Showing 39001 words to 42000 words out of 121577 words

Chapter 14 - TURKEN GIDA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

22 Sep 2025

3055

Saude mu ka gaisa.

"Saude ya gidan ne? Fata komai lafiya ko?

Sai ta amsa mini da lafiya lau kafin ta ce"Anty yaushe za ki dawo? Kai tsaye na ce" Gobe in sha Allahu."
Fatan dawowa lafiya ta yi mini ni kuma na ce zan ƙara kiranta in su Jidda sun dawo daga makaranta.
Daga nan sai na kunna Data saƙonni na ta shigowa. Maganar Yaya Auwal na fara gani na yi saurin buɗewa.

"Zan shigo wannan weekend ɗin fa."

  Cikin jin daɗi na rubuta masa Allah ya kawo shi lafiya.

"Kai da Laila da yara ne?

Yana online amman sanin halin shi da sai ka yi saƙo sai ya ga dama zai buɗe sai na fita, ina duba sauran saƙonnin sunan MA'U da na gani ta yi mini magana ya sa na yi tsaki na wuce ta, na ga an yi mgana a group ɗin gidanmu ban shiga ba domin ban ga an yi tagging ɗina ba kenan mganar ba ta shafe ni ba. Amina ce ta yi min mgana da cewa ta kira waya ta ba ta samu ba na ce mata network ne.

  Sai na fita na je bangaren Status ina ta dubawa. Rahilarmu na ga ta saka status har ina rawan jikin dubawa. Ya Muntari na gani ya na riƙe da jaririyar(Zainab Nihad) ba hoton ne ya ba ni dariya ba, sai rubutun da ta yi a ƙasa.

"Hubby na. Abu Zainab I love u."

  Dariyan da na saka har a sarari, na danna Viocenot ina ƙyaƙyata ma ta dariya kafin na ce"Rahila ma su Hubby, wai Ya Muntarin ne kuma ya koma Hubby? Daga Yaya Muktar ya koma Hubby."

Bayan nan na sakin mata VN ɗin. Sannan na riƙa jere mata sticker na shaƙiyanci.
A yammacin nan dai status ɗin Rahila ne ya nishaɗantar da ni. Ba ta online, abin mamaki shima Ya Muntarin na ga ya yi sreenshoot ya saka a jikin sunanta My Baby.
Haka na ke ta dariya shima sai da na yi tagging ɗin shi.

"Su Ya Muntari Hubby manyan ƙasa."

Ya na online ya turo mini Emojin dariya kafin ya ce"Ke ko? Sadiya dai ta raina Yayan nan na ta ko?

Emojin dariya na tura masa sai na jin kunya sannan na ce"Wace Sadiya ta raina Ya Muntari. Allah ya bar Ƙauna Hubbyn Rahila ta."

  Ni kaɗai a ɗaki ina ta dariya ina tuna wani zamani a can baya har gobe ban manta lokacin da Ya Muntari ya zo gidanmu ba. Mama Allah ya jiƙan rai ta ce" Ya sunan ka ɗan samari."

"Muntari. Muntari sunana Hajiya."

Sai na ji wata dariya ta ƙara kamani har ina buga hannuna a saman cinyata, lokacin da Rahila suka fara soyayya da Ya Muntari ba wanda ya sani, wata rana kawai ya shigo gidan kowa na gaishe shi, da kuma sunan da muke kiran shi kenan  Ya Muntari.

"Barka da dawowa Ya Muktar."

"Yauwa Sannu Rahilatu."

Sake baki na yi ganin yadda Rahila ta wani sunne kai tana dariya, shi ma ya na mata wani kallo. Ba zan manta ranar ba ina bakin famfo ina wanke wanke ita kuma tana bakin madafi ita da Ma'u suna gyaran wake.

  Ga mamakin sunan da ta kira shi. Ga wani kallo da suke ma juna. Tun daga ranar fa Rahila, ta daina kiran shi Ya Muntari sai dai Ya Muktar har faɗa mun sha yi da ita, in na ce Ya Muntari.

"Kai Sadiya. Ba fa Muntari sunan shi ba. Ba ki iya cewa Ya Muktar, muktar ne fa sunan kuke ɓata masa da sunan tsoffi wai Muntari."

