Showing 51001 words to 54000 words out of 121577 words
na kiran suma yan'uwan na ki ki yi musu usuri sun shiga ɗimuwa"
Sai ban ce komai ba amman a raina na ce a dimuwan aka kira wanda ake so.
Ba bari a shiga in da Alhajinmu ya ke Yaya Abubakar ne kaɗai da su Ya Muntari ke zirga zirga. Zama na yi kusa da Gwaggo ba wacce ma na kallah balle in yi mata sannu har Yaya Abubakar ban gaisar ba sabida ya bani haushi har da ya ganni ya na ce min" Ke sai yanzu kika iso?
Cikin gatse na ce" E. Sai yanzu aka faɗa mini"
Hankalinsa ya yi can bai ma jini ba Rahila ce ta zo ta zauna kusa da ni muka gaisa
Yadda ta ga na haɗe rai ne ya sa ba ta jani da magana ba.
"Hala Yallabai baya nan ne?
Kai tsaye na ce"Lokacin da na ji labarin abin da ke faruwa ya fita"
Sai ta yi shuru kafin can ta ce"Ki yi hankuri ni kaina hankalina ya tashi na manta da kiran ki."
Wani kallo na yi mata amman ban iya mgana ba.
Muna nan zaune jugum jugun har wajen azahar sai da aka cire ma Alhajimmu iskar Numfashi tun da sun ce numfashinsa ya daidai ta. Sannan suka maida shi ɗaki na musamman da Mijin Ma'u ya biya duk na ji Yaya Abubakar na faɗin Yaya Hamza ya turo kuɗi shi da Yaya Auwal amman kuma mijin Ma'u ya biya komai. Ina kallo suna ta yi masa godiya su Yaya Murja har tana faɗin" Allah ya saka masa da alheri ba domin alherin Ma'u a gare shi ba yaushe har zai riƙa yi mana Hidima haka? Ma'u ƙi kara yi masa godiya kin ji ko"
Sai ta amsa da toh kawai. Ban yi wani mamaki ba sanin halin su balle Yaya Murja akwai son abin duniya ita kuma Ma'u in ta fahimceka ta san yadda za ta riƙe sosai.
Sai bayan an kai shi ɗaki na musamman ne aka bar mu muka shiga yana barci amman Alhajinmu duk ya rame ya faɗa. Daga gani ya daɗe da ciwo a jiki bai faɗa ba an ce mu bar shi ya samu hutu sosai sai muka fito dukkanmu zuwa kofar ɗakin muka zauna saman kujerun wajen. Mijin Ma'u ya yi ma Gwaggo sallama zai tafi ita kuma ta tafi raka shi.
Sai bayan sun wuce ne Ya Balki ta kalleni taba faɗin" Sadiya ya gida? Ɗazu kin zo hankula ba a kwance suke ba ba a gaisa ba."
Sai na ɗan saki fuska muka gaisa buɗe bakin Yaya Murja sai cewa ta yi" Duk da haka ta ganmu amman ta fi ƙarfin ta ce mana sannu."
Nima sai na kalleta kafin na ce"Saboda me zan ce muku sannu? Kun ware ni a cikin dangi ba wacce ta iya kirana ta faɗa mini halin da ake ciki sai Ya Auwal dake Abuja ne ya kirani ya faɗa mini. "
Yaya Balki ta ce"E ba a kyauta ba to ki yi hakuri. Nima Ma'u ce ta kirani ta faɗa mini ta ce itama Yaya Murja ce ta faɗa mata.'
Shekeƙe na kalle su kafin na taɓe ba ki na ce"Ai da ya ke Ma'u ce ake son ta sani an kirata an faɗa mata ba shikenan ba."
Rahila na taka min kafa wai in yi shuru cikin masifa na ce"Sai kin ƙi faɗan gaskiya! Wa na ke tsoro?
Gwaggo ba ta nan ta na ciki wajen Alhajinmu.
Ya Muntari ne a wajen ya kirana sunana ya na faɗin" Asibiti ne fa nan ba gidan biki ba. Ku bari ku koma gida mana."
