Showing 174001 words to 177000 words out of 182238 words
Chapter 59 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt
ya canja min kaya ba?"
"Yesss"
"Kaya dai har sai da su Alhaji su ka shigo yi min sai da safe su ka ganni da su, na kasa cirewa. Shi da Abba Habibu ne su ka cire min. It took more than 10 minutes saboda su na tsoron fama min ɗinki."
"Ya Rahman" Mubina kanta sai da taji kunya.
"Da su ka gama ne Alhaji ya ce sai na biya ladan wahalar da jikin girma. A gabana su ka cinye naman nan. Harda cewa ranar da za ki tare zai biya mu." Ya ɗan cije baki "Saboda Allah me zai sa ya yi min zancen tariya? Don na ɗan yi kwalliya shikenan sai a fassara ni? Ko ni na kawo fitina duniya ai dole in jira nayi healing ko?"
"Ni dai na shiga uku."
"Wallahi kin shiga. Kazar amarci surukan ki maza sun cinye. An barwa ƴaƴa tarihi."
Kamar za ta yi kuka ta ce "to ni yanzu yaya zan yi?"
Kamal ya ware hannuwansa yana kallon cikin idanunta.
"You can start by giving me that first halal hug."
Bata san abin da zai ce ba kenan da ba za ta zauna a kurkusa yadda kunyarsa za ta kama ta da yawa haka ba.
"Idan ka warke kayi da kan ka." Ta faɗa a ciki-ciki.
"Mubina" ya tsare ta da ido.
"Na'am."
"Now please."
Magiya ce ko umarni? Ita dai bata gane ba. Abin da ta fahimta kawai shi ne zuciyarta tana muradin yin abin da mamallakinta yake so. She gave him the warmest hug. Zuciya da gangan jiki su ka sami kyakkyawar nutsuwa.
A lokacin da Kamal yake tunanin Mubina ta gama biyansa da alkhairi, she brushed his lips lightly da nata. Tsokana ta so yi, reshe sai ya juye da mujiya. Happiness got his happiness and he wasn't willing to let go easily.
Kamal da Mubina Allah Ya ƙara lafiya da zaman lafiya!
***
Wani irin kuka Inna Luba ta fasa daga ɗaki mai firgitarwa. Malam da yake ririta ta tun jin Yaya ta tafi Saudiyya ya fito daga banɗaki da zariyar wando a hannu.
"Luba me ya faru? Mutuwa aka yi?"
Inna Luba kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa. Amarya duk jarabarta jikinta ya ɗan yi sanyi. Shi yasa bata faɗi magana mara daɗi ba da ta fito. Banda haka da tuni ta fara domin tsufa bai rage mata komai ba. Da ƙyar Malam ya samu cikin kuka Inna Luba ta faɗa masa wayar da aka kira ta daga Kano.
"Surukar Abdulƙadir ce ta kira yanzu wai za ta yi min jaje."
"Waye kuma Abdulƙadir?"
"Ƙanin Habibu mana."
"To, sata aka yi ko gobara wani cikinsu ya yi?" Amarya ta tambaya tana jin haushin tsurkun da ta fito kuma da alama labarin ba zai ƙayatar da ita ba.
"Yarinyar nan ce..."
Malam ya dafa bango jiki na rawa. Sai ka rantse bai taɓa nunawa Yaya ƙyama ba. Ya marairaice sosai gwanin ban tausayi.
"Lubabatu bar zancen nan haka. Zuciyata ba za ta iya ɗaukar zancen mara daɗi akan gudan jini na ba."
"Wannan kam dole sai ka ji. Wai anyi mata aiki an cire mata ƙoda guda ɗaya an dasawa wani yaro."
Da wani irin zafin nama Malam ya zabura kamar ba tsohon da yake taku da ƙyar ba saboda ciwon ƙafa.
"Me???"
Yadda taji ta maimaita. Dama su kan gaisa a waya da ita a matsayin surukai. Ashe duk gargaɗin ds Abdulƙadir ya yiwa matar tasa akan ɓoye zancen sai da ta sanarwa ƴan gidansu kaf. Ita kuwa Mamansu da bata san ɓoye zancen ake yi ba ta kira Inna Luba domin ta jajanta mata. Jinjin ta bayar da ƙoda an dasawa wani ɗan balarabe a Makka.