  In ta ce haka sai na balla mata harara sannan na ce"Ke kika san Muktar. To da bakin sa ma ya ce sunan shi Muntari ko Gwaggo?

  A lokacin Rahila ta riƙa tura baki kenan ta na ƙunƙuni. Ta yi ƙokarin sauya sunan Muntari zuwa Muktar amman bai sauyu daga bakina ba, da gayya ma ma ke faɗa Ma'u dai da ya ke makira ce har wani ƙalƙala take yi wajen faɗin sunan.

"Ya MUKTARR."

Makircin Ma'u fa haifaffan ne, ta tsotsa a nono ne shi ya sa in ta buga acting ke yi mata kyau.

  Haka Khaleesat ta zo ta same ni ina ta dariya. Domin mun yi dogon charting da Ya Muntari yana tamnbaya ta laifin me suka yi tun ranar suna Rahila ta ce ban dawo ba, na fa san Rahila ta faɗa masa dalili zai yi min wayau su na maza ne ni ko na ce ya tambayi matarsa ta san dalili.

  "Ke da waye kike ta dariya haka? Ko Yallaɓan ne?

  Ina mirmishi na ce"Wani Yallaɓan? Wai wannan Hubby na Rahila ne."
Ina faɗa ina dariya Khaleesat ta kwashe da dariya kafin ta ce"Au kema kin gani? Nima yanzu na gani ina ta dariya a raina na ce Rahila manya ta Muntarin ta."
  Miƙewa na yi daga kishigiɗen da na ke ina faɗin" Ta fa kashe wannan sunan. Muktar ko Hubby."

Na faɗa ina kwaikwayon bakinta ni da Khaleesat har muna tafawa saboda dariya, Ita kuma faɗi ta ke yi" Ni ya na burgeni ba shi da damuwa. Ga barkwanci kuma ya na son Rahilatun nan ta bakin shi ba."

  Jinjina kai na yi kafin na ce"Ai Muntari na ƙaunar Rahilatu."

"Sadiya ba ki da dama, na shigar ma Rahila. A bar yankan mana Hubby ahto.'"

  Ni dai ina ta dariya. Sai kuma mu ka cigaba da hiran Rahila da Ya Muntari muna cin dariya. Kukan Amna daga bedroom ɗinsu ya sa Khaleesat ta bar ɗakin da sauri ta fita ba daɗewa mijinta ya dawo sai ban ƙara ganinta ba sai dare wajen dinner.

"Sadiya Ya ya? Fatan dai ba matsala ko?

Yaya Hamza ke tambayata. Bayan mun haɗu a Dinining muna cin abinci.

"Ba wata matsala. Yanzu dai ta yi min transfer zuwa Aminu kano ta haɗa ni da wata consultan."

Da kai ya amsa kafin ya ce" Tunani mai kyau.'" Daga nan
bai sake mgana ba. Shi ya fara tashi kafin ya goge bakin shi da Tissue sannan ya kalleni ya na faɗin" Yaushe za ki wuce? Ina kallonsa na ce" Gobe in sha Allahu"

"Ba ki bari weekend mu shiga kanon tare"

Kai na girgiza kafin na ce"Ya Hamza. Yara su kaɗai a gida Yallabai kuma ba ya zama in ya fita tun safe sai dare."

  Ya na wucewa falo ya ce"Wasu yara? Yallaɓan dai amman Jidda yarinya ce? Shekaranta nawa?

"13 in to 14 fa Ya Hamza. "

"Ehem.."

  Ya ce kawai alamun maganarsa ta farko dai itace Yallaɓai dai ina dariya khaeesat na faɗin" E, mana Yallaɓai dai take yi ma kewa kar ta ƙara kwana ta barshi shi kaɗai."

  Mirmishi na yi kafin na rage murya ina faɗin"Da shi ɗin ma, mata ba ta yi kewar mijinta ba? Miji mai kama da dubu irin Yallaɓai na."
Harara ta zuba min kafin ta ce"Mu kuma na mu mazajen masu kama da bolar sharar ki ko?
Ina dariya na ɗaga hannu ina faɗin" Ba ruwana.".

