Showing 27001 words to 30000 words out of 121577 words

Chapter 10 - TURKEN GIDA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

22 Sep 2025

3077

kawai na ke yi ina dariya a raina. Ba aikin da zan yi nima na gyara zama can falo kuma su Ma'u ne, ban son haɗa inuwa ɗaya da ita shi  yasa ban fita ba.

  Ina zaune na ji marata ta karta daman tun jiya da daddare ciwon mara kaɗan kaɗan ya matsamin ba na tunanin al'ada tunda na yi shi a wannan watan. Ban taɓa tunanin in na shiga makewayi zan ga jini ba, jini sosai na gani na zubar mini hankalina ya tashi na wanke jikina na fito, da sauri na ce ma Halima zan ta fi, ko tsayawa ma in bi ta kanta tana cewa lafiya ta ganni cikin gaggawa?

  Na fita falo ina kiran wayar Yusuf ta shiga amman bai ɗauka ba, su Ma'u ba sa falon ƙila sun shiga sallah ne. Hankalina tashe na fita na samu abin hawa zuwa gida ina shiga gidan sai ga wayar Yallaɓai.

"Yallaɓai jini na gani, na bani al'adata ta dawo da mini wasa kamar baya."

Cikin damuwa ya ce"Topha. Yanzu kuma? To da yawa?

Ina cire mayafin jikina na ce"Ina jin sa yanzu haka yana bin kafata. "

"Subhanallah, ko za ki tura mini mganin da suke rubuta miki a asibiti lokacin nan? Na ga kina amfani da shi zubar jinin ya ke dakatawa."

  Kamar in yi kuka na ce"Na daɗe ban je na ga likita ba. Ba zai yuyi na sha mgani ba tare da na je an sake dubani an ga in da matsalar take ba. Ka taimaka mini ka sake kira mini Uncle Abba ina bukatar ganin likita a cikin satin nan."

  Sai ya ce na kwantar da hankalina bari ya kira shi, muna gama wayar a daddafe na tafi tiolet ɗin falo ma ba na ciki ba, kayana duk sun baci ina ma turarradin ban bata ma mai Napep kujera ba, kayan jikina sun lalace na tube na yi wanka kayan kuma na jika su a bucket, haka na fito ina hawaye, ina ta murna side effect ɗin planining ya daina taɓa ni, tunda duk a asibitocin da na riƙa zuwa a baya sun tabatar mini da komai lafiya zan iya samun ciki ko yaushe ne.
Mun kashe kudaɗe a asibitocin kuɗin dake garin kano ba a dace ba, shi ya sa na yi amfani da shawaran mutane na ga gwara na je babban asibiti.

A baya na yi ta fama da ciwon mara da zubar  jini a can wani babban private hospital sun ɗorani kan wani mgani na yi amfani dashi kuma cikin ikon Allah komai ya daidaita. Ina cike da yaƙinin komai zai zama tarihi sai ga shi al'amarin ya dawo sabo.

  Zubar jini nake yi sosai sai da na saka Pampers  daman ina da shi, saboda ina bleeding in ina period shi na ke amfani dashi.

  Ina zaune kawai ina hawaye, abin duniya ya isheni Yusuf ya sake kirana labarin da ya ke faɗa mini ya saka ina hawaye ina dariya.
Likitan da zan gani a Shika ta ba ni dama ranar monday sha ɗaya na safe, in na je zan kira wayar Dr Fadil wanda Uncle Abba ya tura masa lambar.

  Ina mirmishi na share hawayena ina faɗin"Alhamdulillah."
Me na ke tunani. Ina tunanin kamar ina da wata matsalan anan ba a gano ba ne,tun da ba babba asibiti ba ne.
Ina hashashen in na sauya waje da asibiti mai kyau da ke da ƙwararru kila za a iya gano wani abun har na nemi magani domin na samu waraka.

