Showing 102001 words to 105000 words out of 121577 words
Su kuma su Hauwa suka ce wai na yi musu wayau na kwashe tsokoki na bar ma mazajensu kashi ina dariya na ce" To wai na hana ku diɓar musu ne da farko? Bana son son zuciya fa. Ku dai cigaba da zama."
Ranar ma ban kwana ba gida na koma amman tare da Farida da Sameena su Munnira ma gida za ta koma ta kwanta Hauwa ce na ga tana shirin ƙara kwana na ce ta je gida ta kula da mijinta tun da ban ga abin da za ta yi ba in ta kwanan
Uncle Abba da Tariq Rano suka koma suka kwana Yallaɓai kan gida ya dawo su Farida a ɗakin su Jidda na sauke su da safe bayan mun karya mun yi wanka muka koma Gwammaja.
Sai a ranar muka shiga muka ga Amarya. Doguwa ce baka mai jiki. A shashen da muka zauna ajiya yau ma nan muka zauna da farko ba mu yi niyyar zuwa gidan su Anty Zabba ba sai da ta kira Munnira ta ce tun da mun zama yan amarya ta yafe mu shi ne yasa muka shirya bayan azahar muka tafi can anguwarsu ta Rijiyar zaƙi.
Da muka ce ga in da zamu a gidan kafin mu tafi, sai da Anty Bahijja ta yi ƙorafin ne zai kai mu? Ita da Anty Zulaihat wai ai da gangan ta ki sauka anan a yi biki gabaɗaya Mimisco ta kashe bakin su da cewa" Ku bar su je yana da kyau haka a matsayin su na surukan gidan nan"
Dole suka yi shuru. Mun je ma Anty Zabba biki da muka je har tana cewa ta yi fushi nima ta ce ko waya ban kira ba na bata hakuri.
Anty Zabba har ta ɗan rame amman kuma ta yi gayunta tsab da ita itama ta yi taro gidansu cike da mutane yaran nata sai a ranar da za mu taho suka biyo mu zuwa gidan kakaninsu a daran kuma aka zagaya da amarya duka ɗakunan gida mu ma aka tara mu aka yi mata bayanimmu ɗaya bayan ɗaya.
Washegari litini da wuri Ango ya ɗau amaryansa da Rakiyan ƙannensa mata su Anty Nasara suka raka su gidan su Anty Zabba suka haɗa su suka yi musu nasiha daga nan sai filin jirgi suka ɗaga sai garin fatacol sai fatan Allah ya ba su zaman lafiya ya kaɗe fitina.
Shikenan gida ya watse baƙi da nesa da na kusa zuwa talata duk sun koma gidajensu Gimbiya dai ta na nan amman na ji Hauwa na faɗin daga nan Abuja za ta wuce an kira su kan mganar rabon gado. Mganar aikin ta kuma Yallaɓai ya faɗa mini an dawo da ita nan office ɗin NGO da ke reshen Jihar kano. Amman sai ta dawo daga Abuja za ta fara zuwa aikin.
A lokacin da ya ke gaya minibsai da na tambaye shi.
"A wajen Nene za ta zauna kenan?
Sai ya gyaɗa min kai har yana ce min" Nene ma ta karɓe ta. Ta ce sai kuma aure zai raba su."
"Uhm!
Kawai na ce a lokacin amman ban iya sake mgana ba.
Sai bayan bikin Yaya Usman na samu damar yi ma Yallaɓai tuni kan Anniversery ɗin mu ya ce wallahi ya manta gwara da na tuna mishi. To shima zai ba ni kyakyawan surpise a lokacin in sha Allahu ina ta murna ina cewa ko Hajji za ka biya mini? Ya ce Allah ya sa haka.
