Showing 114001 words to 117000 words out of 121577 words

Chapter 39 - TURKEN GIDA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

22 Sep 2025

498

mu sannan har Datti a gida ya yi salla Alhajinmu ya ji daɗi bakin shi har kunnen gashi ga jikokinshi suna ta fira Gwaggo ma ta kasa zama sai ina za ta saka damu take yi.


*Janafty*
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Kz6koexT4Yj4o2zO4xVzrU

INA MATAN DA SUKA DADE SUNA NEMAN MAGANIN SANYI WATO INFECTION MAI KYU BASU SAMUBA, ANYI MAGANI ANYI MAGANI HAR ANGAJI, TOH KICE ALHAMDULILLAH, SABODA ALLAH YA HADAKI DA MAGANIN DA ZAI MAGANCE MIKI KO WANE IRIN CUTTAN SANYI WATO INFECTION DA YA KAMAKI CIKIN SATI GUDA DA YARDAN ALLAH. SHIGO GIDAN BUZAYE WAHALANKI TA YANKE HAJIYA💃💃

INA MAI NEMAN KAYAN GHARA ZAFAFA, MASU INGANCI, MASU KARFI, WANDA ZAI KANKARO MIKI MUTUNCINCI DA KIMARKI, WANDA ZASU DAWO DA HANKALIN ME GIDA GAREKI, SU SA YA MAKALE MIKI DA ZAZZAFAN SOYAYYANSHI, YA DINGA SAKE MIKI KI WARWASA YANDA KIKE SO💃💃 TO ER UWA SHIGO GIDAN BUZAYE KIGA IKON ALLAH DON KUWA ALLAH YA KAWO MIKI KARKEN MATSALANKI NA RASHIN DACEWA DABAKYAYI NA KAYAN GHARA😁💃💃 KUSHIGO GIDAN BUZAYE KU GYARA KUGA IKON ALLAH

*🅿️20*

Rahila ce jirgin danƙaro ita ce karshen zuwa har sai da na yi mata tsiyan tana kusa amma itace ƙarshen zuwa. Tana dariya ta ce
" Ni fa na ɗauka ni ce ma farkon zuwa kawai sai na ga gida ya cika." Muna ta mata dariya ni da Ya Balki.

Amina ta kira waya da ta ji gida cike kowa da kowa na nan kamar ta yi kuka ta ce ta yi missing. Ta so zuwa amma ba ta samu dama ba sai dai ta ce sallar layya in sha Allahu da ita za a yi.
Ya Auwal kuma ni na kira shi a waya ya ce sun ɗan fita da laila ne da yara gidan shuru sallar duk ba daɗi sai ya ce na kunna data ya kira Video call nan ne fa suka gaisa da kowa har da Gwaggo da Alhajinmu an kai musu sun yi mgana da juna.

Ya Hamza kuma na kira wayarsa ba ta shiga ba sai na kira na Khaleesat. Ita ke faɗin ya kwanta ashe bai jin daɗi zazzaɓi kuma ya hana a faɗa ma kowa. Muna cikin wayar ya tashi sai ta bashi wayar dukkanmu muka karɓa muka yi masa sannu da jiki ya ce ya ji sauƙi ya je asibiti maleria ne an yi masa allura kuma an bashi mganguna. Ba mu jima muna mgana da su ba tun da bai jin daɗi daga nan muka yi masa sallama da fatan samun lafiya. Datti dai za su fara jarabawa Jiya da yamma ya koma makaranta.

  Dukkan mu muna ɗakin Mama daman yawancin in dai mun zo gida mun fi zama ɗakin Mama. Gwaggo na ɗakin Alhajinmu suna ta fama da yara. Hira muke yi na can garin mu Yashe bayan sallar nan akwai bikin autar su Ya Muntari wato ɗiyar Baba Aminu kenan Yaya Aina ce ke mganar haɗa guddumuwa daman haka muke in sha'ani ya tashi sai mu haɗa kanmu kowa ta kawo abin da ta ke dashi mu haɗa mu ba ma Gwaggo ita kuma sai ta nuna ma Alhajinmu ya yi ta godiya kuma in sha'anin ya tashi ko ba dukkanmu. Yaya Murja da Yaya Balki suna zuwa ni ce ma ban cika zuwa ba sosai Rahila daman can ne tushen Mijinta tana yawan zuwa amma wannan karon tunda na ji bikin na ce sai na je Yashe na yi sati in sha Allahu tun da na daɗe ban je ba tun ina da cikin Baby da babbar ɗiyar Baba Sani ta rasu muka je gaisuwa kuma a ranar muka dawo ba mu kwana ba.

