Showing 66001 words to 69000 words out of 121577 words
kuma Yaya Abubakar tunaninsa na kan Ma'u ni ce na fara lura da ita da kuma abin da ke faruwa saboda ni ce daman idona ke kan duka motsinta.
Shi Yaya Hamza bai ma san ta na yi ba. Namiji ne mai tsare gida ba ya ɗaukan reni ba shi kuma da yawan sakewa mutane shi kuma Yaya Abubakar yana da sanyi ga arhan dariya shi fa kowa na magana dashi ga surutu ba kamar Yaya Hamza ba. Ga aji ga tsare gida mgana ɗaya bayan ɗaya cikin wayewa shi ya sa na ke ƙaunar Yaya Hamza na kuma saka acikin tunanin irin mijin da zan aura mai hali irin na Yaya Hamza ne sannan na ji a raina ba zan iya auran mai hali irin na Yaya Abubakar ba. Shi daman Yaya Auwal da shi da babu a gidan duk ɗaya. Sai a yi abu goma bai sani ba yana da ƙokari ko yau she yana ɗaki yana karatu in ba na boko ba na arabi. Kuma shi yana da ƙyaluwa ba kasafai ya ke saka baki a wasu abubuwan ba. Shi sai a shekaran ma ya zana jarabawar shiga babban sakandiri.
*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
09069067488.
08032773332.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
I just published "Page 12" of my story "TURKEN GIDA."::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68237857847ebcbfe6d205fe
*🅿️12*
Sulaiman Abubakar Yashe. Shi ne cikakken sunan Alhajinmu. Inkiyan Alhaji da ya samu ba yana nufin ya je ya sauke farali ba ne.
A zamanin baya in mutum ya baro ƙayensu zuwa garin Kano a matsayin jihar ta cibiyar kasuwanci sai a riƙa tunanin ai ka zama Alhaji ballatana in ka samu rufin asiri to mutane da yawa kan iya sakaya sunanka da Alhaji.
Sunan Alhaji ya bi sa har matansa da haka suke kiran shi har muma ƴaƴansa muka wayi gari da sunan a bakin mu.
Alhajinmu haifaffan ƙauyen Yashe ne. Ita kuma ƙauyen Yashe tana cikin ƙaramar hukumar kusada. Ita kuma ƙaramar hukumar kusada tana cikin yankin Jihar katsina ce. Garin kusada manoma ne da makiyaya shi ne sa'arsu da shi suka yi kuɗi har suka arzuta wasu ma. Mallam Abubakar ya kasance kafin rasuwarsa matan auransa biyu Halima(Hajiya Dubu) da Balkisu. Kuma ya rasu bayan Balkisu ta riga su gidan gaskiya. Sai ɗawaniya da nauyin komai ya koma kan Hajiya Dubu.
Kafin rasuwar Balkisu ƴa'ƴanta biyu ne kacal ta haifa sauran duk sun koma Sule da Hasiya. Sai riƙon su ya dawo hannun Hajiya Dubu da ta riƙe su tun suna kañana ba nuna bambamci. Ita Hajiya Dubu ƴaƴanta uku ne biyu maza mace ɗaya. Akwai Aminu sai Muhammad sani sai ƙaramar su Aina'u wacce ta yi aure sai ta rasu wajen haihuwa.
Sulaiman a cikin garin kusada ya gama sakandirinsa daga nan ya yi tunanin haurawa garin kano domin ya cigaba da karatunsa na boko. tun da ya samu na addinin har matsayin sauka. Lokacin ba kowa ke saka ɗan sa a karatun boko ba amman shi Sule da kansa ya kai kansa makaranta saboda ya na sha'awar karatun sosai. Ya tafi kano neman ilimi bayan ya saida gonar da ya gada a wajen mahaifiyarsu. Ashe dalilin haka Kano za ta zame masa mafaka da sillar zama abin da ya zama.
