Showing 90001 words to 93000 words out of 121577 words
ji daɗi a gidan mijinsu sannan kar su zama masu faɗi a cika a dangi amman ita gashi tana yarda ta ga dama.
Ma'u ta karrama mu ba zan raina mata ba. Shema'u sune yan gaba gaba Ma'u mijinta ne babba a maza duk da ya na da yaya mace, amman itama Anty Ma'u sama Anty Ma'u ƙasa sai abin da ta ce. Ina ta mamakin ina abokiyar zamanta Hajiya Zainab? Sai can na ganta ta ci kwalliyarta da kin ganta kin ga wacce ta gaji arziƙi ba haye ba. Ita ba ruwanta gaskiya ba ta son hayaniya ma Ma'u kuma da ya ke yar bariki ne duk ta siye dangin Alhajin da siyasar ta.
Yaya Murja sai da ta yada mini mganar wai sai yanzu na zo biki da rana. Ni ko na ce Yallabai na gida tare muka zo dashi shima ya zo ɗaurin aure.
Shema'u kuma ba ta mini magana ba ta yi wani ɗan iskan ɗinki duk ya kama jikinta fuska da jiki sun sha mai ta yi wani fayau saboda in rama wulakancin da ta mini sai da na bari ta shigo ɗakin da aka saukemu sannan na kalleta ina faɗin
"Shema'u ranar da muka sauke ki a gidan Nene Tariq ke faɗin wai kin karɓi lambar wayar Uncle Abba."
Ba ita kaɗai ba gabaɗaya waɗanda ke wajen sai da suka kalleni daman na yi alƙwarin yadda ta yi min cin mutumci a gidan Rahila sai na rama.
Ina mirmishi na ce" Wai kin roɗa ne? To gwara ma ki bi wani sarki shi Uncle Abba mata har ƴayan sarakuna daga Rano an yi masa talla bai ɗaga kai ba ballanta ke, na san dai zuwa yanzu kin ma san ya fi karfinki tunda lambar wayar ma ba tashi ya baki ta Tariq ne."
Ƙur ta yi min da ido, ni kuma sai na gauraye fuskata da mirmishi Rahila na ta mini sigina na yi kamar ban gani ba har Yaya Murja mai baki ta kasa mgana.
Shema'u kuma dakyar ta iya yaƙe kafin ta ce" Oh. Wannan daman na karɓi lambarsa ne saboda na ga ya yi min kama da wani sai daga baya na gane bashi ba ne, ni fa Sadiya ɗan'uwan mijinki ya yi mini tsufa kaf ma a dangin sa ba wanda zai iya dai dai da Shema'u.'
Ta faɗa cikin danne yanayinta ina dage mata gira na ce"Da gaske?
Cikin renin wayau Anty Aina ce ta yi mgana.
"Sadiya ki bar mganar don Allah."
Sai na yi dariya kafin na ce" An barta."
Shema'u na yaƙe ta fice amman ni kaina na san ta ji abin da ake ji in ka tozarta wani a cikin jama'a sai da ta fita Yaya Balki ta ce ya aka yi ne na gyara zama ina faɗa musu yadda aka ƙare.
Yaya Balki na dariya ta ce" Wannan akwai ɗan jaka da rabi. Zai haɗa fada."
Ina dariya na ce" Kaɗan daga aikin Uncle Abba kenan."
Rahila ta ce ta gane shi ta taɓa ganin shi a gidana Yaya Murja ba ta ce komai ba sai daga baya ta ce" Ko ma dai menene ba kyau cin fuska a cikin jama'a."
Kai tsaye na ce" Ba cin fuska ba ne. Ai naga nan duk ɗayan ne ko?
Ta kalleni na kalleta sai kuma ba ta ƙara mgana ba. Ma'u ba ta ɗakin amman na san za ta ji labari Zaituna kam duk muna tare da ita amman ta ci abinci har da guzurin alale, ni da mangariba muka tafi ni da Rahila da Zaituna Yaya Murja ta ce sai ta kai Amarya amma Yaya Aina da Yaya Balki ban ji suna zencen ba amman dai can muka bar su.
