Showing 24001 words to 27000 words out of 121577 words

Chapter 9 - TURKEN GIDA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

22 Sep 2025

496

ciki ina buɗe ƙofar falo.

  Bai ƙara tada maganar ba har sai da muka yi wanka muka yi shirin barci, har na kwanta kawai na ji sa yana faɗin"Ba ki kyauta ba, ko ma me ya faru ya kamata ki kira ki ji in sun isa lafiya, karki sake irin haka Sadiya."

  Ɗagowa na yi ina kallonsa, in na ce zan yi magana ma ba zai fahimta ba sai na gyaɗa masa kai, yana zaune a gefen gado ya miƙaar da kafarsa ga laptop samansa.

  "Ki yi barcin ki. Zan yi aiki ne."

  Sai na ƙara jinjina masa kai. Zane zai yi, tunda Mijina Yusuf ya karanta fannin zane zane ne Archicture, sai kuma fannin da ya yi ma haye shi ne kwangilan gine gine, shi ya sa ya samu sunan injiniya, tun a sanina da Yusuf mutun ne mai neman na kansa mai fafutuka, ina ta kallonsa yana aikin sa, in muka haɗa ido,  sai ya yi min mirmishi nima na maida masa martani har barci ya sace ni ban sani ba.

  Tun asuba wayar Anty Bahijja ta tashe mu, wai Halima a asibiti ta kwana naguda. C.S ma za a yi mata. Wayar ɗan'uwanta ta kira nima shi ya ke faɗa mini. Na so na huta a gida ranar amman ya na iya cewa ya yi na shirya nu fita tare ya kaini asibitin sai ya wuce Office. Ba ni da mafita haka na sake shiryawa bayan mun karya, ko da sha ɗaya ta yi muna asibiti, wani asibitin kuɗi ne sanda muka isa an shiga da ita tiyatar ma.
Mun iske su Anty Maimuna da Anty Bahijja, Anty Zuwaira ta zo amman ta wuce makaranta suna da taro.

  Muna nan Mutaƙƙa ya zo, bayan mu ga mijinta da yayarsa. Mutaƙƙa tare suka fita da Yallaɓai., ya ce zai kira Hauwa ta yi girki ta taho zuwa anjuma.
Zaman jugum jugum muka yi duk na gaji har aka fito da ita daga Tiyata an samu nasaran ciro mata namiji, an kawo mana jaririn ita kuma sun kaita ɗakin hutu ba ta farfaɗo ba.

  Ranar dai a asibitin nan na yini, gajiya na yi da la'asar na ce ma Anty Bahijja zan ta fi, tunda ita Anty Maimuna ta koma gida, Badawiyya ce ɗiyarta ta biyu ta zo, Hauwa sai wajen biyu na rana ta zo da abinci, ni ban ma iya ci ba, saboda ba na iya cin wani abu in dai a acikin asibiti ne sallah ne da ya zame min dole na fita can haraban asibitin in da masallaci ya ke na yi sallah.

  "Za ki tafi kuma? Ba ki jira ta farfaɗo. Kuma ai na ɗauka sai dare in Tafida ya dawo sai ya ɗauke ki, ku koma gida tare."

  Mamakinta ya kamani, ita wai ba ta da tausayi ne, ko mijin Haliman ya ta fi gida yayar tasa ma tace bari ta je ta dawo. Ni fa na yi iya abin da zan iya yi ko ƙanwata ce ai sai haka, kuma ba zan zauna domin na faranta musu ni na ƙuntata ma kaina ba. Sai na buɗe baki na ce.

"A'a ba mu yi haka dashi ba, gida zan koma na takura da zaman waje ɗaya. Zan dawo gobe da safe in sha Allahu."

  Wani kallo ta yi min kafin ta ce" Uhm! Ni ban ma tsaya bi ta kanta ba na ce ma su Hauwa zan ta fi gida, lamgwabar da kai ta yi kafin ta ce"Na ɗauka sai dare"

  "Wallahi ko Yallaɓai ya ce na zauna sai dare zan faɗa masa na gaji haba. Gida za ni da safe sai na dawo."