Diploma ya fara yi a can kano cikin ikon Allah kuma sai ya samu aiki a NEPA hukumar wutar lantarki na jihar Kano tun da lokacin ana iya ɗaukan masu takardan sakandiri aiki tun da tana da daraja. Samun aikin shi a wajen shi ya inganta masa rayuwa sannan gefe ɗaya ya na kiwo a gida ga Noma Aminu da Sani duk ba su yi karatu ba suna noma sannan suna kiwo. Ya auri matarsa ta farko Maimuna yar nan garin Yashe ne maƙota suke ma. Sun yi aure tun shekarunsa ba su rufe talatin ba itama ta ƴar yarinya a lokacin ta fara zama a yashe kafin ya kama mata haya a anguwa uku ya ɗauketa suka koma can suka fara gina rayuwarsu.
Farkon rayuwar ya fara ta ne da Maimuna(Gwaggo) sai dai kamar auran naTa ya zo masa da tarin buɗi. A shekarun biyun da suka yi aure ya yi noma kuma ya samu amfanin gona sannan ya saida kiwon shi ya siya wasu alherai sai bin sa suke yi da buɗe. Sannan ga albarka samun ƙaruwa ta ɗa Namiji wanda ya ci sunan kakanshi Abubakar. Bayan shi ba daɗewa ta sake haihuwan wani namiji aka sanya ma sa suna Hamza.
Maimuna na da cikin Aina'u Sulaiman ya ƙara aure da Rukayyatu yar kano ce. Sun haɗu kuma Allah ya haɗa zukatansu waje ɗaya. Ya aure ta kuma Maimuna ta karɓeta hannu bibbiyu a matsayin abokiyar zama ba kishiya ba. A ƴan'uwansa ba wanda ya yi mgana kan ƙarin auransa sai Ƙanwarsa Hasiya balle da ta ga tun bayan auran shi kenan abubuwa suka fara lalacewa ko Sulaiman ya yi noma baya samun komai sai kiwon sa da ɗaya da ɗaya suna ta kasawa wasu ma sai dai a tashi a ga gawa shi kenan Hasiya ta ce Rukayya ce da ya auro mai farar ƙafa sai da Hajiya Dubu ta tsawarta mata. Lokacin Hasiya ta yi aure anan garin Yashe amman dai Allah bai bata haihuwa da wuri ba. Ana ta raɗe raɗen wanda ta aura ne baya haihuwa kwata kwata sai da aka raba auran ta sake auran wani saurayi Hashimu shima dai kusan shekaru huɗu shuru ba wani labari.
Cikin wannan halin sai kuma a ka fara rasa wasu abubuwan na dukiya. Sai kuma aka yi ta samun ƙaruwa Gwaggo ta haifi Murja ita kuma Mama ta haifi namiji an saka masa suna Auwalu. Sai dai bai yi sati biyu ba Allah ya yi masa rasuwa.
Sun tashi daga gidansu na anguwa uku ya kama wani a gandun albasa. A can aka haifi Balki da ta ci sunan kakarmu. Sannan Mama ma ta sake haihuwan Namiji sai aka maida mishi sunan wanda ya rasu Auwal.
A yadda Gwaggo ta faɗa mana sun samu cikin mu a Gandun albasa ita da Mama amman kuma ba su haife mu a wannan gidan ba sai a gidan da Alhajinmu ya sake kama musu da ke Fagge shi ya fi girma ne sannan ga iyalai sun fara yawa. Kuma su Baba Aminu suna kawo masa ziyara ba shi da wajen safkarsu.
A yadda labari ya zo mana a bakin Gwaggo. Tsakani na da Rahila kwana arba'in ne. Rahila aka fara haifa, ni kuma sai ranar da Rahila ke cika kwana arba'in sannan aka haife ni. Ni na ci sunan Hajiya Dubu ita kuma Rahila ta ci sunan marigayiya mahaifiyar Gwaggo da ta rasu ba daɗewa a lokacin.
Tsakani na da Amina ko shekara biyu bai kai ba shekara ɗaya ne da wattani daga kuma kan Rahila Haihuwa ta tsaya ma Gwaggo. Amman Mama ta yo auta Abdulsalam ana kiran shi Datti.