Yaya Murja kuma sai ta taɓe baki ta ce"To daman ai mun san baki tsoron kowa mara kunya. Hassada ce da kishi saboda ta ga Ma'u ta riga ta zuwa. An ce ki yi hakuri kuma sai ki na neman gaya mana mgana"
Anty Aina ta tsawatar ta ce a bar mganar ni ko ba na barin ta kwana na ce"Allah ya tsari Sadiya me Ma'u ta mallaka a duniya nan da ni ban da shi sai na yi mata Hassada! Ai ba ta kai ba tukunna dai."
"Zan fa ci ubanki Sadiya ni ba tsaran ki ba ne wallahi."
Zan sake mgana Anty Aina ta daka min tsawa ta na faɗa min" Wai ba na ce ki yi shuru ba ne Sadiya?
Kaina na kawar gefe ina kaɗa kafata cikin bacin rai. Yaya Balki ta ce"Ita Yaya Murja saurun fusata ita kuma Sadiya rashin kunya. Alhajinmu na kwance ba lafiya ma ba za su fasa ba."
"Ba za su fasa ? Me ya faru?
Yaya Abubakar ya faɗa yana ƙariso wajen tare da Ma'u sun jero
Ba wanda ya yi mgana sai Zaituna.
"Sadiya ce da Anty Murja suke cacan baki."
Yaya Abubakar ya kalleni ya kalleta kafin ya ce" Me ya faru?
Anty Balki ce ta maida masa yadda aka yi kawai sai ya juyo yana kallona kafin ya ce" Ni ne nan na kira Murja na faɗa mata na kuma ce ta kira Ma'u da sauran ta faɗa musu. Tun da sun ce ki yi hakuri sun yi kuskure ba shike nan ba? Ko ke shikenan ba a baki hakuri ki hakura?
Ko kallonshi ban yi ba sai da na ji ya ce"To kar ma ki fasa. Ke daman ba ki son zaman lafiya ko da yaushe cikin ƙananun mganganu kike."
Ɗagowa na yi ina kallonsa cikin ɓacin ran dake cikin idanuwana shi kuma sai ya juya yana ma Ya Muntari mgana.
"Ka na ji suna hayaniya ba ka tsawarta musu ba?
Kai tsaye ya ce" Na yi mgana sun ki ji shi ya sa na kyale su. "
Kawai sai ya juya ya na kallona kafin ya ce" Duk wacce ta san hayaniya ya kawota ta tashi ta ƙara gaba. Mu lafiyan mahaifimmu muke nema ba tashin hankali ba."
"Ka yi hakuri ya Abubakar. Sadiya kema don Allah ki yi hakuri. Har ni na kira wayarki ba ta shiga."
Ma'u ta katse surutun na shi.
"To kin ji ma."
Ya faɗa ya na kallona dakyar na iya danne ɓacin raina na kalli Ma'u ina faɗin" Ya wuce."
Sai ta yi mini mirmishi na mayar mata da yake. Kusa damu ta zauna amman gefen Rahila. Shuru kawai na yi ina danne yanayina ni fa daman da Yaya Murja da Yaya Abubakar haushin su na ke ji tun kan abin da ya faru. Kuma har gobe na san suna bayan Ma'u ne. In da suka ijiyeni nima nan na ijiye su.
Kiran wayar Yallaɓai ya sa na tashi na bar wajen.
Yana tambayanta ya jikin Alhajinmu na faɗa masa da sauki da yadda ake ciki.
"Allah ya ƙara sauki muna idar da sallar jumma'a zan taso kin ji ko? Ban da damuwa ok?
Sai na gyaɗa masa kai kafin ya cigaba da faɗin" Yara fa! Ina kika kai su?
"Suna gida tare da Saude."
Sai ya sauke numfashi kafin ya ce"Sai na dawo."
Da haka muka yi sallama. Ganin har azahar ta yi sai na fita haraban asibitin na tambayi wata nurse masallaci sai ta nuna mini. ga mata nan suna alwala mazan dai ina ga waje za su fita su samu sallar jumma'a nima sai na bi bayansu na yi alwala muka shiga masallaci na yi sallah na zauna ina addu'o'i bayan na shafa sai na kira wayar Amina sai ta ce minI ita Yaya Aina ta kira ta faɗa mata mijinta baya nan amman in ya dawo in sha Allahu suna tafe gobe na ce Allah ya kaimu.
