Showing 114001 words to 117000 words out of 182238 words
Chapter 39 - RAYUWA DA GIBI Book Complete By Batul Mamman.txt
suna can ɓangaren maza.
Amarya da ango sun sami waje sun zauna sannan ƴan rakiyar su ka koma nasu waje. Aka shiga cikin taro ka'in da na'in.
An fara da addu'a daga bakin babbar baƙuwa Malama Maimuna. Bayan ta gama aka ce ta faɗi kalmomi biyu zuwa uku na shawara ga ango da amarya.
"Tajuddin da Hamdiyya. Abu ɗaya zan faɗa muku. Duk abin da za ku yi ku tuna cewa kowa cikinku mai kiwo ne kuma abin tambaya akan kiwon da Allah Ya bashi. Duk wanda ya tozarta amanar Allah sai Ya tanadi amsar bayarwa."
MC ya karɓi mike ya ce "wannan fa damu duka take. In kin san satar fita kika yi ki ka zo nan babu ruwanmu. Kai kuma mai shirin samun sabuwar budurwa a nan domin ka ci zarafin ta gida ta hanyar kwaye mata baya kana tona mata asiri to kai ma dai ahir ɗinka."
Dariya aka yi sannan ya ce ina Hajiya Amina aminiyar Inna. Tasowa tayi ita ma ya buƙaci kalmar shawararta.
"Kada ku yarda soyayya ta sanyaku saɓawa Mahalicci. A komai na rayuwa ba a yiwa umarnin da ya saɓawa Allah biyayya ga kowa."
Godiya aka yi musu sannan MC ya ɗora. Agendarsu ta gaba ita ce gasar da aka shiryawa team ɗin ango da amarya. Tambayoyi ne da za su amsa game da juna. Aka sanya kujeru biyu suna kallon juna su ka zauna. A team ɗin ango akwai Sajida, Zee da Halifa.
Team ɗin amarya kuma Yaya Hajiyayye da ta ce ta fi kowa sanin duka ƙannenta, Kamal da Ihsan ɗin Amma.
"Ba zan tambayeku birthday ɗin juna ba."
Ya raba musu takardu guda goma. Kowa a takardarsa zai rubuta amsa da taimakon team members ɗinsa. Wanda ya yi na ɗaya zai sa wanda ya faɗi yin duk abin da yake so.
Ƴan biki aka kasa zaune aka kasa tsaye da ganin wannan sabon salon. Kowa ya zata rawa za a sha yadda aka saba ana liƙi a gaban DJ.
MC ya ce "a rubuta min cikakken kwanan watan ranar da ku ka fara haɗuwa a cikin sakan talatin."
(12/08/2021)
Kusan tare su ka ɗaga takardunsu kafin lokaci ya cika.
Kemara ta ɗauka aka haska a manya manyan talabijin dake manne a jikin bangon hall ɗin ta kowacce kusurwa.
Daga nan ya dinga yi musu tambayoyi akan juna. Kamal, Yaya Hajiyayye da Ihsan da ta rayu da Taj kafin tayi aure a US sun taimakawa Hamdi sosai. Kazalika su Sajida. Aka gama tambayoyi suna kunnen doki.
"Dole a sami na ɗaya da na biyu fa. Team members ku koma ku zauna a barsu su kara su kaɗai."
"Banda ke Hamdiyya, wa Taj yafi so? Kai ma banda kai wa tafi so?"
Suna gama rubutun su ka ɗago kai.
"Happy Taj wa ka fi so?"
"Alh. Hayatu Sule Maitakalmi" ya faɗi da murya mai ban tausayi. Inna sunkuyar da kai tayi ta bar su Amma dasu Mama su da share ƙwalla.
"Amarya wa ki ka rubuta?"
Takardar ta ɗaga masa (Alhaji) ta rubuta.
Ƴan uwan Taj su ka dinga tafa mata suna murna.
"Wa ki ka fi so amaryar Happy Taj?" MC ya tambayeta.
Da murmushi ta ce "Mamana, Yaya" tana mai kallon inda Yaya take a zaune. Baiwar Allah ita ma ƙwallar ta kama yi.
"Taj wa ka rubuta?"
(Duka iyayenta)
MC ya nuna Hamdi ya ce "a tafawa amarya Hamdiyya."
Wurin ya kaure da hayaniya da murnar mutane. Wurin amsa tambayoyin nan ba ƙaramin kiɗima jama'a suka yi ba tun ma suna tare da masu taimaka musu.
Taj ya fitittike ya ce bai yarda ba.
