Showing 54001 words to 57000 words out of 182238 words
Chapter 19 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt
ce min budurwa gareka. Tunda ban san da ita ba, ba za ta zama silar da za ka watsa min ƙasa a ido ba." Baba Maje ya ce a kausashe.
"Ba haka bane Baba" Baballe ya ce a ladabce "ƴar uwarta nake so. Na ɗan jinkirta faɗa mata ne saboda wasu dalilai. Gaskiya ba zan iya aurenta ba alhali ina yiwa ƙanwarta so na aure." Ya ƙarashe kai a ƙasa.
Gumi ne ya tsatstsafowa Baba Maje. Ya dubi ƙofar cikin gidan.
"Danƙari! To yanzu ya kake so nayi? Me yasa ku ke da zurfin ciki ne? Da na sani ko baka faɗa mata ba ai ba zan yi wannan karambanin ba."
"Idan zai bani ƙanwar sai ka sanar da su Kawu a ayi auren goben a madadin na Sajidan. Sai a jinkirta komai tunda ban shirya ba." Baballe ya furta da hope ɗin baban zai amince.
"Dama ko wace ai zan faɗa musu. Ni damuwata ma ita Hamdiyyan za ta yarda ne? Ko ka manta yadda su ka yi da Ummi a makaranta?"
Da sauri Baballe ya ce "Zeenatu ce ba Hamdi ba."
"Wace Zeenatu kuma?" Baba Maje ya ce don kansa ya ƙulle.
Baballe ya yi murmushi "Zee. Naga bata gama makaranta ba. Niyata zuwa ƙarshen shekara idan ta gama na san lokacin na ɗan yi tari. Sai na gabatar da kaina."
Kamar Baba Maje ya make shi don takaici ya ce "banza, kana can kana shiri wane zai shige tsakani sai dai kaji ana batun an kawo kuɗi."
Shi dai tunda yaga kamar ya sauko sai ya kwantar da hankalinsa. Ciki su ka koma tare. Kowa ya zuba musu ido. Baba Maje ya ɗan rissina kai na jin kunyarsu ya faɗa musu yadda su ka yi da ɗansa.
"Alhandulillahi ai duk gida ne." Cewar Abdulƙadir.
"In kun amince dashi maimakon a fara kiran mutane ana cewa an fasa auren gobe, me zai hana a ɗaura nasu. In ya so sai ta tare bayan ta ƙare karatunta."
"Hakan ma ya yi. Bari su dawo daga wajen taron sai a faɗa musu."
In ji Inna Luba.
*
Banda gunjin kukan Zee babu abin da yake tashi a tsakar gidan. Sai da kowa ya watse sannan Inna Luba ta kira su har Halifa ɗakin Abba ta faɗa musu. Sajida ko uffan bata ce ba. Tashi tayi da mutuwar jiki ta koma ɗakinsu. Yaya za ta bita Abba ya hana.
"Ki barta ta sami sararin yin kuka har taji sanyi a ranta."
"Ita kaɗai?" Ta share nata hawayen.
"Wata damuwar tana buƙatar kaɗaicewa kafin zuciya ta karɓe ta. Idan tana buƙatarmu da kanta za ta neme mu."
Zee ya kalla da ta faɗa kan kakarta tana kuka kamar wadda za a zarewa rai.
"Shikenan sai a fara yi min aure bayan ina da yayye?"
Inna Luba tana shafa mata baya ta ce "Ja'ira. Ashe kukan ba na ƙin mijin bane. To ai da sauƙi. Yayyenki kuma ki sani kowacce lokacinta yana hannun Mahaliccinta kamar yadda naki yake."
"Mijin ma bana so Inna." Ta ce tana ƙara sautin kukanta.
"Bana son rashin hankali. Ihun da kike yi maƙota za ki tara mana ko me?" Yaya ta faɗi cikin fushi.
Tana son Iyaa da Baba Maje a matsayin aminansu. Amma auren ne bata da tabbas a kai. Auren da aka yi ta soyayya ma gashi nan bai kafin ayi ya tashi. Ina ga wanda ya yi kama da cushe? Duk son su yi aure da take yi, bata so a wulaƙanta su.
Hamdi ce ta riƙe Zee su ka koma ɗaki. A nan ta tarar da Sajida akan abin sallah. Kuka take yi amma babu sauti. Sai kwararar hawaye kawai. Sau tari ma'anar sunanta tana binta. Mutum ce mai yawan kai goshinta ƙasa wurin Allah.
