganin ya sami lafiya. Bata son ta bari komai ya shiga tsakanin aikinta a kan samun sauƙinsa.

***

Bayan kwana biyu da sallamar Kamal ya wartsake har ya koma shagonsa. Sai lokacin Taj ya sami sukuni da nutsuwa a ransa. Kullum yana tunanin Hamdi amma damuwar Kamal ta ishe shi. Daɗinsa ɗaya da ya koma gidan Ahmad Salwa ta tafi Bauchi. Hankalinsa kwance ya soma fafutukar neman gida don Inna ta faɗa masa bikinsa ba zai ɗauki lokaci ba. Yawancin fitar da Abba su ke yi ko Bishir. Bai fiye neman Kamal ɗin ba saboda yana ganin hutu ya kamace shi ba taya shi neman gida ba. A cikin kwanakin kullum yana waya da Abba. Abban ya so zuwa duba Kamal amma da ta tuna yadda su ka yi Alhaji sai ya haƙura kawai ya kira shi. Yaya har fushi tayi. Ta nuna masa rashin dacewar hakan. Shi dai haƙuri ya bata da ƴan dabarun wayo har ta daina zancen.

Yau alhamis ta kama kwana shida da ɗaurin aurensa. Ya sami sabon gida a sharaɗa self-contain daidai me sabon aure. Mama ce ta bashi shawarar kada ya ce sai ƙaton gida. Gara ya mayar da hankali wajen gina filin da su ka saya shi da Kamal shekara biyu da su ka wuce.

Shirye shiryen biki yana ta kankama. Iyayen basu saka rana ba sai sun ci ƙarfin shirinsu. Masu haɗa lefe su Yaya Hajiyayye kuma an taso Taj a gaba ya kawo size ɗin underwear ɗin Hamdi. Ya gama zille zillensa ta biyo shi har office a Happy Taj ta saka shi a gaba.

"Kirawota a gabana ka tambaya."

"Na ce miki fa zan tambaya yau ɗinnan na turo miki."

"Ai na gaji da gafara sa. Kai ko irin abinnan na angwaye da an ɗaura aure su fara damun amarya da fitina da alama baka iya ba"

Kunya kamar ya fice ya bar mata office ɗin.
"Haba Yaya Hajiyayye. Sai kace wani ɗan is**. Kunyarki ma ta kama ni."

Dariya tayi sannan ta ce "Ka kira yanzu nima jirana ake yi in faɗa."

Ido ya zaro "wa da wa za ki faɗawa? Wannan ai tonon silili ne. Kowa sai ya san girmanta saboda Allah? Sirri ne fa." Ya yi kicin kicin da fuska.

Yaya Hajiyayye me zata yi kuwa banda dariya.
"Sirri manya. Ba dai naji ance weekend za ka kaiwa su Hajiya ita ba? Tana cire mayafi zan aunata tas da ido wallahi."

"Zan fasa kawota."

"Ka ma isa?"

"To umarnin zan bata kada ta yarda ta cire mayafi...kai, hijab ma za ta saka."

"Kayi ka gama. Telan da zai yi mata ɗinkunan biki ma ranar zai zo aunata." Ta ce tana kallon idanunsa.

"Tela kuma?" Ya ambata kamar yau ya fara jin kalmar "Dama har yanzu ana wannan jahilcin Yaya? Na zata yanzu mata ke auna kansu su bawa telan idan ma namiji ne."

Ganin ta same shi a hannu ta cigaba da kunna shi.

"Ɗinkunan maza ai sun fi na mata kyau. Sun san duk wani lungu da saƙo da za su auna saboda shape ya fito."

Abu ya yi tsamari. Taj harda gumi don takaicin yadda idanunsa ke nuna masa Hamdi a gaban wani ƙato yana gwadata. Mantawa ya yi da girman yayar tasa ya ce,

"Wannan dai kafurci ne ƙaɗa'an. Kamar ba a zuwa islamiyya a garin nan?"

