Showing 9001 words to 12000 words out of 121577 words
to ɗayan biyu ne ko rasuwa ko an samu ƙaruwan aure ko na haihuwa.
Ina shiga ko sai na ga Hauwa Jamilu ce ta haihu ƴ'a mace, ƙawarta Samira Aliyu ne ma ta tura hoton Baby da sanarwan haihuwan, na ƙurama hoton Baby ido mai kyau da ita. Ina son haihuwa ina son na ƙara haihuwa har a cikin raina, ko a ina naga an yi haihuwa sai na ji dama ni ce ko da ace daga shi in na yi ba zan ƙara haihuwan ba.
Tagging na yi sai na yi mata barka a ƙasa kuma nace zan kira wayar ita Hauwan, duk da ban da wata ƙawa sanda muka yi BUK amman kuma ina gaisawa da mutane. Daga baya ma bayan mun gama makaranta na fi zumunci tun da in aka yi rashi ko ƙaruwa ko ban je na kan kira waya in kuma za a haɗa gudummuwa na kan tura nawa. Ina yin maganar Samira na Online ta yi min Reply.
"Amin Amin. S Yashe ku kam dai kun gama ko?
Sai na ba ta amsa da cewa" Mun gama me Samira Aliyu?
"Haihuwan mana, kin daɗe fa ba ki ƙara haihuwa ba ina jin"
Emojin mirmishi na tura mata ban yi magana ba. Ina gani Maijidda Bala, ta yi tagging ɗin maganar Samira da cewa" Ƴan boko ne matar Injiniya guda ko matar Yallaɓai zan ce?
Sai da na yi dariyan Sarari saboda ko username ɗina Sadiyar Yallaɓai ce a rubuce.
Kuma Maijidda Bala anguwanmu ɗaya, ta san gidanmu na san na su , duk halina na rashin son sakewa da mutane amman Maijidda na zuwa gidanmu saboda Rahila, to daman duk wanda ya zo gidanmu saboda Rahila ce ko Ma'u su ne masu jama'a. Ba zan taɓa mantawa da maganar Mama tun muna ƴan mata ta sha ce mini" Ke kam Sadiya da wuya ki ta shi aure ki ga jama'a. A yi mutum ba shi da son shiga jama' a kwata kwata."
A lokacin dariya na kan yi kafin na ce"Shike nan sai ke da Gwaggo ku ci min ƙawayen amarya."
Allah Sarki Mama Allah ya sa kina aljannah. Ban biye ma mangaganunsu ba na sauka saboda kar na manta nan take na kira Hauwa na yi mata barka, har tana mini tsiyan ni na gama na ji daɗi na. Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba. Saboda ko me zan ce ba za ta gane ba sai da na ji tana faɗin"Nima daga wannan na faɗa ma Baban Afnan na gama wallahi. Allura zan je a yi min na shekara biyar."
Da sauri na ce"Kul ɗin ki Hauwa. Karki yi wannan gangancin, in kika tsaida haihuwa na shekara biyar to za ki yi ta nadama har na shekaru ashirin ba ki daina ba. Saboda lokacin da kike son ki ƙara haihuwan ba za ki samu wannan damar ba."
Na faɗa ina jin raɗadin abin a cikin raina Hauwa ko cewa ta yi" Ko Sadiya? Sai kawai na rausayar dakai kamar tana ganina kafin na ce" Ku yi na gargajiya ko na musulunci Hauwa. Saboda haka ina gargaɗin ki in ba so kike yi ki ƙare a zuwa gaban Gynea ba."
Hauwa na jin haka sai ta ce to shike nan za ta yi magana da Daddyn Afnan duk yadda ta so na yi mata wata mgana ban yi ba saboda ba close na ke da ita ba, rayuwa ai darasi ne amman da zan buɗe mata cikina sai ta ji tunanin da ke cikin ranta ya fita ba domin komai ba sai tsira daga faɗawa irin halin da ni na faɗa.