Na dawo gida da Waina da sinasir Ma'u ta matsa dukkanmu sai da muka taho dashi
Shi na ci na sha ruwa tunda mai siga ne sai dare Yallaɓai ya je ya ɗauko su Jidda suka dawo gida.
Su sun ci abinci Yallaɓai ne na dafa ma Indomie da ruwan tea ya ci kafin ya kwanta.
Washegari Lahadi da asuban fari sai ga wayar Tariq Allah ya yi ma mijin Gimbiya rasuwa.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Eaman ScholarSphere.
Where ideas Take Shape.
WHAT WE DO.
ASSIGNMENT
PRESENTATIONS.
ARTICLES
PROJECTS.
BOOK
AND MANY MORE.
CANTACT US THROUGH.
02347067793152
MOTTO:
"Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures"
*🅿️16*
Mutuwa ɗaya ce haƙiƙa na tausaya mata ganin ko shekara biyu ba ta rufe da auran ba. Yallaɓai a ranar suka tafi Abuja tare da Uncle Abba da Nene, da Anty Maimuna Anty Bahijja za ta taho daga baya. Sai Hajiya iya Maman farko kaɗai aka bari a gida.
Can suka kwana Tariq da Farida daga kaduna suka tafi. Ni kuma ranar litini na je ganin likita sai ranar na je lab na karɓo sakamakon test ɗina na kai mata shima ta ce lafiya lau ba wata matsala. Sai muka je matakin gaba na A transvaginal ultrasound.
Ta ba ni nan da kwana shidda na dawo.
A ranar su Yallaɓai suka dawo daga Abuja kwanan su ɗaya amman an bar Anty Maimuna acan tare da Nene da Hajiya Kaltume sai an yi uku za ta dawo.
Ranar talata muka je Abuja gaisuwa. Ni da Hauwa da Munnira sai Jamila da Hindatu, Hafsat daman ta na can Abujan ne, sai Mimisco da direbanta ne ma ya tuƙa mu.
Mun iske gidan Gimbiya cike da yan uwa da abokan arziƙi. Kaf yayyenta mata da matan mazan suna nan, Hajiya kaltume da Nene ne tare da ita a matsayinsu na manya. Har Sameena a can na ganta ta ce tun ranar da da aka yi rasuwar ta zo sai an yi bakwai za ta koma.
Tariq ma na nan shi da Farida da yara. Amman dai shi ya ce min da zaran an yi sadakar uku zai koma gida.
Ba Gimbiya ke bin Tariq ba akwai wata mace sannan ita a shekaru ba za ta gaza 33 ba ko na girmeta bai wuce da shekara ɗaya ba.
Lokacin da nake yi mata gaisuwa ta yi matuƙar ba ni tausauyi ta yi kuka idanuwanta sun shige ciki, ba ta mgana sai dai ɗaga kai ba ta ci ba ta sha sai an yi da gaske ta ke tsakura da kuma ta ci sai ta amayar dashi. Ta rame sai farin fata da dogon hanci gabaɗaya sai ta bani tausayi har araina ina yi mata addu'an Allah ya ba ta dangana.
A bakin Sameena na ke jin Alhajin na gidanta ne lokacin da ciwon shi ya tashi. Ashe yana da ciwon hanta a Egypt ya ke ganin likita a daran su ka kai shi babba asibiti a nan Abuja da niyyar kafin a fita dashi waje, da asuban ranar Allah ya yi masa rasuwa.
Allahu akbar. Allah ka sa mu yi kyakyawan karshe.
Mun je gidajen duka matan shi mun yi musu gaisuwa tun da dukkansu suna anguwa ɗaya ne asokoro. Kuma gidajen su ba nisa bai wuce ka ga gida uku a tsakani ba. Yana da manyan ƴaƴa ba shi da ƙananu da Gimbiya ta haihu ne zai iya samun yara. Ba kuma yaro ba ne don ko da ta aure shi ya yi shekara 60 Allah na tuba a lokacin har ina ma Hauwa gulma me za ta yi da tsoho mai mata da ƴaƴa haka? Ashe zaman ma ba mai tsaho ba ne.
