Showing 42001 words to 45000 words out of 121577 words

Chapter 15 - TURKEN GIDA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

22 Sep 2025

3087

sai ni da Amina da ɗan abin da ba a rasa ba nan take na tura masa 20k cikin kuɗin da ke acct ɗina.

"Ga 20k nan ka lallaɓa zuwa karshen wata in sha Allahu."

Godiya ya yi mini kafin ya ce" Yaya Auwal ma turamin 20k zan ɗan yi siyayya kafin goben na wuce."

"Allah ya kai mu."

"Ma'u ta zo gida jiya muka haɗu na ce mata yau zan koma. Shi ne yau da safe ta kirani ta ce na je tana son ganina ta bani kayan tea da sabulun wanka da na wanki."

  Ya na mgana ina masa wani kallo sai da ya gama maganar sannan ya fahimta da sauri ya ce"Wallahi ba ni na roƙeta ba Yaya Sadiya."

  Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce"Allah ya ba da lada." Da na so na yi wata mgana sai kuma na fasa tuna nima na sauya taku akan Ma'u.

  Mun saki wannan hiran sai kuma muka kama na Yaya Abubakar a bakin Datti na ke jin shekaranjiya Zaituna ta kwaso rigima har da yan sanda aka kira mata. Ita wai uwar adashe ta cinye kuɗin jama'a. An ce dakyar suka ba da belinta sai dare da ta yi kwana cell.

  Mamaki ya kamani na riƙe haba ina faɗin"Kai matar nan wai har yanzu ba ta daina saka Yaya Abubakar a uku ba! Shegiya ka rasa abin da take yi da kuɗin jama'a sai ta jawo rigima ta bar ɗan'uwanmu da biyan bashin ta"

  Datti ya ce"Wallahi nima har mamaki na ke yi. Kuma shi Yaya Abubakar ɗin bai iya ɗaukan mataki a kanta ba."
Tsaki na ja kafin na ce"Yaushe wannan zai iya? Tun fa muna gida ni nasan Yaya Abubakar sai mace ta bautar dashi. Da dai irin su Ya Hamza ne kai kasan Zaituna ba ta isa ba. Shi fa yana jin sa kamar ba namiji ba"

  Datti na yar dariya ya ce"Sanyi gare shi ne."
Cikin jin haushi na ce"Sanyin me?  ya dai auro wacce ba ta san ciwon kanta ba. In bai tashi tsaye ba sai ta kashe sa lokacinsa bai yi ba"

  Datti dai ta na dariya. Ban san adadin awannin da muka ɗauka muna hira dashi ba. Ni a bakinsa na ji wai Alhajinmu ma ba shi da lafiya jiya ya yini da ciwon kai nace ni ba wanda ya faɗa min ya ce su Yaya Bahijja duk sun sani sun je sun duba shi har da Ma'u."

  Takaici ma ya hana ni mgana. Sai shi ne ganin raina ya ɓaci ya ce" Ƙila saboda sun ga bakya nan ne." Uhm kawai na ce ina duba agogon wayata tara da rabi na dare sai na zaro ido Yallaɓai bai dawo ba har yanzu.

  Wayarsa na kira ta na ringing amman bai ɗaga ba har sau biyu tuni zuciyata ta harba ina hashashen ko har yanzu yana can Ranon ne tare da ita? Ga Saude ta na jiran mu mu kaita gida ganin har goma ta yi Datti ya ce min zai tafi sai kawai na ce ya tsaya ya tafin mu da Saude gida.

"Ba nan take kwana ba daman?

  Ina miƙewa na ce"Ba a nan ba ne. ta zo ta kwana da yara. Yallaɓai bai dawo da wuri ba shi ya sa na ce ka wuce da ita."

  Sai ya amsa mini, ɗaki na koma na ɗauko 2k cikin jakata na wanda Yaya Hamza ya bani na fito. Sai na iske su afalo Datti ya ba ma su Jidda Chaculate din da ya zo musu dashi ya ce har ma zai tafi ya manta bai ba su ba.