  Bikin bayan salla da sati uku ne. Yaya Aina ta ce ana jibi biki za mu tafi saboda Matar Baba Aminu magajiya mai yi ce ba ta wuce duk wani sha'anin mu ko ba ta zo ba ƙannen Yaya Muntari za su zo gaskiya tana da ƙoƙari daga ita har Baba Aminun suna da riƙo kan zumunci.
Muna cikin hiran ne Marwa ta shigo sai dai ta ce sannanun ku gabaɗaya a ka amsa mata in da na ke zaune ta nufa tana faɗin" Umma Baby ta jiƙa kayanta da ruwa."
(Daman Umma ta ke ce mini kamar yadda su Jidda ke kirana.)

Kai na jinjina kafin na ce" To ai sai ta zauna dashi. Domin ban zo mata da wasu kayan ba."
Da sauri ta ce" Gwaggo ta ce a cire rigar a shanya kar zazzaɓi ya kamata."
Kafin in yi mgana Rahila ta karɓe da cewa" To ba wasu kayan? In sanyi ya kamata fa"
Yaya Balki ce ta yi mgana wannan karon da cewa" Sadiya ce fa da tsiyarta. Ba za a rasa wasu kayan su Baby a gidan nan ba."

Yaya Murja na gefe ta ce" Ko ba na ta ba. Ba za a rasa kayan da za ta saka kafin na ta ya sha iska ba."
Muna cikin mganar Marwa ta fita sai ga Gwaggo ta leƙo ta na faɗin ita ta ce a cire mata rigar a shanya ta samu wata riga ta ba ma Marwa ta saka mata na amsa mata da to Gwaggo.
Yaya Balki ce ke mganar ta ga Marwa ta yi mata girma ne a ido ina mirmishi na ce" Ai na kusa yin suruki in sha Allahu."
Yaya Balki ta amsa da Allah ya sa.

"Aina can Marwa ta yi salla gidan Sadiya ne?

  Ya Murja ta faɗa ta na mai kallon Ya Aina wacce ta amsa da mata da cewa" E. Tun kafin ta dawo daga makaranta ta dame ni da ni Mama a gidan Umma Sadiya zan yi salla na ce to. Ta na dawowa ta gaya ma Baban shima yana dariya ya ce to yar gidan Umma Sadiya a dawo lafiya."
Ina mirmishin jin daɗi na ce" Ai wallahi na ji daɗin haka. Ni da za ku bar mini ita a wajena Ya Aina."

Yaya Balki na dariya ta ce" Topha ƴan mata ba su ishe ki ba ne Sadiya?
"Ina fa suka ishe ni. Ban ƙi dozin ba Yaya Balki."
Muka saka dariya gabaɗayanmu Rahila ce ta ce" Sai Ya Aina ta baki. Ki haɗa da Jidda ki riƙe gabaɗaya."
Ma'u na gefe ba ta ce komai ba ta na latsa wayarta. Ya Murja na sauraran mu amma ba ta yi mgana ba Ya Aina ke faɗin Marwa za ta fara pratical a asibti kuma babanta ba zai bari ba amma don ta riƙa zuwa miki  hutu lokaci bayan lokaci ba zai ce komai ba.

  na marairacewa na ce" Haba Ya Aina. In kika saka baki zai bari mana."
Dariya kawai ta yi ba tare da ta yi mgana ba Yaya Balki ce ke faɗin" Topha! Lalle lamarin Sadiya azimin ne.
"Da gaske take yi."
In ji Rahila ni kuma na juya ina rantse musu da gaske nake yi.