Zee daina kukan tayi ganin yayarta ta fita nutsuwa. Hamdi ta fita tayi alwala ita ma ta zo ta shimfiɗa abin sallah kusa da Sajida. Ganin haka ita ma Zee sai tabi sahu. Sun riga sun yi sallar isha tun ɗazu. Don lokacin shaɗaya ma ta kusa. Alƙur'ani kowacce ta ɗauka ta buɗe inda ya samu su ka fara karatu. Idan ka gansu abin tausayi kuma abin sha'awa. Yayinda ta ƴan uwan biyu ke nemawa kawunansu zaɓin Allah da sassaucin abin da ya tunkaro su, Hamdi su duka biyun take yiwa addu'ar zaɓin alkhairi. Tana fata kowacce ta sami aminci a ƙaddarar dake jiranta a gobe. Kuka kuwa idanuwansu ko gauta albarka.
Duk wannan abu wayar Sajida vibrating take da kiran Safwan. Ita kuwa tayi alƙawarin sake haɗuwarsu ko jin muryar juna sai in sun haɗu bisa kuskure. Ba za ta ɗauka ba balle ace ta kasa haƙuri da wanda babansa ya zo har gida ya ci mutumcin nata uban.
***
A ɓangaren Taj yadda abubuwa su ka kasance sai addu'a kawai. Roƙon Kamal ya yi akan ya kai shi gidan Yaya Babba ya ce babu ruwansa.
"Ina son rabuwa da iyayena lafiya. Naga kai wannan is the last thing on your mind. Duk nasihar da nayi maka bata shige ka ba."
"Don Allah Abba bai baka tausayi ba?"
"Ya bani, amma addua ce kaɗai taimakon da zan iya yi masa. Da za ka haƙura da auren Hamdi ni kuma nayi maka alƙawarin auren Sajida."
Haushin Hamdi da yake ji ya tuna, sai dai kuma wannan bai isa dalilinsa na haƙura da ita ba. Wannan tsiwar yake son ƙurewa da salon soyayyar da ya tanadar mata. Zafin kai kuwa ya yi imani da cewa bata kai shi ba. Zai gayyato ta cikin rayuwarsa su hau sama su faɗo tare. Barinta ne dai ba zai iya ba. Domin duka wannan rigimar tasu bata kama ƙafar son da yake yi mata wanda ya yi masa shigar farat ɗaya ba.
Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa isa gidan Yaya Babba sai kawai ya canja shawara. Taɓo mai adaidaita sahun ya yi.
"Don Allah ka yi haƙuri. Kantin Kwari zani."
"Malam lissafin kuɗinka fa zai canja."
Taj ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu uku sabbi fil ya bashi.
"Ko akwai ciko?"
Mai adaidaita ya saki murmushin da ya koma dariya.
"Yallaɓai sai dai idan kuma sadaka za ka ƙara min akan wannan."
Taj dake neman taimakon Allah sai ya ƙara masa dubu biyu.
"Idan mun je in jira ka ne Yallaɓai?
"Da ka kyauta. Inda ka đauko ni zan koma."
*
Alh. Hayatu na zaune a cikin ofishinsa dake hawa na biyu a katafaren ginin store ɗinsa mai suna Maitakalmi Enterprises dake kantin Kwari yaji ana ƙwanƙwasawa tare da sallama lokaci guda.
Muryar wani yaron shagon ce wanda ya kasance ɗa a wajen wata da su ke ƴan maza zar da ita.
"Kawu dama..."
"Matsa na shiga" Taj ya ce da ɗan saurayin.
Da sauri ya yi gefe, yayin da Alhaji ya tashi tsaye saboda gane muryar da ya yi.
"Me ya kawo ka?" Ya ce da kakkausar murya.
Yaron da ya nuna masa office ɗin don bai taɓa zuwa ba tunda aka yi ginin sai yau ya kalla. Cikin sauri ya rufe ƙofar ya bar wajen. Taj ya juyo ya kalli mahaifinsa sai kawai ya sauke gwiwoyinsa duka biyu a ƙasa.
"Alhaji na zo neman izini da amincewarka ne." Ya faɗi yana kallon uban.
"Dama nayi wannan isar a rayuwarka ne?"
Zuciyarsa dokawa take da ƙarfi saboda fargaba. Amma ya san cewa indai ya rasa goyon bayan Alhaji, ba zai taɓa auren wadda yake so ba.
"Ka fi ƙarfin komai a rayuwata."
"Shi yasa ka zaɓi barina akan ka ajiye burinka?"
Taj ya girgiza kai "baka bani zaɓi ba a lokacin da ka koreni Alhaji. Hukunci kawai ka yankewa kuskurena."