"Ni fa da gangan na faɗi saboda nayi zaton ba za ta iya amsa nawa ba tunda ban taɓa faɗa mata ba."
MC ya ce "Kaga rigimammen ango" aka bushe da dariya "abin da za ta saka ka kake gudu?"
"Eh wallahi. Na san me wahala za ta saka ni." Ya sha kunu da wasa.
"Wai haka?"
"A'a" ta amsa mischieviously. Kai kana ganin farincikinta ka san amsar bata kai zuci ba.
"To ke mu ke sauraro"
Hamdi ta zaro ido "wai a nan zan faɗa?"
"Eh mana" cewar MC
"Iyayenmu fa duk suna nan" ta kalli saitin teburin iyayen nasu a kunyace.
"Ga takarda ki rubuta masa ba sai mun ji ba."
(Don Allah ka daina yi min waƙar India)
Tana bashi ya saka loudspeaker a bakinsa ya karantawa kowa. Aka fara dariya da ya ce a bashi fili.
"Waƙar ƙarshe zan yi irin wadda ake mirginawa a ƙasa ana kuka a gidan boss."
Hamdi duka hannuwa tasa ta rufe fuskarta.
"Na fasa kada tayi mana kuka." Taj ya faɗi yana murmushi.
Mutane suna ta dariya. MC ya ce Taj ya faɗi wani abu kafin su koma mazauninsu.
"Nagode Allah da Ya bani Hamdiyya Habib Umar. Allah Ya bamu zaman lafiya."
MC ya turawa Hamdi speaker saitinta "ke kuma me za ki ce?"
Ta kalli Taj ta rufe fuska da gefen mayafi "Amin....au mungode zan ce."
"Awwnnnnnnn" ɗin mutane kamar ta fasa dodon kunne. Aka dinga tafa musu har su ka zauna.
Mutane sun nishaɗantu matuƙa. Daga nan aka fara rabon abinci wanda a yau ma'aikatan Happy Taj su ka baje kolin basira wajen yin wanda yafi na kullum daɗi. Nau'in girki na gaske kala kala aka yi. Luciousbites da kanta ba saƙo ba kuma ita tayi snacks da kuma daddaɗan youghurt da furarta wanda ake sha ana santi. Juice kuwa sai wanda mutum ya zaɓa.
Babu mutum ɗaya da zai ce ya tafi gida da yunwa. Kowa yaci ya ƙoshi.
Bayan an gama ne DJ ya soma nasa aikin. Anti Zahra tana bawa Hayat ruwa ta hango Ahmad yana yi mata signal. Wayarta yace ta duba. Tana ɗauka call ɗin Salwa na shigowa. Kira yafi arba'in. A zatonta abin da zai ce ta duba kenan shi yasa ta ɗauka.
Salwa ta saki wata wawiyar ajiyar zuciya "Anti ina ta kira..."
"Banji ba ne Salwa. Ya gida?"
A gadarance ta ce "ina waje tun ɗazu. Kin taho da katina?"
Anti Zahra ta kalli Ahmad da har yanzu alamar duba waya yake yi mata da hannu tace "wane katin?"
"Ba a aiko min ba?"
"Ke da kike Bauchi ai ban san za ki zo ba."
Tashi tayi ta bar yaran a wajen ƴan uwanta da suke seat guda ta ƙarasa wajen Ahmad. Waje su ka fita saboda hayaniya.
"Ya zance ki duba waya ki tsaya amsa kira kuma?"
"Sorry, na zata kiran Salwa kake nufin na duba." Ta nuna masa missed calls.
"Ƙyaleta. Nayi miki text nace na taho da Mami bata da lafiya. Gobe zan kai ta asibiti in sha Allah."
"Subhanallah. Shi ne muke nan? Bari na ɗauko su Aisha mu tafi."
"Kada ki damu. Salwa na gidan. Bana so mu koma ne kiga baƙi. A can ma ya dace na sanar dake to kuma ban sami nutsuwa ba."
Murmushi tayi masa "babu komai. Amma Salwa fa ta ce min tana waje."
"Waje kuma?"
"Eh, kati take so in..."
"Koma ciki."
Yayi maganar yana sauko matattakalar da za ta sada shi da hanyar fita. A waje ya ganta tsaye can gefe ta rakuɓe kamar wata almajira. Duk sauron wajen nan ya tabbata ya gama cinyeta. Ta ɗan bashi tausayi amma bai nuna mata ba.
"Taho mu je."
Masu gadin suna ganin shi su ka bata hanya ta wuce. Magana ta so yi masa amma babu fuska. Da sauri sauri ya ding tafiya sai da su ka shiga hall ɗin sannan ya nuna mata inda ango da amarya suke.
