Showing 24001 words to 27000 words out of 182238 words

Chapter 9 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt

da hawaye ta ce "Baba ka yafe min."

"Ba dole na ba? Idan nayi miki baki rayuwarki ai sai tafi haka lalacewa. Ki tashi ki haɗo kayanki don kin gama karatu kenan."

"Alhaji ba ayi haka ba." Principal ta sa baki "ka bari mu ɗauki matakin da ya dace."

"Maje kada ka ɗauki hukunci cikin fushi."

"Kun san Allah ɗaya ne ko? To wallahi yarinyar nan ta gama karatu a ƙarƙashin ikona."

Ya kalli Uncle B ya yi wani irin murmushi mai ciwo sannan ya ɗaga waya ya kira ɗan yayarsa police. Makarantar ya kwatanta masa.

"Ku taho yanzu don Allah."

"Yallaɓai da ka bari an kira masa ƴan sandan dake kusa da nan. Ka san kowanne laifi ana shigar dashi a unguwar da ya faru."

"A kira su. Shi wannan ɗana ne saboda haka ina jiran zuwansa saboda ina son komai ya tafi da jagorancin wani nawa."

Suna wannan zance Uncle B ya matsa gefe yana ta bige bigen waya da hargagin iska. Bayan ya gama ya cigaba da masifa yana doka teburin Principal.

"Baki san ko ni waye ba a garin nan wallahi. Ina da damar sanyawa a rufe makarantar nan baki ɗaya a yau idan na so."

"Ka daɗe baka aiwatar ba. Mutumin banza. Girma da matsayinka basu ƙara maka komai ba sai sanya hannu wajen ɓata tarbiyar yaran mutane."

A cikin minti talatin motar ƴan sandan da VP ya kira ta iso makarantar aka yi awon gaba da Uncle B. Baba Maje da Ummi da VP ɗin su ka tafi tare dasu. Principal ta sanar da malamanta wajibcin neman iyayen yara a kurkusa domin tattaunawa da gujewa maimaicin abin da ya faru.

Hamdi da Abbanta su ka fito tare fuskokinsu babu walwala sosai. Shi yana cikin damuwar halin da abokinsa ya sami iyalinsa, ita kuma tana cike da kunyar ya san irin matsayin da ta ajiye shi a matsayinsa na uba. Hannunsa ta riƙe ganin yana raɓewa gefe guda.

"Abba in kai ka ka ga ajujuwanmu?"

"A'a Hamdi." Ya zame hannunsa.

"Ba ka yafe min ba ko?" Idanunta su ka kawo ruwa.

"Ban taɓa fushi dake ba. Ba dai na son sake bar miki abin faɗi a cikin abokan karatunki." Ya ce a sanyaye.

Wannan furuci nasa ya sanyata kuka sosai. Ta roƙe shi da ya jirata a nan inda yake za ta dawo bayan ya hanata kukan. Tana tafiya ta samu ɗalibai na dinning hall ana cin abincin rana. Duk da yadda take wasiwasi amma da ta tuno da maganar da Principal tayi mata sai taji zuciyarta ta daina tsoron komai.

"SS3 A" ta ƙwala kira da ƙarfi.

Tashi su ka yi wasu kuma su ka amsa da baki.

"Ku zo ku gaisa da Abbana."

Ai kusan rabin hall ɗin ne su ka fita a guje. Aka kasa controlling ɗin su. Tana gaba har inda ta barshi tsaye. Kawar da kai taga ya yi tayi murmushi ta zaga gabansa.

"Abba an zo gaishe ka."

Tunda yake kullum yaransa su ka zo gida da ƙawa basa taɓa cewa a gaisa da shi. Ƙawayen ma bai san kowa ba sai na dangi ƴaƴan ƴan uwa.

Ya juya suna ta ina wuni shi kuwa ya kasa amsawa saboda kada jin muryarsa yasa a yiwa ƴarsa dariya.

"Abba ka amsa mana" Hamdi ta ce tana dariya kamar ba ita ba. Yarinyar da kullum take cikin ƙunci da damuwa.

Ya buɗe baki ya dinga amsa musu. Ƴan matan nan maimakon nuna ƙyama sai yake ganin kamar ya burgesu. Wasu basu taɓa ganin ɗan daudu a kusa haka ba. Kamar wani abin sha'awa su ka dinga girmama shi. Kan Hamdi ya kumbura suntum saboda daɗi. Ranar da taimakon malamai aka ƙora su duka har ita cikin makaranta sannan ya samu ya tafi wajen Baba Maje.