A ƙiyasu mu goma ne cif a gidanmu. Ta bangaren Mama mu huɗu ne ta bangaren Gwaggo kuma su shidda ne sau zuwan Ma'u da muka zama mu goma sha ɗaya. Mun ta so cikin gata saboda Alhajinmu ya na ta samun ƙarin girma a wajen aiki sannan kuma har gobe bai daina noma da kiwo ba. A gidanmu kowa da halin shi misali kamar ni ina da tsiwa sannan ga taurin kai ina da nacin magana. Za ka ganni kamar ban san me na ke yi ba nan kuwa ina ankare da motsin kowa tun taso wata Allah ya yi ni da son jiki har suna Mama ta saka min Sadiya yar laushi. ina da sakin jiki amma ga ƴan'uwana ba ni da sakewa da mutane ba kuma tsoro ba ne kawai ni haka Allah ya halliceni ban cika son mutane ba sosai shi ya sa bayan Rahila da muka yi damben kuruciya tare ban taɓa wata ƙawa ba. Sabanin ita Rahila mai sanyi ce ga hakuri sannan tana da faram faram da mutane kuma kowa na ta ne shi ya sa in yara sun zo gidanmu tabbaci wajen Rahila suka zo ni ko mutm ya so mu saba ba na barin haka ta faru sai na janye jikina.
Kamar ta bangaren Yaya Abubakar da Yaya Hamza ne. Shi Yaya Abubakar ba shi da zafi shima dai akwai sakewa da mutane ga surutu saɓanin Yaya Hamza da bashi da wasa ƙwata ƙwata. kamar misalin Yaya Auwal ne shi kuma wannan ɗan i dont care ne. Abu goma za a yi a cikin gida bai ma san an yi ba shi fa rayuwarsa kawai yasani sai ko in ya ji yunwa ya ci abinci. Yaya Aina itama ba ruwanta ba ta da faɗa amman Yaya Murja ta fi kowa shegen shisshigi da shiga abin da ba ruwanta ga sa ido sannan ba ta da haƙuri kamar zawo ta ke. Shi ya sa ba mu taɓa shan inuwa ɗaya da ita ba ita faɗa ni kuma rashin kunya. In aka duba Amina da Datti. Gwara ma Datti ita Amina miskila ce irin Auwalu sha'ani ko an saka su aciki ma ɓata lokaci ne abu nawa zai faru a cikin gidan suna nan amman ba dai ka ji bakin su ba. Shi ya sa na ce a gidanmu kowa da irin halin da ubangiji ya yi masa dai dai gwargwado da zai zauna da mutane.
******
*2000*
*Ɗorayi*
Hajiya Dubu ce ta ƙure Radiyo ɗin ta a tsakar gida tana sauraran gidan radiyon jihar kano ana karanto labaran yammaci. Zaune take saman tabarma daga can ƙofar ɗakinta. Gwaggo na gefen ta suna jin labaran jefi jefi Mama ma dake can gefe tana tankaɗen garin masara a cikin farantani. Tana ɗan saka musu baki jefi jefi.
Ina kwance a kan gadon Hajiya Dubu har wani ƙara nitsewa ne ke yi. Ba wanda ya san ina ciki saboda gadon mai rumfa ne. Kuma san da na shigo har Hajiya Dubun ba ta sani ba. Yau alhamis ba islamiya kuma ni ce ke da girki gabaɗaya na gaji. Da rana alkubus ɗin alkama na yi gabaɗaya a gajiye na ke daman kun sani yar laushi ba na son aiki kawai ina kwance bayan na idar da sallar la'asar ina hutawa Mama ta leƙo ta ce min na fito na ɗora miya a lokacin tura baki na yi kafin na ce.
"Mama Tuwo kuma?
"E."
Haka ta faɗa tana kallona idanuwana har ya ciko da ƙwallah. Gaskiya dai na gaji kuma a ƙasa ƙasa sai da na ce na gaji Mama ta yi tsaki ta na sakin labule kafin ta ce"Ke daman ai ko kina kwance ne sai kin ce kin gaji. Malama ki taso kar dare ya yi kin kuma san Alhaji ya hana ku tuwon dare."
