Showing 69001 words to 72000 words out of 182238 words

Chapter 24 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt

mahaifin amaryar ɗan daudu ne."

A take fuskarsa ta canja da furucin Hajja. Ta kalli Amma da mamakinta ya fi na Anti.

"Kada ku ce min baku san ɗan daudu bane baban nata?"

Amma ta kalli Taj tana neman ƙarin bayani a tsorace.

Ɓoye ɓoye dama can ba halinsa bane. Balle kuma yanzu da ya riga ya yi aure. In ya rufe yau anjima ko gobe magana za ta fito. Saboda haka a taƙaice ya labarta musu yana aiki da Abba da kuma abin da ya faru lokacin auren Sajida har zuwa jiyan.

"A taƙaice dai ba auren soyayya bane. Yarinya mai asali girɓatacce irin wannan dama sai dai auren alfarma." Cewar Anti.

Hajja kuwa cewa tayi "kakarta ce kawai ta yanke saƙa. Wannan kishi da ita ma ɓata lokaci ne Anisa. Kawai ki sa a ranki ke kaɗai ce."

"A'a fa Hajja" Taj ya katse musu hanzari kafin a kai matakin da zai faɗi baƙa.

"A'a me?"

"Ina sonta."

"Taj" Amma ta kira shi don ta san hali.

"Am serious Amma. Ina roƙonku don Allah kada a sake tada zancen mahaifinta ko yanayin auren. Nema nayi ba bani aka yi ba. Please" ya kallesu ɗaya bayan ɗaya.

For once sai jikin Hajja ya yi sanyi. Magiya Taj yake amma irin wadda mai yinta yake fata da tsananin burin samun biyan buƙata.

Tashi Hajja tayi ba tare da tayi magana ba. Ta dai ƙarewa Taj kallo sai taji babu adalci idan ta cigaba da sanya shi a kwana.

"Ina ɗan uwanka Kamalu"

Taj ya dubeta girarsa a cure "yana gida."

"Idan ka koma ka ce ina nemansa. Shi sai ya zo su daidaita da Anisa idan bashi da wata."

"Hajja!!!"

Anisa, Taj da Anti su ka kirata lokaci guda. Ta taɓe baki.

"Ku bar Hayatu da halinsa. Ban taɓa ganin wanda Allah Ya azurta da iyali masu kyakkyawar mu'amala da ɗabi'a kamar nasa ba. Shi yasa nake kwaɗayin haɗa zuri'a dashi ba wani abu ba."

Bata jira jin me za su ce ba ta fita. Anti ma fita tayi da niyyar yiwa Daddy magana. Bata maraba da tumbling ɗin ƴarta da Hajja take yi. Ita ma Anisa bayansu ta bi. Sai dai kafin ta fita ta tsaya tayi masa magana.

"Allah Ya sanya alkhairi Ya Taj."

"Nagode Anisa. Kuma don Allah kada ya zama reason na lalacewar zumuncinmu."

"Tun farko dama kayi min bayani. Babu wani abu. Sai mun zo ganin amarya."

Da ya rage su biyu a falon Taj ya kalli Amma "that went well right?"

"I think so." Ta bashi amsa da fatan hakan ne.

Breakfast ta kawo musu. Bayan sun gama ya faɗa mata komai ds komai da ya danganci Abba da aurensa.

"Yaron nan da a ɗan daba ka tashi sai an wahala da kai. Banda rigima ka rasa ƴar wanda za ka auro sai Simagade? Kai yanzu ka yarda Yaya Hayatu ba zai kawo matsala a gaba ba?"

"Da Allah na dogara Amma. Bana son yin wannan tunanin saboda ban hango abin da zai rabani da Hamdi ba."

"Sunanta ya min daɗi fa. Hamdiyya. Ɗazu da ka faɗa har zan magana na kama bakina kafin Hajja ta zageni."

Cikin farincikin shiryawa da Amma ya bar gidan da yamma. Ta so ya kwana amma ya dage gara yaje hotel. Zaman nasa a ganinsa tamkar rashin kunya ne. Zai kyautu ya bawa mutanen gidan damar sake karɓarsa idan ciwon abin da su ke tunanin laifi ne ya ragu.

***

A yau sha'anin biki ya ƙare. Kakan Safwan ya wakilta masu ɗauko amarya Sajida zuwa gidansa. Dama Umman Safwan ɗin bata da damuwa ko kaɗan. Babansa ne baya so. Bayan koke koken amarya da ƴan uwanta da kuma Yaya, gidan kakannin Safwan aka wuce da ita.

Tsohon nan ya yi musu nasiha sosai da jan kunne.