Taj da Hamdi ke tsaye a filin rawa taƙi motsi. Ya riƙe hannayenta yana magana tana dariya. Ce mata yake ko dai ta saki jikinta ko ya kama break dance yanzun nan.
"Kin gani Salwa? Ke ya fara sani kafin Hamdiyya. Da yana sonki da kece a tsaye a can. Don Allah ki samawa kanki lafiya ki jira naki mijin."
"Na haƙura Yaya. Tafiya ma zan yi." Ta ce kamar gaske.
"Jirani a nan in faɗawa Zahra. Nan da kamar 15 minutes sai mu tafi."
Yana barin wajen tayi gaba. Ido rufe ta nufi inda su Taj su ke. Sun bar rawar sai hotuna da ake ta ɗauka. Tun kafin ta ƙarasa inda suke Hamdi ta hangota. Gabanta ya kama faɗuwa sai ta soma karanta Ayatul kursiyyu. Salwa na zuwa ta shige tsakaninsu ko sallama babu.
"Ya Taj ayi mana hoto."
Yadda kafaɗarta take gugar tasa ko Hamdi da suke tsaye tun dazu bata yi wannan tsayuwar dashi ba. Matsawa yayi da sauri yana a'ziyya a zuci sai ji yayi ta riƙe masa hannu. Wani maiƙo maiƙo da danshin da ya yi zaton na gumi ne daga hannun nata duk ta shafa masa.
Idanun Hamdi a take su ka rikiɗe sai dai ganin idon mutane sai ta daure zuciyarta. Taj na jan hannunsa ya fara jin ciwon kai Salwa sai ta sake ƙarfin riƙon.
Basu san daga ina ba kawai sai wani hannun su ka ji ya kama hannayensu dake haɗe ya raba.
"Zan ci mutumcinki Salwa akan yarona kin ji ko."
A matuƙar tsorace Salwa ta dubi Inna. Hanjin cikinta su ka kaɗa. Layar da take shirin sakawa a baki ta tauna sannan ta umarce shi da ya biyota ta saɓule ba tare da ta sani ba. Barin wurin tayi da wani irin sauri. Tana tafiya Inna ta duƙa da sunan Allah a bakinta ta ɗauki layar. Sunan ɗanta ta gani ɓaro ɓaro a jiki. Ta haɗa ido da Hamdi da taga komai ta matsa kusa da ita.
"Kama shi ku zauna. Zan faɗawa Amma a rufe taron haka."
Kai Hamdi ta gyaɗa. Ta riƙo Taj da idanunsa su ka birkice. Bayan sun zauna tana ta tofa masa addu'a a fakaice ya dawo daidai. Ya ce ta tashi ya kaita gida.
"Su Yaya fa?"
"Bishir zai kai su. I need alone time with you."
"Na'am?"
"Nace muje na kama mana hotel."
"Wallahi ba haka ka ce ba." Ta faɗa a tsorace.
Dariya ya yi mata "Ki ka ce baki ji ba."
"Da wasa nake."
"Matsoraciya."
Addu'ar rufe taro aka yi. Kowa ya tashi cikin murna da jindaɗin wannan biki mai ban sha'awa. Baballe ya ɗauki Zee, Safwan ya ɗauki Sajida sannan Taj ya tafi da Hamdi.
Ahmad da Anti Zahra kuwa mamakin duniya ne ya kama su da su ka shiga gida su ka tarar ana bushashar cin shinkafa dafaduka da farfesun kifi wanda ɗaya daga cikin ƴaƴan Anti Zabba'u ta dafa.
RAYUWA DA GIƁI 28
Batul Mamman💖
This page is sponsored by SAFFADEMPORIUM the world of amazing scents. Kun san da wuya na tallata abin da ban sani ba. To jama'a akan saffademporium ni ɗin jiyau ce kuma ganau. Ido ya gani, hanci ya shaida! Safiyya Ummu Abdoul our one and only Chairlady ta Fikra Writers Association ita ce mamallakiyarsa. Komai na Fikra kuwa daban yake. Akwai Raudha turaren carpet da kujeru, Naeema airfreshner, oils zafafa guda biyar, turaren kaya na maza da mata. Khumra masu tsayawa a rai da kuma turaren wuta.
Za ku iya samunta a manhajar instagram @saffademporium ko wannan layin 07010137848.
Sayen nagari...mayar da ƙamshi gida!
~~~~~~~~
Kun kira
Kun turo saƙo
Kun zo dubiya har asibiti
Ni kuwa me zan ce da masoyan SonSo idan ba kyakkyawar addu'a da fatan alkhairi ba?