"Jar uba! Kin ga kira Ɗandaudun nan ki haɗa mu kawai. " Baba Malam ya nuna kansa yana jijjiga jiki "Ni za a ha'inta? Ɗiyar tawa za a feɗe daga zuwa ibada? Dama can ban yarda yana da kuɗin kai Jinjin Saudiyya ba. Matsiyaci mai tafiyar mata. Ina yi masa kallon wanda ko ƙuda ba zai iya kashewa ba ashe ja'irin ƙodar ɗiyata zai sayar. Allah Ya isa Habibu!"
To Inna Luba dai babu bakin kare Abba Habibu domin kuwa bata san gaskiyar me yake faruwa ba. Ana haka gida ya kaure da tsine-tsine da zagin bawan Allah Abba Habibu sai ga wani ɗan saurayi cikin jikokin Amarya. Inna Luba ta miƙa masa wayarta ko zama bai yi ba.
"Ya'u maza lalubo min lambar Sajida ka kira."
Ya'u ya yi abin da ta ce ba tare da tambayar komai ba duk da mamakin da ya cika masa zuciya. Kiran na shiga ya miƙa mata wayar sai dai kafin ta ankara Malam ya karɓe ya manna a kunne yana masifa.
"Maza-maza ki yiwa ubaki waya ki ce ya kira ni yanzun nan."
"Baba Malam me a ka faɗa muku?" Sajida ta fahimci ba lafiya ba "don Allah ka tsaya nayi maka bayani."
"Ƴal ƙwal uba har ki na da bayanin da za ki mani? Me ya hana ki neman mu kafin yanzu tunda da alama kin san komi" ya yi ƙwafa "wato kun haɗa kai da baban ku za a kawo muku kuɗin jini ku wanki biyar ku tsoma biyar, ni da na san zafin haihuwarta kuma a barni da kukan rashin ɗiyata. To wallahi ba ku isa ba. Nemo shi ki ce masa lallai a mayar mata da ƙodarta."
Sajida ta sake kwantar da murya
"Baba Malam ka yi haƙuri. Ba abin da ka ke tunani bane. Yaya taimako tayi da ceton rai."
"Da ƙodarta? Ke Sajada, kada ki raina min wayau mana don kawai kin ga ina rayuwa a ƙauye. Tun Kaka da Kakanni ban taɓa jin an cire sassan jikin wani an dasawa wani ba. Zancen nan bai yi kama da wanda hankali zai ɗauka ba."
Haƙurin ta sake bashi ya ji haushi ya surfa mata zagi daidai wa daida. Ya ce kuma ta saka a ranta cewa Yaya na dawowa zai maka Abba Habibu a kotu a raba auren su. Jin haka Inna Luba ta karɓe wayarta ta ce da Sajida tayi maza ta nemi Abbansu.
"Idan bai kira ni ba to nima zan bi shawarar Malam." Ta katse kiran.
Hankalin Sajida ya tashi sosai. Ranar kwanan su Taj biyu da tafiya Madina ta kira ta sanar da Abba Habibu yadda su ka yi da su Baba Malam. Murnar sauƙin da su Yaya ke samu sai ta koma ciki domin kuwa nasa hankalin ba ƙaramin tashi yayi ba. Alh. Hayatu ya yi Allah wadai da halin surutun wasu mutanen.
"Wani lokacin sai ka yi tunanin akwai masu ɗokin zama ƴan yaɗa labari mara daɗi. Suna rawar jikin zama farkon waɗanda za a ji mummunan labari daga bakinsu. Banda haka wane irin rashin nazari ne zai sa a kira tsohuwa a tayar mata da hankali irin haka?"
"Yanzu ta ina zan fara? Ta yaya zan yi musu bayanin da za su fahimta?"
Abba Habibu cikin damuwa, Yaya kuma tana ta kuka. Tausayinsu ya kama Hajiya, musamman da ta tuna rayuwar ɗanta ce ta janyo mu su.
Jikin kowa yayi sanyi. Sun kira su Inna Luba amma ko kusa Baba Malam bai bata wayar ba. Shi kaɗai ya dinga faɗa kai ka rantse tunda Yaya ta taso bai taɓa juya mata baya ba. Maganganunsa duka ana ji domin faɗa yake yi iya ƙarfinsa. Har cewa Yaya ya yi ta tabbatar ta karɓi takardarta kafin su dawo. Hajiya dai sai da tayi kuka mai isarta. Yanayin ɗakin ya koma wani abu daban a tsukin lokacin.