"Ki kwantar da hankalinki, sai mu je tare in sha Allahu "

  Ajiyar zuciya na sauke kafin na ce" Shi ke nan,  Allah ya kaimu nan da kwana shidda kenan ko?

  Sai ya amsa mini ganin duk na damu sai ya shiga lallashina, da cewa in sha Allahu ba wata matsala. Cikin yaƙinin da na ke dashi na ce" In sha Allahu."
Bai kashe wayar ba sai da ya ga na sake har muna hira da dariya sannan ya kyaleni.

Amman bayan mun gama wayar tagumi kawai na yi ina tunanin makomar rayuwata. Ina kwaɗayin na ƙara haihuwa, an ce komai na mahaifata lafiya kalau zan iya samun ciki kowani lokaci amman sai yaushe? Sama da shekaru uku tun ina saka rai har na fara gajiyawa? Ni kaɗai na yi ta kukana ina sharan hawaye kasa komai na yi kafin su Jidda su dawo makaranta jinin ya ɗan tsagaida sau ɗaya na sauya pampers, ban yi musu ko abinci ba cewa na yi su sha goldenmorn sannan in sun huta Jidda ta dafa musu ko farar taliya ne su ci da mai, ɗakina na koma kawai na kwanta  ina jin kasala na rufe ni.



*Janafty*
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

*🅿️06*

Har bayan mangariba ina cikin ɗaki ban iya fitowa ba, na ci kukana har na ƙoshi na lallashi kaina. Baby ta zo za ta dameni da surutu na ce ta je Yaya Jidda ta kunna mata Cartoon. Ita kanta yarinyar ta lura da yanayina har yadda ƙasan idanuwana suka kumbura.

  "Umma ba ki da lafiya shi ne kike yin kuka?

  Sai da ta saka ni mirmishi, kanta na shafa kafin na ce" Lafiya ta ƙalau. Je ki wajen Jidda, kun yi sallah ko?
Sai ta gyaɗa mini kai.

  Jin abin da na ce ya sa sai ta juya ta fice daga bedroom ɗin na bita da kallo tana fita na ƙara fashewa da kuka, ƴaƴa biyu gare ni su Allah ya ba ni, yanzu in ban ƙara haihuwa ba suka zo suka mutu fa?
Tuna haka kaɗai sai da ya sa na ji kamar jinina ya yi sama, domin ji na yi numfashina na barazanan barin jikina gabaɗaya tsabar tashin hankali da damuwa.

  Daga ƙarshe suma sun gaji da zama a falo su kaɗai sun saba in ina gida tare muke yi salolli da azkar mu yi karatun Qur'ani sannan na duba littafansu na makaranta muna yi muna hira, su kaɗai gare ni domin a wannan rayuwar ƴan'uwanka ma suna gudunka, Mijin ma ba lalle ya zama mai amana ba, su ko ƴaƴa ko akan bola uwa ke kwana ba su isa su sauya ma tuwo suna ba.

  Ganin har an yi sallar isha'i takwas ta gota ban fito ba sai ga Jidda ta kwaso mini Baby sun shigo har Bedroom ɗina, ina cikin bargo na dunkule suka hawo har saman gadon suna kiran sunana.

'"Sannu Umma? Kan ki ke ciwo?

  Haka Jidda ta tambaya, sai na yi ƙoƙarin goge idanuwana na miƙe zaune ina faɗin"Na ji sauƙi, kun yi sallar isha'i? Jidda ta ɗaga min kai kafin ta ce"Har karatun Qur'ani mun yi na ƙara ma Baby na ta karatun"

Kanta na shafa kafin na ce"Allah ya yi miki albarka Jiddan Umma."
Baby ta ɓata rai tana faɗin"Ban da ni Umma? Sai itama na shafa kanta ina saka mata albarka, kantowa ta yi saman jikina, ni kuma sai na koma ina wasa da jelan kitsonta na 2step da akayi mata, da ya ke suna da tsawon gashi ni suka ɗauko duk da shima babansu da dangin shi gabaɗaya suna da cikar suma.