Ina nan zaune ina ɗan duba wayata amman ban shiga group ɗin gidanmu ba sannan ban shiga na ɗaiɗaikun su da suka yi min magana ta private ba saboda nasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Fita na yi zuwa Instergram ina kallon kwalliya domin ni Allah ya yi da son abu fashion. Domin har certificate gare ni akam koyon kwalliya ba ma ɗaya ba sannan ina da na koyon saloon da gyaran jiki, shi ya sa wayata cike suke da ire iren su. Ban san na ɗau lokaci haka ba sai da Saude ta zo ta ce mini ta gama da ciki za ta gyara falo sannan na ba ta waje, bayan na ce in ta gama ta ɗora min ruwa a gas ta dafa taliya fara tunda ina da miya a firiza.
Bedroom na koma na yi zama ma ina ta kallon Videos ɗin yadda ake kwalliya da na ɗaurin ɗan kwalli a istergram daman ni can na fi auki, kiran sallar azahar ya tada ni na ijiye wayar na je na yi sallah lokacin har Saude ta tsane taliyan da na ce ta dafa guda biyu, ni na karɓe ta na ce ta shiga ɗakin su Jidda ta yi sallah ni kuma sai na fito da miyar na ɗumama.
Na saka ma kaina sauran kuma na bar shi a cooler. Ƙaramin falo na koma na kunna kallo sai na sauya tasha zuwa Mb2 na iske a wani film mai kyau sai na barshi, filet ɗin abincin na kan jikina ni kuma na miƙe kafata saman cafet ina cin abinci ina kallo har Saude ta fito sai na ce ta ɗauko kofin ta tsiyayo mini ruwa a Dispenser.
Sai ta kawo mini sannan na kalle ta ina faɗin" Ki ɗiba abinci ki ci sai ki zo ki wuce gida kin san kina da makaranta."
Da toh ta amsa min ta wuce kitchen ta diɓo taliyan ta zo ta zauna a kasa ta na ci, ba hira muke yi ba sai ni ce ma ke mata tambayoyi.
"Babanku ya dawo?
Sai ta ce min a'a sai na girgiza kai kawai, lagos ya ke zuwa kwadago in ya tafi sai ya yi rabin shekara bai dawo ba ya bar iyalansa da wahala.
Ni na riga ta tashi, na tafi da filet ɗin hannuna da kofi zuwa kitchen na saka a sink ɗin wanke wanke.
Leda na samu na buɗe drower ɗin cabinet ɗin kitchen ɗin na auna mata shinkafa tiya biyu sai taliya da maracaroni da na diɓar mata tunda nima abincin nawa ya yi ƙasa.
Bedroom na koma na ɗauko mata 2k daga cikin jakata sannan na dawo falon lokacin ta gama cin abincin sai na ce ta wanke hannu ta zo.
Ina zaune ta zo ta zauna gabana ta na faɗin" Ga ni Anty"
Ledan na tura mata gabanta lokaci ɗaya ina mika mata kuɗin hannuna ina faɗin"Ki kaima mamanku kin ji ko?
Ta karɓa tana faɗin"An gode Allah ya saka da alheri." Na amsa da Amin ina faɗin"Ki yi sauri ki hau mashin ne biyu ta kusa."
Sai ta amsa minI, tare muka fita saboda zan rufe gida tana fita na maida gidan na rufe na dawo falo ina kallo, film ɗin horror ne ya ɗauki hankalina sai da aka gama shi amman za a yi part 2 ɗin shi.
Uku na rana na koma ɗaki na kwanta sai barci ban ta shi ba sai huɗu da rabi, sai na yi alwala na yi sallah na ga tunda huɗu ta wuce sai kawai na ce bari na yi azkar ɗina.
Ni kaɗai a gida kamar mayya na matsu su Jidda su dawo sai shidda suka dawo saboda biyar da rabi ake tashin su kafin ya je ya ɗauko su shidda ta yi tunda makaranta boko da isalamiya ne. Dawowarsu ne ya sa na fito falo suna bani labaran makaranta suna cin abincin, Baby ce mai surutun Jidda irin Babanta ne tana da sanyi sosai ba kamar Baby ba.
