Showing 93001 words to 96000 words out of 121577 words
ma ƴa'ƴan shi da suka rasa uba suma sun dangana amman ita ba alamun dangana a lamarinta.
Na tuna ni kaina fa uwata ba ta a duniya nan na ɗau tawakalli Yallaɓai ba shi da uba shima ya ɗau dangana. Har wani lokacin in na jin masa shaƙiyanci ko ina son ya yi min wani abu ya ce ba zai yi ba sai na marairai ce ina faɗin." Yallaɓai ka tausaya mini ka ga ni fa marainiya ce.'
In na ce haka a lokacin sai ya yi dariyan nishaɗi kafin ya ce" Au ke sai yanzu kika san ke marainiya ce? Mu ai mun daɗe cikin maraici kuma ba mu mutu ba."
Ko kuma ya ce" Ke ba marainiya ba ce Alhaji ai bai mutu ba ko kin kashe shi ne? In ya faɗi haka daga ni har shi sai mun ƙyalƙyace da dariya. Saboda mun yi shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma Annabi muhammdu manzonsa ne, sannan rayuwa da mutuwa duk ta na hannun shi ne.
Sai dai ta bangaren Gimbiya ba ta san wannan ba, tun da a ka yi rasuwar nan saboda ba ta jin mganar kowa sai na Yallabai a rana ban san adadin sai nawa ya ke kiran waya a ba ta ba, yana lallashinta ta samu ta ci wani abu. Ko in ta fara kuka sai su kira shi su ba ta ya yi ta mata nasiha, duk wannan ƙokarin da ya ke yi mata ba ta dangana ba. Bayan wanda yan'uwa ke yi mata shima duk bai sa ta dangana ba. Tun ina tausayinta har ta koma ba ni haushi. Na yi ta tunanin ita ko wani irin so ta ke yi masa haka. ko dai garken yaya ta tara da shi sai haka amman aure duka duka wata ashirin ba ciki ba goyo haba lamarin nata ya yi yawa har na fara gajiya da jin labarin halin da ta ke ciki a bakin Yallaɓai in yana faɗa min Daughter ta zama abin tausayi, tun in yana faɗa ina nuna jimami har na daina saboda lamarinta ya wuce na musulma mai tawakalli ya koma hauka da jayayya da ubangiji.
Nan ko sati ba a yi ba sai da Yallaɓai ya koma Abuja ya kwana ɗaya sannan ya dawo. Wai ta shige ɗaki tun safe ta rufe kanta tana kuka kuma tun daren jiya ba ta ci komai ba su Nene sun yi sun yi da ita ta buɗe ta ƙi har azahar shi ne Nene ta kira Yallaɓai a waya ta ce ya bar duk abin da ya ke yi ya zo Abuja. Shi ne fa ya na ma office ya dawo gida ya na faɗa min tare da cewa na haɗa masa kayan tafiya na kwana ɗaya tun da ba zai yuyu ya je a yau ya kuma dawo ba.
A lokacin ne na furta masa abin da ke zuciya ta.
"Haba kamar dai ba ta da tawakkalli. Wai kanta farau mutuwar miji?
Na faɗa ina mai sakin tsaki tun da shima yana kan aikinsa ne amman an wani ta da shi zuwa Abuja. Ni ina ganin gulma ne ace duk cikin yan'uwanta da suke uwa daya uba ɗaya mata da maza ba ta ga wanda za ta riƙa jin mganarsa ba sai Yallaɓai da zaman da ya yi a gidansu na ɗan lokaci ne, za a ce ya fi mata yan'uwanta da suka fito ciki ɗaya ne?
Tsawa Yallaɓai ya daka mini kafin cikin ɓacin rai ya kalleni ya na faɗin" Sadiya wannan wani irin mgana ne?
Kallonsa na tsaya yi saboda sai na ga kamar ban faɗi wani abu mara kyau ba.
"Me na ce? Gasikiya na faɗa hakuri ake yi. In ta na wannan abun kamar tana faɗa da Allah ne."