Ta gimtse dariyarta da ƙyar "mu ne kafiran kuma yau Taj?"

"Allah Ya baki haƙuri" ya ce yana kumbure kumbure.

Dariyar da take dannewa sai da ta fito. Tayi mai isarta ta ce to lallai a yau ɗinnan take so ya tura mata kafin ƙanwarsu da ta tafi UK da mijinta ta dawo nan da kwana uku.

Tunda ta tafi yake tunanin yadda zai tambayi Hamdi. A ganinsa mai baki amma yana da kunya. Ga amaryar tasa ita ma gwanar tsiwa. Ƙarshenta daga tambaya ta fassara shi.

*

A unguwar tasu ya yi Isha tare da Abba. Ya jira shi ya sanar da Yaya zuwansa sannan ya shiga su ka gaisa.

"Kwana biyu mun tada kai tsaye. Naji kana ta yawon neman gida."

"Yiwa kai ne Yaya."

Abba ta kalla don bata daina fushin zuwa dubiya ba "Kamal bai yi fushi damu ba ko?"

Shi da ya san komai a bakin Zee ya riga ya fahimci Abba tsoron zuwa yake kada su haɗu da Alhaji. Nuna mata ya yi babu komai tunda ba jimawa ya yi ba. Kwana ɗaya ne.

"Allah Ya ƙara masa lafiya." Ta tashi ta ce "Me za ka ci a ɗora maka? Yau abincin ana magariba da kowa ya ci aka bayar saboda zafi. Abbanku kuma ya ce a ƙoshe yake bamu ajiye masa ba."

Shi da ba wata surukuta yake yi da su ba sai cewa ya yi zai ci indomie. Abba ya miƙe saboda sabo zai tafi kitchen ɗin.

"Girkin matarsa zai ci. Don Allah zo ka tafi ka watsa ruwa ka huta."

"Au...haka ne fa" ya furta yana jin kamar ya faɗawa Yaya gaskiya. Baya son su fara jindaɗin kasancewa tare bayan ya san auren ba mai ɗorewa bane.

Dariya su ka bawa Taj. Yaya ta ce ya jira yanzu za ta turo Hamdi.

*

Tana jin takun Yaya ta gyara filo ta kwanta. Dama tunda taji muryarsa ta san sai an nemeta. Ba kuma son ganinsa take yi ba. Abubuwa uku ke damunta. Haushin abin da Alhajinsa ya yiwa mahaifinta da wa'adin da ya basu, sai kuma rashin nemanta da ya yi na tsayin kwanakin nan. Na ƙarshe kuwa kewarsa ce da ta mantar da ita rashin son girkin da yake yi. Ranar da taji Kamal ne babu lafiya dai tayi masa uzuri amma sai taƙi kiransa ta kira Kamal ɗin.

"Tashi kafin ranki ya ɓaci." Yaya ta kai mata duka a cinya. Ta tashi tana sosa wurin.

"Kina fa da zafin hannu Yaya."

"Wuce ki ɗan gyara fuskarki ki je ki dafawa Taj indomie."

"Indomie kuma? Ba ya iya dafawa ba? Ya tafi gidansu mana." Ta turo baki.

Hannu Yaya ta kai za ta ɗalle bakin ta gudu.

"Bana son rashin ɗa'a Hamdi. Kuma saura idan kin je ki kasa gaishe shi. Mara kunya kawai."

Yaya na fita tayi saurin cire kayanta ta saka riga da wando na bacci ta ɗora hijabin da ya wuce gwiwarta kaɗan. Fita ta zo yi Zee ta kama kiran Yaya.

"Zo kiga a yadda za ta fita."

Saurin rufe mata baki tayi "gulma dai haramun. Ina ruwanki?"

"Babu ruwana amma dai a matsayina na mai jin maganar iyaye zan so ƴar uwata ma tayi hakan."

