Showing 63001 words to 66000 words out of 121577 words
"Sai kun samu hutun makaranta. Tun ga ma Asma'u in za ta je ganin gida ke da Rahila za ku riƙa rakata."
Kallonsa na yi kamar zan yi mgana sai na fasa. Sai kawai na bige da faɗin" Yaushe Hajiya za ta dawo gidanmu da zama?
Alhajinmu ya muskuta kafin ya ce"Sai na gama ginin gidana Dubu. Akwai ɗakin Hajiya sai na ɗauko ta zauna damu? Hakan ya yi ko?
Sai na gyaɗa masa kai ina mirmishi. Labarin makaranta ya tambayeni na gyara zama ina bashi labari sai da aka kira sallar mangariba sannan hiran mu ta katse.
Kowa ya yi alwala domin gabatar da Sallah. Alhajinmu shi da Yaya Abubakar da Yaya Auwal sai Datti suka tafi masallaci Yaya Hamza baya nan ya na Niger can ya ke karatun babban sakandirinsa. Shi Yaya Abubakar je ka ka dawo ya ke yi anan cikin garin kano.
Ina zaune a gefe ina ganin yadda ƴan gidanmu ke kara kaina akan Asma'u da Yaya Murja ta fara laƙaba mata sunan Ma'u da ya kashe Asma'un ma gabaɗaya. Kowa na rawan jikin tambayata abin da take so ta ci Rahila har tana ɗaukan kayanta ta na saka shi cikin jakar kayan mu na sawa tun da kayanmu na waje ɗaya ne. Ni dai ko magana ta fatar baki ba ta haɗa mu ba kusa da ita ma ban je ba. Har da Gwaggo da Mama a masu kai da kawo akan Ma'u.
Sai da aka yi isha'i su Alhajinmu suka dawo. Kowa ya ci tuwon da Mama ta yi amman ban da ni ba kuma ba na jin yunwa ba ne ina ji amman Rahila ce ta baƙan ta mini rai.
"Mama ki haɗa mana Tuwon mu tare da Ma'u ko Sadiya?
Tsabar haushi sai kawai na ce"Ni ban ci.".
Saboda na ga daga zuwan yarinya amman Rahila ta fifita ta sama da ni kawai sai na ce na ƙoshi.
Gwaggo ta kalle ni kafin ta ce"Me kika ci?
Sai na rausayar da kai kafin na ce"Bakomai."
Sanin halina na tsirfa wani lokacin sai Mama tace a rabu dani.
Ranar na sha mamaki domin Ma'u kasa cin tuwo ta yi tana ta jagwalgwalawa har su Alhajinmu suka shigo a ka shimfiɗa babban tabarma a tsakar gida ana zazzaune ana cin tuwo ni kuma ina daga gefe ina kallon kowa ɗaya bayan ɗaya.
"Bakuwar nan fa kamar ba ta cin Tuwo"
Yaya Abubakar ya faɗa duk sai suka kalleta. Haka ne ko ba ta ci sai wasa take yi da shi a hannunta.
"Ko ba ta cin Tuwo ne Alhaji?
Cewar Gwaggo. Mama ke ce tambayan Ma'u ko ba ta cin tuwo dai dai lokacin da Alhajinmu ya ce"Anya. Ban sani ba. Asma'u a siyo miki wani abun ne?
Sai ta kalle shi amman ba ta yi mgana ba.
"Za ki sha shayi?
Yaya Abubakar ya faɗa sai ta kalle shi sannan ta ɗaga kai alamun eh. Na sandare a zaune lokacin da Alhajinmu ya ciro kuɗi daga aljihunsa ya ce Yaya Abubakar ya je ya haɗo kayan haɗa shayi a haɗa ma Asma'u tunda ba ta cin tuwo. Da fitansa da sauri da tashin da Rahila ta yi ta ce bari ta sa ruwan zafi sai Mama ta ce akwai ma a saman tukunya a madafi.
A daran nan dai Ma'u shayi ta sha da buredinta. Ahalin har Alhajinmu tuwo ya ci. Gabaɗaya hankalin yan gidanmu na kanta kamar sun ga wata sabuwar hallitta. Ina ji Alhajinmu na kora bayanin wace ce Ma'u a garemu gabaɗaya.
