Showing 18001 words to 21000 words out of 121577 words
dariyan nishaɗi kafin ya buga sitiyari lokaci ɗaya yana faɗin" Ma'u. Ma'u na, ba ki da dama."
Mirmishi ta sake yi tana kara narke masa, dariyan ya sake yi kafin ya ce"Alhaji Ghali na gaishe da Amarya Ma'u."
Cikin yar dariya ta ce"Ina amswa. Ya iyalan nasa? Ya amsa mata da suna lafiya kafin ya ɗora da faɗin" Kin san ko har gobe in na je gidan sai Hajiya Fati ta yi mini tsiyan ba ki zo mata Allah ya sanya alheri ba, lokacin bikin ƴa'ƴanta."
Kai tsaye Ma'u ta ce"Ayya. Ba ka gaya mata bana nan ba ne lokacin? Kuma ai Hajiya ta je ta wakilceni"
Ya na dariya ya ce"Nima haka na ce, da Hajiya da Ma'u duk abu ɗaya ne a waje na."
Taɓe baki ta yi, a farko sannan ta ɗan saki fuska kaɗan. Hira ya cigaba da yi mata, sai faman taɓe baki ta ke yi, in zai juyo sai ta sakar masa lallausan mirmishin da ta san ya na kunna sa har cikin zuciyarsa.
Kanta ta maida jikin window din motar tana kallon hanya har ga Allah ba ta son surutu, surutun ma a wajen Namiji, ba haka ta so mijin auranta ya kasance ba, ta na son namiji mai Aji da kamewa amman mai ake yi da gidahumin namiji, waiwayawa ta yi ta na ƙara kallon Mijin nata wani abu da ya daɗe da tokare mata zuciya duk sanda ta kalleshi a matsayin mijinta ya sake ta so mata. To ta san ba ta san shi me ya sa ta aure shi?
Ba saboda kowa ba ne sai Saboda da BAABA. da kuma KUƊI. Ba domin kuɗin Alhaji Mustpha ba, da ko hanya ba za ta iya haɗawa da shi ba, tunda ya yi yamma da irin zaɓin mijin da ta daɗe tana mafarkin samu. Alhaji Mustpaha irin ƙauyawan kanawan nan ne, shi bai yi boko ba sai arabi, amman fa ya san kan kasuwanci yana kasuwancin Fata sannan kuma ɗan chajin ne, yana da kuɗi sosai. Kuma mahaifinsa ma har ya mutu sana'ar fata ya ke yi, shi ya sa zuru'arsu ke da kuɗi, amman bayan nan mugun bagidajen ƙauye ne, mara lissafi. Sannan ita ba ta taɓa hango kanta a matsayin macen da za ta yi aure ta zo a mace ta biyu, ta tsani zama da kishiya a rayuwarta saboda mahaifiyarta tun auranta na fari ba ta ji daɗin kishiya ba, kafin ta zo ta auri mahaifinta mutuwa ta zo ta raba, sannan a auranta na uku ma gidan kishiyiyon ta je, da har gobe ba ta huta ba. Shi ya sa ta yi fatan samun gidanta ita kaɗai ta gina shi duk yadda ta ga dama ba wai ya kasance ita ce zata shiga gidan da wata ta gina ba.
Amman kaddara ta riga fata, ko da ya ke Sadiya ce ta sauya mata kaddaranta. Domin saura ƙiris ta cika mafarkinta ta yi sanadiyar lalata komai, shi ya sa itama ba ta da wani buri sai na ganin ta lalata ma Sadiya jin daɗin duniyarta ta gigita mata rayuwarta yadda ƙwatankwacin yadda ba ta samu abin da ta ke so ba, itama ba ta fatan Sadiya ta cigaba da samun abin da ta ke so, in ma ta samu to za ta yi sanadiyar lalata shi ya zama baƙinciki a gare ta. Tana da burika da dama akan Sadiya waɗanda ko kwatansu ba ta cika ba. Nasara a kan Sadiya yanzu ta fara yi in a baya ita ta ta yi kuskuren barin Sadiya yin nasara a kanta wannan ƙarnin baya ne da ya shuɗe. Wannan ƙarnin na yanzu ita ce za ta cigaba da samun nasara akan Sadiya daga nan har abadan.