  Ba ta biye min ba, nan ta bar ni ina ƙarisa cin abinci ta bi mijinta falo suna hira nima ina gamawa ganin mata da miji na buƙatar privacy sai na ce musu zan shiga na kwanta. Ina shiga na yi shirin barci Yallaɓai na kira an ci sa'a yau ɗin ya koma gida da wuri.

  "Yaushe za ki dawo? Yallaɓan Sadiya ya yi kewarta sosai."

  Ina jin kewata a muryansa nima cikin muryan kewan na ce"Gobe gobe nan Yallaɓai. Kwana biyu ban ji ɗumin ka ba kamar ban da lafiya Am baby na."
Kalamai na ƙarshe suka bashi dariya har sai da ya dara, hira muka yi sama sama na ce ya haɗa ni da su Jidda ya ce suna falo suna kallo tare da Saude.

"Ki dawo gobe Sadiya ta. Da gaske Yusuf ya yi kewar HalimatuSaddiya."
Ina mirmishi kamar ya na ganina na ce"In sha Allahu Yallaɓai na."
Mun ɗan dade muna waya ina ta bashi labarin Ya Muntari fa ya koma Hubby ina dariyan shaƙiyanci ya ce"In kika dawo za ki haɗu da Rahila kun fi kusa."

  Hiran sa ya ɗauke min hankali na tsawon lokaci sai da ya ce min zai yi wanka sannan muka yi sallama.
Nima daga nan na ijiye wayar na yi addu'an barci ba daɗewa sai barci.
Yallaɓai na baya son tafiyan dare ya sa da wuri na shirya. Kafin Yaya Hamza ya fita sai da ya sake ba ni 10k ya ce na yi na mota sai na yi kawaici na ce"Yallaɓai fa ya ba ni na mota ina ta saka ka ɗawainiya Ya Hamza"

  Wani kallo ya yi min ban san lokacin da na karɓi kuɗin ina cewa" Allah ya ƙara ma nema albarka."
Kai tsaye ya ce"Amin. Yallaɓai mijin ki ne, ni kuma Yayanki ne kin ga ne? Sai na ɗaga masa kai ina danne dariyata. Mun rabu ya ce shima suna tafe karshen Sati na ce gida zai yi albarka Zaratan Alhajinmu za su yi hutun karshen mako a gida.

  Ƙarfe goma mu ka yi sallama da Khaleesat daga nan na hau adaidaita zuwa tasha ina zuwa motar kano saura mutum huɗu na shiga ba daɗewa ta cika muka tashi. Ban samu Yallaɓai a waya ba sai na yi masa saƙo.

Mun shiga kano ɗaya da wani abu ne. Daga tasha na samu abin hawa sai gida. Ba key a hannuna sai na buga get ɗin Saude ta zo ta buɗe mini tana ganina ta washe baki ta na faɗin"Sannu da zuwa Anty Sadiya."
Ina shiga gidan na ce"Yauwa Saude ya gidan"
Ta biyo ni tana karɓan ƙaramin akwatina.
A falon farko na jaɓe ta kawo mini ruwa na sha na huta sannan na iya tashi na ƙarisa ciki na ɗauro alwala na gabatar da sallar Azahr da ta suɓumu ce mini a hanya.

*Janafty"
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

*🅿️08*

Ina idar da Salla Saude ta kawo mini abinci shinkafa da miya ce, daman na yi miyata tun kafin na tafi Zariya.

Ban iya fita ba a cikin ɗaki ta kawo mini komai na ci ta kuma zo ta ɗauke filet ɗin da kofin ruwa. Ni na ce ta jira su Jidda su dawo daga makaranta sai ta tafi saboda yau ɗin ba su da islamiya. Saude ba ta karatun boko amman tana allo tana kuma islamiya.

Khaleesat kawai na iya kira na faɗa mata na isa gida lafiya sai Yallaɓai da na kira bai ɗauka ba sai na tura masa saƙon na sauka lafiya.