Zuciyarsa hasala tayi. Ɗan nasa ya fishi gaskiya. Wannan ne ya ɓata masa rai.
"Rashin kunya ka zo ka yi min?"
"Ban isa ba." Ya ɗaga kai daga durƙuson da ya yi "aure nake so ka yi min gobe don Allah."
"Ka fara shan ƙwaya ne Tajuddin? Ni za ka tunkara da wasan kwaikwayo irin wannan?"
"Ƴar wajen Habib Umar ce. Simagade na Soron ɗinki."
Yana gama magana ya rufe idanuwansa saboda jiran saukar mari daga Alhaji. Da yaji shiru na wasu daƙiƙu sai ya buɗe idanunsa. Abu na farko da Alhaji ya fara ce masa shi ne,
"Me ka ke taƙama da shi ne Taj? Kuɗin da kayi ne kake jin ya isa ka kawo min zancen banza irin wannan?" Ya nuna ƙirjinsa "Ni? Ni za ka cewa kana son auren ɗiyar Habibu?"
"Bana taƙama da komai Alhaji sai matsayina na jininka. Ka juya min baya a karo na farko amma Allah Ya tsareni daga faɗawa rayuwar da kake guje min. Ba yin kaina bane. Ba kuma isarka bace ko tawa. Albarka ce kawai daga Allah wadda na tabbata kullum kana roƙa min."
Kallon mamaki kawai Alhaji ya dinga yi masa. Yana kuma tuno kalaman Gwaggo na ƙarshe ƙarshe a gare shi da take cewa Taj tamkar shi ne a madubi. Yadda yake haka ya haifo ɗa irinsa. Duk lokacin da yake son taƙwara ɗansa, to ya fara bari shi ma duniya ta tanƙwara shi.
"Shi yasa yanzu ma ka shirya saɓa min saboda kana jin komai zai tafi yadda kake so?"
"Wannan karon ina jin tsoron idan ka barni kada na saɓawa Allah akan soyayya..."
"Kai Taj ka kiyayeni. Ni kake faɗawa waɗannan maganganun?" Alhaji ya furta kansa na yi masa wani irin nauyi.
"Ina sonta Alhaji." Ya faɗa kai tsaye abinsa.
"Ita ƴar Habibun?"
"Eh."
"Zo ka zauna"
Don dai shi tsayuwa tana neman gagararsa. Kan kujera su ka koma. Alhaji ya daɗe yana tunani kafin ya ce da Taj,
"Ka tafi gida ka jirani."
"Gidan Yayan za ka zo?" Ya tambaye shi da wata irin murna don ya san ina yake nufi.
"Gidana nake nufi Tajuddin. Ka je can ka jirani."
Godiya ya yi ya tashi ya fita. Sanin me Alhaji zai ce sai Allah. Shi dai buƙatarsa ita ce ya sami damar yin auren da zai fidda Abba daga kunya gobe da izinin mahaifinsa. Haƙuri ya bawa mai adaidaitan ya ce inda za shi ya canja. Mutumin ko a jikinsa tunda ya caski kuɗi.
*
Mutane sun kai biyar da Alh. Hayatu ya bawa aikin yi masa duk wani binciken da ya dace akan Abba Habibu. Kafin isha'i dukkanin bayanai sun riske shi. Tun daga zamansa a Lagos bayan ya yi aure har batun auren babbar ƴarsa da za ayi gobe. A duka bayanan yafi mamakin dalilin da yasa Taj da Kamal nemo Simagade. Da kuma aikin da Taj ya bashi. Share wannan ya yi ya kira mahaifin Safwan domin kuwa ya san shi duk da ba wai abokai bane. Shi kuma yadda yake mutunta Alhajin yasa ya faɗa masa auren nan fa babu da dalilinsa. A ƙarshe yadda ya fahimta wanda kuma da ƙamshin gaskiya a ciki, auren ragewa Habibu baƙinciki Taj yake son yi.
Dariya ce ma ta kama shi. Wato ta wannan hanyar Habibu ya zaɓi ya dawo cikin rayuwarsa. Lallai zai nuna masa kuskurensa a lokacin da ya dace.
*
Gida kowa murna ganin Taj ya shigo kuma ya ce Alhaji ne ya yi masa izini. Inna harda kukan farinciki. A gidan ya yi Magriba sannan Kamal ya dawo. Yana ganinsa ya sha jinin jikinsa.
"Wace tsiyar ka ƙulla?"
"Alkhairi dai. Zancen auren Hamdi nayi masa."
A harzuƙe Kamal ya ce "ba ka da hankali ko? To wallahi yana da bindiga. Ƙarshenta ma harbeka zai yi."