Duk da na zo garin da Yaya Auwal ya ke ban je ba. Saboda gaisuwa muka zo kar a ce daga zuwa ina yawo. Sai dai na kira Lailan na faɗa mata mun shigo garin, sai ta ce in da sarari za ta shigo ta yi musu gaisuwa.
Yallaɓai na bari, a gida shi da yara amma mun yi mgana ya ce gobe ranar uku za su dawo sai na ce kawai in sun dawo daga makaranta ya faɗa ma Salisu ya kai su gidan Rahila tunda ya ce za su kwana washegari sai a haɗu gabaɗaya a koma kano.
Shi ya sa na kira Rahila na ce, za a kawo mata su Jidda su kwana a wajenta kafin mu dawo tun da Salisu ya san gidanta. Saude kuma Yallaɓai baya nan ban taɓa kwatantan barin ta ita kaɗai da yara a gida ba.
Duk anan gidan Gimbiyar muka kwana. Abinci sai dai a kawo shi a dafen shi komai ga shi. Saboda ya na da kuɗi dan kwangila ne ya tara abin duniya kuma a baya ya yi siyasa.
Washegari ranar da aka yi sadakar uku da wuri su Yallaɓai suka iso shi da Uncle Abba da su Kawu Sa'adu sai Anty Bahijja. har cikin gida kuma sun shigo an yi ma juna gaisuwa.
Ni ina can ɗakin da muka kwana ba mu haɗu ba sai can yamma ma. Mun dai yi mgana ta waya da daddare kuma sun ƙara shigowa, a bakin Munnira na ji ta na faɗin wai Tafida ne ma ya matsa ma Gimbiya da lallashi har ta amince ta sha tee ɗin da yawa kuma sannan sai yau aka ji ta taɓa buɗe baki ta yi mgana amman ga Tafida kaɗai. Ban yi mamaki ba sanin shaƙuwarsu kuma a lokacin ai abar tausayi ce.
Washegari muka dawo kano amma mun bar Nene a can ita da Hajiya Kaltume da sauran ƴan uwanta. Mota ɗaya muka shiga da Anty Bahijja na ji suna mgana da Mimisco da cewa wai Gimbiya ba ta mgana da kowa sai Tafida sannan shi kaɗai ke ba ta abu ta karɓa ta sha. Su Nene haka suke yi kamar za su ari baki amman ba ta cin komai ba ta mgana sai kuka.
Anty Bahijja ta ƙare maganar ta da cewa" Ga shi kuma kin ga ba gari ɗaya ba. Balle a ce ko da yaushe ya riƙa zuwa ya na matsa mata ta ci abinci"
Ina kujeran zama ta tsakiya saboda motar irin babba ce ta yara ta mijin Mimisco ne.
Ni da Hauwa muna zaune waje ɗaya har muna haɗa ido muka kalli juna amman ba mu yi mgana ba.
"Ba matsala ba ne. Jiya mun yi mgana Hajiya ana tunanin da an yi arba'in Gimbiya za ta koma Rano."
In ji Mimisco sai Anty Bahijja ta ce" Ai ya ma fi sauƙi. Allah dai ya ba ta dangana baiwar Allah."
Mimisco ta amsa da Amin.sai ita Anty Bahijja ta ƙara da cewa" To Nene fa? Ko itama tare da Hajiya Kaltumen za su zauna har arba'in ɗin?
Sai ta yi shuru kafin ta ce" In za ta iya sai ta zauna. Tunda na taho mata da magungunanta da ta manta. Gida daman ba wani abu take yi ba."
Muna jin su suna ta tattaunawarsu har muka iso kano. Da ya ke mun iso da wuri Yallaɓai suna baya mun riga su yo gaba gaskiya. A bakin hanya na ce su sauke ni na samu adaidaita zuwa gida.