  Na ba ma Saude 2k ɗin ina cewa"Yallaɓai bai dawo ba sai gobe zan shigo anguwan. Ki gaida mamanku sai na zo."
Ta karɓa tana min godiya Baby ta makale mata sai ta je dakyar na riƙe ta na ce ta bari ranar da ba makaranta sai su je can Ɗorayin su kwana.

  Har haraba na rakasu. Suna fita na rufe get ɗin muka dawo cikin gida. Ganin dare ya yi sai na rakasu ɗakin su suka yi shirin barci sai da na tabbatar sun yi addu'an barci sun kwanta sannan na rage musu hasken ɗaki na rufe musu ƙofa na dawo falon farko na kame kan kujera. Ga TV a kunne amman ba na fahimta duba lokaci kawai na ke yi a wayata har goma da rabi har sha ɗaya na dare Yallabai bai dawo ba. Bai kirani ba sannan na ƙara kiran shi amman bai ɗauka ba again.

  Na yi ta ƙokarin boye yanayina. Na zauna ina jiransa a falo ni kaɗai duk kwalliyan da na yi ta gama susucewa. Lallashin kaina kawai na ke yi ina zaune. Sha ɗaya da mintina sha ɗaya sannan na ji ana buɗe get da ƙaran shigowan mota.

  Ajiyar na sauke ina zaune har ya shigo falon. Muka haɗa ido dashi ya na shigowa da leda a hannunsa mirmishi ya ke yi min irin na shi mai sanyaya mini zuciya.
Amman sai na ji na kasa maida masa martanin mirmishin na shi, ya ƙariso har gabana ya na sauke ledan hannun shi ya ɗago kawai ni kuma na miƙe na wuce ma mukunnin wuta na kashe hasken falon na fice a falon na bar shi tsaye sake da baki yana bina da kallo.
Na sake kashe hasken falon na biyu daga nan na shiga tiolet na kama ruwa ko da na fito na same shi a cikin ɗaki yana tsaye kawai ya harɗe hannu a kirjinsa yana kallona.

  Yi na yi kamar ban gan shi ba. Na isa gaban wardrope na laluɓo rigar barcina. Ina shirin tuɓewa na ji ya rumgumeni ta baya ƙamƙam bayan ya sagalo hannunsa ya riƙe rigar barcin dake hannuna.

  Na ja shima ya ja kawai sai na sakar masa. Numfashi ya fesar min ta saman wuyana. Duk ina jinsa sai na yi masa bakam mugun haushin sa na ke ji da wani abu mai zafi da ya tokare mini a ƙirji.

"Sadiya ta. Fushin kike yi da ni?

Haka ya faɗa ya na mai zuro da kansa wajen fuska.
Kauda kai na yi kafin na ƙwace jikina ya juyo muna fuskantar juna ni da shi cikin basarwa na ce"Fushin me? Ka yi wani abu ne?

  Haka na faɗa kai tsaye kuma na miƙa hannu ina faɗin"Ba ni rigar barcina. Ina so na yi shirin kwanciya ne "
Sai ya maƙe kafaɗa alamun ba zai bayar ba. Ni kuma kawai sai na juya na sake buɗe wardrope ɗin na ɗauko wata itama yasake ƙwacewa na bar masa na sake ɗauko wata itama ya sake ƙwacewa a ƙufule na kalle shi kafin na kira sunan shi.

"Yusuf.."

Haka na faɗa ina tsare shi da ido. sai ya yi wani iri da fuska kafin ya ce" Yallaɓan naki ne kuma yau ya dawo Yusuf?

"Ai sunan ka ne ko ba sunan ka ba ne Yusuf?

  Na faɗa cikin gatse ina hararan shi. Sai ya yi dariya ni kuma sai na juya ina ƙara laluban wata rigar barcin kai tsaye ya ce" Ko sau dubu za ki ɗauko sai na ƙara ƙwacewa gwara ma ki tsaya mu yi mgana."