******
Bayan wata ɗaya da bikin Yaya Usman. Kuma a yanzu dai muna cikin watan ramadan ne har mun yi azumi takwas. Da azumi ya gabato Yallaɓai bashi da kuɗi a hannu ya samu kwangilan aikin nan na kaduna akwai kuɗin shi da ya saka a ciki, to kuma ya saba duk shekara ana yi masa kunin sadaka Maman Saude sannan yana rabama yaran dake ƙarkashin sa kuɗi ko kayan abinci.
Wannan karon ma da bai da kuɗi kayan abinci mu a ciki ya ce. A ɗibar ma Mutakka da gidan su Saude. Yaran shi na Office kuma kuɗi ya ba su, sannan gidanmu kuma 30k ya ba ni na kai musu da ƙwai da yawa da dankalin turawa wanda Uncle Abba ya kawo mana an cire ƙwai a gidan gonan shi Dankalin ma shi ya kawo mana buhu a ciki na dibar ma gidanmu da Muttaƙa.
Nene ma Uncle Abba ya kawo mata kwai da kayan gona muma ma mun shaida su kwaiba da mangaro har muna kyauta. Muttaƙa ma Hauwa ta ce ya samu alheri tunda shi kaɗai ne bai kai su karfi ba. Geron da Mijin Mimisco ya raba ma su Yallabai a ciki ya ce na diɓar ma su Gwaggo sauran kuma a ka kaima Balaraba na kunun Sadaka. Duk da daman a gidanmu ba mu da matsala komai akwai Yaya Hamza da Yaya Auwalu da suke da ƙarfi sun wadata su da komai, sai dai ihsani da kyauttawa namu amatsayin su na iyayenmu.
Mijin Amina ma ya aiko da kuɗi sauran alherin da aka samu ta bangaren su Yaya Balki an tura shi can Yashe wajen su Baba Sani. Ko Mijin Ma'u mota guda ya kawo na kayan abinci Baaba ai tana cikin alheri shi ya sa Yaya Aina ta ce a can kura Baaba ce yar gaban goshi to tana da ƴa tana auren mai kuɗi kuma ana aika musu da alheri. Ni Rahila ke faɗa,mini har dangin Babanta da azumin nan ta kai musu alheri.
Gimbiya ta dawo wajen Nene da zama saboda aikinta. Sun je Abuja tare da ƙanin mahaifinta Tafidan Rano an raba gadon dukiya ta samu gida biyi anan Abuja da kuɗi masu yawa na tumanin takaba dukkansu huɗun rabon su kenan. Su gwara su da ƴaya ita bayan tumin takaba ba ta samu komai ba. Yallabai na ji suna waya kan tana son a saida gida guda ɗaya a siya mata a fili anan kano kuɗin ta kuma Mota ta ke son siya. Da ya ke komai sai ta yi shawara da shi abin da ya ce kar a yi ta bar shi kenan wanda ya ce a yi kuma shi take yi. Ta ɗan yi facaka da ƙudin bayan Mota ta siya manyan suturu da gwala gwalai, har su Jidda ta siya ma Takalma da dogayen riguna daga Dubai oder ma ta yi, sai yan uwa suka yi mata faɗa suka ce ta fara tunanin kasuwancin da za ta fara tunda kuɗin gado kamar ruwa su ke za su ƙare ba tare da ta yi komai da su ba.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/FAtGNQc8Y8pB008TuxFJVo
Eaman ScholarSphere.
Where ideas Take Shape.
WHAT WE DO.
ASSIGNMENT
PRESENTATIONS.
ARTICLES
PROJECTS.
BOOK
AND MANY MORE.
CANTACT US THROUGH.
02347067793152
MOTTO:
"Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures"
*🅿️18*
Azumi ya raba tsakiya, mun gama goma na marmari mun shiga goma na wuya kamar yadda hausawa ke faɗi.
Yau in muka kai azumi mun kai sha biyar kenan, a duka shekarun da muka kwashe da aure ni da Yallaɓai na saba duk watan ramadana Yallaɓai ba ya kaiwa dare a waje a gida ya ke yin buɗe baki tare damu haka ya sabar mana kuma nima haka na saba.