Suna gama cin abinci suka sauya kaya zuwa na gida. Unform ɗin Jidda ta ce za ta wanke na ce yamma ta yi, tunda suna da guda biyu ta bari zan wanke musu gobe da safe
Tare muka yi sallar mangariba, muna idarwa a ƙaramin falo muka fara karatu. Jidda na suratul maryam ne Babby kuma tana ƙasa ƙasa sai da suka biya na jiya na ƙara musu sannan muka yi azkar tare. Muna gamawa sai muka miƙe muka yi isha'i tunda an kira. Muna idarwa na bar su a falo suna kallo ni kuma na shiga kitchen na dafa ma Yallaɓai tea daman na dafa masa farar shinkafa tunda shi taliya ba ta dame shi ba, ina gamawa na shiga wanka ina wankan ma na ji shigowar motar Yallaɓai.
A gurguje na shirya cikin riga da wando, wandon plazo ne mai buɗewa ta kasa. Rigar kuma Top ce mai wuya ta kama jikina sai na gyara gashin kaina na tufke a tsakiya na saka wata hula mai love a saman kaina kalan pick . Tsakiya babu komai, kwalliya na yi kamar yadda na saba na saka jan baki na kamar yadda na saba.
Na ji ƙaran bude ƙofa ganin bai shigo ba ya sa na san ya shiga tiolet ne.
Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ina zaune a gefen gado ina bin shi da mirmishi bayan na amsa sallamarsa.
Hannuwana ya buɗe minI na tashi da sauri na faɗa masa ya rumgumeni. Nima sai na ƙamƙamesa ina fadin"Barka da dawowa Yallaɓai na."
Ya na shinshina ƙamshin humran dake jikina ƙasa ƙasa ya ce" Uhm. I like it."
Ɗagowa na yi muna kallon juna kafin na ce'Me? Yana mini wani kallo ya ce"ƙamshin ki mana."
Far na yi masa da ido kafin na ce"All is yours"
Kumatuna ya shafa kafin ya ce" Allah ya yi miki albarka." Na amsa da Amin.
Ruwan wanka na ce zan haɗa masa ya yi wanka sai ya ci abinci.
Shi kuma sai ya ce"E. sai mu ta fi wajen kiran Alhaji ba"
Gyaɗa masa kai na yi ba tare da na yi mgana ba. Sanda ya shiga wanka ni kuma na je haɗa masa abinci bayan ya fito ya sauya kaya zuwa wani yadi riga da wando ɗinkin zamani. Falon farko mu ka je saman dining ya ci abinci su Jidda kuma suna ƙaramin falo
Bayan mun gama ba mu tsaya ɓata lokaci ba ya ce na saho hijabi mu ta fi, daman na fito da Hijabin jalbab mai ruwan ƙasa har ƙasa sai na saka takalmina iri ɗaya da wanda Yallaɓai ya saka daman tare ya siya mana.
Na ce musu Jidda su kula da gida za mu je gidansu Gwaggo mu dawo. Baby taa saka rigiman sai ta je Babanta ya tsaya yana lallashinta da zai siyo mata ice cream sannan ta yarda na ce in za su kwanta su kashe komai za mu fita da key da toh Jidda ta amsa da yi mana a dawo lafiya.
Sai da muka fita da motar sannan Yusuf ya koma ya rufe get ɗin
Sannan ya dawo muka kama hanya mun ɗauki hanya kenan na kalle shi kafin na ce" Na gwada kiran ka yau ban same ka ba."
Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce"Nima na kira ki ban same ki ba."
Sai ya kalleni kafin ya ce"Me ya faru?
Kai tsaye na ce"Kan mganar komawata Abu shika ne, Uncle Abba bai ƙara kiran ka ba?