Daga nan na haye gado na kwanta sai barci daman na gaji bayana har wani sagewa ya yi. Barci na sha sai la'asar na iya tashi da na ji kiran salla daga masallacin gefen mu. Daƙyar na iya tashi na shiga tiolet na ɗauro alwala na yi salla. Sai bayan na yi sallah sanna na samu daman rage kayan jikina saboda ɗazu gajiya ya sa ban iya sauya kaya ba kawai na kwanta.

  Daga ni sai siket na ciki under. Sai bra na zauna a gefen gado ina duba wayata. Sai na ga Rahila ma ta kira ita da Datti.
Kiran Datti na fara bi bayan mun gaisa sai ya ce.

"Yaya Sadiya kin dawo ko kina can Zariyan ne?

Kai tsaye na ce"Na dawo ɗazu. Ya aka yi ne? Su Alhajinmu dai lafiya ko?

"Kowa lafiya. Zan koma makaranta gobe ne ina so na shigo yau da daddare."

Kai tsaye na ce" To sai ka zo."
Daga haka muka yi sallama. Sai na bi bayan kiran Rahila kamar ta na jira ta yi zaraf ta ɗauka.

"Sadiya Allah ba na son wulaƙanci."

  Ina danne dariyata na ce"To Sadiya yar laifi. Me kuma na yi?
Cikin jin haushi ta ce"Ban sani ba. Sunan mijin nawa ne abin shakiyancin ki?

Ina dariya na ce"Allah ya huci ran gimbiya Rahila a gidan Hubby."

Ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce"Shegiya Allah zan rama ne."

"Ba a kira mu sunan sabon sunan Ya Muntari ba? Ko ba a riga an yi taron ba ne?

Na san ta buɗe baki ne ta kasa mgana saboda yadda na ji ta yi shuru. Fahimtar haka ya sa da sauri na ce"Allah ya huci zuciyar My Baby"

Tsaki ta yi mai ƙarfi ta ƙatse wayar ta barni ina ta dariya. Sake kiranta na yi ba ta ɗauka ba sai na kyaleta. Ijiye wayar na yi na tashi na saka wata rigata ta zaman gida yar doguwa mai sauƙin kwari sannan na fita falon farko na iske Saude zaune ita kaɗai ta na kallo.

  Zama na yi nima ina ta ya ta. Kallonta na yi kafin na ce"Ko za ki bari in Yallaɓai ya dawo ne mu kai ki gida Saude?
Kanta na ƙasa ta ce"To Anty"
Saboda in samu in yi ma Balaraba godiya sannan mu ƙarisa gida in gaida su Alhajinmu.

  Muna nan a falo biyar na yi na ce ta mayar mini Tauraruwa an fara Indiyan hausa sai ta sauya mana tasha ana wani film mai kyau, har su Jidda suka dawo daga makaranta suna ganina gabaɗayansu suka faɗa jikina suna murnan ganina nima da fara'ata na tare su Jidda da ta yi girma ban iya ɗaga ta ba, amman na ɗaga Baby sama ina mata dariya.

  Faɗi take yi" Umma mun yi kewarki."
Ina shafa kumatunta na ce"Nima na yi kewarku ƴa'ƴan Umma."

  Ni na cire ma Baby Uniform na kuma zauna tare da su suka ci abinci suna ta bani labarin makaranta ina sauraransu. Bayan sun gama cin abinci na ce Saude ta taya Jidda su wanke Uniform ɗin su da safuna. Suka bar mu ni da Baby a falo tana ta min labarai ina sauraranta zuciyata kamar farar takarda saboda farincikin na dawo gida na ga iyalaina cikin koshin lafiya.

  Har aka kira mangariba lokacin su Saude sun dawo cikin gida sun gama wankin na ce su yi awala su yi salla. Ni ma na shiga ciki na ɗauro alwala na yi sallah ina kan darduma ina azkar na ɗauki wayata abin ya ba ni mamaki na ganin Yallaɓai bai kirani ba kuma na san ya ga kirana kuma ya ga saƙo na.

Ban yi fushi ba sai na sake kiran shi sai da ta kusa katsewa ya ɗaga kirana.

"Yallaɓai na."

  Dagacan bangaren na ɗan ji hayaniya ban kawo komai ba sai na yi tunanin ƙila yana wani waje na mutane sosai.

" Ina Rano. Amman yanzu zan taso."