"Ɗiyar ƙanwata ce Hasiya. Mahaifinta ya rasu ɗan nan garin Yashe ne. Ta dawo hannun Hajiya da zama shi ne da na je na ganta na taho da ita za ta zauna da mu har abada."
"Allah ya taya mu riƙo Alhaji."
Gwaggo da Mama har suna haɗa baki wajen faɗa.
"ƴar uwan ku ce Ina fata za ku kalleta a matsayin jini ɗaya."
Yaya Abubakar ya amsa da in sha Allahu.
Yaya Murja ta yi karaf ta ce"Muna son ta Alhaji. Ga ƙawa ma na yi mata Rahila."
A lokacin ƙankance ido na yi ganin ta haɗa hannun Rahila da Ma'u waje ɗaya. Saboda sun zauna daman a kusa da juna ne. Ita kuma Rahila sai mirmishi take yi a yayin da Ma'u ke kallon kowa da idanuwanta. Tun kafin zuwan Ma'u daman ni da Yaya Murja ba ma zama a waje ɗaya saboda ta na da faɗa ni kuna ina da baki ta bakin ta ta ce ba ni da kunya manya na mgana ina saka musu baki.
"Har da Dubu ma. Saboda na ga za su yi tsara ya sa na samu karfin gwiwan ɗauko Asma'u."
Alhajinmu ya faɗa sannan idanuwansa suka fara laluɓena sai ya ganni a can baya ina zaune.
"Dubu..'
Ya kirani kamar yadda ya saba kirana sai na amsa. Sai ya ya fito ni da hannu na taso na zo gaban shi.
"Dubu ba ki ga yar'uwan ki Asma'u ba ne?
Na juya muka kalli juna ni da ita sai na kauda kaina kafin na ce" Na ganta."
Ya na mirmishi kafin ya ce"To ga ta nan ke da Rahila na bar ma Amanan Asma'u. Ku yi ƙawa da ita kun ji ko?
Ni dai kai na ɗaga Rahila ce ta amsa har ta na cewa" Alhajinmu a saka ta a makarantar mu don Allah"
Sai kawai na ji Alhaji na faɗin "In sha Allahu tun da daman Hajiya ta ce ta gama firamari sai na saka ta a tare daku har islamiya ma"
Sai kawai Rahila ta rumgume Ma'u tana murna.
A lokacin Yaya Abubakar ya kalleni ya ga na haɗe rai sai kawai ya kalli Ma'u yana faɗin" In Sadiya ta yi miki wani abu kar ki raga mata ki rama kin ji ko?
Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya yana nuna ni. Ana ta dariya har Alhajinmu. Amman ni ban yi dariya saboda ni ban ɗau abin da wasa ba. Mun ƙara kallon juna ni da Ma'u na wani lokaci sannan kowa ya ɗauke kansa.
Yaya Murja har tana faɗin" Wallahi kuwa. In Sadiya ta ga sakenta ai ta shiga uku."
Mutane biyu da suka fara bin bayan Ma'u tun kafin tafiya ta yi nisa. Suna faɗa mata abu mara kyau game dani.
A wajen kwanciya ma na ga abu. Mu uku muke kwana a karamar katifa a ƙasa ni da Rahila da Amina. Amman sai Rahila ta jajibo mana Ma'u ban iya shuru ba sai da na ce" Rahila a ina za ta kwanta? Ko ke za ki kwana a ƙasa ki bar mata wajen ki?
Daga mgana sai aka ga laifina. Kawai sai Yaya Murja ta fara zagina su suna babban gado ita da Yaya Balki. Gwaggo sai da ta shigo ta raba faɗan da har Yaya Murja ta ce Ma'u ta dawo gadon su ta bar mun katifar sai Gwaggo ta ce Amina ta koma wajen su Yaya Murja mu kuma mu kwanta mu uku ban ji daɗin hukunci Gwaggo ba amman ba ni da mafita ni ta kafafunsu na kwanta Rahila na bari da kwanciya filo ɗaya da Ma'u.