  Ni na san halin ɗan kayana. Shi ya sa na dakata na juyo ina kallonsa kafin na ce" Ni fa ba ka yi min komai ba. Kawai dai ina so na kwanta ne."

Takowa ya yi gabana ya saka hannunsa guda ɗaya ya riƙe min hannuna guda ɗaya ya zaunar da ni a gefen gado sai ya durƙusa a gabana lokaci ɗaya ya na riƙe duka hannuwana cikin tafin hannunsa.

"Am Sorry. Na yi dare. A gidan Baba Hajiya ta matsa mini sai na tsaya na ci abinci sannan kuma Tariq ya zo gida shi da iyalansa shi ya tsaida ni muna hira ban san dare ya yi ba. Na ga kiran ki ina hanya shi ya sa ban ɗauka ba."

  Har ya gama mganarsa ina kallonsa. Zuciyata ta ɗan yi sanyin jin ba abin da na yi tunani ba ne amman ban nuna masa ba sai na ƙara hade rai har ina kauda kaina gefe.

"Ki yi haƙuri kin ji ko? 

Ya faɗa ya na matse min yan yatsuna. Zare hannuwana na yi daga cikin na shi sannan na miƙe ina faɗin" Na ji."

  Daga haka kawai na fara ƙokarin tuɓe kaya da sauri ya taso ya rike ni lokaci ɗaya ya na faɗin"Ban riga na natsu na ga kwalliyar ba. Ballantana har na yaba na biya tukwaici shi ne kuma za ki hana ni samun wannan ladan?

  Ya faɗa ya na tsare da ido. A idanuwansa na fahimci ya gaji kuma ya na bukatar wanka ya huta. Sai kawai na ƙwace hannuna ina faɗin" Na yau dai ka makara. Amman ƙila gobe in ba ka makara ba ka  rabauta"

  Da sauri ya riko ni na faɗo jikinsa sai ya rumgumeni ya na faɗin" kin manta kin ce yau zamu sabunta amarci? Na taho mana da kazar amarcin mu part 2"

"Shima ka Makara. Amarci kuma ka gama shan romonsa shekaru goma sha a baya."

  Na faɗa ina ƙokarin kwace kaina kai sai ya juyo da ni muna fuskantar juna na buɗe baki zan yi mgana ya haɗe bakin mu waje ɗaya yana kissing ɗina ni kuma na ƙi bashi haɗin kai sai kawai ya matse min cikina da ɗayan hannunsa ɗayan kuma ya riƙe wuyana dashi tamau yadda ya matse bakin mu waje ɗaya in na ce zan ƙwace kaina da karfi zan wahala sai kawai na saki na miƙa masa kaina tare da ragamar rayuwata bayan nima na saka duka hannunawa na zagaye ƙugun shi.

  Mun daɗe muna sumbatar juna har sai da ya gaji sannan ya sake ni. Ya na maida numfashi ina maidawa. A tare muka kalli juna gira ya ɗagamin kafin ya ce" Amarya ta."

Hararan shi na yi kafin na ce" Haka ake Ango kai duk ya fara furfura? Ni jarumi ne angona."

  Na faɗa ina gyara zaman rigata da ya zame min. Wata dariya ya yi kafin ya ce"Bari in yi wanka yau ƙila da rabon har Gwaggo sai ta zo jinya ina ga."

  Ina jin haka na ɗaga hannu ina faɗin" Yallaɓai na."
Rigarsa ya cire yana yar ɗariya ya ce"Sadiya ta."
Na san halin shi wallahi in ya so mugunta in na shiga hannu har sai na dawo ina magiya. Har mamaki na ke yi Yallabaina kullum kamar ƙara masa ƙarfi ake yi. Duk da mun yi aure yana tashen samartaka.  Amman yanayinsa na yanzu ya na ninka yanayinsa a baya ne.

  Bin sa a baya na yi ina faɗin" Yallaɓai gajiyan tafiya ba ta sake ni ba. Ko na kwanta ne?