  Jidda ta yi ta yi ta zubo mini abinci na ce ta bari in na tashi zan sha Tea. Wanka na ke so na yi ga kaya can da na ɓata ma ban wanke ba, Baby har ta yi barci a jikina sai na ce Jidda ta ɗauketa zan ta shi.

  Tashin ta ta yi, domin ba ta iya ɗaukanta Baby akwai jiki a cure,  bayan ta tashi ta kama hannunta zuwa ɗakinsu na ce ta tabbatar ta kaita tiolet ta yi fitsari, na ɗan ƙara samun natsuwa ganin jinin ya ɗan tsagaita amman bai ɗauke gabaɗaya ba. Wanka na yi, na fito kenan na ji buɗe get na san Yallaɓai ne.

  Ba ni da wani ƙarsashi sai kawai na zura wata rigar barcina doguwa, kaina buzu buzu ko ta kan shi ban bi ba, haka na koma gefen gado na zauna ina tunanin abin yi? Sai na ji kamar ina rasa tunanina na wani lokaci saboda halin damuwar da na ke ciki.

  Ina jin sa sai da ya shiga ɗakin yara ya gansu sannan ya ƙariso Bedroom ɗin mu, yanayin yadda ya ganni kamar ƙanwar mahaukaciya shi ya san ya yau ɗin fa ba lafiya.

  Hannuwansa ya buɗe mini alamun in ta so amman na kasa tashi, kallonsa kawai na ke yi hawaye suna cika mini kwarmin idanuwana. Shi ko ganin naƙi tasowa ya sa ya tako gabana, hannunsa akwai brief case ɗinsa sai wasu takardu, sai da ya sauke su saman madubi sannan ya ƙariso gabana ya durkusa lokaci ɗaya ya na rike mini duka hannuwana.

  Ina jin ya riƙe ni sai kawai hawayen da na ke ta riƙewa suka kwaranyomin a saman fuskata, marairaice fuska ya yi kafin ya ce"Haba Sadiya ta, ba na ce ki bar damuwa ba? Kin kuma ce min kin bari? To me ya sa kike kuka kuma? Kalle ki fa Yallaɓanki ya dawo amman kin kasa taran shi da irin mirmishinki da kika san ya na kwantar masa da hankali, sai ki tare shi da kuka? Alhalin kin san kukan ki dai dai yake da yi ma kwanciyar hankalinsa barazana?

  Ya ƙarishe faɗa, ya na kallona ni kuma sai na ji raunina ya bayyaana share mini hawaye ya ke yi da tattausan hannayensa duka biyu, faɗi ya ke yi" Ki daina kuka, ki bar wannan kukan? Kina so na shiga damuwa ne?ko so kike yi nima na fara kukan? Uhm Sadiya ta?

  Sai kawai na riƙe masa hannunwansa da duka hannayena guda biyu, ban san ma lokacin da na barƙe da kuka ba, kuka wiwi kamar Jidda. Daman a jikin Yusuf kawai na ke samun daman wannan kukan, ba ni da uwa da ace Mama na raye ita zan yi ma wannan kukan. Gwaggo kuma ba na zuwa gaya mata matsalolina ita da Alhajinmu ba na so su shiga damuwa, sannan duka ƴan'uwana ba ni da sakewa da kowa sai Rahila, itama ta na da ji da na ta auran ba zan ta zuwa ina damunta, a ɗakin mu Yaya Auwal ne kuma shi Namiji ne sannan ya yi nesa da mu, Amina kuma ƙanwata ce itama kaduna ta ke aure, Datti kuma yana makaranta sai in ya zo gida hutu.

  Dole dai kafaɗan Yusuf ne abin jingina na in yi kukana shi kuma ya lalace wajen lallashina, har a raina ina jin ƙila watarana wannan kafaɗan da na ke kwanciya na yi kuka za ta iya yi min nesa da wat rana sai dai na yi kuka na a saman gwiwoyoyina ba zan iya samunsa a duk lokacin da na ke bukata ba, tunda ƙila ba lalle ya ƙare rayuwarsa da ni kaɗai ƴaƴa biyu kacal ba, ahalin ya na da yadda zai yi ya samu abin da ya ke so na mallakan yara da yawa.