Ana haka sai ga kiran tawagar Madina. Dama kullum sai sun kira an gaisa. Hajiya na karɓa ta ce a bawa Yaya Kubra wayar. Sai da ta fara gargaɗinta akan kada maganar da za su yi ta fita musamman zuwa kunnen Hamdi sannan ta tambayeta shawara.
"Ke ce likita Kubra. Me ya kamata mu yi? Ta ina za mu ɓullo mu su ta yadda za su fahimci girman taimakon da Yaya tayi har ma su yaba mata?"
"Hajiya turo min numbar da zan same su."
"Bari na karɓa sai na turo miki. Amma don Allah ki kiyaye."
Kallo su ka bita da shi har ta tura numbar sannan tace musu su duka babu mai ilimin da zai iya yin bayanin da su Inna ba za su ɗauka son zuciya ba.
"Mu bata dama tunda ɓangaren aikinta ne. Na san Kubra, za ta yi abin da ya dace."
*
Gidan Baba Malam fa babu lafiya. Inna Luba kwanciya tayi zazzaɓi ya rufe ta yayinda maƙota su ke ta zaraf-zaraftu a ƙofar gidan ana ta zuwa jaje da ganin ƙwaf. Amarya ce ta fice fit ta fesawa waɗanda ta san za su tayata yaɗawa. Kafin wani lokaci gari ya ɗauka. Abin ne da mamaki ace mutum ya bayar da ƙoda sukutum kuma yana nan da rai.
Waya na ringing Inna Luba ta tashi da sauri ta ɗauka. Yaya Kubra ta gaishe ta a ladabce sannan ta buƙaci Innar ta haɗa ta da matashi ko matashiya idan akwai a kusa.
"Yarinya ko me za ki ce ki faɗa min kawai."
"Don Allah ki yi min wannan alfarmar Inna. Ki taimaka."
Ba don ta so ba ta fito tsakar gidan. Cikin sa'a tayi kiciɓis da Ya'u. Har yanzu bai koma gidansu ba tunda ya san me yake faruwa. Rigimar kakarsa Amarya da Inna Luba ba sabgarsa bace. Yana ɗasawa da kowa a gidan.
"Inna kina buƙatar wani abu ne?" Ya matso kusa da ita da sauri.
"Gashi" ta bashi wayar ta koma cikin ɗakinta.
Ya'u ya saka waya a kunne ya ce "hyalo?"
Kai tsaye Yaya Kubra ta bijiro masa da buƙatarta bayan ta gabatar da kanta kuma taji daga ɓangarensa. Yadda take magana kaɗai ya yi masa kwarjini don jikinsa har rawa yake wajen amsa mata.
"Aiki ka ke yi ko karatu?"
"Aiki ne. Ina koyarwa a wata pravet a nan kusa da mu."
"Masha Allah. Mal. Ya'u nawa ne albashin ka tsakani da Allah?"
"Et fife (8,500) ne." Ya amsa mata cikin basarwa. Ba ya so tayi tunanin shi ɗin cima zaune ne.
"To zan baka dubu ashirin a yau in sha Allah idan buƙata ta ta biya."
Gigicewa yayi sosai yana ta doka murmushi ba ji ba gani. Ta gama da shi da tunaninsa kaf.
"Me ki ke so nayi?"
"So nake ka samo min waya mai yin bidiyo call na whatsapp."
"Shike nan?" Ya tambayeta da mamaki.
"Ƙwarai kuwa. Idan an samo ka bani lambar in saka data domin wayar za ta iya ɗaukar lokaci."
Ya'u baki har kunne don farinciki ya ce "wayata tana yi sai dai bani da data sannan wassof ɗin ma ya yi ispiya."
"Wannan layin?"
"Eh."
Cikin minti biyar Ya'u yaga 25G. Gani yayi abin kamar wani mafarki da zai iya tashi kodayaushe. Shi da ya saba saka datar naira ɗari zuwa ɗari biyu sa'i da lokaci ina zai kai wannan? Ya yi updating komai da sauri sannan da kansa ya kira. Dr. Kubra Hayatu tayi masa wani irin kwarjini. Ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta sannan ya kaiwa Inna Luba wayar. Kafin a fara jawabi Baba Malam da Amarya suma sun hallara. Ya'u yana gefe Yaya Kubra ta zauna tayi mu su gwari-gwari game da ciwon Kamal, zuwan Yaya asibitin, bayar da ƙodar da ma zuwan Abba Habibu.