***

Ganin su Inna ya yi saurin ɗaukewa Taj damuwar da ya shiga. Sai gashi ya zage yana ta hira kamar ba shi ba. A cikin hirar ne ya tambaye su ko akwai wani abu a tattare dashi da zai sa ayi masa kallon namijin da bai cika ba.

Ya naɗe hannun rigarsa har saman kafaɗa irin yadda yara su ke yi.

"Saboda son burge Alhaji har gym nake zuwa ina motsa jiki. Yanzu wannan..." ya nuna dantsensa "bai isa a kirani namiji ba?"

Kamal kula ya yi da Salwa da ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci da yadda tayi saurin ɗauke ido daga kallon hannun Taj. Shi kuma gwanin ya kama ƙasan riga zai ɗaga wai ya nuna musu packs ɗin ƙirjinsa. Gudun kada ɗan uwansa ya kunyata shi ne ya kai masa duka a hannun.

"Dalla malam rufe wannan sandar raken."

Taj da yaji zafi ya rama dukan "ɗan baƙinciki in ka isa ka buɗe naka mai kama da taliya."

"Mama kina dai jin abin da yake faɗa min ko?" Kamal ya faɗi yana miƙewa tsaye.

"Laifinka ne fa Kamal. Kai ka fara dukansa" Mama ta goyi bayan Taj.

"Saboda ya dawo daga America za ki nuna min wariya? Ke fa ki ka hana raini tsakaninmu."

Su Hajiya sai dariya su ke yi. Taj ya sami goyon baya ya cigaba da tsokanarsa.

"Ka ci sa'a ban auro baturiya ba da kaga asalin wariya. In taho da ƴan ƴaƴana farare su na Mom...Dad...who is this black man" ya nuna Kamal aka sake tuntsirewa da dariya. Ya cigaba da tsokanarsa "Duk ƴan uwa su taru a kansu ana son burgesu. Kai kuwa naka sai dai kaji ana cewa 'Sule maza tafi wurin babarka ta goge maka majina' "

"Banza ƙazami. Wai majina kamar tashin Soron ɗinki. Kuma don wulaƙanci ba ma Sulaiman ba Sule zan haifa?" Kamal ya faɗi yana shure shi da ƙafa.

Taj dariyar da ya san za ta ƙular dashi ya cigaba da yi.

"Sule Kamalu Hayatu Sule. Irin ƴan chubby yaran nan masu ɗan ƙaton ciki ba."

Ba ka jin komai a falon sai dariyar iyalin ta farinciki. Salwa da take ganin duk motsin Taj wani salo ne daban mai tafiya da zuciyarta ce kaɗai ta ƙare da murmushi.

Kamal da Taj su ka gaji da wasansu na dambe da girma bai hanasu yi ba su ka koma cin abinci daga plate ɗaya su na hirar da babu mai ji.
RAYUWA DA GIƁI 9




Batul Mamman💖




***

Irin kukan da Iyaa tayi bayan jin tsiyar da Ummi take shukawa dole ya bawa mutum tausayi. Bayan an kai ruwa rana a station ɗin da su ka je Baba Maje ya gane duk inda yake tunanin Ummi ta wuce nan. Fitina da gagara ta ƴan matanci kam tana bugawa a bayan idonsa. Ya sake yarda ba a shaidar ɗan yau. Ba don da bakinta ta amsa laifukanta ba da ya yi rantsuwar sharri ake yi mata. Ummin da ya sani daban. Wadda ya dawo da ita gida daban.

Abin baƙinciki shaiɗanin tsohon najadun da yafi kowa hure mata kunne Uncle B ashe makanike ne. Matansa biyu da ƴaƴa goma sha uku. Sau ɗaya ake ɗora tukunya a gidansa. Irinsu Ummi ke cinye ɗan abin da yake samu. Ita da yake tunanin raba hanya da ita saboda rashin bashi haɗin kai tuntuni ashe silarta asirinsa zai tono. Sai da ya yi sati guda a ƙulle kafin a yarda a bada belinsa. Shi ma kuma an haɗa masa da muguwar tarar da zai ji jiki wajen biya.