  Tiolet ya shige ya na faɗin"Ki kwanta mana na hana ki ne? Gwara dai ki yi ma kanki faɗa ki ɗauko kazar amarcinki a fridge ki fara ci kafin na fito. Zan karɓi maiƙon kazata a daran nan in sha Allahu."

  Nakwa nakwa na yi da fuska har lekoni ya yi yana dariya. Ba ni da mafita kitchen na fita na bude fridge ɗin na ga kazan dankwaleliya ce a faranti na sako mana kazar dai ta bakin shi ta sha maiƙo ga albasa da kabeji.

  Ruwa na ɗauko mana da lemu bedroom ɗin na kawo mana ba daɗewa sai gashi ya fito daga wanka ɗauro da Babban Towel a ƙugunsa ya ganni zaune saman cafet da farantin kaza a gabana.

  Ya kalleni sai ya saka dariya ni kuma sai na gimtse fuska cikin nishaɗi ya ce" Ke fa kika ce na taho da kazar amarci yau za mu tuna amarcin mu. Kin ga fa ke kika saka mini rai da kwaɗayi."

  Shuru na yi kawai na fara gutsiran kazan ina ci, shima sai da ya shafa mai ya saka gajeren wando sannan ya zo ya zauna ya na tayani cin kazan tun ina share sa har na saki yana bani a baki ina bashi mun ci kaɗan ba da yawa ba. Sannan na kwashe komai na maida kitchen sauran kazan kuma na saka a fridge.

  Wanka na shiga na gyara jikina. Bayan na fito na shafa mai na saka humra sai na saka wata rigar barcina ƙarama mai buɗewar gaba Yallabai na saman gado ya na jirana da na tsaya masa yanga ma tasowa ya yi yana faɗin" Kin san dai ina da karfin iya ɗaukan ki ko?

Cak ko ya ɗaga ni sama amman sai da ya yi nishi.

"Wai wai. A gaishe da Yusuf."

Ya faɗa ya na jinjina nauyina ni kuma sai na kwashe masa da dariya na ƙara hantsila kafata da ya sa na gagari karfinsa mu ka faɗa kan gado. Bin sa na yi na danne ina faɗin" Wayyo karfin Yallaɓaina ya fara ƙarewa."

Ya na jin haka ya mirgina ni na dawo kasan sa ya kalleni sai kawai ya girgiza kai ya sauka daga kaina. Gadon ma ya sauka gabaɗaya ya je ya kashe hasken ɗakin sanɗa ya fara yi in ganin duhunsa na yi gefe ina dariya ina faɗin" Yallaɓai wasa fa nake yi"

Ban tsira ba sai da ya yi sufa ya dira kaina a saman gado. Ya turmusheni yana faɗin" Ƙarfin Yallaɓai ya ƙare ko?

Ina ta dariya. Haka muka dinga mirgina daga kudu zuwa yamma kafin dai mu natsa sai da muka yi wassanin da muka saba. Ni da Yallaɓai muna da wasu abubuwan da in ba mu yi ba ba ma jin daɗi. Yallaɓai ya ɗauke ni a komai na shi haka nima, za mu yi ta wassani muna dariya kafin mu faɗa farantama juna, cakulckuli ya rika yi mini kamar zan shiɗe sannan ya bi ni ya danne ya haɗe bakin mu waje ɗaya.

  Baki shi ke yanka wuya. Domin da gaske amarcin aka sake maimaitawa. Ni fa har da su Mama na ke kira da asuba Yallaɓai na ta yi min dariya ko kallon shi ban yi ba. Dirza na sha a hannun shi har sai da na gane ba ni da wayau ta bakin shi ya ce ya goge reni ne ina tunanin ƙarfin sa ya kare har ce min ya yi ko mata goma ne budare zai iya da su a dare ɗaya ai sai na saki baki ina kallon shi. Domin ai Yallaɓai ya fi ƙarfina.

  Ranar bai fita ba a gida muka yini tare. Kuma ta bakin shi maiƙon jikina duk sai da ya gama siɗe shi. Sai dare muka samu fita zuwa ɗorayi muka je na duba Alhajinmu daga nan na shiga gidan su Saude na yi ma Balaraba godiya.