Sai a lokacin ya tuna ya ce"Kash! Ya kirani amman shaf na manta ba mu yi mganar ba. Amman bari yanzu zan kira shi."
Ni ya miƙa ma wayar ya ce na kira shi, Kawu Abba daman ya saka masa da na kira sai na saka a speaker har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.
"Kawu barka da dare."
Shuru bai yi mgana ba.
"Uncle Abba barka da dare"
Wata murya a dakushe ya ce"Yusuf in ma bashi kake nema na kuɗi ba ni dashi wallahi. Wanda ma nake binka EFCC ne za su ƙwatar mini haƙƙina."
Daga ni har Yusuf sai da muka kyalƙyace da dariya.
Ni ce na ce"Haba Uncle Abba ba amana yanzu sai ka kai mini Yallaɓai EFCC?
Jin muryata ya sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce" Sadiya? daman kina kusa? Na amsa masa da e, sannan muka gaisa dashi.
Shi kuma sai ya bige da faɗin"Yallaɓan nan naki ya ci bashina kamar gadon ubansa yaƙi biyana. Gwara babbar hukuma ta shiga ciki, in na je gaban manya sai a saka sanayya a ciki gwara a kame shi ko amansu ne sai ya yi."
Yusuf na dariya ya ce" Na ci fa halas, abin da ya yi Nene shi ya yi ka fa Kawu Abba." Kai tsye ya ce"Ko? To ai ko ita Nenen ta ci kuɗina sai ta biyani ballatana kai."
Ni dai ina ta dariya ganin sun sarƙe da gaddama shi Yusuf ya na faɗin ya ci halas kawu na fadin shi ba ƙanin Uban shi ba ne na uwarsa ne bashi da gadonsa. Zungurin kafar Yallaɓai na yi sannan ya yi gyaran murya yana fadin"Sadiya ta ce a yi maka tuni ka yi mganar da Dr Fadil ɗin?
Kawu Abba dagacan bangaren ya ce"Kash na manta. Amman bari na kira shi na ji yadda muka yi zan kira ka."
Sai ya kashe wayar, dai dai Yusuf na faɗin" Kina ganin komawarki can da ganin likitan ba damuwa?
Sai na gyaɗa mai kai ina fadin"E, ba matsala can ma ƙwararru ne. Tunda na yi ta nan ban dace shi ne aka ban shawara na gwada can ɗin."
Sai ya jinjina kai, bai yi magana ba sai ni ce na cigaba da faɗin"In ina da appoitment na ganin likita tun ana gobe zan je zariya na sauka gidan Ya Hamza bayan na gama ganin likitan sai na dawo."
Kai tsaye ya ce"E hakan ma ya yi. Allah ya sa a dace."
Na amsa masa da Amin.
Mun shiga anguwan ɗorayi kawu Abba ya sake kira ya ce sun yi mgana da abokin nashi Dr Fadil shi likita ne a bangaren zuciya amman ya ce ya yi ma wata Dr Nayami mgana musulma ce amman ba bahaushiya ba ce, ya ɗan yi mata brief na matsalata ta ce zuwa sati mai zuwa za ta iya bani appiotment in har ya tabbata zai kira Kawun ya sanar dashi.
Jin haka ya sa sai na ji daɗi kamar na je ta shaida mini zan iya sake samun wani cikin haka na riƙa ji. Daidai lokacin Yallaɓai na gyara parking a kofar gidanmu da ke anguwan Ɗorayi.
*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
09069067488.
08032773332.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*
*Janafty*
*03/10/2024*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z
*🅿️03*
Gidanmu na nan a farko layin shiga anguwar Ɗorayi. Yanayin fasalin gidan babba ne sannan tun daga waje za ka fahimci tsarin gidan na tsohon ɗan boko ne.