  Lallashina yake yi da duka iya kalamansa bakinsa, amman sai da na ji zuciyata ta rage kunci sannan na daina kuka na koma shassheka, rumgumeni ya tashi ya yi bayan ya zauna gefen gado, yana ɗan tapping ɗin bayana alamun lallashi.

  Ɗagowa na yi ina kallonsa fuskata jage jage da hawaye, shi kuma sai ya saka haɓan hannun rigansa zai share mini hawaye da sauri na kauda kaina na saka hannu ina sharewa da kaina cikin muryan damuwa ya ce"Me ya sa kika hanani na share miki hawaye Sadiya?

  Cikin dakushewar murya na ce" Saboda kar ka ɓata kayan ka."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Kaya? Me nene kaya? Ban so kar ki sake hana ni share miki hawaye, domin ina fatan har ƙarshen rayuwata na zame majinginar in za ki yi kuka, sannan na zama mai share miki hawayen ki, ba na so na ji kamar na gaza miki ne Sadiyata."

  Kai na girgiza kafin na ce"Ko ɗaya. Ba ka gaza mini ba Yallaɓai. Sai ma ni ce na gaza maka, na kasa ba ka farincikin da ka ke so, na kasa sake Haihuwa Yusuf, wallahi ina so na ƙara haihuwa ko ɗaya ne? Ko ɗaya ne ko? Ai kana so ko?

  Haka na ke faɗa da sauri da sauri  sai ya lura kamar ma na fara fita hayyacina sai ya yi ƙokarin rike mini hannu lokaci ɗaya yana faɗin"Shii. Kin manta muna da ƴaƴa? Ƴaƴan mu biyu Sadiya muna da Jidda muna da Baby? Me ya sa za ki yi ta damuwa bayan muma muna da ƴaƴa ba wai ba ki taɓa haihuwa ba ne"

  "Ba za mu rayu da ƴaƴa biyu ba Yusuf, in suka zo suka mutu fa?

  Haka na faɗa, ina jin har hannuna da ke cikin na Yusuf na rawa. Kallona kawai ya tsaya yana yi cikin mamaki kafin ma ya samu zarafin mgana na cigaba da faɗin.

  "Ina ta tunanin me ya sa lokacin da na kawo shawaran zan yi planning saboda makaranta ba ka hana ni ba? Me ya sa ka biye mini? Me ya sa ka amince, da ka hana ni da ka bar ni, na yi ta haihuwa ai wahala ba ta kisa, ba zan mutu ba sai lokacina ya yi, me ya sa ba ka hana ni ba?

  Haka na faɗa da ƙarfi sannan lokaci ɗaya ina jijjiga hannayensa, Kasa motsi ya yi sai kallona ya ke yi, yasan na fita hayyacina kuma ko ya yi magana ba zan saurare shi ba, sai kawai ya kamani ya yi mini wata irin rumguma da ƙarfi sai da na ji numfashina ya na barazana ɗaukewa dole na yi shuru amman fa na fashe masa da kuka.

  Ƙamƙam ya riƙeni yana faɗin"Ba na so, me ya sa kike irin wannan tunanin? Ba za su mutu ba in sha Allahu ba yanzu ba."

  "Yara suna mutuwa fa Yusuf? Ko Baby in ta mutu fa?

"Na ce ki bar cewa haka ko?

Ya yi min tsawa bayan ya ɗago ni yana mai ƙureni da ido.
Sai na sadda kaina kasa ina kuka.