Muna waya Khaleesat na kirana bayan na katse sai na kirata jikin Alhaji ta tambaya na ce da sauƙi ya na barci ita ke faɗa min suna hanya na yi musu fatan isowa lafiya. Na daɗe a masallaci sai da Rahila ta kirani ta ce ko na tafi ne? Na ce a" a ina masallaci.
"Oh mu ai nan muka yi tamu sallar. Ki zo ga su Baba Aminu nan sun iso."
Sai na ce mata gani nan zuwa. Ji fa har mutanen jihar katsina sun ji labari sun iso amman ni ana raina min wayau. Kuna ina da tabbacin cikin su ne wata ta kira su ta faɗa musu.
Na fito daga masallacin zan wuce bangaren dakin da Alhajimmu ya ke na ci karo da Baaba Asiya ta na ta neman ɗakin kamar ma ta na kiran waya ne ƙila Ma'u take kira sai na ƙarisa wajenta ina faɗin" Baaba."
Sai ta juyo ta na kallona fuskarta kadaha kadahan kamar yadda muka saba karɓan juna tun bayan faruwan rushewar auran Ma'u da Yaya Hamza da na zama ni ce sila."
"Yauwa. Ma'u bari ma ga Sadiya na gani."
Daga haka ta katse wayarta. Da yar jaka a hannunta da kayanta a ciki.
"Sannu da zuwa Baaba"
"Yauwa dai."
Sai na mika hannu zan karɓi jakar sai ta hanani ta wuce gaba tana faɗin" Ina ne ɗakin da aka kwantar da Yaya Sulen?
Ban damu ba na wuce ina faɗin" Ciki ne."
Ba tun yau ba ni na san ta tsane ni ita da yarta. To nima dai ɗin ba wani son su nake yi ba shi ya sa ban taɓa damuwa ba matar da na san ba ta ƙaunar uwata ina zan taɓa ganin farinta.
Ta bakin Hajiya Dubu da ke yawan faɗin" Asiya ki daina wannan dabi'un naki karki tsufa kuma tsufar ta zo ta yi miki gardama."
Allah ya jiƙan Hajiya Dubu da gafara. Mutuwarta da mutuwar Mama sai nima na mutu zan iya mantawa da su.
Muna tafe ina gaba ta na baya har zuwa ɗakin da Alhajinmu ya ke. Baba Aminu ne ashe da Baba Sani suka zo. Ma'u na ganin uwarta ta yi wajenta tana mata barka da zuwa.
Ban ƙara ta kan su ba na isa wajen su Baba Aminu ina gaishe su.
"Lafiya lau! Dubu ce?
Sai na ansa musu domin kaf gidan su Alhajinmu ba mai kiran sunansa sai dai Dubu saboda na ci sunan Hajiya Dubu ce kuma ita ɗin mai Daraja ce ta matsayin uwa a wajen su.
Da ɗaya da ɗaya likita ya ba su izinin shiga su ga Alhaji. Da suka fitio ne na ji Baaba na faɗin Yaya Sule ya ya ɗan farka yana ta mganganu har yana kiran sunan Ruƙayya
Gabana ya faɗi Mama kenan fa. Kar shima dai Alhaji tafiya zai yi ya bar mu? Likita ne ya ce daga yanzu ba wanda zai sake ganinsa sai dare a barshi ya huta.
Kowa ya ji labari amman ban da Datti na ce aƙyale shi saboda suna da test kar mu ɗaga masa hankali. Ma'u ta kira gida yar aikinta ta yo abinci direba ya kawo tare da Zainab. Dukkanmu ba wacce ta koma gida sai Zaituna da mijinta ya ce ta koma gida Gwaggo ma sai bayan la'asar da su Baba Aminu suka matsa sannan ta yarda Yaya Abubakar ya ɗauketa a mashin ɗinsa ta koma gida ta yi wanka sannan ta ɗauko ma Alhaji wasu kaya ruwan zafi da kayan Tea Ma'u ta saka an kawo. Abincin da ta kawo shi kowa ya ci amman ban da ni. Har su Baba Aminu shi suka ci Rahila ta ce ba zan ci ba na ce ta san ban iya cin wani abu a asibiti.