Hantara da kyara su suka marabceta daga dawowarta gida. Ta zama mujiyar da bahaushe yake kira mai baƙin jini. Iyayenta ba su dake ta ba don ciwon abin da tayi ya kai maƙura. Yayanta Baballe ne dai ya kasa zama bayan yaji kukan Iyaa yayi yawa a waya da tana labarta masa. Ya niƙi gari ya taho Kano ya sakar mata ƙarfinsa. Zaneta ya yi ciki da bai babu wanda ya hana shi. Sai ma dare da jikinta ya yi mugun tsami ne Iyaa ta tada ta zaune.

"Sau nawa ki ka zubar da ciki Ummi?"

Duk soyewar zuciyarta da ya hanata kukan dukan da ta sha wannan tambaya sai da tayi sanadin zubar hawayenta. Hannu ta ɗora akan bakinta tana danne kukan.

"Iyaa? Ciki kuma?"

"To Ummi meye abin mamaki a ciki? Samarin da su ke kashe miki kuɗi ƙannen uwa ne ko na uba da za a ce zumunci suke yiwa?"

Hawaye take ita ma ga tsoron kada Ummin ta amsa zargin da su ke yi mata ita da Baba Maje.

"Wallahi Iyaa ban taɓa yarda na bada kaina ba."

"To me ki ke basu ko me su ke samu a madadin kuɗinsu? Don dai bana jin shaiɗancin naki ya yi tsamarin da za ki asircesu su dinga bin umarninki."

Shiru Ummi tayi. Hankalin Iyaa ya sake tashi ta dinga kai mata duka da hannu ta ko ina.

"Ki faɗa min gaskiya kafin zuciyata ta buga."

"Iyakarsu tattaɓani amma bana yarda da..."

Da sauri Iyaa ta tashi don bata son kuma jin ƙarshen zancen.
"Ya isa. Kin yiwa kanki."

Fita tayi ta bar Ummi tana kuka. Kuma duk wannan abu bai zama ishara ya tuna mata yadda ta dinga cin zarafin mutane dole rana irin ta yau ta zo ba. Sunan Hamdi kawai ke yawo a zuciyarta. Ko harararta aka yi laifinta take ƙara gani. Musguna mata da ta dinga yi a makaranta ai bai shafi komai na karatunta ko rayuwarta ba a tunaninta. She was just having fun. Ba ita kaɗai bace senior mai yi wa na ƙasa da ita hawan karkatacciyar kuka, saboda haka bata ga dalilin da zai sa ita kaɗai ce rayuwarta ta kife irin haka ba. Da me ake so ta ji? Sanin waye Uncle B ko fitowar sirrinta? Ko kuwa rabata da makaranta a matakin ƙarshe da iyayenta su ka yi don ta ɗauki bidiyon ɗan daudu?

"Wallahi sai na rama Hamdiyya. Babu wanda ya isa ya saka ni kuka ban saka shi ba."

Da wannan kalaman ta goge hawayenta a fusace ta kwanta tana shure Siyama da ƙafa don ta ɗan matso ɓangarenta cikin bacci.

***

Kwanaki sun ja inda a farko farkon watan August ɗaliban sakandire su ka kammala jarabawar fita. An yi WAEC har ta fito kafin a gama NECO. Da taimakon Allah da kuma dagewar karatu Hamdi ta sami kyakkyawan sakamako.

Kwana biyu bayan kammala jarabawar makaranta ta shirya gagarumin taron sallamar ɗalibai. Iyaye da ɗaliban suna shiryawa wannan rana wasu tun farkon shiga SS3. Ɗinkin ankon wata shuɗiyar atampa su ka yi mai adon fari da yellow. Tun kafin hutu aka fitar amma lokacin Hamdi bata ƙarɓi ƙyallen ba. Saboda ko kusa bata sa ran zuwa. Sai bayan faruwar lamarin nan taji a jikinta ta daina ɗararewa. Allah Ya taimaketa kafin a gama jarabawar lokacin visiting da Sajida da Zee su ka zo mata ta basu.

"Abba fa ya bar sana'arsa Hamdi. Ki haƙura kawai a kawo miki ko cikin kayan sallarki ne." Zee ta faɗi bayan ta gama kallon atampar.

Mangareta Sajida tayi "Yaya bata gargaɗeki akan faɗa mata ba?"

"Gaskiya fa na faɗa mata don kada ta sa rai." Zee ta bata amsa tana ƙunƙuni.

"Ya Sajida me yake faruwa? Ba don saboda ni ya daina ba?" Hamdi ta tambaya hankalinta na tashi.

Bayanin abin da ya faru su ka yi mata. Sannan Sajida ta ce kada ta damu in sha Allahu za a saya a ɗinka kafin ranar.