Harara kawai ta gallawa Zee ɗin. Ta koma gaban ɗan madubinsu ta fesa body spray sannan ta shafa hoda da man leɓe. Dama niya tayi taje masa tana hamma ta ce bacci take ji.

"To uwar iya...haka yayi ko kuwa sai na cire hijabin?"

"Da yafi bada citta don wallahi har laɓe sai nayi muku."

Hamdi ta tafa hannuwa "gulmawiya, shi yasa naga kin yi saving sunan Baballe da Sadiq a wayarki? Wato ɗan zuwan nan da yake yawan yi har ya kwance miki hadda. Kin manta kukan bakya so ɗin da ki ke yi."

Zee taji kunya sosai. Sai ta cije don Hamdi ba za ta rabu da ita da wuri ba.

"So muke mu rigaku haihuwar da Ya Taj ya ce ku za ku fara yi."

"Na shiga uku. Zee zancen haihuwa yayi miki? Da wa zai haihun?"

Zee ta ƙyalƙyale da dariya "Hamdiyya Habib mana"

Tana faɗin haka ta fice daga ɗakin. Hamdi ta gama jimamin maganar ta fito da ƙudurin fara cika umarnin Abba. Za ta cigaba da nunawa Taj bata son girki da ma wasu abubuwan da take jin za su taimaka wurin ɓata masa rai.

*

Danna waya yake su na chatting da abokinsa Wakili da su ka yi karatu tare a Indiya ta shigo. Sallamar nan ciki-ciki da gaisuwar.

Taj ya yi kamar bai ji ba yaƙi amsawa. Sai da ta shigo cikin falon ya ɗaga kai ya kalleta.

"A dinga sallama ƴan mata."

Ta juya idanu "Ai nayi."

"Banji ba." Ya faɗi lokaci guda ya shagala da kallonta. A garajen fitowarta hijabi ruwan madara ta saka mara kauri. Da kaɗan ya wuce babu a jikinta. Rikita masa lissafi yaga tana neman yi ya wayance da cewa "ba za ki iya sallamar bane in tafi?"

Ta turo bakin nan "to Assalam alaikum."

"To wa alaikum salam."

"Guda nawa kake ci?"

"Me?"

"Indomie ɗin mana."

"Oh, ki kimanta." Ya gyara zama abinsa.

Tana son tambayarsa ko me da me za ta saka a ciki amma bata son yawaita yi masa magana. Fita tayi ya ajiye wayar da dama amfaninta rage masa kallon ƙurillar da yake yi mata.

Ita kaɗai ta kama tsaki da ta tuna yanzu ƙila fa duk yadda za ta dafa zai ji bata yi ba saboda sabo da girki. Yanke shawarar yinta normal kawai tayi. Ta ɗauko attaruhu da albasa za tayi grating amma bata san gejin cin yajinsa ba. Ƙarshe dai guda biyu ta saka da ƙaramar albasa. Ta raba jajjagen biyu sai taga kamar yayi yawa. Kaɗan ta saka ta dafa indomie ɗin dashi. Sai ta kuma soya wani da curry da ɗan maggi cikin mai daidai suyar ƙwai. Yana fara ƙamshi ta juye ƙwai uku da ta kaɗa a kai. Ƙamshinsa har falo. Ta kawo cucumber ta yanka rabi a zagaye ta jera a gefen plate ɗin mai ɗan zurfi kaɗan ta tsakiya. Indomie ɗin tana ƙarasawa da sauran ruwa mara yawa ta juye sannan ta rufe kanta da ƙwan. Yadda bata son ci da sanyi shi yasa tayi gaggawar kai masa.

Tana ajiye tray ɗin ana ɗauke wuta. Taj ya kunna torchlight ɗin wayarsa ya hasketa tayi saurin rufe ido.

"Hamdi da zuciya ɗaya kika dafa min dai ko?"