Wajajen biyar Yaya Hamza suka iso tare da Khaleesat da yayansu Amna da Tasleem. Ba daɗewa tsakani sai ga Yaya Auwal da Anty Laila suma sun iso asibtin diret ko gida ba su je ba sai da suka leƙa Alhajinmu suka ganshi sannan hankalinsu ya kwanta. Yaya Auwal yana zuwa ya ba da kuɗi aka siyo kata katan ɗin ruwa da lemuka. Ya yi kuma oder abinci na dare tunda muna nan ba wacce ta iya koma gida sai Gwaggo. Ita kuma a can gida Yaya Abubakar ya siya anta ya kai mata za ta dafa ma Alhaji tunda sun ce yana bukatar cin wani abu mai ruwa ruwa haka.
Yallaɓai na ji sa shuru har bayan mangariba sai da na kira sa ya ce bai dawo da wuri ba ne. Zai je gida ya yi wanka sai na ce ya taho da su Jidda tare da Saude asibitin ya amsa min da toh.
Gabaɗayanmu muna asibitin har sai da likita ya yi mana tsiyar Alhaji ba zai mutu ba zai ta shi mu je gida hakanan saboda sun ga zugan ne da yawa.
Tare da Alhaji Mustapha Yallabai suka shigo wajen da muka zazzaune. Kowanne da leda su Jidda na baya Yallaɓai dai kayan lambu ya siyo shi kuma mijin Ma'u ban sanin masa ba. Su dai an bar su sun shiga duba Alhaji ya farfaɗo da sauki wannan karon har sun gaisa ya ce ina yan matansa Yallaɓai ya ce suna waje suma sun zo duba megidansu.
Ganin ya farfaɗo da sauki sai likita ya ce mu shiga gabaɗaya mu duba shi amman da sharaɗin ban da hayaniya kuma muna dubashi mu fito mu tafi gida. Haka ko aka yi ɗaya bayan ɗaya muna ƙarisa gaban gadon shi muna gaishe shi yana amsawa ga jikokinshi kusa dashi Jidda har ta na bare masa ayaba ta nufi bakin shi tana cewa" Alhaji ga ayaba."
Aka saka dariya Baba Aminu na cewa" Ka ji min ja'ira tun ɗazu ta ganni amnan ba ta bare min ayaba sai Yaya Sule dake kwance rai ga hannun Allah."
Su dariya mu ma muna ta dariya Alhajinmu ya buɗe baki ta saka mai sai da ya haɗiye sannan ya ce"To ai ta ga duk yinii yau ina kwance ban ci abinci ba. duk ta fi min sauran matan nawa ita maimuna ban ma ganta ba "
Yana mgana sai ga Gwaggo ta shigo ta na faɗin" Gani nan na zo. Wace ce ta zo za ta yi min fashi miji."
"Gani nan. Tunda kin yi tafiyarki kin bar shi."
Jidda ta faɗa ta na mirmishi gabaɗaya aka kwashe da dariya ban da Baaba da ke wani taɓe baki kamar ta ga kashi.
Yaya Hamza ya ce" Ai sai ba ɗiyar Sadiya ba."
Anty Aina ta karɓe da faɗin" Ai Baby ce Sadiya sak. Jidda kuma Yallaɓai ce ba ta da hayaniya"
Likita ne ya zo ya ce dubiyar ta isa haka kowa ya fita shi ya sa muka yi ma Alhaji sallama muka fito. Khaleesat na haɗa da Saude tunda can gida za su kwana na ce su wuce mini da ita. Ina jin Ma'u na neman yan kwana a gidanta ba ta samu ba Anty laila yar kano ce amman nan gida ta ce min zata kwana Baaba dai ban sanin mata ba na dai ganta da yarta suna ƙuskus. Baba Aminu daman gida ne Baba Sani ne aka bari zai kwana da Alhajinmu Yaya Abubakar ya so ya je gida ya Huta ya ce miye amfanin shi? Shi zai zauna ya kwana har a sallami Alhaji.