"Kin yi nadama ne? Ko ba ki yi planining ba. In abin da Allah ya kaddaromana kenan Sadiya ba fa mu isa mu tsallake wannan kaddaran ba, kuma planning ba laifi ba ne domin kin nemi tazara saboda karatun ki, ko malamai ai suna mgana kan a yi tazaran haihuwa, me ya sa yanzu kike nadama? Ko an ce kina da wata matsala ne? Kin je asibitin nan an yi duk gwaje gwajen an tabbatar da lafiya lau mahaifanki. Side effect ne, kawai ya taɓa ki, kuma kusan daman komai na rayuwan yana da nashi amfanin da rashin shi, me ya sa za ki zauna ki rasa hankalinki? Har kina yi ma ƴaƴan mu fatan mutuwa?

  Kafaɗata ya rike duka biyu, sannan ya kira sunana har sau biyu na amsa sannan na ɗago ina kallonshi.

  "Kar na kara jin mganar mutuwa a bakin ki kin ji ko?
Sai na gyaɗa masa kai kawai ba tare da na yi magana ba, shi kuma sai ya koma ya na sharemin hawaye yana faɗin"In Allah ya so za ki kara haihuwa, in bai so ba duk som mu da haka ba za ki ƙara ba. Ubangiji ne ke iya tsara ma bawa rayuwarsa tun daga ranar haihuwarsa har ranar mutuwansa."

  Jikina ya yi sanyi, shi na ke kallo kafin na ce" Kai fa? Haka za ka zauna. Na san kana son yara a kallah dai ko ba da yawa ba kamar biyar haka."

Bai yi min mgana ba sai da ya gama gogemin fuska tas da haɓan rigan shi, ya na kauce ma mganar ne, ya mikar da ni yana faɗin"Mu je ki yi wanka"

  Kai tsaye na ce"Na yi wanka fa" muryata a shake, shima kai tsayen ya ce"Ba irin wannan ba, irin wankan da kika saba mini"
Ban san lokacin da na yi mirmishi ba, har cikin tiolet ya kaini, ya duka ya sumbaci bakina sannan ya fice ya barni, na ɗan samu natsuwa shi ya sa na ƙara tuɓewa na sake yin wanka lokacin da na fito ya na ɗakin shi ya taya ni na shafa mai na shirya, kwalliya ya ce yana so na yi masa ina shagwaɓewa na ce"Wani kwalliya kuma da daren nan Yallaɓai na?
Hararana ya yi kafin ya ce"Bashi za ki biya,  ki yi mini abin da kika saba na more kallon ki kafin na kwanta,."
Ganin na yi shuru ya sa ya marairaice ya na faɗin"Ko ba ki so na samu natsuwa daga kallon ki ne?

  Ina jin haka na yi saurin girgiza kaina. Kwalliyar na yi masa na saka riga da wando. Wandon mai ɗamewa ne, rigar ma haka shi ya tayani na gyara gashina na saka rebon zan saka hula ya ce na bar mai kayansa ahaka, to kayansa ne shi ya sa bar masa kayansa.

  Na faɗa masa ban yi girki ba, taliya ne Jidda ta dafa, sai ya ce kar na damu ya siyo mana kaza. Falon farko muka fita ya ɗauko mana kazan muka baje a saman cafet muna ci, ya na bani a baki ina bashi muna hira haka sama sama sannan jefi jefi muna kallo.

  Na leƙa su Jidda har sun yi barci daman guda biyu ce muka ci ɗaya muka saka musu ɗaya a fridge, bayan mun gama ci muka ɗora da sanyayar maltina Yusuf ya kwashe komai da muka gama ya gyara wajen, ya kawo mini tissue ya goge mini hannuna da bakina shima ya goge na shi, kujeran mai zaman mutum ɗaya muka zauna ni na kwanta saman jikinsa,   shi kuma ya saka hannu ya rumgumeni yana wasa da gashin kaina, muna hira sannan muna kallo a tashar Mb2 ne ana wani film ɗin Horror ina ta cewa ina jin tsoro amman Yusuf ya ƙi sauyawa wai ba wani tsoro.

  Mu ne har 12 na dare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login