Na fi mintina talatin kafin na taso sai da Mama ta ƙara leƙowa tama faɗin za ta make ni. Ni kaɗai ne a ɗakin Amina ta bi su Rahila yau wata yar islamiyan mu na aure ni daman ba na zuwa biki ban je ba ina gida amman daga baya na fara nadama da na sani na bisu sai na ga wanda zai tsaya har a ce ya yi tuwon dare. Shekaru wajen biyu kenan Alhajinmu ya ce aikin gidan da ya dawo kanmu ni da Rahila da Ma'u tun da alokacin mu ne ƴan matan gidan muna cikin shekaru na sha tara ne kuma muna zangon karatu na ƙarshe a matakin babban sakandiri a makarantar GGSS ƘAWAJI dake kwanar dakata a jihar kano.
Yaya Balki ma ta yi aure shekaru wajen huɗu da suka gabata. Yanzu a gidan daga mu sai Datti da ke ajin ƙarshe a ƙaramar sakandiri sai Amina dake ƙokarin shiga matakin farko a babban sakandiri. Sai Yaya Muntari da ya dawo gidanmu da zama shekaru uku yana karatu anan FEC KANO. Sai Hajiya Dubu da Alhajinmu ya ɗauko ta bayan mun tare a sabon gidanmu dake Ɗorayi.
Domin Alhajinmu tuni likafa ta cigaba ya koma aiki da Hukumar KEDCO na jihar Kano.
Sai Yaya Abubakar da ke karatu a jami'ar Bayero yana karantar Vitnary ya na shekara ta uku ne. Sun ɗaɗe a gida shi da Yaya Hamza kafim su samu su ci jarabawar babbar sakandiri a lokacin samun jami'ar ba ta wahala cin jarabawar sakandiri ne mai wahala wajen sau uku suna sake rubutawa sannan suka ci. Shi sai ya zauna a gida nan kano shi kuma Yaya Hamza sai ya lula Sokoto Usman ɗanFodiyo University Udus. Acan ya ke karantar accounting shima yana shekara ta huɗu ne. Yaya Auwal kuma yana Nasara state University Keffi. A shekaran nan ya tafi shima.
Mun zama ƴan mata duk wani tantanin budurci ya gama bayyana mana. Alhajinmu yana da burin in mun gama sakandiri mu yi aure. Ban san dai tunanin sauran ba amman ni ba ni da burin aure yanzu sai na gama jami'a na samu aiki saboda a lokacin Alhajinmu ya samu ƙarin girma manaja ne a hukumar wutar lantarki ta jihar kaduna kuma ya samu daman ƙaro karatu tun a zamanin baya. Ni ma sai na ji ina sha'awar haka. Rahila dai na san cewa ba ta da ra'ayi mai zurfi kamar nawa, Ma'u kuma har gobe ba jituwa a tsakanimu shi ya sa ni ban san me take ciki ba. Amman shekarun sun tura da ya sa na ƙara aminta da zargina na cewa Tana son Yaya Hamza shi kuma ba ta gabansa duka ɗaya ya ke ɗaukan mu. Shi kuma Yaya Abubakar a yanayin yadda ya ke kafa kafa da Ma'u son ta yake yi ita kuma baya gabanta ni dai ina gefe ina kallon komai ina tunanin ta yadda Ma'u za ta ɓullo ma lamarin ƴan'uwa guda biyu. Amman na ci alwashin ba zan bari ta zo gidanmu ta raba mana kan yan'uwa ba na san halinta ba ta da kirki kanta kawai ta sani.