Amma wannan azumin sai al'amarin ya ɗan sauya. Saboda ya samu kwangila gina ma'aikatan nan na kaduna gabaɗaya ma'aikatan shi suna can kaduna shima yana zuwa har ya kwana ma kafin ya dawo sai ya zama na in baya gari sai dai mu yi buɗe baki tare da yara. Ranar da muka kai azumi na sha uku ya dawo daga Kaduna na yi masa har kunin tsamiya da ya ke matuƙar so, amman bai shigo gidan ba sai wajen tara na dare. Na kira shi a waya na ji ko bai dawo daga kadunan ba ne? Sai ya ce mini ya dawo ya na Gwammaja da ya faɗa mini haka har a cikin raina ban yi zargin wani abu ba, sai da ya dawo na kawo masa abin buɗe baki bai ci abinci ba,kunin ma kaɗan ya sha ya ce mini cikin shi ya cika a lokacin sai da na yi mamaki sanin Yallaɓai ba ya iya cin komai a waje sai ya dawo gida barin ma da azumi saboda ya san ina gida na shirya masa abin buɗe baki kamar yadda na saba.
"Ka ci wani abu ne a can Gwammaja?
Tambayar da na yi masa a lokacin kenan. Shi kuma kai tsaye ya ce mini Nene ce ta matsa masa sai da ya tsaya ya yi buɗe baki. Na ɗan yi mamaki saboda hakan bai taɓa faruwa ba ai Nene ta san ya na da mata me ya sa za ta ce sai ya yi buɗe baki a wajenta? Amma sai wata zuciya ta kitsa min kyakyawan Niyya cewa ita ɗin uwa ce a gare shi ta na da wannan damar kuma abu na rana ɗaya. Sai ko a fuska ban nuna masa damuwata ba na basar da komai ya wuce sannan ya faran tamin rai da ya ce da Asuba na ɗumama masa kuninshi ya na so ya yi sahur da shi.
Haka ko aka yi da asuba bai ci komai ba kunin na ɗumama masa ya sha da buredi ni kuma da yara muka sha tea sai na soya mana ƙwai muka haɗa da shi. Ranar kuma da wuri ya dawo gida muka yi buɗe baki tare ana kiran sallar isha'i ya yi alwala ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi sallar tarawihi kamar yadda ya saba ni kuma ni da yara daman muke yin namu a gida.
Sannan da rana kuma da ba na komai sai na yi ta karatun Qur'ani tunda duk watan Ramadan in ya zagayo sai na yi sauka kamar yadda na saba.
*****
Saude tana zuwa da safe ta yi min yan aikace aikace sannan ta ɗan rage mini aikin yamma tunda kafin la'asar ta ke komawa gida sauran aikin kuma ni na ke yi Jidda na kama min ɗan abin da ba a rasa ba.
Yau alale na yi mana mai kifi da ƙwai sai na yi mana zoɓo, Yallaɓai ya aiko da kayan ciki sai na yi ferfesu shi kuma sai na dafa masa ruwan tea da ya ji kayan ganyen shayi na citta saboda ya na so duk dare Yallaɓai zai sha kafin ya kwanta. Muna da kayan marmari sai na ce Jidda ta raba biyu sauran kuma su yi fruit salat ni da Yallaɓai kuma sai na yayyaka mana tunda shi ya fi son cin su a haka. Bayan mun gama haɗa komai na bar ma Jidda gyara Kitchen ɗin amma bayan na haɗa duka kayan buɗe baki a falon su Jidda in da muke zama gabaɗayan mu a saman cafet mu yi buɗe bakin tare.