"Sai kun ji kon ƙi ji. Ku gani kuma ku ƙi gani sannan auren zai yi ƙarko. Musamman gareki jikata" Sajida ta kalle shi da jan ido "duk wanda ya sami dama a dangin nan zai faɗa miki magana son rai akan asalinki. Wannan ko ka hana wani sai ya yi. Saboda haka ki koyi kawar da kai. Inda ba za ki iya ba kuma ki kare martabar mahaifinki. Ina mai tabbatar miki da an kwana biyu zai bi jiki. Kowa zai haƙura matuƙar kun zauna lafiya. Kun bawa maraɗa kunya."

Safwan ne kaɗai ya iya yi masa godiya. Sajida kuwa in banda sharar hawaye babu abin da take yi.

*

Ana can ana ƙarasa guntattakin gyara a gidan amarya Zee ta fice daga ɗakin da Hamdi take yiwa turaren wuta ta koma wajen gate ta kira Taj. Yamma ce liƙis. Tana ta addu'ar samunsa a wayar. Tayi sa'a kuwa bugun farko ya ɗauka. Sai kuma ya kashe ya kirata.

"Zee amarya."

Sake tsokanarta ya yi "to uwargida. Tun yanzu har an fara kishi kenan."

"Don Allah ka bari"

Yanayin muryarta ba yadda ya saba ji bane. Shi yasa bai ja wasan ba ya nemi ta sanar dashi dalilin kiran. Muryarta rawa ta fara, sai kuma ta kama kuka. A haka ta faɗa masa maganganun da taji Abba yana faɗawa Hamdi jiya ba tare da sun san ta biyo su ba.

Ashe tun shigowar Hamdi cikin gidan ta taso za ta tsokaneta akan me taje yi a waje sai taga Abba ya ja ta zuwa soro. Fuskarsa da ta gani da damuwa ita tayi sanadin binsu da tayi. Tana gama jin abin da ya ce tayi saurin komawa ciki.

Jijiyar kansa tashi tayi sosai. Ɓacin rai ya rufar masa. Ya rasa dalilin da yasa Alhaji yake yi masa haka.

"Ya Taj don Allah ka saketa ba sai tayi maka abin da zai ɓatawa Abbs suna ba."

"Yi shiru Zee. Maganar nan da wa kika yi bayan ni?"

"Babu kowa." Ta ja hanci.

"To don Allah ki yi min alƙawarin riƙeta a ranki kin ji."

"Sakin fa?"

"Hamdi ta zo kenan. Idan ku ka yi wasa ma duk sai ta riga ku haihuwa."

Wayar ta cire daga kunnenta saboda kunyar kalamansa. Kamar ya sani ya ce

"Oh sorry, ƙanwa ce fa ke."

"Idan tayi maka laifin da zai sa ka saketa fa?"

"Kada ki damu. Just focus on yourself. Ki gama karatunki ki kuma riƙe mutumcin aurenki. Ni da Hamdi in sha Allah anyi auren kenan."

"Tsoro nake ji kada babanka ya yiwa Abba wani abu."

"In sha Allah babu abin da zai faru. Ina son sister ɗinki. Zan kuma tsare mutumcinta da na duka family ɗinku."

Ya ɗauki lokaci sosai wajen kwantar mata da hankali. Sannan ya yi mata godiya da ta tunkare shi da zancen. Wayar Kamal ya nema da su ka gama don ya faɗa masa yaji a kashe. Ya yi ɗan tsaki. Tun asuba fa Kamal ba yadda ya saba yake ba. Komai daina yi masa daɗi yake saboda yana jin tamkar wani ɓangare na jikinsa baya tare dashi.
Jirgin tara na safe ya yi booking ta waya kafin ya kwanta.

***

Hannuwa da ƙafafunsa ya kalla hankalinsa ya sake tashi. A kumbure suke. Fuskarsa kuwa kamar an hura balloon. Magungunan jiya ya ɗauko yayi ta dubawa ko akwai wanda ya sha ba daidai ba amma babu. Gabansa ya dinga faɗuwa da tunanin me zai faru idan yanayinsa ya cigaba a haka. Babbar matsalarsa ma ita ce yadda zai samu ya bar gidan ba tare da kowa ya gan shi ba. Daga daren jiya zuwa yanzu ya fita hayyacinsa baki ɗaya. Wayarsa ya nema ya kunna domin magana da likitarsa sai yaji ana taɓa ƙofar ɗakinsa.

Hankalinsa ya sake tashi da ya kalli kansa a madubi.

"Waye?" Ya furta da ɗan ƙarfi.