Kawai sai Yallaɓai ya fara faɗa ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Wai na san zafin mutuwan miji kuwa.?
Ni ko kai tsaye na ce" Ban san na miji ba. Amman ai na san zafin mutuwar uwa ko?
Na faɗa ina kallon shi saboda na ga zai wani hau kaina daga faɗin gaskiya saboda ma na ƙara kunsa ma sa kai tsaye na sake faɗin" Kuma na tabbata ba yau aka saba mata rashi ba. Ai ta rasa uba da yan'uwata me ya sa ba ta yi haka ba sai yanzu? Gaskiya ku yi mata faɗan ta zama mai tawakkalli kuka ko rufe kai a ɗaki ba shi zai kawo mafita ba."
Ni kaina tsaye na ke mgana kuma shi kan shi Yallaɓan ya san ni.
Amman a mamakina kai tsaye ya kalleni kafin ya girgiza kai ya na faɗin" Na yi miki uziru saboda ba ki san zafin mutuwar miji ba. Amman ba shi zai hana na ce ba ki da tausayi ba Sadiya."
Baki buɗe na kalli Yallaɓai ya na sauya kaya cikin nuna kaina na ce" Ni ce ba ni da tausayi Yallaɓai?
Kai tsaye ya ce" Ƙwarai da gaske. Domin duk mai tausayi tausaya ma halin da Daughter ta ke ciki zai yi ba maganganun banza marasa tushe ballantana makama ba. Shirme kawai."
"Daga faɗin gaskiya?
"Ki riƙe gaskiyan ta ki ba a so."
Haka ya maida mini amsa a fusace.
Ajiyar zuciya kawai na sauke domiin na ji raina na tafarfasa zan iya maida masa martani amman sai na ƙyale shi, ɗakin na bar mishi kayan na shi ma ban gama haɗawa ba na ce ya haɗa da kan shi tun da da ga faɗin gaskiya sai na yi laifi ya je can ya tare saboda kula da ita. Da zai tafi ko sallaman da muka saba ba mu yi ba, shima fuska a haɗe nima na haɗe nawa ko haraba ban raka shi ba, daga falo na yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya.
Amman Yallaɓai ya ba ni mamaki, yadda ya wani ɗau zafi daga fafin gaskiya. Wani abu ke tsaya min a maƙogwaro in na ji yana ambaton ta da Daughter ƙatuwar mace shima ya na namiji magidanci da wani sanabe da iyayi.
Har ya je ya yi kwanan ɗayansa ya dawo ba mu yi waya ba. Ya san halina yadda bai kirani ba nima ban neme shi ba su Jidda suna ta tambayan Abba na ce ya ta fi Abuja.
Da ya dawo ban yi masa tarban da na saba ba. Ni ban haɗe rai ba sannan ban sakar masa ba, sai dai lokacin da ya dawo sai bai dawo da fushin ba. Shi ya fara saki sai nima na saki amman na so ya cigaba ya sanni ni sai na iya gaba dashi ba wani abu mai wahala ba ne a wajena. Amman kalmar ba ni da tausayi da ya kirani da shi ya taɓa ni kuma sai da na yi masa mgana sai ya ce na yi hakuri amman nima ai bai dace na ce haka ba, kenan har a lokacin bai ga gaskiyan abin da na faɗa ba to ai shike nan ni kuma na saka a raina ba zan kara mgana ba.
Abin da ma ya faru a can ɗin ban tambaye shi ba shi da bakin shi ya ke faɗa mini Ulcer ta kama Gimbiya sannan kuma jininta ya hau sai da likita ya zo gida ya duba ta. Bakina ƙanin kafata na ce Allah ya ba ta lafiya domin na fahimci Yallaɓai kiris ya ke jira da ni ya yaɓa mini mgana.