"To ke in kina son ɗauka shi Yallaɓan na ki na so ne?

Ya Murja ta faɗa tana kallona da sauri na ce" Haba Ya Murja na ɗauka ke mai shaidar Yallaɓai na ne. Ba Marwa ba ko wacce bai sani ba ne na kawo na ce ina so zan riƙe wallahi ba zai ce komai ba. Ballatana ma Marwa shi ya fara cewa ko za mu karɓo Marwa ne ta dawo wajen mu da zama Sadiya? Shi ya sa ma kika ji na yi mgana."

"Oh."

Kawai ta ce ba ta ƙara mgana ba. Yaya Balki ce ta karɓe mganar da cewa" Kuma fa hakane. Yallaɓan na ki ba shi da matsala gaskiya."
Rahila ma ta amsa da cewa" Shi da ke son yara. Allah ne dai bai bashi da yawa ba."
Ita dai Yaa Aina ba ta ce komai ba sai dai ta na ta mirmishi daga karshe ta kashe mganar da cewa babanta ba zai bari ba ni kuma na ce zan sako Yallaɓai a gaba mu zo tambaya Rahila na dariya ta ce" Shike nan ma an kashe boss ɗin."

Muna ta dariyan mu cikin nishaɗi. Daman fa ko haɗuwa aka yi waje ɗaya Ma'u da Ya Murja sun fi tsame kansu gefe ana hira sai jifa jifa suke saka baki tun ballatana ma in ina wajen. Ni kuma ban damu da su ba in suka sako ni na yi da su in ba su sako ni ba na juya na yi da waɗanda ke yi da ni. Zaitunan Yaya Abubakar tana ɗakin Gwaggo tun da ta zo sai barci kamar wata kasa Yaya Balki ta ce Allah ya sa ba ciki ne da ita ba Ma'u ta kwashe da dariya ta na faɗin" Kuma kamar kin san ta yi yaye ba."
Ya Aina ta ce" Kai wannan mata ta Abubakar. Allah ya sauwaƙe."

Ni kuma sai na kada baki na ce" Ku barta ta haihu. Iya rabon ta a duniya fa za ta haifa. "
Sai Rahila ta ce kuma gaskiya ne. Gwaggo ce ta leƙo ta ce an kira salla ga ƴayanmu can har sun yi alwala mu ma sai mu tashi jin haka yasa muka firfito domin yin alwala ni ban samu buta ba sai na zauna ina jira Anti ta gama da na ta butan ta bani sai da ta idar da alwalan sannan ta kawo min na amsa ina faɗin" Su Anti an zama yan mata."

Ta na dariya ta rufe fuska kafin ta ce" Anty Sadiya ina goron sallah na."
Kai tsaye na ce" Gorom sallah kike so?
Sai ta gyaɗa min kai. Ni kuma sai na rausayar da kai kafin na ce" Goron salla ai a gida ake ba da wa Anti. In kina son goron salla sai ki zo gidana ki karɓa. Yanzu ma kin makara salla ta wuce sai dai kuma ta layya in muna raye."

Ita Anti ba ta damu da mgana ta ba cikin dariya ta ce" Kai Anty Sadiya."
Nima ina mata dariyan na ce" Ƙwarai Anti. Salla layya in kina son goron salla ki zo gidana da wuri ni kuma sai na cika miki jaka da kuɗi."
Gwaggo na bakin famfo tana alwala ta na jin mu ta dai yi mirmishi ba ta saka mana baki ba.
"To Anty Sadiya in sha Allahu zan zo. Wannan salla a gidan Umma Ma'u na yi shi ya sa."
Ina mata mirmishi na ce" To ai shiken nan na ma san Ma'u ta cika miki jaka da goron sallah ba ki buƙatar tawa ko?
Har ga Allah ni a wasa na yi mganar kawai sai gani na yi Ya Murja ta bankaɗo labule ta fito da hijabi a jikinta da alamun ta idar da salla ne kallona ta yi daga sama har ƙasa nima ko cikin mamaki na ke kallonta sai kawai ta daka ma Anti tsawa ta na faɗin ta wuce ta je ta yi sallah sai yarinyar ta wuce ɗakin Gwaggo da sauri.
Kamar zan yi mgana sai na fasa na fara tafiya wajen famfo Gwaggo ta taso za ta shiga ɗakinta.