A yayinda da nake post babu abin da yake yi min daɗi sama da kyawawan addu'o'in biyan buƙata da ku ke yi min. Wannan addu'ar ita ce babban abin dake ƙarfafa min gwiwar typing ko da jikina baya min daɗi domin bawa bai san alkhairin bakin mutane ba. A yau ina mai ƙara godiya ga Allah da ku bakiɗaya. Na sauka lafiya na kuma sami lafiyar jiki bayan aikin da aka yi min. Ahmad Amir dani da duka ahalinmu muna godiya da karamcinku.
Nayi kewarku da sharhinku mai sanya ni nishaɗi. In sha Allah zan cigaba da posting sai dai ba zai zama kullum ba. Sai kun ƙara haƙuri saboda yanayi ya ƙara canjawa. Ga ƙaramin goyo, yara, ɗawainiyar gida da aiki. Duk da haka kada ku sare da tunanin jira zai dinga tsaho. In Allah Ya yarda labarin zai cigaba cikin amincin Allah.
SonSo
***
Idan kaga yadda ake shiga gidan Alh. Hayatu sai mutum ya rantse gayyar mutane ce masu zuwa biki. Nan kuwa kaf ɗinsu ahalin gidan ne. Babu bare ko ɗaya sai masu aiki. Ƴaƴansa ne da jikoki. Kuma a haka wasu ba a nan za su kwana ba. Falon kamar ba zai ɗaukesu ba saboda yawa. Da yake an gama gajiya, rabon wajen kwana kawai aka tsaya yi.
"Duk wanda ya san ya fita ya bar kaya a falo ko cikin ɗakuna tun wuri aje a kwashe. Ba za ku dame mu da cigiya ba gobe." Cewar Ummukulsum ga jikokin. Ita ce babbar ƴar Yaya Hajiyayye kuma jika ta farko a gidan ta girmi Firdaus ƴar ajin su Hamdi.
"Ni dai ban ga kayana da na ajiye a nan ba..."
Cigiyar da take gudu tunda ta san komai wajenta ƙannen za su zo nema mazansu da matansu aka fara yi daga rufe bakinta. Kula su ka yi falon a gyare yake. Aka tambayi masu aiki kowacce ta ce ba ita tayi ba kafin su tafi. Abin da mamaki dai.
"To ko dai Alhaji ne? Naga motarsa..."
Hamɓare bakin mai maganar Yaya Samira tayi kafin ta kai ƙarshe.
"Baban namu ne zai yi muku gyaran falo don rainin wayo?"
"Gani Mugenbo shugaban marasa kirkin duniya ko?"
Muryarsa su ka ji kafin su gan shi yana fitowa daga ƙofar ɓangarensa dake cikin falon. A gurguje masu ƙuruciyar ciki su ka yi kansa saboda sabon da su ka yi dashi. Ƴan matasan kuwa su ka shiga sunne kai.
Manyan kuma dariya su ka yi. Su sun fi sanin baban nasu akan ƴan baya baya da su ka taso lokacin da ya fara fushi da Taj. Tsaurin ra'ayinsa bai hana shi kamanta mu'amalantar iyalinsa yanda addini ya tsara bakin gwargwado a lokacin ba. Dalilin da yasa ma ya sami damar iya tafiyar dasu akan ra'ayinsa kenan koda zuƙatansu basa son abu. Ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da zata sa iyalinsa su butulce masa.
Cikin jikokin wani ɗan shekara biyar zuwa ya yi jikinsa ya tsaya yana fuskantar wadda ta ce ko Alhaji ne ya kwashe kayan.
"Alhaji ba ya yin aikin mata. Shi ba ɗan daudu bane."
Tsit falon yayi. Kunya ta kama su aka rasa mai kwaɓarsa. Alhaji ya jinjina maganar musamman da ya karanci yadda kowa ya sha jinin jikinsa. Duk sai yaji babu daɗi.
Murmushi ya yi na jin kunyarsu ya dafa yaron "kwashe kaya da ninkewa ai ba aikin mata bane kaɗai Amir. Duk wanda zai iya saka kaya ya kamata ace zai iya ninke su."
"Laahhh, Uncle Taj ma ba ɗan daudu bane kenan ko?"
"Me yasa ka ce haka?" Alhaji ya tambayi yaron da sakakkiyar fuska don ya bashi amsa.
"Saboda duk wanda ya iya cin abinci shi ma ya kamata ya iya dafawa."