Bayan arba'in da kwana uku Gimbiya ta dawo Rano. Mimisco ta je tare da ita ma aka maida ta rano. Sai yayyenta maza da suka je saboda sun gana da yan uwan marigayin da yaran shi. Farko sun nuna ba su so tafiyar ta ba sun nuna gwara ta zauna a gidanta ta gama takaba sai su kuma ƴan uwanta su kawo dalilin halin da ta ke ciki in ta koma gida ta na ganin mutane za ta samu ta dawo dai dai ba kamar zamanta anan ba, da haka suka amince ta koma gida amman sai da aka kai ta duka gidajen matan ta yi sallama da su. Suna kuka tana kuka an kwashe mata duka kayanta a ka rufe gidan aka mika makullin ga iyalanshi tunda sun ce suna kan tatrara abin da ya bari ne bayan an gama za a bincika in da baahi a biya in babu kuma in lokaci ya yi za su nemesu domin rabon gado.
Gimbiya ta yi sallama da garin Abuja, aikin nata ba mganar shi daman tun da aka yi rasuwar ba ta je ba. Ana tunanin in komai ya lafa a yi mata transfer ko zuwa cikin garin kano ne. Kwana biyu tsakani da dawowarta na je yi ma Nene bangajiya tun da sai da ta ƙara kwana a Reno sanman ta dawo gida ita ce ma ta ke bani labarin abin da ya faru kafin ta tahowar su.
"Allah sarki. Allah ya yi mishi Rahama ita kuma Allah ya ba ta dangana."
Nene ta amsa da Amin kafin t ce" Ai an fara karɓa mata rubutu wajen wani malami a can rano. Da safen nan mun yi mgana da Hajiya ta ce ta fara sha da safe. To Saudatu ta rame ta lalace ta fita hayyacinta. Rayuwarta akwai tausayi sosai."
Nene ta ke faɗa cikin rawan murya. Ni kuma sai na ce" Har yanzu ba ta fara dangana ba Nene? Sai ta ce a hankali dai amma in na ga Saudatu sai na tausaya mata.
A gidan na yini ina nan Hauwa da Munirra suka zo da su Suwaiba domin yi ma Nene gaisuwa da barka da zuwa kaf ahalin gidan nan Yaya Usman ne kawai bai zo ba da Anty Zabba amman dai sun yi gaisuwa ta waya, har Muhammad Kabir da Nafisa sun zo gaisuwa daga katsina.
Sati ɗaya da dawowarta Yallaɓai ya ce na shirya muje Rano domin na ƙara yi musu gaisuwa ban yi musu ba na shirya ashe tare da Mutakƙa ne da Hauwa sai na ji daɗi a motar Yallaɓai muka je ranar weekend yara kuma wajen Nene muka bar su gabaɗaya.
Mun je mun iske mutane cike a gidan a kallah dai ba za ta yi kaɗaici ba. Sannan ga babbar Aminiyarta babbar ɗiyar Anty Zuwaira Naja'atu duk da ita Gimbiya ta girmi Naja'atu amman kuma Allah ya haɗa wannan kawancen lokacin da aka yi rasuwar ita da mijinta ba sa ƙasar suna Italy. Kuma lokacin da aka yi rasuwar ta so dawowa sai matslan visa ya hana ta sai dai su yi mgana a waya to faa sai cikin satin nan ta dawo. Amman a kano take aure da yaron wani mashuririn ɗan kasuwa a garin kano mai suna Buhari manga. Ba su cika ma zama a Nigeria ba yawancin kuma duka yayan da Naja'atu ta haifa guda uku a kasar waje ta ke zuwa ta yi renon cikin ta ta haihu.
Ita muka iske tare da Gimbiya wacce ta faɗe ta rame sai dogon fuska da hanci bakinta duk ya bushe idanuwanta duk sun zurma. Tana sanye da hijabi da caabaha. Mun gaisa da Naja'atu duk ba wani damuwa da mutane ta yi ba, irina ce shi ya sa na ke yi mata uzuri ban cika damuwa da halinta ba ammam duk in da muka haɗu za ta gaisheni da tambayan su Jidda.