Inna Luba tayi kuka babu adadi ba. Muryarta duk ta dashe.
"Yanzu ƴar nan kina da tabbacin rayuwar yarinyar nan ba za ta tawaya ba?"
"In sha Allahu babu abin da zai biyo baya sai tarin alkhairi. Addu'a da kulawa kawai take buƙata."
Baba Malam kuwa cewa ya yi "Idan gudan ƙodar ta sami matsala fa?"
Yaya Kubra ta jinjina tambayar don ta san da wuya a rasa mai yi.
"Komai na Allah ne Baba. Addu'a da kulawa kaɗai za ku iya yiwa Yaya. Sanin gobe kuma sai Allah maɗaukakin Sarki. Abu guda nayi imani da shi, Allah ba Ya taɓa barin wanda Ya fawwala Masa al'amuransa ya taɓe. Mu kyautatawa Allah zato, in sha Allahu babu nadama a cikin sadaukarwar Yaya."
"Allah Ya sa ƴar nan. Allah Ya dawo mana da ita lafiya."
Yaya Kubra ta tausayawa Inna Luba matuƙa.
"Inna na san Yaya a ƙalla za ta yi wata a ƙasar nan kafin ta sami sahalewar shiga jirgi daga hukumar lafiya. Saboda haka ki fara haɗa jaka. Zan yi magana da ƙannena ma za mu ji yadda za ayi a samar mi ki passport da visa."
"Allahu Akbar. Ni ɗin?" Ta kalli Baba Malam "wai Saudiyya zan tafi. Ikon Allah. Allah Buwayi gagara misali. Ni dai Lubabatun ko wata ƴar nan?"
Yaya Kubra ta sha dariya kafin su gama waya. Tana kuma ankare da fuskar Baba Malam. Yaƙe kawai yake yi.
Alhaji ta kira ta tura masa lambar Ya'u ta ce ya kira ya haɗa su Yaya da Innarta. Haka kuwa aka yi. Sun ji daɗin ganin juna. An dai sha koke-koke da addu'o'i. Har Kamal sai da su ka gaisa da shi. Ya yi musu godiya sosai da alƙawarin zuwa har gida idan ya dawo in sha Allah.
***
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah SWT. Yau kimanin sati uku kenan da yiwa Kamal dashen ƙoda. Sauƙi ya samu sosai domin duka an sallamo su daga asibiti. Likitoci dai sun hana su barin ƙasar domin suna buƙatar kulawa sosai har na tsahon wata biyu zuwa uku.
"Ina ganin gara na kama mana gida kawai. Zaman hotel ba zai yiwu ba" Alh. Ya ce da matansa suna zaune duka su huɗun tare da shi a ɗakin hotel.
Inna ta ce "Hakan ma shawara ce, amma kafin nan ya kamata a san masu zama don a kama ɗan daidai. Sauran yaran nan su zo su koma gida haka nan."
"Kamar kin shiga zuciyata akan raguwar nan. Mata sun baro mazajensu sun tare a asibiti ayi ta hayaniya kullum" cewar Mama.
"Kamawa fa tayi." Umma mai ɗan sauƙin ta ce tana murmushi.
"Tunda dai suna samun lafiya mu kanmu sai mu ragu. Ko kuwa Alhaji?"
"Wannan shawarar ku ce. Ni dai ƙafata-ƙafar Habibu da iyalinsa." Ya gyara zama yana sauraron su.
Hajiya aka bawa dama. Ta zauna ta gama lissafinta ƴan uwanta su ka yi na'am. Umma za a bari tare da Bishir. Sai kuma Taj da Hamdi saboda zamanta kusa da Yaya yana da mahimmanci. Mubina ma babu inda za ta je. Sauran kuwa Alhaji ya ce da kansa zai faɗa musu su shirya nan da kwana uku su za su tafi. Sannan akwai wanda zai nema a samar mu su gida.
"Dr. Hadifi ya ce yana son ganin mu ni da Habibu. Idan mun dawo zan yi magana da su."
*
Bakin Abba Habibu ya kasa rufuwa bayan fitar Dr. Hadifi daga ofishinsa inda ya barsu su yi shawara kafin a bashi amsar batun da ya zo da shi.
"Habibu ba ce wani abu mana."
Abba Habibu ya girgiza kai "wallahi bani da abin cewa. Ni dai abin ya yi min girma. Anya zan karɓa kuwa?"