Wajajen tara muka bar asibitin Gwaggo a motar Ya Auwal. Shi Yaya Abubakar ya ɗauki matarsa a mashin dinsa ita kuma Rahila ya Muntari shima yana da mashin Baaba kuma a motar mijin yarta ni kuma a motar Yallabai ni da Ya'yana.
Mun yi sallama gabaɗaya Yaya Murja ta riga tafiya daman da megidanta ya dawo suka tafi tare Anty Aina ma mijinta na da wata tsohuwar benz shi ya zo ya ɗauketa.
Sai goma saura muka shiga gida yunwa na ke ji ya sa Yallaɓai ya siya mini tsire a hanya da lemu sai ya siya biredin da zamu ƙarya da shi da safe in Allah ya kaimu.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SSADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
*🅿️10*
Tun da na tashi da safe na fara tunanin wani abinci zan dafa na kai ma Alhajinmu. Gashi kayan abincin mu duk sun ƙare kuma Yallaɓai har yanzu bai ce mini komai ba. Da safe ma Tea muka sha shima kayan tea ɗin saboda ya na yawan siyan shi ne ba sai ya ƙare ba shi ya sa shi ya kan zama na ƙarshen ƙarewa.
Na daɗe ina tunanin abin da zan yi. Kafin na tsaida shawara yin tuwon shinkafa miyar agushi tunda shinkafar tuwon kaɗai gare ni. Sannan ina da kayan miya nikaƙƙe a frizer sauran kayan cefanen ba zai gagara ba. Tun safe na kira wayar Ya Auwal mun yi mgana ya ce sun je ma asibitin sun duba Alhaji da safe jikin sa da sauƙi ya na ta barci sun ɗan dawo gida su karya ne sannan su koma ni ma na ce in na gama abin da na ke yi zamu zo asibiti tare da Yallaɓai in sha Allahu.
Yana falon farko ya na aiki na je na same shi na faɗa masa ina so zan yi ma Alhajinmu girki in za mu je mu tafin mai dashi.
"Me za ki dafa masa?
Ya faɗa ya na ture takardan gabansa lokaci ɗaya yana kallona.
Kai na rausaya kafin na ce" Tuwo zan yi masa miyar agushi. ".
Kai ya jinjina mini kafin ya ce" Kina buƙatar wani abu ne?
Kai na gyaɗa kafin na ce"E. Ina son Nama da ganda. Sai ganyen Ogun ina da sauran stock fish da agushi ɗin."
Sai ya gyaɗa min kai kafin ya ce" Shike nan. Zan yi ma Musbahu waya sai ya siyo ya taho dashi."
Duƙawa na yi na sumbaci bakinsa kafin na miƙe ina faɗin" A huta lafiya Yallaɓai na."
Kai ya jinjina min yana ɗan mirmishi fita na yi daga falon bayan na rufe masa ƙofar saboda zane ya ke yi ba ya son hayaniya ɗakin su jidda na shiga ba hasken sai da na kunna dukkansu suna kwance suna barci ga darduman da suka yi salla nan da azkar din su ko kwashewa Jidda ba su yi ba ban tashe su ganin yau asabar kuma suna hutun Tahfeez ya kamata su huta tattara kayan na yi na maida shi a muhallin shi sannan na gyara ma Baby kwanciya ita kuma Jidda na zare mata Hijabin jikinta ganin da shi ta kwanta. Sake kashe musu hasken ɗakin na yi bayan na rage musu iskar fankar a hankali na rufe ƙofar kar ƙara ya tashe su.
Tuwon na kunna gas na fara ɗorawa. Saboda ina so mu fita da wuri duk da za mu fara biyawa ta Gwammaja mu kai su Jidda sannan mu wuce asibitin. Ɗaki na koma ina gyarawa saboda Yallaɓai ya ce na haɗa kayanmu waje ɗaya mai wanki zai zo ya ɗauka sai na firfito da kayan ina haɗawa. Ni kaya ba su da yawa atamfofi ne da lesuna ƙananun kayana ni na ke wanke su da kaina in na