Tun daga wannan ranar Ma'u ta zama yar gida ko na ce tafi ma wasu yan gidan sakewa tun da tama da masu tsaya mata. Da ya ke Rahila tafi mu girman jiki ni kuna siririya ce ina da tsawo ba can can ba amman yanayin fasalin jikin mu ɗaya da Ma'u. Mama ta saka na tsinta kayana na ba ma Ma'u saboda sune za su yi mata kafin Alhajimu ya siya mata wasu kayan saboda wanda ta zo da su duk sun yage an zubar. Sannan Yaya Murja ta yi mata tsifa suka rakata gidan kitso.
Komai fa nuna mata suke yi ga shi ba ta cin Tuwo sai dai in tuwon shinkafa ne miyar ganye. Ba ta cin dambu ba ta shan fate tsirfa dai kala kala kuma an ɗaure mata gindi. Duk ranar da aka yi ɗaya daga cikin su sai dai a siya mata wani abun ko kuma a dafa mata wani abun ta ci ita yar gata.
Islamiyarmu aka fara saka ta. Sai da aka yi albashi Alhajinmu ya saka ta a makarantar mu ta Goverment Girls Junior Secondary School Diso. Kuma abin mamaki da irin sunan da muke amfani da shi. ASMA'U SULAIMAN YASHE. lokacin da Yaya Abubakar ya kai ta makaranta za a saka sunan Babanta mahaifi sai ta kalli Yaya Abubakar ta na faɗin"Ba sunan Alhajinmu za a saka mini ba?
Shi kuma Yaya Abubakar bai yi shawara da kowa ba ya sanya mata sunan Alhajinmu wanda dashi ta ke alfahari har gobe kuma har abada.
Sai da ya dawo gida ya faɗa Alhajinmu kuma bai ce don menene ba. Ba aji ɗaya aka sanya mu ba mu muna A ita kuma ta na B. Anan ne ta haɗu da Shema'u da daman halinsu yazo ɗaya. Rahila ce ke wani rawan jiki akan Ma'u amman ni sai na iya kirga ma maganarmu yadda ba ta mini mgana nima ba na yi mata kowa harkan gabansa kawai ya ke yi. Tun kafin kowa ya lura ni na fara lura da makircin Ma'u saboda ni ke kula da duka motsinta a gaban mutane saliha ce sai a makaranta in ka ganta tare da ƙawarta ba ka ce ita ce ba. Ban taɓa nuna ta a makaranta na ce ƴar uwata ba ce saboda ni ba ni ma da ƙawaye Rahila ce kaɗai na ke tare da ita. Amman ita Rahila mai jama'a ce kowa nata ne ni kuma ko ana son ƙawancen dani ba na ba da fuska ki gaji da naci ki haƙura ba islamiyan ba bakon ba.
Sai ya zamanto komai za a yi mana a gida guda uku ne tare da Ma'u. Ta zama yar gaban goshin Yaya Abubakaar shi ke koya mata karatu baya shigowa hannun rabbana sai ya yo mata tsaraba. Sannan Yaya Murja yadda take ƙaunar Ma'u ko ni yar uwanta ba ta sona haka. Alhajinmu ma gata yake nuna mata shi da su Gwaggo. Tun ina mamaki har na daina na sadakar da Ma'u ta samu tasiri mai yawa a zukatan yan gidanmu.
Baaba Hasiya ta zo ta duba Ma'u bayan ta yi wattani huɗu a tare da mu. Lokacin tun ba mu gama zama cikakkun mata ba na ji Baaba na yi ma ƴarta huɗuba da cewa" Kin samu rayuwa mai inganci Asma'u. Ki kwantar da kanki ki yi ma Yaya Sule da Gwaggo biyayya domin ita ce matar Fari. Wancan Rukayyar ba ta gabana. Sannan ki samu cikin yaran nan na Yaya Sule Maza wani ya yaba dake sai ki yi auran ki kin ji ko?