Wanka na je na yi, saboda na gaji kuma yau ɗin nan ina ɗan jin azumin nan kaɗan ina fitowa wanka ana kiran salla daman ina da Dabino a ɗaki na yi buɗe baki Jidda ma na san ta yi na ta Baby dai daman azuminta rabi da rabi ne in ta ɗauka da ta yi rabi sai ta fara kukan yunwa Babanta kuma ya ce ta ci abincinta da cewa ta yi rabi gobe ma in ta yi rabi ɗaya kenan. Sai da na saka wata doguwar rigata na Atamfa sannan na ta da salla daman na ɗauro alwala ina cikin sallar na ji ana kiran wayata sai da na idar na jawo na duba sai na ga Amina ce sai da na shafa salatin da fara sannan na kira ta daga baya.
Mun gaisa ne ta yi mini barka da shan ruwa. Mu ɗan tambayi lafiyan juna kafin mu yi sallama Amina akwai ƙokari tunda aka shiga watan Ramadan duk bayan kwana biyu sai ta kirani ta yi mini barka da shan ruwa ita da Rahila suna da wannan ƙoƙarin a gidanmu. Ni ma dai farkon watan na kira duka yan gidanmu na yi musu barka da shigowa watan Ramadana wata mai albarka har Ma'u sai da na kira ban wareta ba wannan karon sannan Alhajinmu ma mun yi waya dashi sau uku kenan shi da Gwaggo saboda tun ranar da muka kai azumi na uku da na je gidan kai musu saƙon Yallaɓai ban ƙara komawa ba washegari kuma na je Gwammaja na gaishe da Nene tun daga kuma ranar ne ban ƙara fita ba.
Wayar ta ɗan dauke min hankali na buɗe data ina ganin masu turamin saƙon Happy iftar group ɗin Gidanmu na shiga na ga Ya Abubakar ya turo addu'a daman shi ke da wannan ƙoƙarin Ya Hamza ya yi tagging ya ce Allah ya ba da lada. Sai ni ma na yi Tagging na ce Amin tare de cewa fatan mun sha ruwa lafiya? duk ba sa kusa da wayarsu tun da an sha ruwa ana can ana hada hadar buɗe baki sai nima na fita daga nan na ɗan duba saƙonnin private sai na ga Munnira ta yi min mgana da cewa Matar Yallaɓai sai na tura mata da amsa da cewa matar ƙanin Yallaɓai sannan na saka mata emojin dariya na fita. Datar na kashe na ijiye wayar saman gado sannan na cire hijabin jikina na ninke ina mamakin me ya tsaida Yallaɓai har yanzu bai dawo ba? Tunda Office ya je bai ma fita da wuri ba sai bayan da a ka yi sallar azahar.
Falo na fita dai dai Jidda ma ta fito da Hijabinta alamun ta idar da sallah ne.
"Barka da shan ruwa Umma."
Ina kallonta na ce" Yauwa barkan mu dai Jiddan Umma. Ina Baby?
Sai ta ce min ta na ciki ta na sallah, ganin ta juya za ta koma ɗaki ya sa na ce" Taho ki yi buɗe baki mana Jidda.'
Cikin mamaki a fuskarta ta ce" Umma Abba bai dawo ba?
Kai na kaɗa kafin na ce" Yana hanya in sha Allahu. Taho ko kunin ki zuba ki sha cikin ki ya warware."
Sai ta amsa da toh hijabin jikinta ta cire ta zauna nima sai na zauna ta zuba mini kunun na ce kaɗan itama sai ta zuba nata sai ga Baby ta fito jikina ta faɗa tana faɗin" Umma azumi na goma.'
Ina dariya na ce" Lalle Baby mai himma ce kai kai har azumin ki ya kai goma?
Ta na washe baki ta ce" Umma ke guda nawa kika yi? Ina kallonta na ce" Ai muna tare da ke nima azumina goma."
"Yaa Jidda fa?
Ta faɗa tana kallonta ina dariya na ce" itama dai dai da naki." Sai ta miƙe ta na tsallen murna Jidda ta kalleta amma dai ba ta yi mgana ba saboda ba ta da hayaniya sosai.