  Tana min dariya ni kuma na sha kuni, mun yi nesa da su Badawiyya, ta rakani har haraba asibiti sannan ta koma ita kan zama daram tun da sai Mutaƙƙa ya dawo zai biyo ya ɗauketa su koma gida  yara ma gidan Nene ta kai su wajen Jawahir.

  Ko da na isa gida na gaji, wanka na fara yi sannan na nemi abin da zan ci indomie na dafa na ci sannan na dawo dai dai. Sai a lokacin na samu daman duba wayata na ga ashe Yaya Auwal ya kirani har sau biyu ban gani ba sai na bi bayan kiran na shi.

Bai ɗauka ba sai na kyaleshi, Dan Abuja ne masu aiki a gidan kuɗi ba sa ɗaga kira sai dai su kira, ba daɗewa sai ga shi ya sake kirana. Bayan na ɗauka mun gaisa da tambayan iyalai.

  "Ke wai me ya faru ne? Na ga ana ta cewa kun samu matsala da Ma'u a can group na gida?

Baki na taɓe kafin na ce"Rashin Fahimta ne. Amman Alhajimu ya daidaita mu."

Sai kawai ya ce"Oh. Ku ma dai kamar wasu yara. Sadiya kin girma fa ya kamata ki daina wasu abubuwan.".

  Da toh na amsa shi sanin halin shi, busy shi baya bashi daman zama ya gane abin da ke faruwa na kuma san sai yanzu ne hankalinshi ya kai kan abin da ya faru, daga nan muka sauya wata hirar.

"Yaya Auwalu me zan samu ne?

  Ya na yar dariya ya ce"Me zan samu dai Matar injiniya?

Baki na rufe ina yar dariya kamar ya na ganina kafin na ce"Ku ne masu kuɗin a hannun ku fa, ni dai faka faka ko yar wata ashirin ne ina jira."

  "Allah ya kawo."

  Daga haka muka yi sallama, bayan na ce ya gaida Aneesa da yara, nima ya ce in gaida su Jidda, mun gama waya ba daɗewa sai ga alert ɗin 10k ya turamin na yi mirmishi, shi ya sa fa nake son Yaya Auwal ba ya kiran banza, irin Yaya Hamza ne, ba su ba ka ɓacin rai amman kuma za su saka ka farinciki.
Ba irin su Yaya Abubakar ba, shi ai wani lokacin kamar wani mace haka ya ke jin kansa.

  Sau ɗaya na kira Alhajinmu muka gaisa bayan ya yi mana Sulhu da Ma'u. A raina na yi niyyar sai an yi wata ban je gida ba, Ma'u ta cigaba da zuwa a madadina.
Yaya Murja, har yau ban buɗe sakon ta ba ni fa ba na son munafurci,  Rahila daman ita ban saka ta a lissafi ba ta da matsaya. In na ce ta na tsoron Ma'u sai ta ce ba haka ba ne, amman dai na san cewa tana ƙaunata, takaici na ɗaya tafi kaunar Ma'u sama da ni.

  Sai can mangariba Yallaɓai ya kirani wai ina asibiti ne? Na ce na dawo gida sai ya ce shi zai biya sun yi waya da Anty Bahijja ta ce Halima ta farfaɗo na ce to ya gaishe ta.

  Sai can dare ya dawo,  bayan ya yi wanka muka zauna a dinining ya ci abinci, muna hira sama sama akan dai wani aikin kwangilan makaranta da ya yi sama da wattani goma shuru ba a biya su ba sun gama processing komai suna ta saka rai shuru, ni har na saba saboda na san yanayin aikin na su, kafin kuɗin su zo duk sai na hannun ya gama ƙarewa an jigata. Ko da zamu kwanta hirar da muke yi kenan, ina faɗa masa ko kayan abinci sun yi ƙasa ga haihuwan Halima ma, Allah dai ya rufa mana asiri.