Mahaifiyar Amir kasa tsayuwa tayi saboda tsoron me Alhaji zai yi bayan jin amsarsa. Ta kalli yayyenta su Yaya Kubra tana neman ceto.
Matan gidan ne ƙarshen shigowa dama. Saboda haka daga baki bakin ƙofa suke tsaye. Hajiya tana kallon idon Alhaji ta yiwa Amir tambaya.
"Kai ka san waye ɗan daudu?"
"Eh mana" ya amsa da karsashi na yaron da aka yiwa tambaya mai sauƙi "sune masu yin haka..." ya ɗaga hannuwa ya tafa da iska "ahayyyeee cass, rass... ko?"
Hannuwansa Bishir ya yi saurin riƙewa ya ce "dare ya yi, ayi shirin bacci a kwanta haka nan."
Da sauri sauri su ka dinga watsewa aka bar Alhaji a tsaye cikin tunani da wata irin kunya. Yau kuma yaro ɗan shekara biyar ne ya shiga sahun masu faɗa masa gaskiya? Kuma wannan karon a gaban mutanen da yake jin ya isa dasu ta kowacce fuska!
"Alhaji na ce Allah Ya bamu alkhairi."
Da muryar Umma tunanin da ya fara ya kau ya dawo da hankalinsa ga matansa. Hajiya ma sai da safen tayi masa ta shige yayinda Mama tayi masa tambayar ko ya gama da kwanukan abincin dare da ta ajiye masa domin ta kwaso. Amsa ya bata sannan ya mayar da dubansa ga neman Inna don tunda su ka shigo ko tari bai ji tayi ba. Jiran ta ce masa sai da safe kamar ƴan uwanta yake sai yaga bata wajen.
'Fushi take? Me kuma nayi? Ba na bada izinin yin bikin ba? Sai da safen ma yau ban isa ace min ba?' Ya ayyana a zuciyarsa.
"Ba tare ku ka shigo da Abu bane?" Ya tambayi Mama.
Yanayinta yaga ya sauya sannan ta ce masa ya shiga ɗakin Innar ya sameta. Hankalinsa tashi ya yi don ko bata faɗa ba yaji a jikinsa babu lafiya. Tabbas Hajiya da Umma ma basa cikin walwalar da yayi tsammanin za su dawo da ita.
Ɗakin ya shiga kai tsaye ya tarar da ɓangarenta da ƴan kwana. Wuce na falon ya yi ya shiga ainihin ɗakin baccinta inda nan ma wasu ke ciki. Sai dai suna ganinsu su ka fita. Zai yi magana ta riga shi ta hanyar miƙa masa wannan layar.
Ya miƙa hannu zai karɓa kenan sai Inna taga ya yi baya da hannunsa da sauri yana zaro idanu.
"A'uzubillahi..."
"Ka san ko mene ne kenan?" Ta ajiye layar a wajen madubi jikinta a sanyaye.
"A ina ki ka samo ta?" Ya tambaya cikin matsanancin tashin hankali fiye da wanda tayi tsammani.
"Sal..."
Kafin ta kai ƙarshen sunan ya gane wa za ta ce. Ya ɗaga layar yaga sunan Taj. Ransa kuwa ya yi mummunan ɓaci.
"Ɗana? Me matar nan ta taka da har take tunanin zan zuba ido ta mayar min da ɗa mutum mutumi?"
Inna na jin haka nata hankalin ya sake tashi.
"Mugun tsafi ne ko? Innalillahi. Tun a wajen naga ya fara runtse idanu."
Maganarta sake tunzura zuciyar Alhaji tayi. Sirrin da ya sakayawa Mami albarkacin Ahmad ya dawo masa tar cikin ransa. Haƙiƙa kamar sauran matansa ita ma so ya saka shi aurenta. Ta zo da fitina da neman rigima. Kullum cikin takalar Hajiya da Mama faɗa dake gidan a lokacin take. Aka mayar masa da gida filin kai ƙara. Wani abin idan tayi shi kan shi sai ya yi mamakin mene ne abin tashin hankali a ciki da har za ta nemi faɗa. Abin mamakin ma shi ne kasancewar shi ɗin jajirtaccen namiji ne amma ko zai ari baki wajen yi mata faɗa da nasiha anjima ko gobe ma sai ta ƙara. Sannu a hankali ya shiga karantarta inda ya fahimci ashe asiri take yi masa, kuma yawan rigimarta tana yi ne domin aunawa taga ko sihirin ya ci. Bai gama tsinkewa da lamarin ba sai da yaga wannan layar da yaji da kunnuwansa ranar da Zabba'u ta kawo mata tana cewa sunanta Raƙumi da akala. Har tana yi