Sai da na isa gidana na yi salla na dafa indomie na ci sannan na dawo hayyacina. Sannan na kira Yallaɓai sai ya ce min suma sun kusa ƙarisowa, sai na ce ya kira Salisu ya faɗa masa in ya dauko su Jidda daga makaranta gida zai kawo su na dawo sai ya ce to.
Ni kuma sai na kira Rahila na ce mata na dawo sai ta ƙara min gaisuwa ni kuma na yi mata godiya har ta na cewa" Uban godiya ke fa ba ki da hali wani lokaci."
Daga nan ta kashe wayarta ta bar ni ina dariya.
Bayan Rahila da Laila ba wanda na faɗa ma an yi ma su Yallaɓai rasuwa sai gashi kwana ɗaya tsakani da dawowarmu daga Abuja a group gidanmu na ga Yaya Balki na yi min gaisuwa da na tamnbayi in da suka ji sai ta ce Yaya Murja ta faɗa mata da ta je gidanta itama ta ce Ma'u ce ta faɗa mata.
Abin sai ya bani mamaki na ga ni dai ba tamin gaisuwa ba. Amman ta je tana faɗa, ban yi mamaki ba tunda tana tare da Anty Bahijja ta kuma yarda da ita shi ya sa wasu labaran na dangin mijina kafin ni na kai ga furta ma wani Ma'u ta yaɗa shi a gari. Tsaki na yi a fili kafin na ce" Wannan ai gwara ta kashe auran nata ta auri Nasir ko Musabahu da wannan bin diddigin na ta."
A daren kuma sai ga ta ita da Alhajinta wai sun zo ma Yallaɓai gaisuwa. Kuma abin da ya ɓata mini rai shi Alhajin ya kira Yallaɓai ya faɗa masa za su zo amman Ma'u ba ta kirani ba, shima Yallaban ya kira wayata bai samu ba ƙwatsam na gansu lokacin shi bai ma riga ya dawo gidan ba.
Da ɗan fara'ata na karɓe su. Bayan mun gaisa sun yi mini gaisuwa sai na ce ai Yallaɓan bai dawo ba sai ya ce ai sun yi mgana dashi ya na kan hanya. Kafin ya ƙariso na kawo muusu ruwa da lemu na yi shinkafa da miya na kawo musu suka ce sun ƙoshi sai da suka ci abinci sannan suka fito daga gida.
Ba ko daɗewa sai ga shi ya iso. Saboda mu ba su waje sai na ja Ma'u zuwa falon na biyu na kora su Jidda ɗakin su bayan sun gaida Ma'u ta amsa cikin fara'anta har tana faɗin" Jidda idon ki kenan? Ina nan dai ina jiran ki a wannan hutun."
Sai Jidda ta fara kallo na, sai na yi saurin cewa" A'a ni ba ruwana ki tambayi babanki in ya barki in an yi hutu sai ki je."
Da sauri Ma'u ta ce" Ai ni dai na san Yallaɓai ba zai hana ba."
Sai kawai na ɗan yi yake. Muna zaune ba mgana sai baɓatun talabijin.
"Ashe kin je Abujan kema?
"Uhm"
Na faɗa ina kauda kaina ba na son kallon Ma'u saboda kallonta ba alheri a cikin yanayin kallon ta.
"Allah ya jikan sa."
Na amsa da Amin shuru na wani lokaci sannan ta ce" Allah sarki ta ba ni tausayi rashin miji ba daɗi."
"Ai fa kam."
Na faɗa ban bama mganar muhimmamci ba.
"Allah ya kawo mata kyakyawan zaɓi."
Na amsa da Amin na ɗauka daga nan maaganar za ta tsaya sai kawai na ji tana faɗin.
"Anty Bahijja na gaya mini halin da ta ke ciki kamar in yi mata kuka ta ce mini ba ta cin abinci sai kuka ba ta kuma mgana da kowa sai Yallaɓan ki"
Kure ta da ido na yi domin na san daman sai ta zo wannan gabar."