Shiru yaji babu amsa. Sai zura muƙullai da ake tayi a ƙofar. A gwaji na biyar aka buɗe ƙofar ɗakin wanda bai taɓa zaton akwai spare key ba. Idanunsa da ƙyar su ke buɗuwa saboda hasken fitilun waje da su ka shigo.

"Abba? Bishir?"

Fitilar ɗakinsa aka kunna gami da rufe ƙofar ɗakin nasa.

"Kamal? Shaye shaye kake yi?"

A gigice ya ɗago idanunsa da suke buɗewa da ƙyar saboda kumburi ya kalli wadda ke tsaye a kansa.

"Umma?"=
RAYUWA DA GIƁI 20


Batul Mamman💖




_Gaisuwa ta musamman ga baiwar Allah da ta tura saƙo OpenDiaries. Ina fata kin sami sauƙi. Allah Ya inganta Ya raba lafiya. Abba Habibu Simagade yace a baki haƙuri ba niyyarsa kenan ba. Shafin yau naki ne._


Ina ƙara tunatar da masu karatu posts weekdays ne kawai don Allah. Nagode sosai. SonSo


***

Na ɗan taƙin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta so ƙullewa har ma ya faɗi abin da bai yi niyya ba. Cikin sa'a sai ya tuno abin da ya tanadi faɗawa duk wanda ya ganshi a wannan yanayin. Murmushi ya yi mata sannan ya ɗaga hannuwa da ƙafafunsa yadda za ta gansu sosai.

"Mene ne wannan Kamal? Me ya same ka kake irin wannan kumburin?" Ta ƙarasa inda yake tana tattaɓa shi.

"Allergy ne Umma. A haka ma kumburin ya sauka sosai."

"Subhanallahi" ta matsa hannunsa na dama "akwai zafi?"

Kai ya girgiza mata. Ya zauna ya shirga mata bayanin ƙanzon kurege wai allergy gare shi kuma har yanzu likitan bai gano mene ne jikin nasa baya so ba.

"Anya ya san aikinsa kuwa? Me yasa baka je wurin yayarka ba?"

Gaban Kamal ya faɗi da tsoron kada Umma ta matsa masa akan zuwa wajen Yaya Kubra. Ita ce babba wajen Mama kuma sananniyar likitar ɓangaren lalurorin mata. Yana zuwa wajenta asirinsa zai tono.

"Ita da take gynae? Wannan ba ɓangarenta bane."

"Amma ai ba za ta kasa sanin likitan da ya dace da kai ba a asibitin Malam (AKTHA) ko? Ni dai bari nayi mata waya. Wannan kumburin ya bani tsoro. Har wani baƙi naga kayi."

"Kai Umma, idonki ne." Ya wayance.

Da ƙyar ya hanata kiran yayar tasu. Ya tabbatar mata likitan da yake gani ma ƙwararre ne. Harkar allergy wani zubin sai an wahala kafin a gano mene ne jiki baya so har yake reacting irin haka. Baiwar Allah sai ta yarda da zancen nasa. Ta kira masa Abba ta ce ya zo ya kai shi asibiti.

"Amma me ya sa ka ɓoye mana? Jiya ina kallonka kafin ku fita wajen sirikin Taj da Innarku ka shige kitchen ka watsa magani. Kuma yau kowa ya ce bai sanyaka a ido ba. Shi ne tsoro ya kamani. Ko ƙwaya ka fara sha."

Halin ciwon da yake ciki bai hana shi dariya ba.

"Abin da ban yi da ƙuruciya ba Umma?"

"Yo Allah na tuba shaye shaye lokaci gare shi? Kai dai kawai Allah Ya kare ku da sauran zuri'ar musulmi. Zamanin ya zo da hanyoyin ɓata tatbiyar tsofaffi balle kuma matasa masu jini a jika."

Tunaninsa na yadda zai je wajen likitarsa cikin sauƙi ya sami solution. Umma ta sa Abba ya kai shi asibitin. A hanya kafin ya ƙarasa ya tura mata saƙo ta bashi amsa. Roƙonta ya yi da sirranta lalurarsa a gaban Abba.

Da taimakon Abba ya iya shiga asibitin. Dauriya da ƙarfinsa sun soma ƙarewa. Wata Nos tana ganinsu ta hanzarta kiran likitar wadda dalilinsa ma ta fito don yau ranar hutunta ce.

Wata kyakkyawar matashiya ce ta fito sanye da baƙar abaya da ƙaramin hijab. A fuskarta gilashi ne mai ɗan kauri dake taimakawa ganinta. Madaidaicin tsayi gareta amma kuma she is a bit chubby. Sai dai ƙibar ba mai yawa bace. Ɗakin taimakon gaggawa tasa aka shigar mata da Kamal aka kwantar akan gado.