"Na haƙura." Hamdi ta ce a sanyaye tana tuhumar kanta a matsayin wadda ta kasa godewa mahaifinta a lokacin da yake yi musu.

"Anti Labiba ce ta bani kuɗi da zan taho. Allah zan iya saya miki." Sajidan ta bata amsa tana dariya.

Daga nan su ka koma wata caftar mai daɗi. Sajida tayi saurayi a Abuja daga zuwa taya cousin ɗinsu zaman jego. Mutumin da gaske yake. Yana aiki da rufin asirinsa. Ƴan maza zar su ke da mijin Anti Labiban (ƴa a wurin babbar yayar Abbansu Anti Zinatu).

Ƴan matan uku su ka haɗa kai su na ta murna kamar ma anyi auren an gama.

Zee ce ta dakatar da shewar tasu "Kin dai yi masa bayanin Abba ko?"

Fari Sajida tayi da idanu tana faɗaɗa murmushinta "Kada ku damu. Ya ce sai da su ka yi magana da mijin Anti kafin ma ya yi min magana. Yanzu dai ku sa rai da zuwansa nan da wata guda. Lokacin ma kin dawo gida ko?"

"Su Ya Sajida an fara kashe murya a waya kenan." Hamdi ta tsokaneta.

"Zan ɗauko rahoto kafin ki dawo. Dama bata yi na gani ba don kada na fesawa Yaya."

"Kin fa raina ni Zee. Ni da na raineki."

Dariya Zee da Hamdi su ka yi. Ita Zee SS2 take don tsiransu da Hamdi babu yawa.

***

Aikin gini ya soma kankama son Taj ba ɓata lokaci ya zo yi ba. Shawarar Amma ya karɓa ya yi ginin a iya restaurant da shaguna ƙalilan. Wani Architect ya kwatantawa abin da yake so. Nan da nan aka zana masa plans kala uku. A ciki ya zaɓi ɗaya. Shi da Kamal kullum sai dare su ke komawa gida. Shi ya tafi gidan Ahmad, Kamal kuma ya koma don muddin ya kwana zai gamu da fushin Alhaji.

Tsarin da aka ɗauko ya bada ma'ana sosai. Gini ne da aka yi ɓangare uku manne da juna. Na tsakiyar yafi girma da faɗi kuma shi kaɗai ne aka ɗorawa bene. Na hagu anyi kitchen ƙato da komai domin aikin fulawa. Cake, doughnut, meatpie, samosa, pies da dangoginsu. A wadace yake sai dai babu wurin zama a ci a ciki. Idan mutum baya son fita akwai ƙofa da za ta sada shi da tsakiyar wato ainihin restaurant ɗin. Ɓangaren dama wanda shi dama za a fara tararwa shi kuma kana gani za ka san na masu gashin nama da kifi ne. Ko yanzu da ake matakin gini kaɗai kana gani zai burge ka. A tsakiyar sama gabaɗayansa kujeru da teburan zama ne. Sai wasu ɗakuna biyu domin masu gudanar da taron da zai iya cin mutane hamsin. Meeting, seminar, reunion da sauransu amma banda biki. Ɗakunan ɗaya normal ne ɗaya kuma VIP. A ƙasa ma da wurin cin abincin sai ɓangaren masu haɗa natural juice da za ayi bayan kayi order. Saii kuma makeken kitchen ɗin Taj da ma'aikatansa. Har ila yau a farfajiyar wajen an keɓe wani waje da aka soma tayar da garden. Za a ƙawata wajen da liluka da wajen guje guje da wasan yara. Sai kuma cikon alƙawarin da ya yiwa kansa. Zai gina madaidaicin boutique da gininsa zai kallon restaurant ɗin ya bawa Kamal amma bai faɗa masa ba.

Yau sun bar wurin duba aikin da wuri sakamakon zazzaɓi da ya rufarwa Taj gadan gadan. Kamar wasa ya ce kansa na ciwo, sai gashi kafin su isa gidan Ahmad yana rawar sanyi. Ɗauke hanya Kamal ya yi su na cikin tafiya. Taj ya ɗago kansa da ya yi nauyi da ƙyar ya dubi hanya.

"Sayar dani za ka yi don kaganni haka Happiness?"

Kamal ya yi murmushi "kwantar da hankalinka. Ai an taya kuma naji ba tsada za ka yi ba."

"Ka ci bashi don sai na rama."