Taj ya ƙyalƙyale da dariya. Kamal ba dai tsoro ba. In anyi magana kuma ya ce Taj ɗin ne matsoraci.
Wuraren tara na dare Alhaji ya dawo. Yana hawa sama ya kira Taj. Bai nuna masa ya san komai ba. A gabansa ya kira Yaya Babba ya yi masa magana.
"Ɗanka ne ya ɗauko aure bagatatan. Wasu matsaloli ne su ka taso da su ka sanya auren dole ayi gobe. Zan zo gidanka da safe kafin lokacin mu yi magana."
Yaya Babba farincikin jin Alhaji ya tsayawa Taj bai bashi damar zurfafa tambayoyi ba.
"Kana iya komawa gidan yayan naka. In sha Allahu gobe za a ɗaura."
Godiya mara adadi Taj ya yi masa.
"Ba sai ka faɗawa matana na ba domin ko Abu ba za ta baka goyon baya ba. Zan yi musu magana da kaina."
Duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shigo shigo ba zurfi Alhaji yake masa, sanin cewa baya magana biyu yasa bai ji ko ɗar ba. Ya tabbata za ayi auren in sha Allah.
***
Gidan Abba Habibu tamkar ba shi bane jiya da yamma ake ta hayaniyar shirin zuwa sisters' eve. Yau shiru kamar babu mutane. Gashi dai ba a yi shelar me ya faru ba. Amma ganin ƴan biki babu walwala sai kowa ya sha jinin jikinsa.
Banda ƴan mazan gidan Alhaji babu wanda ya san da maganar ɗaurin auren sai ƴan uwansa maza. Su duka mamaki bai hanasu haɗuwa a masallacin juma'ar da za ayi auren bayan an idar da sallah ba. Kamal ne ya bawa Taj sababbin kayansa masu babbar riga. Ya tuƙosu a mota zuwa masallacin. Sai dai jikinsa tamkar anyi masa duka. Gani yake akwai abin da zai biyo bayan wannan ɗanyan kai na Taj. Alhaji ba zai barshi ya sha ba.
Ana idar da sallah Liman ya yi sanarwar ɗaurin aure kamar yadda aka faɗa masa. An fara da Abubakar Maje Garba (Baballe) da Zeenatu Habib Umar akan sadaki naira dubu hamsin. Masallaci ya đauki kabbara.
Abba yana share ƴar ƙwallar farinciki sai yaji an taɓo shi. Yana juyawa damansa ya yi tozali da Alh. Hayatu. Ba ƙaramin ruɗewa ya yi ba kuwa.
"Kwantar da hankalinka. Sunan yarinyar wajenka da Taj yake so za ka bani. Ina fata ka yi masa izinin aurenta."
Abba baki ba rawa ya ce "Yaya Hayatu..."
"Kada ka damu. Nima short nktice da ya bamu ne ya hanani zuwa mu yi maganar. Ya sunanta."
"Hamdiyya."
Alhaji ya juya fuskarsa ba yabo ba fallasa ya faɗawa Yaya Babba. Shi kuma ya sanar da Liman. Nan aka sake sanarwa. An ɗaura auren Tajuddin Hayatu Sulaiman da Hamdiyya Habib Umar akan sadaki dubu ɗari biyu.
A karo na uku sai ga wani tsoho an gunguro shi akan wheelchair. Ba kowa ne ya turo shi ba kuwa illa Safwan. A gaban Abba ya tsayar da kujerar. Ya ɗuka a kunyace. Tsohon ya dubi Abba da murmushi a fuskarsa.
"Ni ne mahaifin Sabi'u. Kuma ni zan yiwa jikana waliyyi. Ina fata za ka haƙura da abin da ya faru jiya wanda bani da masaniya. Sai ɗazu yake cewa wai an fasa. Shi ne na kira Safwan ɗin ya yi min bayani."
Baba Maje ne akan gaba wurin cewa sun amince. Nan take Liman ya ɗaura aure na uku. Safwan Sabi'u Mamman da Sajida Habib Umar.
Allahu Akbar
Abba sakaya fuska ya yi cikin babbar riga yana kukan farinciki.
RAYUWA DA GIƁI 17
Batul Mamman💖
***
"Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshiia ƙasa a miƙa godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ƴan matanki a sa'a guda. Wannan farar juma'a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ƴan dugwi dugwi iyalan Baba."
Ba kowa bane da wannan aiki sai Ƴar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka amshe guɗar su na yi. Yaya fitowa tayi daga ɗakinta inda ta fake da shiryawa ta zauna rarrashin Sajida da Zee. Hamdi na gefe ita ma tana basu baki tare da taya su kuka.