Haka kawai ya ce mini. Cikin mamaki na ce"Rano kuma? Aikin ne ya yi dare haka?

"A'a. Tun dazu muka tashi na biya gidan su Nene ne. Yanzu dai ina gidan Baba ne."

  Kai na gyaɗa kafin na ce"Allah Sarki. Ka gaishe su."
Sai ya ce mini za su ji, naji ana mgana a kusa dashi ban gane da muryan ba amman ta mace ce.

Ina shirin mgana na ji ya na ce min" Ga Sameena ta dawo daga kano yau."
Bai bani damar mgana ba kawai na ji muryan Sameena.

  "Matar Baba ɗazu da rana na dawo gida. Ashe sai yau kika dawo?
Sai na amsa mata. Mun gaisa sannan tace za ta sake dawowa in sha Allahu.

"Ko kafin ki dawo ni na zo ba."

Tana dariya ta ce"Allah ya sa'
Daganan muka yi sallama sai ta miƙa ma Yallaɓai wayarsa.

"Yallaɓai ka dawo da wuri. Ka siyo min kaza a hanya saboda yau za mu sabunta amarci ne."
Na faɗa cikin wani salo. yar dariya ya yi kafin ya ce"Amarya ko? To shikenan ango zai taho kazar amarci.'
Ya faɗa kamar cikin raɗa domin na ji ya rage murya.

  Mirmishi na saki kamar yana ganina na buɗe baki da niyyar mgana kenan na ji muryanta. Muryan da ba zan manta da ita ba saboda daban take. Ko mgana za ta yi cikin isa da gadara da salo. Kuma kamar ta fi yin salo matuƙar da za ta yi mgana da Yallaɓai.

"DADDY. Ba ka ji ba."

Yaushe ta zo garin? Haka na ke tambayan kaina a cikin raina. Baki na saki lokacin da na ga kawai Yallaɓai ya katse wayar ba tare da ma mun yi sallama ba.

Gabana ya faɗi Ras!. Amman sai na lallashina kaina da cewa duk tsiyanta dai ita yanzu matar wani ce. Ba ta isa ta bibiyan min miji da auranta ba ko ita ta yi Yallabai na aminattace ne ba zai taɓa biye mata ba.

  Kauda tunanin komai na yi a cikin raina na tashi na cire hijabin da na yi sallah. Gyaran ɗakin na fara duk bai da datti na san Yallaɓai na gyarawa. Sai da na share na gyara gado na goge komai na saka turaren wuta a ɗaƙin ya ɗau kamshi sannan na shiga wanka. Daga can na ɗauro alwala na fito bayan na shafa mai na yi kwalliyata kamar yadda na saba domin Tarban Yallaɓai na cikin zumuɗi da muradi mai girma. Da gaske ne na yi kewarsa sosai.

  Ina sallar isha'i Jidda ta shigo ta na faɗa mini Uncle Datti ya zo. Shi ya sa ina idarwar na ɗauko wayata zuwa falo ina sanye da riga da wando na wani material na saka mayafi abaya baƙi a saman kaina ina tashin kamshi. Kaina ba kitso har lokacin amman ina tunanin zuwa gobe zan je a wanke mini na yi kitso.

  Mun gaisa da Datti da tambayan su Gwaggo ya ce duk suna lafiya. Saude na ce ta zuba masa abinci. Bayan ta kawo masa na ce ta ja su Jidda ɗakin su ta zauna kafin Yallaɓai ya shigo.

Datti na cin abinci muna hira sama sama.

"Na ɗauka sai wani satin za ka koma. Ya Auwal na tafe wannan weekend ɗin fa."

  Sai da ya sha ruwa sannan ya ce min" Na so haka amman ranar Friday an saka mana wani test ne, ina bukatar komawa na yi karatu"

  Kai na jinjina kafin na ce"Haka ne. Allah ya bada sa'a. "
Da ya ke yana karatu ne A kaduna state University KASU"

Ko bai faɗamin ba na san abin da ya kawo shi. Alhajinmu yanzu ba kuɗi duk suna gona daman karatun na su shi Ya Auwal  da su Ya Hamza ne ke taimakawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login