"Ta ce min shi kaɗai ke iya cewa ta ci abinci ta ci kuma shi kaɗai take yi ma mgana. Abun mamaki ko da ya ke na ji labarin an ce daman sun shaku da juna."
Ta fada tana mini mirmishi.
"Haka na ji."
Nima sai na ba ta amsa amman ban nuna wani abu daga saman fuskata ba."
"Allah sarki. To bakomai tunda na ji Anty Bahijja na faɗin ana arba'in za a dawo da ita Rano Sai na ce ai ko ga shi kusa ina Rano ina Kano? Yallaɓai sai ya riƙa zuwa yana kula da ita baiwar Allah abin tausayi.'
Ta gama faɗa har tana bayyana jimamin a saman fuskarta.
Ni na san da biyu ta yi wannan maganar sai kawai na yi mata mirmishi kafin na ce" Gaskiya ne. "
Sai na datse bakina ban kara yin mgana ba amman ina kallonta ta gefen ido tana mirmishi kafa ɗaya ta ɗora kan ɗaya kamar falon gidan Alhajin na ta ne.
Yadda ta ga na haɗe rai ina duba wayata ya sa ba ta ƙara mgana ba. Ba daɗewa ma sai ga shi Yallaɓai ya leƙo ya ce Ma'u ta fito za su wuce tsabar haushi iyakata a bakin kofa ban fita haraba ba Yallaɓai ne ya fita ba su shigo da mota ba sun yi parking daga waje ne.
Kamar maganar Ma'u ba za ta dame ni ba, sai gashi kuma tana sukan raina ace wai komai ya faru a dangin mijina sai Ma'u ta sani in na ji haushinta ta wani fannin kuma ban ganin laifinta ba kowa ya ba ta dama ba sai yayar Mijina. Ta kuma wani bangaren itama Anty Bahijja sai na ke yi mata uzuri saboda in dai Ma'un da na sani ne makircinta zai iya siya mata kowa da kuma wannan makircin ta siye Anty Bahijja. Renin na ta har ya yi yawan da za ta zo har gidana tana gaya min mgana na ci ji yatsa da na ƙyaleta amman dai na san za ta ƙara wata rana dole za mu haɗu.
Washegari na koma asibitin domin ganin likita. Wannan karon ma Dr Aisha ta ce vaginal ɗina komai lafiya lau sai matakin gaba na A hysterosalpingogram a type of X RAY, that allows your provider to see your uterus and follopian tubes. Dr Aisha ta faɗa mini scan ɗin is very painfull tunda na cikin mahaifa ne. Ta gaya mini zan iya bucking anan asibitin ko mu fita waje, da na kira Yallaɓai sai ya ce kawai na yi bucking anan asibitin, ban dawo gida ba sai da na yi bucking sun ba ni sati ɗaya na dawo su yi min scan ɗin. Ban damu da wahala ko wani abu ba babban burina na kai ga matakin nasarata shine a gabana.
******
BAYAN SATI UKU.
Bayan sati da huɗu rasuwar mijin Gimbiya a lissafi kuma bai fi saura kwana biyu ya yi arba'in da rasuwa ba.
Kuma har alokacin Nene da Hajiya Kaltume ke zaune da ita sai dai yan'uwa da ba su samu zuwa ba sukan je domin yi mata gaisuwa.
Har na ji Yallaɓai suna mgana da Mimisco akan a cikin satin su Nene za su dawo da Gimbiya gida.
A cikin sati ukun da suka gabata lamarin Gimbiya ya fara ba ni mamaki har na fara tunanin ko ba ta da tawakalli ne kuma har sai da na furta ma Yallaɓai har ya ji haushina. Haba abun nata ya yi yawa ba kanta farau rashin miji ba Allah na tuba sauran matan shi da suka yi shekaru aru aru da shi ma sun ɗau dangana haka