Har muka gama shan kunu ba Yallaɓai ba dalilin shi Baby sai cewa ta ke yi Umma ina Abba? Sai na tashi na shiga ciki na ɗauko wayata na kira shi bai ma ɗauka ba a lokacin sai da na ƙara kira sannan ya ɗaga wayar na ji hayaniya a in da yake amma ba sosai ba.
"Yallaɓai na barka da shan ruwa."
"Barka da shan ruwa Sadiya ta."
Shima ya maida min martani. Mirmishi na yi mai sauti kafin na ce" Kana ina ne? Na ga an sha ruwa ba ka dawo gida ba."
Sai kawai ya ce" Ina nan zuwa na ɗan shiga Gwammaja ne duba Nene Daughter ta kirani ta ce da zazzaɓi ta yi ni"
Cikin jimami na ce" Ayya. Allah ya ba ta lafiya ka gaishe ta."
Ya amsa mini da Amin sai kawai ya ce mu yi buɗe bakin mu kar mu jira shi in ya dawo sai shi ya yi na shi ban kawo komai ba na yi fatan Allah ya ƙara sauki mu ka yi sallama.
Tare da yara muka yi buɗe baki ba mu ci abinci ba kawai kayan marmari muka sha sai ferfesu. Sai da muka yi sallar isha'i da tarawehi sannan muka ci abinci ni alale ɗaya na ci ma na ji cikina ya cika Jidda ta gaji da wuri ta kwanta Baby ne ma ta ɗan daɗe ba ta yi barci ba tana kallon cartoon sai da na kora ta na ce ta je ta kwanta saboda makaranta. Duk da ma yanzu 12pm suke tashi saboda azumi.
Tun ina saran dawowar Yallaɓai da wuri har na fidda rai sai na fara tunanin ko Jikin Nenen ne ya yi tsanani har sake kiran shi na yi ban same shi ba duk na damu. Ina ta tunanin Allah ya sa ba jikin Nenen ya yi tsanani ba ne kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tunda ni dai ba waya muke yi ba sai wani abu na jaje ko barka ni ba ma zan iya tuna last muka yi waya da ita ba gaskiya amma ina da lambarta kuma nima na san ta na da nawa tunda muna ganin status ɗin juna.
Har na fara gyangyaɗi na ji ƙaran buɗe get sannan da shigowar motar Yallaɓai sannan na mike ina duba agogon wayata goma da rabi har ta gota sha ɗaya saura na dare. Ajiyar zuciya na sauke na fita zuwa falon farko dai dai ya buɗe kofar falon ya shigo muka ci karo da juna ni da shi.
"Ya jikin Nenen?
Da haka na tare shi domin a zato na jikin nata ne ya yi tsanani ya sa bai shigo gida da wuri ba. Lumshe idanuwansa ya yi daga gani a gajiye ya ke saboda ya na ƙarosowa gabana ya rumgumeni yana mai sauke ajiyar zuciya nima sai na rumgumeshi ta baya ina faɗin" Nenen na lafiya ko?
Cikin muryan gajiya ya ce" Lafiya lau. Na gaji Sadiya ta ko'ina na jikina ciwo ya ke yi min."
Ko bai faɗa ba na ga hakan a muryan shi da yanayin shi sai kawai na ce mu je na haɗa masa ruwan wanka ya yi wanka sai ya ji daɗin jikin shi. Muna riƙe da hannun juna har bedroom ɗim mu ina tambayan shi ya jikin Nene ya ce min da sauƙi likita ya zo gida ya dubata. Maleria ce ta kamata cikin tausayinta na ce" Allah sarki. Allah ya ba ta lafiya. Amma dai ta ijiye azumin ko?
Sai da ya gyaɗa min kafin ya ce" Yau ɗin ma ta ɗauka da jikin ya zafi sai ta ajiye"
Ina taya shi tuɓe kayan jikinsa ya ke tambayata su Jidda na ce sun kwanta. Kai ya kaɗa kafin ya ce" Na