"Ke Sadiya.."

Ya Murja ta yi mini kira cikin gatsali sai na juya ina kallonta cikin mamaki. Ba ma ni kaɗai ba hadda Gwaggo.

"Me ya faru Ya Murja?

Na faɗa ganin kamar tana sakin huci kawai sai ta nuna ni da yatsa ta na faɗin" Daga yau in kina so ki yi min rashin kunya ki zo gare ni kai tsaye ne ba sai kin rakuɓe a jikin ƴa' ta kina gaya min mgana ba. Ba na son rashin kunya."
Galala na yi da baki ina kallonta kafin na samu zarafin mgana Gwaggo ta tsawarta da cewa" Murja me kuma ya kawo wannan mganar?

A fusace ta ce" Ba ki ji mganganun da ta ke faɗa ma Anti ba ne? Ta nuna kamar da gayya ne ban tura Anti gidanta ba na tura ta gidan maƙiyarta Ma'u ba. Duk na fahimci mganganunta."
Gwaggo ta yi tsaki kafin ta ce" To ni ban ji haka ba. Mganar su kawai suke yi na tsakanin uwa da ƴa."
Nan fa Ya Murja ta ce ita fa k a taufau da ita na ke yi. Ƙara nuna ni ta yi da yatsa kafin ta ce" Daman ba tun yau ba kin sha faɗan wai na fi son Ma'u da ke da ita kawai na ke shiri yayana ma gidanta suka sani. To yadda kika faɗan ne domin Ma'u ta fi ki ladabi da biyayya sannan ita ta ja ƴa'ƴana a jiki ke kuma da ba ƙi kaunar su ba ki ja su a jiki ba. Kin ga ko kar ki ga laifin su in ba su je in da kike ba. Gidan kuma Ma'u da ki ke jin haushin suna zuwa yanzu suka fara zuwa. Sai dai baƙin ciki ya kashe ki Sadiya"

"Murja me ye haka don Allah.?

Ya Aina bayan ta fito daga ɗakin Mama itama sanye da hijabi ita da Ya Balki da Rahila. Ma'u dai ba ta fito ba ni kuma tsabar mamaki ma na kasa magana.
"Ya Murja Alhajimmu na ciki fa. Gaskiya wannan ba girman ki ba ne. Sadiya fa ba da ke ta ke mganarta ba."
A fusace Ya Murja ta ce" Ba za ku gane ba ne. Ni na san ga in da ta dosa. To me ye na damuwa don ƴaƴana ba su je in da ta ke ba. Marwa da kika zaɓa kina so ita ai kin gayyaceta kuma ta je suma in kika nuna kina so su je ɗin za su je."

Sai a lokacin na fahimci haushina ta ke ji saboda Marwa. Kai wannan mata ta ɗoramin karan tsana.
Ba na so na yi hayaniya saboda Alhajinmu kawai sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Ki yi hakuri Ya Murja na ga ƙin ɗau zafi har ga Allah ba da wata munafa na faɗi mganar da na faɗa ba. Amma in ta ɓata miki rai Allah ya baki haƙuri. Mganar Anti na zuwa gidan Ma'u ban taɓa sawa a kaina ba domin da ni da Ma'u  duk ɗaya ne. Ke ma kuma ina so ki gane wani abu da Anti da Marwa ɗaya suke a wajena ba Bambamci."

  Ina gama faɗin haka na juya na wuce wajen famfo ina taran ruwa a buta. Na san dukkansu sun yi mamakin sanyina har sai da Gwaggo ta ce" Shike nan Sadiya kin gama magana. Ke kuma Babba kwabo kin ji kunya tunda har yau Sadiya ta fi ki hangen nesa."
Ganin ban kulata ba ya sa ta koma ɗaki fuu. Kuma kowa ita ya ba ma rashin gaskiya a wajen. Sai bayan da na ɗauro alwala na shigo cikin ɗakin ne Ma'u ta ke ce min" ki yi hakuri Sadiya ki fahimci Ya Murja don Allah itama ba da wata munafa ta yi miki mganar ba.'