"Allah Ya baka haƙuri. Yadda nake jin yunwa idan kayi fushi dani da alama Salwa ba za ta bani abinci ba yau."

Wani irin kallo Taj ya yi masa na neman alaƙar fushinsa da cin abincin Kamal amma ya kasa ganewa.

"Wani abu ne ya haɗaka da ita?"

"No" Kamal ya bashi amsa mischieviously.

"Meaning?"

"A bar zancen sai ka warke."

Taj bai matsa ba. Kansa kuɗa yake kamar zai cire. Asibiti Kamal ya kai shi duk turjiyarsa. Abu ya kai da ƙarin ruwa don likitan ya ce jikinsa babu kuzari. Gashi sakamakon gwaji ya nuna yana da malaria da thypoid duk shi kaɗai. Sun haɗe da rashin hutu sun kayar dashi lokaci guda.

"Amma ba kwana zan yi ba ko?"
Ya tambayi likitan bayan an gama saka masa canula a hannu.

"Ka godewa Allah da ka iya shigowa nan da ƙafafunka. Your temperature is abnormally high."

Da Kamal ya barshi ya rufe ido don ya gaji sosai. Bayan fitar likitan da Alhaji yaji Kamal ɗin yana waya. Ya sanar dashi halin da yake ciki. Ƙaguwa ya yi yaji me Alhajin zai ce don kamar ya ƙwaci wayar a hannun Kamal. Ya dai daure har su ka gama. Shiru bai ji Kamal ya isar da saƙon Allah Ya ƙara sauƙi ba.

Sai da ya bari ya gama waya da su Inna da Ahmad sannan ya tambaye shi.
"Bai ce komai bane?"

"Yana hanya ne da alama ba ya ji na sosai" Ita ce kalmar da Kamal ya ƙirƙiro ya faɗa masa.

"Hmmm"

Kamal ya dawo kusa da shi "Happy kayi haƙuri sannan mu cigaba da addu'a."

Abinka da ƴan dangi. Lokaci ƙanƙani asibitin ya fara cika da ƴan uwansu. Kowa ya zo faɗan rashin hutu yake yi masa.

*

Don son tabbatar da zarginsa, Kamal kiran Salwa ya yi ya faɗa mata bayan ya sanar da Ahmad. Tunda yaji ya ce baya gida shi ne ya kirata. Ai kuwa abin da ya yi tsammani yaji. Rikicewa tayi ba tare da ta sani ba.

"Ya Kamal yana iya magana?"

Ya yi murmushi "eh, ko in bashi ne?"

Da sauri ta ce "a'a" kunya na lulluɓeta da ta fahimci za ta bada kanta. Awa guda bayan sun yi wayar ta kasa sukuni. Jira take Zahra matar Ahmad tayi maganar zuwansu dubiya tunda tayi arba'in yanzu amma taji shiru. Bini-bini ta ɗaga waya ta duba lokaci. Da ta kai matakin da ba za ta iya haƙuri ba sai ta tambayi Zahran.

"Anti Zahra na ce ko sai Hayat ya taso in an kai shi islamiyya za mu wuce asibitin?"

Zahra ta zaro idanu tana laluben wayarta "ba ki da lafiya ne Salwa? Ina yake miki ciwo? Bari na faɗawa Daddy."

"Ƙalau nake Anti. Dama maganar duba Yaya Taj ne."

Zahra tayi murmushi "lahhh kada ki damu. Daddy ya ce zai biyo muje yanzu. Ke kuma ki zauna saboda Hayat."

"In zauna?" Salwa ta ce ba shiri.

"Ina jin babu lallai ya kwana tumda yace min suna ta waya da Kamal. Meeting ne ya hana shi fita da wuri."

Rasa bakin magana tayi ta fita kawai. Zahra ta bita da ido ba tare da kawo komai a ranta ba.

Da Ahmad ya dawo ko shiga gidan bai yi ba ya kira Zahra ya ce ta fito bayan la'asar. Kafin ta gama shirya Aisha Salwa tayi saurin fita wajensa.

"Ya Ahmad kana ganin daga gida ba za su fassara rashin zuwana duba shi ba ace don ba ɗan uwana bane?"

"Ke, gidanmu babu irin wannan kin ji. Bana son Hayat yayi missing islamiyya shi yasa nace ki zauna."

"Naga kamar zamu iya dawowa kafin ya taso."

Wani irin kallo mai tattare da tuhuma ya yi mata.

"To ko mu zauna ke ki je?"

Diriricewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login