Abba ya gama tsorata da yanayinsa. Yana ganin ta farke sirinji cikin sauri ya ce "Doctor kinga jikin nasa duk ya rikice kafin mu ƙaraso. Don Allah ki gane mene ne ba ya so sai mu kiyaye."

"Ɗan bamu wuri" ta ce idanunta akan Kamal. Patient ɗinta mai ɗan banzan taurin kai.

Hankali a tashe Abba ya fita. Ya shiga fareti a wajen yana addu'ar a shawo kan matsalar da wuri.

Yana fita Mubina ta rufe ƙofar emergency ɗin ta shiga bawa Kamal taimakon da ya kamata. Kimanin minti talatin kafin jikin nasa ya fara daidaita. Ya buɗe ido a hankali ya sauka cikin nata.

Ranta a ɓace yake sosai. Kallon da tayi masa ya sanya shi murmushi. Ya đaga hannunsa guda ba wanda take yi masa ƙarin ruwa ba ya kama kunnensa.

"Sorry."

"Ya kake so nayi da kai? Ni a rayuwata babu abin da na tsana kamar ɓoye ɓoye."

Ya ɗage gira ɗaya "a taƙaice dai kin tsaneni."

Shan kunu tayi "ban ce ba."

"Don Allah ki yi haƙuri." Ya tashi zaune "Zan iya tafiya?"

"Jikin naka..."

Sallama aka yi, kafin ta amsa Alhaji ya turo ƙofar ta buɗe gabaɗaya su ka shigo tare da Abba. Kai idan kaga fuskar shi sai ya baka tsoro. Hannuwan babbar rigarsa sun sauko amma yau ya manta da wani matsayi. Ɗansa kawai yake son gani.

"Me ya same ka?" Ya kalli Dr. Mubina "Doctor me ya same shi?"

Kamal bai bari tayi magana ba don ya kula ganin Alhaji ya kiɗima ta.

"Allergy ne Alhaji."

"Kai ne likitan?" Ya sake dubanta idanunsa na daɗa firgita ta "ina jin ki."

"Allergy ne kamar yadda ya ce."

"To an gano mene ne jikin nasa baya so domin a kiyaye?"

"A'a, muna dai kan..."

Kafaɗarsa Alhaji ya riƙe "Kai tashi. Visar ina da ina gareka yanzu da ba su ƙare ba?"

Mubina taga yadda bakinsa ya kasa tattaro amsa saboda sanin kafiyar Alhajin.

"Don Allah ka ɗan ƙara mana lokaci Alhaji. Lifestyle changes muke ta gwadawa. In sha Allah a hankali zamu gane trigger ɗin."

"A hankali fa ki ka ce doctor. Jira zan yi har sai wani mummunan abu ya same shi?"

"Kayi haƙuri. Rashin bamu dama yana daga cikin abubuwan da ke sa a dinga ganin kamar bamu san aikinmu ba."

Yadda ta tare shi kai tsaye ta bashi wannan amsa sai ya sanya shi murmushi. Yana son mutane masu confidence.

"Ya sunanki ne?"

"Mubina...Mubina Sa'id Kibiya."

Fuskar Alhaji washewa tayi. Shi ne harda dariya irin tasu ta manya.

"Ikon Allah. Ke ƴar wajen Marigayi Dr. Sa'id ce?" Ta gyaɗa kai a hankali "kai masha Allah. Ƙasar nan ba ƙaramin rashi tayi ba. Arewa tayi rashin jajirtaccen likita. Allah Ya masa rahama."

Idanun Mubina da ƴar ƙwalla ta ce "amin."

Sakin jiki Alhaji ya yi su ka gama magana ya ce ya bata damar yiwa Kamal dukkan abin da ya dace domin samun sauƙinsa. Ya ƙara da cewa baya so ta sallame shi a yau. A kumbure gaɓoɓinsa su ke duk da a haka Abba ya ce wai ya saɓe. Fita su ka yi da Abban zai raka shi. Kamal kuma Mubina ta ce lallai ya koma ya kwanta.

"Ai dole na. Idan na koma gida yau ba za mu ƙare da daɗi ba."

"Gaskiya yana son ka." Ta faɗi tana murmushin yadda uban ya nuna kulawarsa akansa.

"Ai baki ga komai ba. Sai ƴarsa na labour room ake gane waye Alhaji. Wallahi in dai ba baya gari ba da shi ake zaman asibiti daga lokacin da yaji an tafi haihuwar har a fito da baby."