Domin Alhajinmu kafin ya yi Ritire(Ritaya) sai da ya riƙe mukamin babban darakta na kamfanin wuta na jihar kano(KEDCO). Bayan kasancewarsa manomi. Kuma gidanmu na da ga cikin rukunun gidajen da suka daɗe a anguwar tun da sama da shekara ashirin duk da ko mu kanmu muna da wayau lokacin da muka dawo gidan tun a wancan lokacin zamani na kwance. Sai dai yanzu lokaci bayan lokaci yana samun ƴan gyare gyare da kwaskwarima daga su Yaya Hamza.
Ni na fara fitowa daga Motar. Yallaɓai na kuma an kira wayarsa ya tsaya a mota ya na mgana.
Kofar gidan namu tar da hasken wuta gabaɗaya ma anguwa akwai hasken ƙwakwayen da suke kofar gidajen wasu mutane dake cikin rukunin anguwan ta Ɗorayi.
Gidanmu na ke kallo ina tuna wasu shuɗaɗɗun al'amura da suka faru damu a cikin gidan masu daɗi da akasin su. Yallaɓai ne ya katse min tunani da cewa" Kin ga ko na manta ɗazu musabahu ya zo offishina ya bani saƙo ya ce in ji Yaya Muntari mijin Rahila."
Sai a lokacin na ɗago ina kallonsa ya fito daga mota ya na nuna min kullin abu a baƙar leda, yadda ya ga na taɓe baki ya sa ya san tabban nasan da saƙon.
"Bar shi a motan kawai."
Bai yi musu ba sai ya koma cikin motar, ina hangensa daga waje ya buɗe akwatin motar ya jefa sannan ya fito yana ƙoƙarin rufe motar hasken wata mota da ke tunkaromu ta kashe mana ido daga ni har shi sai da muka saka hannuwammu muka kare fuskokin mu dashi.
"Kai. Waye wannan da ba zai rage filita tunda ya shigo cikin anguwa ba."
Na kasa magana ne saboda mamakin ganin motar ba wucewa ta yi ba, kusa damu itama ta gyara parking, tun kafin ma na ciki su fito na shaida su waye tun daga cikin motar akwai hasken fitila.
"Ma'u ce.."
Haka na faɗa a cikin raina dai dai san da ta buɗe murfin mota ta fito shima mijinta ya fito daga can bangaren direba.
"Alhaji Mustapha ne, da Ma'u ashe."
Yusuf ya faɗa ya na sakin mirmishi, na kalle shi wani abu ya yi mini tsaye a zuciyata. Lalle Alhajinmu wato zaman yau bayan ni da Ma'u har da gayyar mazajen mu kenan?
Kara haɗe rai na yi, ganin Ma'u na nufoni shi kuma Yusuf ya nufi Alhaji Mustaphan shi adole ya ga ɗan'uwan mijin yayarsa. Ƙaramin tsaki na ja dai dai lokacin da Ma'u ta ƙariso kusa da ni ta na faɗin"Sadiya kema Alhajinmu ya kira ku ne ke da Injiniya?
Ta faɗa lokaci ɗaya ta na ɗora hannunta saman kafaɗata. Sai na ji kamar ta ɗora min cuta da sauri na kauce ina yi mata wani irin kallon ke ki kiyayeni. Ita kuma ta na bi na da wannan munafukin mirmishin nata na yaudara.
Ƙoƙarin sake matsowa kusa da ni take tana yi min mirmishinta da ba alheri a cikin sa. Tsaki na ja mai karfi na juyawa na fara tafiya zuwa ƙofar da za ta sada ni da cikin gidanmu na ji muryan Ma'u da ɗan karfi ta na faɗin"Haba Sadiya. Ke shike nan abu ba ya wucewa a wajen ki? Na yi ta ba ki haƙuri fa?
Sai da na kai kofar gidan sai na juya ina kallonta sai na ga har su Yusuf ma sun dawo da hankalunsu kan mu, dariyan gefen ba ki na yi. Ni ai sai dai na rubuta littafi guda akan maƙircin Ma'u daman ta yi ne domin hankulansu ya dawo kan mu, shigewata cikin gida na yi ina ji Yusuf na kiran sunana