  Washegari na shirya ya sauke ni gidan Halima na ƙara gaishe ta. Tunda ban samu suna ba na kuma ɗan jima tun da har girki na yi mata ita kaɗai a gidan ga jego. Jawahir ce ke zuwa mata kuma ta koma makaranta sai ƙanwar mijinta itama kuma yau ɗin ba ta samu zuwa ba.
Muna ta hira a bakin ta ma na ke jin wai Yaya Usman zai ƙara aure mijin Zabba'u.

Na girgiza da jin zai ƙara aure. In na duba yadda Anty Zabba ta ke son mijin nan na ta bata iya haɗa shi da kowa ga ta da kishin tsiya. Halima na faɗa min saboda maganar auren bai faɗa mata har sai da aka saka rana ta yi ta tashe tashen hankula daga karshe ma ta yi yaji a mganar da ta ke gaya min ma tana gidansu anan kano.

  Sai uku na rana na koma gida saboda girki. Saude suna da walima sauka a islamiyarsu ba ta zo ba. Ni dai na yini ina mamakin auran Yaya Usman ko alama Yallaɓai bai faɗa mini ba Hauwa ma ina ga ba ta sani ba. Munnira mun kwana biyu ba mu waya ba. Ita kuma daman Anty Zabba ɗin ba ma yi sosai iyaka in an haɗu a gaisa ne kawai tunda ba ma garin suke ba in ba wani sha'ani ko rashi ba sai mu shekara ba mu ga juna ba. Daman mutuniyata Hauwa ce sai Munniran da ba kamar yadda muke da Hauwa ba.

  Mu da ɗan yawa mu surukan a gidan marigayi Alhaji inuwa. Mu shidda ne har da Amaryan muhammad Kabir da bai daɗe da yin auran ba. Shi likitan jini ne yana katsina yana aiki da medical center can ya ke zaune da matarsa.
Ni da yake kowa ya san halina ba ni da shisshigi kuma in ma ka shige min ba lalle na iya mu'amala dakai ba sai in Allah ya haɗa jininmu to ballatana ma mai hali irin na Anty Zabba da shigen takama da ji da kai. Ko don ta na taƙamar mijinta na ta kuɗi sannan iyayenta ma wasu ne babanta tsohon alƙali ne a jihar kano mahaifiyarta kuma daga masarautar zazzau ta ke. Ni iyakata da ita in an yi wani abu da ya kamata na kira ina kiranta itama an aka yi min rasuwa ko rashin lafiya ta kan kirani ta gaishe ni. Ba sanayyar da zan iya kiran ta na ji labarin abin da ya faru ko Halima saboda ta na yar gida ce shi ya sa ta ji labarin.

  Har wajen biyar na yamma ina ta tunane tunane na kasa ma tashi na ɗora girki. Na kira wayar Hauwa ba ta shiga na ji kanun labari in ta sani sai kuma ban same ta ba. Ni kuma ba na son kiran Munnira ko yaya ne ina ɗan rike girma na, ganin har su Jidda sun kusa dawowa makaranta ban yi girki ba ya sa na tube na shiga kitchen store na fara dubawa sai na ga gabaɗaya kayan abinci sun yi ƙasa shinkafa ba ta wuce tiya daman shine buhun ƙarshe sannan taliya kwara biyu macaroni ma ya ƙare indomie ma ina ga tun ina Zariya ta ƙare tun da daman ko da zan tafi ƙawayanni na bari.

  Shinkafa tuwo ce kawai ta rage da ɗan yawa. Na yi tagumi ina kallon store ɗin ko kayan su maggi robobin sun yi ƙasa na tuna suma tun watan can da ya gabata ba a siye su ba. Kayan abinci kuma daman in Yusuf ya samu kuɗi ya kan siya da yawa haka in shinkafa ne buhu biyu uku haka taliya da macaroni katan uku ko biyu da yawa dai yadda za mu daɗe ba mu nema ba. Ina tunanin gashi kayan abinci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login