A yadda muka taso a haka muka girma. Ni da Rahila mune masu tsawon. Sai dai muna da bambamcin jiki ita Rahila ta fi ni kiɓa. Ma'u kuma muna da yanayin jiki bamu da kiɓa amman ita ba ta kai mu tsawo ba ta ɗauko tsawon mahaifiyarta ne Baaba dake can kura ta hayyaffa da wasu ƴaƴan bayan Ma'u. Amman kuma duk wanda ya ganmu ya san mu ɗin jini ɗaya ne. Ballatana ni ban cika yawo da Ma'u ba sai dai makaranta in ya zama dole a gida kuma ta shafa mini lafiya saboda ba na ƙyaleta. Sannan dawowar Hajiya Dubu gidanmu ya sa ba ma wanda ya isa ya taɓa ita da Yaya Abubakar sun sha artabu a kaina. Tun kuma da Hajiya ta dawo gidanmu na tattara kayana na koma ɗakin ta can na ke kwana sai in har na ga dama ne nake shiga ɗakin mu duk saboda kar na haɗu da Ma'u za mu kwana gida ɗaya mu tashi amman ba za mu yi ma juna mgana ba. In ko faɗa ya haɗa mu in na fara gaba da ita sai mu yi wata ba mu yi mgana ba sai in Rahila ta gaji ta kai ƙarar mu wajen Alhajinmu in ya yi mgana sai Ma'u ta ce in ta yi mini mgana ba na tanka ta. Sai a ɗora laifin a kaina amman thank god Hajiya na nan ita ce ke zama justice ɗina in dai akan Ma'u ne.
Bangaren Yaya Murja ma ba ta sauya zani ba. Ko bayan auran ta in dai za ta zo gidan da abun arziƙin da za ta kawo ma Ma'u da Rahila har da Amina ni kuma sai ta ce ba ni da kunya. Ni ma da na gane ko gidan zan iya kirga zuwana, na fi zuwa gidan Yaya Aina ko Yaya Balki in ma fitan ya kamani kenan. Har a lokacin ba ni da wata kawa da zan iya nunawa amman Rahila da Ma'u suna da ƙawayen su. Barin ma Ma'u ƙawarta din nan Shema'u har lokacin suna tare su Gwaggo duk sun santa ta na zuwa nan gida itama Ma'un ta na zuwa gidan su saboda su haɗu da Ma'u su yi ta munafunci har can dakata tare suke a makaranta. Ni dai kamar yadda ban son Ma'u itama Shema'u ban ƙaunarta domin gabaɗaya halin su ɗaya. Za mu haɗu sau goma a makaranta sannu ba ta haɗamu da Shema'u amman in ta zo gida tana mini fara'a kamar ta Allah. Na daɗe da yarda da mganar hausawa da suka ce sai hali yazo ɗaya ake abota. To akwai mugayen hallayar Shema'u da Ma'u da suke kamamceceniya.
****
Mama ta shiga madafi ta ga na ɗora miya tana tafasa ko ƙashin miyan ma da Muntari ya shigo da shi ban saka ba sannan ban ko ɗora tuwo ba. Ba ta yi mamaki ba sanin halina sai ta fito tana faɗin" Sadiya me take son zama ne ni Rukayya?
Gwaggo na zaune ta ce"Me ya faru hala?
Sai ta kaɗa kai tana nufar ɗakin mu kafin ta ce" Ba ta ko ɗora tuwo ba. Kuma miya na ta dahuwa ko ƙashin da muntari ya shigo da shi ba ta saka ba."
Lokacin ta ɗaga labulen ɗakin tana kwala min kira ina daga ɗakin Hajiya har na fara barci.
"Ba ta fa a ɗakin"
Hajiya hankalinta na wajen jin radiyonta ba ta ma jin su. Gwaggo ce ta leƙo dakin Hajiya ta na kiran sunana na ji har gyara kwanciya na yi. Ban ankara ba sai ji na yi an ɗaka mini duka a cinyata da sauri na miƙe ina sosa wajen sai na ga Mama tsaye a kaina tana huci.
Cikin tura baki na ce"Kai Mama a cinya fa kika dake ni."
"In ba ki tashi ba sai na mare ki a fuska yanzu."
Ina jin haka na yi saurin saukowa daga gadon saboda na san halinta tana da saurin hannu. Ina fitowa na ga har mangriba ta yi Gwaggo ta kalleni ta na faɗin" Sadiya ho. Ke ko koyi da ƴan'uwanki ba kya yi. Su in dai suna da aiki akan lokaci suke gamawa."
Haushin aikin dake gabana ya sa ban ko