A ɗakin Hajiyar Tafida muka zauna ita kuma Gimbiya da ƙawayenta suna ɗakin Hajiya Kaltume kamar acan aka sauke ta tana takabar nata. Muna Rano har bayan la'asar na yo alwala daga bayin waje Hauwa ta rigani yin na ta shiga ɗakin Hajiya ni kuma lokacin da na yo tawa sai na ga maza sun shigo yan gaisuwa sun shiga ɗakin sai na wuce ɗakin da Gimbiya ke ciki Naja'atu ma ta bani darduma na shimfiɗa na ta da salla.
Na kai raka'a ta biyu na miƙe a raka'a ta uku Yallaɓai ya shigo na ji muryan Mutaƙka da na Uncle Abba sai na wasu mazan amman tun da ina salla ba zan iya sanin su ba. Ina ji Mutaƙka na yi ma Gimbiya sallama daman kuma Yallaɓai ya ce bayan la'asar za mu tafi.
Daga nan sai kowa ya fita har Naja'atu aka bar Yallaɓai da Gimbiya. Ban sani ba ko shi ya gane ni ce ke sallah ko kuma bai gane ni ba amman ita ta san nice na ke yin salla a wajen
Suna ta gefen damana ne, ina kai sujjadar ƙarshe na ga Yallaɓai ya duƙa a gaban Gimbiya yana mai kiran ta da sunan da ya saba kiran ta dashi.
"Daughter."
Sai ta ɗago ta kalle shi a marairaice kafin ta amsa murya shaƙe.
"Daddy."
Dai dai lokacin da na ce" Assalamu alakum waramatullah
Hagu da dama da kuma ƙarfi, ina juyawa bangaren dama muka haɗa ido da Yallaɓai har da ita Gimbiyan
Ina salla ne amman kirjina na wani irin suya ne. Kallon yadda ya gurfana na yi a gaban Gimbiya har gwiwar kafarsa na gugan kafafunta da ke tankwashe sai kawai na kauda kaina na miƙe ina na ɗe darduman da na yi sallah da shi.
Ko kunya ya ji da ya ganni sai ya yi saurin matsawa baya ya na mai miƙewa tsaye.
"Da man ke ce ke salla?
Ya faɗa ya na kallona sai kawai na kalle shi kafin na ce" E"
Sannan na ijiye darduman a saman hannun kujera kafin na kama hanyar barin ɗakin ina faɗin" Ku cigaba da mganar ku."
Ban san ko sun bi ni da kallo ba saboda ni ban juyawa ba har na fice daga ɗakin.
Ba dota ba doya ba daddy ba Dada. Tun daga lokacin na rage fara'a har Hauwa sai da ta tambayeni ko lafiya na ce lafiya lau kila Yallaɓai ya tsargu ne ya sa bai daɗe a ɗakin ba ya fito ya leƙo nan ya na cewa mu fito za mu biya gidan su Nene kafin mu wuce.
Sallama muka yi musu, sannan mun kara shiga wajen Gimbiya muka ƙara yi mata Allah ya jikan rai ya ba da danganta ta amsa a hankali. Daganan sai gidan su Nene muka je muka gaida Innayi ko minti talatin ba mu yi ba muka kamo hanyar gida. A cikin zuciya na ga to damuwar ta mace ce, namiji fa sunan shi Namiji ba abin da ba zai yi ba sai kawai na watsar da abin na ɗan saki fuska Yallabai daman suna hira da Mutaƙƙa ya nna ta faman sako ni a ciki da a shake na ke amsa masa sai daga baya na saki jiki muna ta hira. Sai da muka biya Gwammaja muka ɗau yara sannan muka kai su Hauwa gida muka wuce namu gidan
Yallaɓai dai kamar ya kama kan shi ni dai ƙala ban ce masa ba sai shi ne da za mu kwanta ya ɗauko mganar.