Kallonta kawai na yi ni kam wani makircin Ma'u ne ban gani ba sai kawai na ce" Bakomai. Ita za ki ƙara ba ma hakuri saboda na ga kamar ta ɗau zafi da ni."
Ina gama faɗin haka na saka Hijabi na ta da salla. Bayan na idar sai muka ci abinci na ga dai Ya Aina ta keɓe da Ya Murja na kuma san faɗa ta ke yi mata shi ne na ga ta ɗan saki ranta a raina na ce matar nan me na yi mata wai ta tsane ni ne?
Muna cikin cin abinci sai ga Ya Abubakar ya shigo ganin abinci kala kala muna ci ya sa ya ce"Kai. A ina aka samo abinci nau'i nau'i haka kamar an samu sabon restaurant?

Rahila ce ta faɗa masa kowaccem mu ta dafo abinci daga gidanta sai shima ya samu waje ya zauna ya na faɗin" To shi ne ana wannan shagali aka manta da ni? Ni ne fa the head of the family"
Ya Balki ta ce" Mun ɗauka Zaituna ta yi maka kyakyawan beta kafin ta fito gida"

  Ta faɗa ta na kallon Zaitunan da ke ta cin abincinta jin an taɓo bangarenta ya sa ta yi saurin cewa" Laa shi ya ce in taho ba sai na tsaya na yi abinci ba."
Rahila ta ce" Ehem daman na san za a rina."
Yaya Aina ke faɗin" Ke kam Zaituna ban san yaushe za ki wayau ba. Ko mu kin ga mun taho ba mu yi girki ba? Ga shaida nan tunda gashi nan kina ci in da kin dafa kafin ki fito mijin ki zai zo ya na neman abinci?
Kanta na kasa ba ta yi mgana ba Yaya Abubakar ya wani girgiza kai kafin ya ce" Ƙyaleta Aina ta yi lokaci ne."
Daga haka kawai ya miƙe ya ce ya na ɗakin Alhaji a kawo masa abinci. Zaitunan Ya Aina ta tasa ta ce ta saka mai ta kai masa ta na fita Ya Murja ta ce" Mata kamar mai almatsutsai"
Ya Aina ta ce" Lafiyan ta ƙalau iskanci ne kawai da ta samu shi Abubakar ɗin mai sanyi."

Ni dai ina jin su ban tanka ba ina ta cin abincina ni shinkafa da waken da Rahila ta dafa na ke ci su kuma su Ya Aina sun ci nawa sun kuma ci na Ma'u ita waina ce da Sinasir. Mganar gaskiya duk cikin mu Mijin Ma'u ya fi kuɗi kowa kuma ya san haka amma duk da haka dukkanmu ba za a ce muna cikin halin rayuwa ba dai dai gwargwado mazajen mu na da rufin asiri. Mijin Ya Murja ne ma sai a hankali domin ya samu matsala can kwanaki an kore shi daga wajen aiki ya fi shekara uku a gida amma dai an ce ya koma shi ya sa Ma'u ta samu dama tana taimakonta ita kuma kwaɗayi ya sa idanuwanta ya rufe. Ni ba na kyautar ganin ido ko ka gode min in na yi niyyar yi maka alheri na yi, in ban yi ba shike nan ba zan yi domin duniya ko kai da zan mawa ka yabeni ba ita kuma Ma'u daman halinta ne ta yi alherin da duniya za ta sani a yabe ta a kuma san tana yi ɗin da son nuna ita fa mijinta na da kuɗi domin in dai Ma'u ta san za a zo gida a haɗu ƙarshen kayanta a kyau da tsada ta ke sakawa. A fuska ba ta nuna wani abu amma ga ni da na san halinta ni na san ta na da halin son a sani.

  Yanzu ma muna cin abincin ta na ba da labarin Alhaji Mustapha ya ce zai ba ta jari na miliyan biyar ta fara kasuwanci shi ne take neman shawarammu wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login