  Ko a baya in ƙannensa ko yayyensa cikin ƴaƴansu sun samu karuwa in bashi da shi, ni na ke yi wani lokacin ma ba na jiransa in akwai kuɗi a hannuna, tsakaninshi da su dabam nima haka, in ban yi ba sai surutu ya tashi ko ba yawa ina zuwa na miƙa, ban damu da a gode ko kar a gode ba abin da na san zan iya shi na ke yi ba ruwana  da yin abu don wani ya gani ko ya yaba, kai tsaye na ke yin al'amarina ka zauna da ni domin Allah ko akasinsa ruwanka ni ba ruwana harkan gabana kawai na ke yi.

  Da safe ma da ya shirya zai fita cewa ya yi ko zai ijiyeni a asibitin ne, na ce a'a ya je kawai in na shirya an juma zan je da kaina  ina zan bi shi na je saman jumgum kamar ni ce na haihun. Sai azahar na fita bayan na ci na ƙoshi na je na iske asibitin cike duk da fa an ce a bar ta ta huta, dangin mijin ma kaɗan ne duk iyalan marigayi inuwa ne.

   Na iske Anty Zuwaira da  Anty Maimuna. Anty Bahijja ne ba ta zo ba sai dai su Suhailat. Hauwa ma can na isketa amman ba ta daɗe da zuwa ba. Ban daɗe da zuwa ba Sai ga Hajiya Iya,  tare da Suwaiba. Muna asibitin Maman farko ta zo tare da su Zulaihat, daga gidan gaisuwan suke, anan na yi ma Mama gaisuwan ma, Anty Zuwaira ce ta ce min wai ta daɗe ba ta ganni ba, ina yar dariya na ce"Mimisco ba ki zaman gida ko an je bakya nan."
Mirmishi ta yi kafin ta ce" In na dawo ai za a faɗa min kin zo ko? Har su Jidda ma ana yi min rowan su?

  Hakuri na ba ta na ce suna gidan Anty Maimuna amman za su zo mata in sha Allahu, Anty Maimuna na kusa ta na ji ta fara faɗin itama da ya ya na aikasu sai da ta yi ta mita ban takan ta ba, itama Mimisco ɗin da ya ke yar ba ruwanta ne ba ta wani maida kai kan mganar Anty Maimuna ba.

  Ni dai na ga mun yi yawaa a asibitin ana la'asar na yi musu sallama, na ce zan biya na gaida Nene an ce ta kwana da zazzaɓi, tare koma da Hajiya Iya, a gidan Nene na yi sallar mangariba sai na kira Yusuf na ce ina Gwammaja, in ya ta so daga Office ya biyo mu ta fi gida.
  Nenen ma ta ji sauƙi, tunda Anty Zuwaira ashe ta zo da safe sun je asibiti an duba ta an bata mganguna.
Ni dai na ce har da hayaniya saboda yaran Halima suna nan kuma ba sa jin magana sun cika ƙiriniya.

  Har goman dare muna gidan Nene mun shiga gida sha ɗaya na dare, a gajiye nake ko wanka ban yi ba na yi shirin kwanciya. Tunda na ci Tuwo a gidan Nene, dije ta yi shi da rana da miyar taushe. Na bar Yusuf na ta aiki a bisa laptop ɗinsa ni dai na yi barci na barshi ban san lokacin da ya gama ya zo bayana ya kwanta ba sai dai farkawa na yi kawai na ganshi kwance ni kuma duk na rufa masa kafafuna bawan Allah ya na shan bugun dare.

  Da safe da Inna Mariya ta kirani ƙanwar Mama ce tana gaya mini rasuwar, Yayar babansu Baaba Atu, Allah Sarki na ji mutuwarta ko kwanaki da muka je Gandun albasa mun shiga mun gaisheta ashe jinya ba na tashi ba ne. Ni na kira Amina na faɗa mata rasuwan ita tunda ta na nesa a kaduna take aure sai dai ni na shirya, kuma mu daman a gidanmu duk abin da ya faru a bangaren Gwaggo gabaɗaya ake zuwa haka bangaren Mama, tun Mama na da rai har ta rasu haka muke yi, Aminar ce ta shiga group ɗin gidanmu ta faɗa rasuwar sai na ji Anty Balki suna faɗi a haɗu a gida sai a tafi gabaɗaya a raina na kunsa sai dai mu haɗu a can. Yaya Auwal kawai na kira na sanar mawa ya ce Yanzu suka gama waya da Alhajinmu ya ce ya gashi ma a hanya zai tafi jana'iza mun gama wayar da cewa ya ce karshen wata zai shigo kanon in sha Allahu.