"Dazu Allah ban san ke ce ke sallah ba."
Na yi kamar ban ji sa ba sai ya ƙara cewa" Kin san da ya ke sai a hankali. Na shiga yi mata sallama na ke ƙoƙarin lallashinta ta riƙa cin abinci."
"Haka fa. Ai ka kyauta."
Daga nan na juya masa baya na ja bargo. Ban sani ba ko yabi ni da kallo amman ina da tabbacin ya yi haka. Bai takuramin ba amman ya raɓo ta bayana mun kwanta.
*****
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya. Wattani wajen biyu sun zo sun shuɗe kamar tafiyar iska. Har su Jidda sun yi jarabawa 3rd tearm sun yi hutu. Jidda Gidan Mimisco ta tafi hutu ita kuma Baby gidan Yaya Maimuna gida tsit daga ni sai Yallaɓai sai Saude da ke zuwa yi min aikace aikace.
Bangaren asibitina kuwa tuni na yi nisa a gwaje gwajen da ake yi minib wanda na yi na ƙarshe shi ne Pap smears ne kuma har na karɓi result ɗin wannan satin da ya wuce na kai ma Dr Aisha cikin ikon Allah ta ce mini shima ba wata matsala.
In da na ke ɗan samu salama kenan kuma ta na bani hop ɗin duk da saura gwaje gwajen ba mu gama ba, ba ni da watsala lokaci ne bai yi ba in ya yi zan ƙara haihuwa.
Zuwa lokacin shiryen shiryen bikin Yaya Usman ake yi domin cikin watan da za mu shiga kafin azumi za a yi bikin na shi. Anan Gwammaja za a yi bikin tunda ɗaurin auran ma a kaduna ne. Yadda Yallaɓai ya faɗa mini gabaɗaya da Anty Zabba da yaran za su zo kamo sai an gama biki za su koma fatakot har da amaryan.
Har anko ƙannensa su Nasara sun fidda Atamfa ce mu ma duk mazajen mu sun yi mana mu da yara. Aure dai ya tabbata ba fashi amarya na dawowa daga london aka tsaida date ɗin biki.
A kuma tsuƙin ne na kirga za mu yi 15 years Anniversery da aure ni da Yallaɓai zuwa bayan sallan azumi da kwana shidda kenan. Ni kaɗai a raina na shirya za mu yi walima tun da tun na 10years ba mu kara ba lokacin Baby ta cika shekara ɗaya sai muka haɗe da birthady ɗin ta.
Ba mu kara yi ba sai wanman karon na ke fatan mu sake yi. Daman a gida ne daga ni sai shi sai yara muka yanka cake ɗin mu sha hotunan mu da ciye ciye washegari kuma Yallaɓai ya fita damu mu wajen wassani da sauran su. Tun tuni na so na yi masa mganar amman bai samun lokaci Alhamdulillah yana ta samu kwangila bayan gama gina gidan buredi a Rano dalilin haka ya samu kwangilan gina bayuka na wasu makaratun sakandiri a garin na Rano sai ya kasance zamansa a nan office ba sosai ba sai dai Musabahu ya zauna wani lokacin gidan bulo kuma daman sun ɗauki yara ma su kula da shi, shi dai Musabahu manaja ne kawai.
Abin da na fara lura da shi shi ne Gimbiya ta fara ƙoƙarin takura ma rayuwar aurena ta na daga can gidansu tana takaba.
Ni na san cewa Yallaɓai na zuwa ganinta tun da yana yawan zuwa Rano. Ban kuma taɓa nuna damuwata ba ko na nuna fuska ban ji daɗi. Sai dai na ga ba ta da hankali in ya dawo gida sai ta kira shi a waya ta ji wai yadda ya koma gida. Da safe kuma ta iya kiran sassafe tsirfa kala kala daga ta ce Anty Bahijja za ta ba da saƙo a kawo mata sai ta ce Nene sai ta ce Anty Maimuna wani lokacin ita ce ma za ta