"Me ka gani?"

"Wuta aka ɗauke. Kin san mu a India yanzun nan sai mu fassara abu."

Murmushi tayi don ta fara gano tsokanarta yake da zancen Indiyan nan.

"To Shah Rukh Khan. Da me ka fassara ɗauke wutar?"

Taj ya haɗiye abincin da ya kai bakinsa ya ce "Da lokacin waƙa cikin duhun dare mana. Muna bin bango muna rawa."

Toshe bakinta tayi ta kama dariya. Abin nasa azimun. Wai bin bango. Ganin ya tsura mata idanu amma bai fasa cin abincin ba shi ne ta ce.

"Bin bango kamar wasu ƙadangaru."

"Kin ci sa'a yunwa nake ji da na tashi na gwada miki yadda ake yi."

"Bana ma son sani" ta zare wayar fitila daga inda aka jona chaji ta kunna. A take haske ya wadata a falon. Ta buɗe fridge ta ɗauko ruwan sanyi ta ɗauko da kunun ayan da Yaya ta haɗa da rana.

Ta kawo gabansa ta ajiye a gefen tray ɗin sannan taje ta kawo kofuna guda biyu ta dire masa. Kujerar nesa dashi taje ta zauna

"Nagode" ya ce bayan ya gama. Abincin kaɗan ya rage.

Hamdi ta kalle shi da wutsiyar ido "banlbu daɗi ko? Ba irin haka ka saba dafawa ba?"

"Ke dai ki ce kina son in yaba miki. To nayi. Yayi min daɗi sosai."

Bata yarda dashi ba "duk iya girkinka?"

"Girkina daban, na matata Hamdiyya ma daban. Zan dinga taimaka miki a kitchen amma ba kullum ba. Ina son in dawo gida kamar kowane namiji in ci abincin da matar gidan ta dafa."

Yana lura da yadda maganarsa tayi mata daɗi. Ba dai ta son nunawa ne. Shi kuwa indai tana da kunnuwa to ba zai fasa faɗin maganganun da za su yi tasiri a zuciyarta ba. Tashi yayi ita ma ta miƙe.

"Bari na ƙarasa gida na huta kuma."

Tray ɗin ta duƙa ta ɗauka ya ce "na faɗawa Yaya ranar asabar zan zo mu je gidanmu."

"Gidanmu ko gidanku?" Ta ce a tsorace.

"Saurin me kike yi? Gidan iyayena ba gidana ni da ke da ƴaƴanmu ba"
Ya ƙare maganar yana kashe mata ido.

"Sai da safe" tayi masa fuskar shanu. Hira dashi tana yi mata daɗi amma biyewa zuciya ganganci ne.

"Oh, don Allah ɗauko min underwear ɗinki na sama da na ƙasa ana son ganin size."

Tray ɗin hannunta ta kusa saki da taji me ya ce. Bata ankara ba taji hannuwansa sun damƙi nata. A karo na biyu su ka ji wannan yanayin da ya bambanta da in sun taɓa kowa. Zame nata hannun tayi ta bar masa tray ɗin.

Taj ya ce "yauwa yi sauri. Kuma don Allah wankakku."

Wata uwar harara da ta banka masa ba shiri ya ajiye tray ɗin a inda ta ɗauka.

"Ai gaskiya ce. Naji an ce ƴan mata maimaici su ke na sati biyu ko ma fi kafin su wanke."

Kamar za tayi kuka ta ce "Don sharri? To ba zan bayar ba. Idan ma bokanka ne yake so kace masa na hana. Ya turo aljanu su satar masa."

"Dare ne dai kuma babu wuta. Ki cigaba da kiraye kirayen abubuwa. In su ka zo..." ya faɗi a hankali yadda zancen zai shigeta.

Ai kuwa bayanta ta kalla da sauri ta ɗan matso kusa dashi. Tausayi ta bashi. Duk tayi wiƙi wiƙi da idanu.