Ina laɓe ina jin su kuma ba niyyata na yi laɓe ba na zo shiga ɗakin ne na ji suna mgana na tsaya. Ban ankaraa ba sai ga sun fito. Baaba Hasiya daman in dai ta zo a ɗakin Gwaggo ta ke sauka ba ta sauka a ɗakin Mama na taɓa jin tana faɗa ma Alhajinmu a wani zuwa da ta taɓa yi wai Mama mai farar ƙafa ce tun da ya aure ta al'amarinsa ya ja baya tun da ga Lokacin na san ba ta ƙaunar Mama kuma mun taɓa zuwa Yashe a ɗakin Hajiya ta yi ma Mama rashin kunya har Hajiya Dubu na yi mata faɗa ina ƙarama a lokacin amman na ƙasa mantawa da abin.
"Ke lafiya? Ko laɓe kike yi mana"
Baaba ta katse ni tana hararata. Sai na kalleta kafin na kalli Ma'u sai kawai na ga ta yi mini wani kallo kafin ta ce" Daman Baaba ba ta sona. tun da na zo gidan nan."
Sai kawai na saki baki ina kallon Ma'u Baaba kuma ta fara tafa hannu ta na faɗin" To ai sai ta kore ki. Shegiya mai mugun hali to Asma'u zama daram in ji mai naguda."
Maganarta ya jawo hankalin su Mama da Gwaggo Ranar Lahadi kowa na gida.
Baaba sai ta fara kuka tana faɗin labe ta kama ni ina yi musu ta na fitowa ta ganni shine ta fara min faɗa na yi mata rashin kunya har ina zagin Ma'u ina cewa ta zo cin arziƙi ba gidan ubanta ba ne"
Ban mantawa maganar har sai da ta kai kunnen Alhajinmu. Yaya Murja har ta na marina saboda ta dunguremin kai na ce Allah ya isa ta mare ni. Yaya Abubakar ya saka ni kneel down ban ji ba ban gani ba. Ni kuma ban ƙaryata su ba amman na yi ma Ma'u wani kallo ganin tana yi mini dariya. Alhajinmu ya yi min faɗa fata fata abin da bai taɓa yi min ba yana ƙara jadadda mini Asma'u ba bare ba ce ƴ'a take kamar kowa.
Ina ji ina gani Ma'u ta zo gidanmu tana mini iko. Sai ta takale ni da faɗa ni kuma ban gane makircinta ba sai na tanka ta shikenan in aka zo jin ba'asi sai ta marairaice ta fara kuka tana faɗin na ce mata in ta gaji ta koma gidan ubanta kafin Ma'u ta rufe shekara a gidanmu har gwammatina a wajen Alhaji ta hambarar da shi da makircinta kowa ba ya faɗin abu mai kyau akaina ko abu ya haɗamu sai ace Ma'u ce mai gaskiya ni ce mara gaskiya.
Har Rahila ce mini ta ke yi" Don Allah Sadiya ki daina takurama Ma'u a cikin gidan nan. Ban ga abun da ta tare ki miki ba."
Itama goyon bayan Ma'un take yi kenan daga lokacin na fahimci gwara na miƙe na kwaci kaina domin ba ni da mai goyon bayana ko Mama ce na je na faɗa mata sai ta ce ni ce ba ni da gaskiya ba mai cewa a tsaya a bincika. Mutum ɗaya ne bai taɓa goyin bayan Ma'u ba shi ne Yaya Hamza lokacin da ya dawo hutu mun taɓa wani dambe da Ma'u akan ina zaune a ƙofar ɗakin mu ina gyaran jakar makaranta ita kuma ta fito wanka. Ga hanya na bata amman da ya ke makira ce sai da ta ga ba kowa a tsakar gidan sai ta takani za ta wuce ni kuma na miƙe na jawota ta baya wajen ta tsaya sai kafartaa ta turguɗe sai ga ta a ƙasa amman yarinyar nan sai ta fasa ihu ana taruwa ta ce ni na saka mata kafa ta faɗi.
Lokacin an saka ranar auran Yaya Murja ita ta saka mini hannu Yaya Hamza ya tsawatar ashe ya na daga can ƙofar ɗakinsu ya na ganin abin da faruwa.
"Yaya Hamza Sadiya ta ɗora ma Ma'u karan tsana tun daga ranar da Alhajinmu ya kawo ta gidan nan saboda ta ganta ba ta son tashin hankali."
Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce"Ita ta ce miki ta tsane ta? Ya za a yi ta tsane ta sai dai in akwai abin da take yi mata ne wanda ba ta so."
Yaya Murja za ta yi mgana ya ɗaga mata hannu kafin ya ce"Ki daina ɗaukan bangare ɗaya a matsayinki na babba ki zama adala. Ina can daga ƙofar ɗaki na ga abin da ya faru. Ke ce ba ki da gaskiya ta ba ki hanya amman saboda tonon faɗa kika takata ta miƙe ta jawo ki sai aka yi rashin sa'a kafarki ta turguɗe kika faɗi ko ba haka aka yi ba?
Ya faɗa ya na tsare ta da ido. Duk rashin kunyarta sai ta sadda kai ƙasa ta kasa mgana shi Yaya Hamza akwai tsare gida ba irin Yaya Abubakar ba ne shi kamar wani mace yake jin kansa.
Kai tsaye ya ce Ma'u sai ta bani hakuri dolenta kuma ta bani a kausashe ya kalleta kafin ya ce" Kar ƙi kara takalanta. Ni na san Sadiya ba ta faɗa ba a taɓa ta ba. Ku zauna lafiya da junan ku.'
Sai ta gyaɗa kai. Ni kuma sai ya riƙe hannuna zuwa ɗakinsa yana lallashina. Tun daman akwai fahimtar juna a tsakanimu. Ina kuka ina faɗa masa makircin Ma'u sai abin ma ya bashi dariya cikin dariyan ya ce" To ke ma ki riƙa ramawa mana. Ki daina bari ta na samun galaba a kan ki."
Shi mamaki ya ke yi ƴar Ma'u ta iya makirci tunda ya ganin ma idanuwansa.
Zaman Yaya Hamza a gida sai na samu lafiyan Ma'u. Tsoron shi take ji ko maganarsa ta ji yanzu za ta shiga taitayinta. In ya na waje ba ta iya wani motsin kirki har sai ya gama hutun shi ya koma tun kuma daga lokacin nima na gane in ta yi mini abu na rama kafin ta kai ga haɗa min makircin ni
Na haɗa mata amman ba ya tasiri tun da ni daman na yi ƙaurin suna sai ya kasance Ma'u ta riƙa cin nasara akaina ko a makaranta in na ganta tare da ƙawayenta suna nuna ni suna dariya barin ma wannan shegiyar ƙawar tata mai kama da biri Shema'u na tsane ta har acikin raina.
Mun je Yashe sau ɗaya bayan zuwan Ma'u gidanmu. Mun yi sati ɗaya har gidan Babanta mun je sai na ƙara raina mata kamar ma ba sa son ta. Domin ba a wani tarbe mu ba shi ya sa ita kanta ba ta zauna ba. Sai da muka dawo kano sai ita da Rahila suka shirya suka tafi kura in da Baaba ke aure ni kuma na ce ba zan je ba. Daga kuma lokacin in faɗa ya haɗa mu da Ma'u sai na yi mata gori da cewa in ta ji na dame ta
Za ta iya komawa gidan tsoho a ƙauye nan dai gidan Ubana ne kuma ba ta isa ta hanani sakewa ba saboda na daina tsoro ko a gaban waye za ta kai ni ta fahimci makircinta ba ya yi mini aiki sai ta koma itama ramawa. Na samu sauƙi Yaya Murja ta yi aure a shekaran 1996. Yaya Balki kuma ba ta kai Yaya Murja zafi ba.
Sai da bikin Yaya Murja sannan na fahimci Ma'u ta ɗau huɗubar Baaba saboda Yaya Hamza ya dawo gida ya gama babban sakandiri shi da Yaya Abubakar duk suna gida jarabarwarsu ba ta yi kyau ba sai sun sake yi. A lokacin na fahimci in dai ta gan shi yanzu za ta fara gyare gyare lokacin muna Ajin biyun ƙaramar sakandiri ne amma har Ma'u ta san ta yi ma namiji karairaiya.
Abin da na fahimta kamar tunaninta na kan Yaya Hamza shi