Anti Zinatu ce kaɗai ta san zaman me su ke a ɗakin. Ita ce ma ta tura musu Yayan domin wani ciwon uwa kaɗai ke iya maganinsa.
Hamdi na jin muryarsa ta haɗe rai bayan fitar Yaya daga ɗakin.
"Wai namiji kenan. Mtsewww."
Lulluɓi Yaya tayi ta fita soron. Ƴar Ficika ya wangale baki.
"Sai muka ji abin arziƙi ko Jinjin? Allah Yasa abokan zamansu ne."
Ita ma takaicin ɗaga muryar tasa take yi. Ga zaƙin murya gashi bai iya tausasa harshe. Ta tabbata kowa na jinsu a ciki.
"Da ka ɗan rage maganar saboda ƴan biki ba su san auren Zee aka ɗaura ba maimakon Sajida. Sannan kana cewa amare uku sai ayi zaton..."
"Ba zato bane Jinjin. Ƴaƴan Simagade sun zama farinwata sha kallo. An so tozarta shi sai gashi Allah Ya aurar dasu lokaci ɗaya."
Yaya dai bata fahimci inda ya dosa ba. Gani take wani zancen yake haɗawa da wani. Sai kawai ta koma ciki. Aka yi ta tambayarta me yake nufi kuwa don duk sun ji.
"Shirmen Ƴar Ficika ne. Shi da ko wurin ɗaurin auren basu je ba?"
Rufe bakinta ke da wuya Halifa ya shigo gidan kamar an jeho shi daga sama. Haki yake da ƙarfinsa saboda gudun da ya sha ba na wasa bane. Tun daga masallacin juma'ar unguwarsu har gida. Tafiyar kimanin minti talatin. Ƙafafunsa sun yi buɗu buɗu.
"Yaya! Yaya!!" Ya dinga ƙwala kira kamar makaho na neman ɗan jagoransa.
"Kai Halifa lafiyarka kuwa?" Wata maƙociyarsu ta tambaye shi.
"Ina Yaya?" Ya faɗi yana dariya.
Banda Yaya, duk matan da su ke gidan fitowa su ka yi. Yana ganinta ya taho da sauri, sai kuma ya tsallaketa ya rungume Sajida.
"Wai mene ne Halifa? Ka sanya mu a duhu" cewar Inna Luba.
Murmushi ya yi yana duban ƴan uwansa.
"Yaya an ɗaura. Duka su ukun an ɗaura musu aure."
Dafa shi Inna Luba tayi zuciyarta na bugawa.
"Nutsu ka yi min bayani. Su waye su ka yi auren?"
"Ya Sajida da Yaya Safwan."
Sajida ta bar jikin bangon da ta jingina tayi da sauri, ta rufe bakinta da hannu. Wasu zafafan hawaye suna sauko mata. Hamdi ta rungumeta tana cewa "Alhamdulillah."
Anti Zinatu ta ce "Mata biyu aka aura masa kenan? Naji ka ci mutum uku."
Ya murmusa da farincikinsa "a'a, sai Ya Hamdi da Happy."
Inna Luba ta ware idanu a tsorace "Hafi? Mutum ne?"
Yadda yake murna kai ka ce shi ne angon mata uku. Gyarawa ya yi yadda za ta gane da kyau.
"Ya Taj. Shugaban inda Abba yake aiki yanzu."
Cikin Hamdi wata irin ƙullewa ya yi. Taji ya saki lokaci guda yana neman tsinkata a gaban mutane. Duk da haka danne shi tayi da hannu biyu.
"Kai ka san bana son wasa irin wannan. Wace Hamdin kake nufi?"
"Wallahi ke ce Ya Hamdi. Babansa kawai muka gani ya cewa Abba yana nemawa ɗansa aurenki. Sadakinki fa dubu ɗari biyu. Cash in faɗa miki."
Daga inda ya yi rantsuwar ita Hamdin ta daina jin komai sai bugun zuciyarta. Wannan wane irin mugun wasa ne Halifa yake yi mata haka? Aure? Ita ce tayi aure kamar wata kayan wasa? Kuma wai da Taj. Waye ma Taj? Kamar ta san sunan.
Sama-sama taji muryar da ko gane mai ita ba yi ba tana cewa "Ku riƙeta...Sajida kama hannun. A'a rungumota kawai kada ta kai ƙasa."
Luuu haka taji ƙafafunta suna narkewa su kaɗai za su kaita ƙasa. Kafin