"Yayata ce ta ce na tambayeki fa."

"Size ake tambaya ai. Ya za ka ce in baka?" Hamdi ta ce da mamakin irin nasa tunanin.

"Don kada ki faɗa min ba daidai ba. Nafi son komai accurate."

"To ba zan bayar ba. Ka kamanta yadda ya dace." Ta ɗora hannuwa a ƙugu.

Taj ya san bata da masaniyar shigar da tayi. Da bata yi wannan tsayuwar a gabansa ba.

"Don't dare me Hamdi. In ki ka yi wasa da hannuna zan kamanta."

Da sauri ta koma bakin ƙofar falon har tana tuntuɓe saboda gigitar kalamansa.

"Matsoraciya."

"Naji."

"Za ki turo size ɗin ko in sa Zee ta ɗauko min na tafi dasu?"

Zai aika ta sani yanzu. Tunda ya iya faɗa mata zasu riga haihuwa ai komai ma is possible yanzu.

"Zan turo." Ta ce a hankali.

"Good girl. Sai jibin ko?"

Kada azo tafiya ya ce su biyu kaɗai shi yasa ta ce masa da Zee za su je. Shi kuma ya ce a'a don yanzu matar aure ce. Sai ta ce to da Halifa.

"Haka kawai sai in ɗauke ki da ƙato a mota?"

Hamdi ta ɓata rai "Halifan ne ƙato?"

"Yanzu duk duniya daga Abba sai ni sai Alhajina ne kaɗai normal maza a wajenki. Sauran kowa ƙato ne."

"Kaima ƙaton ne kuwa."

"Mijin ƙatuwa ba."

Dariya yake yi da yayi maganar. Sai gata tana murmushi. Fushi dashi ma da alama ɓacin lokaci ne. Sai da safe ya yi mata ya tafi. Ta tattare kwanukan ta tafi kitchen tana wankewa hirarsu na dawo mata. Da ta gama gidan tsit yayi mata. Yau ko inji Halifa bai fito ya kunna ba da aka ɗauke wuta. Bata san Yaya ce ta hana ba. Wai ƙarar za ta dami Taj.

Ƙaramin table ɗin da ta ɗora masa tray taje ɗaukewa sai taga wayarsa. Ta ɗaga ta juyata a hannunta. Dole masu iphone su ke jin kansu. Wayar a hannu ma daban take. Abba ta yanke shawarar bawa da safe don da alama yau sun yi baccin wuri.

Kimanin rabin awa da tafiyarsa taga kira daga wani suna an sa Anti Zahra. Sai da aka kira na biyu sannan ta ɗauka. Muryarsa taji ta saki ranta. Ya ce ta ajiye wayar zai zo ya karɓa washegari.

"Zan bawa Abba ya taho maka da ita."

"To nagode. Goodnight."

*

Famfo iya famfo Mami ta yiwa Salwa. Tunda ta koma gida da ramar kwana biyu amma kamar tayi jinya hankalin Mamin ya tashi. Ta kira Ahmad ta ƙare masa tanadi. Harda kiransa wanda baya kishinta.

"Aure kuma tunda tana so ko uban naku bai isa ya hana ba."

"Mami kin fi so ta kai kanta inda ba a sonta? A ƙarshe ta dinga fuskantar wulaƙanci."

"Rufe min baki. Matan gidanku sun gama cinye maka zuciya baka iya taɓuka komai. Arziƙin Taj kai kana da rabinsa ne?"

"Kowa rabonsa yake ci Mami. Don Allah ki daina biyewa Salwa."

Cikin faɗa tayi masa tsawa "Salwa za ta dawo. Ina so ka yiwa Alhajin naku maganarta don na san yana ƙaunarta. Ita wadda Taj ɗin ya aura na riga na samu bayani akanta. Bata da wani abin nunawa balle ta kara da jinina."

Ta inda take shiga daban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login