Alh. Hayatu ya ce "me zai hana? Roƙa kayi?" Ya yi gyaran murya "ba ka ganin kamar wata dama ce daga Allah SWT?"
"Har na isa a bani abu makamancin wannan?"
"Kada ka yi saɓo mana. Kowane bawa da arziƙinsa Allah Ya ke halittarsa. Kuma rabon mutum baya taɓa wuce shi. Ko dai ka je da ƙafarka ko ya biyo ka har inda kake."
"Haka ne. Allah Ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi."
"Amin amma don Allah ka yi shawara mai kyau."
Abba Habibu ya yi murmushi "Zan yi istihara in Allah Ya yarda."
*
Zuwa yamma kowa yaji abin alkhairin da ya sami Abba Habibu. Dr. Hadifi ya yi masa kyautar gidan abinci sukutum a nan cikin birnin Jeddah. Tsohon ginin na Kawunsa ne ya saya ashe zai yi masa amfani. Abinnda Yaya tayi ya burge shi matuƙa, sai kuma ya tuna a hirarsu Abba Habibu ya ce ya taɓa sana'ar abinci a nan.
A hoto ya nuna musu gidan. Kusan komai na kayan aiki akwai, gyaran da za a yi kaɗan ne sai kayan abinci da za a tanada. Yayi masa alƙawarin yi musu igama shi da Yaya da duka ƴaƴansu. Sannan zai yi masa gyare gyare da kuma zubin kayan abinci na farko kafin ciniki ya kankama.
"Ku buɗe Nigerian restaurant wanda yake serving abincin ku na gargajiya." Ita ce shawarar da ya bashi.
Kamar haɗin baki duka shawararzu guda. Ya karɓa. To dai ya karɓa ɗin ranar da ragowar masu tafiya za su wuce. Ba su tafi ba sai da su ka je aka ga waje aka sanya albarka.
A gida ma ƴan uwa da su Zee anata murna da rawar jiki.
"Ki bar tunanin tafiya dai kina da aure. A daure a koyi larabci saboda idan na dawo zai yiwu na daina jin Hausa."
"To nima ai ba yanzu za ayi biki ba sai na kai level 4."
Daga cikin ɗaki Anti Zinatu ta ɗago murya "to uwar iya. Ke da yanzu ki ke jarabawar gama sakandire kike kiran level 4 saboda sallamamme ne ya aure ki? To bari iyayen naki su dawo naji ko da yawunsu ki ke wannan saɓon mai girma. In baki yi wasa ba wallahi ranar asabar zan ce da Baballen ya zo ku tafi."
Hankalin Zee tashi yayi tana neman yin kuka. Halifa kuwa dariya harda ƙyaƙyatawa.
***
Godiya da kyautatawar da Ahmad ya yi wa Zahra ba a cewa komai. He truly appreciated kulawar da ta bawa Mami duk da irin zaman da su ka yi a baya. Da ya fito daga wajen Mamin ne ya yi mata zancen Salwa.
"Babanta ne ya damu wai naje naga gidanta."
"Hakan ne ya kamata dama. Ba fa a canjawa tuwo suna."
"Ina ki ka baro amala da fufu? Ko duk ba ƴan uwan juna bane?"
Tayi dariya "ba zan yi musu da kai ba. Don Allah ka ɗauki matsayinka na babba ka wakilce kowa ka je ka ganta. Babu mamaki ma kaga ta sauya. Aure ai ba wasan yara bane."
"Allah ko? Shekararki nawa ne a ciki tuna min."
"Lokaci ɗaya mu ka yi da kai." Ta zolaye shi.
*
Da yamma Ahmad ya kira Salwa ba don ya so ba. Ita kuwa da azama ta ɗauka don ta fidda ran sake ji daga gare shi. Gashi tana jin kunyar zuwa gidansa. Alh. Usaini har gorin dangi yayi mata. Bata yi shawara da kowa ba ta kira Anti Zabba'u. Ai kuwa ranar taga tashin hankali. Irin haukan da su ka yi a gidan Ahmad su ka kwatanta a nan. Alh. Usaini ya zo ya gani ya ci musu mutumci la'ada waje daga su har ita. Banda Mami ta jawo musu ai da yanzu dangi sai sum ture na uwa da uba. Kai ba don abin da tayi ba hatta iyalin Alh. Hayatu sai sun