"Kun ji daɗi. Shi ne kake ɓoye masa halin da kake ciki?"

"Duk tsaurinsa yana da mugun rauni akan ƴaƴa. Sanin matsalata alhalin babu abin da zai iya yi min damunsa kawai zai yi."

Haƙura Mubina tayi. Ta kula da indai izinin Kamal take jira babu wani cigaba da za a samu wajen binciken sama masa waraka. Zaɓi guda ya rage mata. Za kuma tayi amfani dashi in sha Allahu.

Bata tashi ƙara sanin wane irin gida ya fito ba sai da taga matan gidansu da ƴan uwansa suna ta tururuwar shigowa. Ɗakin ba ma zai ɗauki rabinsu ba domin kuwa harda jikoki. Wannan yasa ta tunani akan hanyarta ta gida. Yanzu a ce duk yawan nan nasu babu wanda jininsa da na Kamal ya zo daidai?

***

Taj bai tashi sanin a asibiti Kamal ya kwana ba sai da safe. Da fari ya yi niyyar komawa gidan Amma domin su gaisa da Daddy. Sai ga wayar Naja tana sanar dashi labarin da ta samu daga gida. Ya duba wayarsa babu wanda ya kira shi. Jinjina kai ya yi ya ɗauki jakarsa ya fita. Allah Ya taimake shi bai haɗu da ɓacin rana ba. Jirgin ya tashi akan lokaci. Kai tsaye asibitin ya wuce daga airport. Ya samu ana ta rikici a bakin ƙofa tsakanin wata nos da ƴan uwansu mata. Ta tare ƙofar ta hana mutum biyar shiga. Na ciki su bakwai su ma tayi tayi sun ƙi fitowa. Ana ƙorafin sun yi yawa a ɗakin, su kuma sun ce babu wanda ya isa yasa su fita daga wajen ɗan uwansu.

"Ga wani ma nan ya shigo. Shi daga wani garin ma yake." Autar gidan ta faɗi a tsiwace.

"To ko ma dai waye zuwa za ku yi ku fita. Idan ba haka ba zan sanar da na gaba dani. Doka ce ba a son a wuce mutum uku a ɗakin mara lafiya." Nos ɗin ta ce da takaicin waɗannan mutane. Bakiɗayansu kamar masu kan dutse. An rasa mai lallaɓata ta haƙura ko kuma yasa baki su fita.

Wata ma cewa tayi "ku sallame shi mana. Muma yayarmu likita ce. Allah na tuba don dai ƙarin ruwa da allura wanne ne ba za ta iya ba?"

Ran Nos ɗinnan ya ɓaci matuƙa. Idan an zo ita za a yiwa faɗan barinsu a ɗakin. Da taga Taj ne ma ta ɗan saki rai. Ta san dai duk yadda za ayi namiji daban yake da mata.

"Kai ma ɗan gidansu ne?"

Caraf wata mai tsohon ciki ta ce "Baki ga kama da mara lafiyan ba?"

"Don Allah ka faɗa musu su ragu. A bakin aikina nake. In kowa bai min magana ba wallahi likitarsa sai tayi. Ta ce baya buƙatar hayaniya."

"Ya Taj barni da ita. So take ta nuna mana ta fi mu son ɗan uwanmu. Ba fa surutu zamu yi ba."

Kamal ba jin an ambaci Taj ya yi hamdala. Shi ma sun ƙi sauraronsa. Kansa har ya fara ciwo. A tunaninsu allergy ɗin ne shi yasa su ka dage. Basu san halin da yake ciki magana ma dauriya kawai yake yi ba.

"Happy. Don Allah kasa su bi dokar asibitin. Ni kaina doctor ɗin ba za ta barni ba idan ta gansu."

Nos dai tana jin sunan da aka kira Taj daga waje da wanda mara lafiyan nan ya kira shi, bata san lokacin da ta ce "Happy Taj? Kai ne mai HappyTaj don Allah?"

Ƴan bani na iyan gidan Alh. Hayatu ne su ka amsa mata. Harda mai cewa da ta ɗauka su ɗin local mutane ne take son wulaƙanta su.

"A bakin aikina nake." Ta nanata musu.

Da laluma da rarrashi Taj ya samu su ka bi tsarin asibitin. Da mutum bibbiyu aka dinga shiga ana fita. Nos ɗin tayi masa godiya bayan kowa ya tafi ta barshi ya shiga shi kaɗai. Abin mamaki yana zama ya kira sunan Kamal sai yaji shiru. Ɗaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login