  Ina faɗa ma Yallaɓai rasuwan yace na shirya mu tafi Allah ya sa ya samu jana'iza. Tea kawai muka sha muka fita sai Gandun albasa, can ne asalin gidan su Mama, itama Baaba Atu ɗin da jinya ta yi tsanani ne, su kawu su ka ɗaukota zuwa gida anan aka yi jinyarta. Ta yi aure a kura mijinta ya rasu amman yayanta duka mata ne duk suna can, ko da muka je dai duk sun iso, tun da rasuwar ta asuba ce can muka iske Alhajinmu da Datti, har da Yaya Abubakar.
 
Ni kuma sai na shiga cikin gida. Inna Mariya ce kaɗai mace a yan'uwan Mama da suka rage uban su ɗaya, sai su Kawu Nafi'u da suma uba suka haɗa, Inna Madiyana ta riga ma Mama rasuwa itace suke uwa ɗaya uba ɗaya, namijin ma tun kafin a haifemu ya rasu.
Duka iyayensu sun mutu, daman ko da muka taso ba mu san kakkaninmu na bangaren uwa ba, mun dai san ta bangaren Uba. Allah ya jiƙan ki Hajiya Dubu.

  Sai bayan an yi jana'iza an tafi kaita sannan sai ga su Yaya Balki, Yaya Aina, Yaya Murja. Sai Zaitunan Matar Yaya Abubakar. Sun shigo kenan ana gaggaisawa sai ga Ma'u itama ta iso, Gwaggo daman tare da su Alhajinmu suka zo.
 

  Saboda gidan gaisuwa ne ya sa ba su yi min wata mgana ba mun dai gaisa. Sai can bayan an dawo daga kaita maza sun shigo sun yi gaisuwa masu tafiya sun tafi masu tsayawa suna ƙofar gida suna karban gaisuwa.
Yallaɓai mun yi sallama ya ce zai leka Office zuwa anjuma zai zo ya ɗaukeni, Alhaji mustpha ya zo, Alhajimu dai da Datti suna kofar gida Yaya Abubakar kuma ya tafi.

  A waya Yaya Auwal ya kirani na ba ma Inna Mariya ya yi mata gaisuwa  ya ce ya yi ma su Kawu Nafi'u ta wayar Alhaji, wasu ƴan uwan namu ma na daɗe ban gansu ba sai nuna ni ake yi ana faɗin diyar Rukayya ce marigayiya, muna gidan har dare, Ma'u da la'asar ta tafi, mun gaisa da fara'a kamar yadda nima ta yi min.  Anty Aina ma ta tafi ta ce za ta yi girki ita da Anty Balki, Anty Murja ce kawai sai ni da Gwaggo.

  Muna ɗakin matar Kawu Ali tare da su in da ake karɓan gaisuwa  Yaya Murja ta kalleni bayan mun idar da sallar mangariba.

"Kin kyauta Sadiya  har ni na kiraki kiƙi ɗauka na yi miki magana ta wasop nan ma shuru, ni fa yar gaskiya da gaskiya ce, daga kuma ƙin ta sai ɓata."

  Kallonta kawai na yi ban yi magana ba. Ta yi ta faɗa har ta na ce min"Ma'un da kika tsana ga ta nan da ita wajen gaisuwan nan in ba masoyinka ba waye zai yi maka haka? In ta biye ta naki ai da ba za ta zo ba."
 
  Kamar in yi tsaki sai kuma dai na fasa na kyaleta, Gwaggo ce  ta tsawatar  mata ta ce ta bar maganar Alhaji ya riga ya kashe ta. Ni dai ƙala ban ce mata ba na fahimci gwara na riƙa yin shuru zai fi mini alheri. A lokacin Rahila ta kirani ta yi min gaisuwa bayan mun gama waya Anty Maimuna ta kirani ta ce Tafida ya ce an yi mana rasuwa. Su Jidda suna gidan Nene in mun taso mu biya mu ɗauke su. Ta yi min gaisuwa na tambayi jikin Halima ta ce da sauki suna saka ran gobe su sallamesu su maida ta gidanta.

  Sai Taran na dare muka bar gidan, nan na bar Gwaggo tare da Alhaji za su koma gida, Yaya Murja ma ta na nan mijinta ɗan gareji ne in ya taso zai biyo ya ɗauke ta.
Sai da muka biya Gwamnaja muka ɗauko su Jidda, Baby ta makalemun tana faɗin"I miss u Umma."
Ina dariya na ce"Miss u more my Princess."

  Sun yi kitson su, sannan an siya musu sabbin lunch box da sock da sandal ɗin makaranta suna nuna min nace sun gode. Nene na falo zaune ta ji sauƙi ta yi min gaisuwa ta ce Maimuna ta faɗa mata da ta kawo su Jidda. Har Hajiya Iya sun yi min gaisuwa, sun ce in suka samu lokaci za su leƙa tunda Nene ba ta jin daɗi.

  Washegari Litini ma ban zauna ba. Amina ta iso daga kaduna ni kuma na tsaya a gida na yi girki sannan na tafi dashi. Ko da na je Ma'u ta yo abinci ta aiko da shi alale. Yaya Aina ma ta yo awara ta kawo hatta Gwaggo ta dafo abinci ta zo da shi, Rahila ma ta zo gaisuwa a ranar, haka muka yi ta jigilan zuwa har ranar uku, Hauwa ta zo mini gaisuwa ita da Mutaƙƙa. Muniran Nasir ta zo min gaisuwa, Anty Zabba'u kuma a waya muka yi magana tun da mijinta soja ne, Yaya Usman suna parthercourt ne su Yaya Hamza ma duk ta waya suka yi mana gaisuwa.

  Sai da aka yi uku na samu hutu a gida wannan zirga zirgan ya sa na ji duk jikina ba daɗi  sannan sai na yi ta ganin juwwa ban kawo tunanin komai ba sai rashin zama waje ɗaya. An sallami Halima tana gidanta ni ban ma je ba, Amina ranar huɗu ta koma kaduna ni dai ban sake komawa ba sai ranar biyar daga nan sai ranar da za a yi bakwai. Da la'asar kuma na wuce gidan Halima domin na ƙara duba ta. Tun da tun bayan da ta koma gida ban samu zuwa ba.
Sun ɗaga suna sai sati biyu sannan za a yi.

  Ban yi mamakin ganin Ma'u ba, saboda tana shiga dangin mijina da sunan ta na yi ma Anty Bahijja kara, ni kuma na san  ba haka ba ne, tana ganina ta taso ta tare ni, na saki fara'an da ke faman fuskata. Wacce itama nata iya saman fuskarta ne. Tare da ƙawarta Shema'u suke, wacce haɗuwa ce ta tun muna makaranta. Shema'u na ganina ta tare ni da fara'a tana fadin" Hajiyar Injiniya Afuwan. Ban ɗauka maganata ta ranar za ta yi miki zafi ba. Don Allah ki yi hakuri."

Mirmishi na yi mata kafin na ce"Ayya rashin fahimta ne. Ya wuce."

  Ban zauna wajensu ba na shiga cikin ɗakin mejego muka gaisa, na ɗauki Baby, ina kallo ta na gefe ta ce"Anty Sadiya ya haƙuri? Yaya Tafida ya ce an yi miki rasuwa"
Sai na amsa mata, muna ɗan taba hira su Sulahait ne a gidan sai Hauwa da Jamila, Hauwa ce ke ta aiki, kallonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login