Ba ta ma san sun iso gida ba, sai da ta ji yana hon sannan ta farga da har sun iso gida, gidan Asma'u ƙaton gida ne mai kama da Aljannar duniya, amman duk wannan daular ba ya gabanta matukar ba ta ɗanɗana ma Sadiya irin ɗacin da ta ke ji a cikin zuciyarta ba, ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba.
Ita ta fara yin gaba zuwa cikin gida. Ta bar Alhajinta na magana da megadi, a falon gidan ta ci karo da ƙanwarta Zainab ƴar kimanin shekaru 16 zuwa 17, da ke hannunta tana zaune ta na kallo, abin sai ya ba ta mamaki ta na ganinta ta yi saurin miƙewa tana sosai ido, wani kallo Ma'u ta yi mata kafin ta ce"Uban me kike yi har yanzu ba ki yi barci ba?
Cikin In ina Zainab ta fara faɗin" Ina. Ina. Kallo ne."
Kafin Ma'u ta samu zarafin magana Alhaji Mustapha ya shigo falon kawai sai ta fasa maganar da za ta yi sai ma ta kalleta tana faɗin" Kin tabbatar da kin saka su Baba ƙarami sun yi fitsari kafin su kwanta ko?
Da sauri ta ɗaga kanta, Alhaji Mustapha na tambayan me ya faru? Ba ta tsaya bashi amsa ba ta kama hanyar ɗakinta lokaci ɗaya ta na faɗin" Ki kashe kallon nan ki je ki kwanta."
Daga haka ta shihe koridon da zai sada ta da ɗakin barcinta a ƙasan ranta ta na ji kamar ta ce Alhaji ya je gidan Hajiya yau ba ta cikin Mood ɗin da za ta iya dauriyan kwana dashi.
Shi ya sa ta na shiga ɗakin barcin na ta ta maida ƙofa ta rufe. Wayarta ta sauke nan saman gadon da mayafinta sannan ta buɗe kofar tiolet ta shiga wanka za ta yi, ta na cikin wankan ta ji Alhajin nata na ƙwanƙwasa mata kofar, tsaki ta ja a fili da ɓoye wani abu na suƙan zuciyarta dagacan ƙasa.
Ta na fitowa ɗaure da Towel, har lokacin bai tafi ba ko ya tafin ma ya sake dawowa.
"Ma'u. Ma'u ta,..'
Tsaki kawai ta ƙara ja a fili sannan ta isa ga kofar ta murza key, ta na buɗewa kawai ta juya ta dawo cikin ɗakin gaban madubin da ke shake da kayan kwalliya ta tsaya shi kuma cikin jallabiya ya shigo yana mai washe baki.
"Au wanka kike yi ne?
Juyowa ta yi sannan ta gyaɗa masa kai tana mirmishi, shi kuma sai ya rumgumota ta baya fuskarsa da nata na bayyana ta cikin madubin, Asma'u ta yi mirmishi, mirmishin da a saman leɓenta kawai ya tsaya, tana kallon Alhaji Mustapha kansa har ya fara furfusa ga uban sauƙo, a fuskarta mirmishi ne, amman a ƙasan zuciyarta ƙuna ne da wani irin turiri da ya ke ta so mata.
Ita ko za ta iya yafe ma Sadiya? Kai ina sai ta gigita rayuwar Sadiya. Sai ta yi sadiyar zama sanadin da farincikin Sadiya zai yanke na har abada. Yadda ita ba ta zauna ita kaɗai ba, itama Sadiya burinta ba zai cika ba, sai ta gayyato mata damuwowi masu tarin yawa a rayuwarta wannan alƙwarin ASMA'U SULAIMAN YASHE ce.
******
*BAYAN KWANA HUƊU*
LODGE ROAD.
JUMMA'A.
Karfe 7:40am na safe Salisu ya zo ya ɗauki su Jidda zuwa makaranta. Suna tafiya ban huta ba na shiga ɗakinsu ina haɗa musu kayansu, na zuwa gidan Anty Maimuna ko jiya sai da ta kirani a waya tana gwaɓa mini magana wai wannan satin ma hala gidanmu za su je? Ban biye mata ba na ce yau in sha Allahu za su zo.
A ƙaramar jakar baya na Jidda na haɗa musu kayansu da duk abin da za su buƙata, tiolet na shiga na ɗauko musu brush na fito kenan sai na ga Yusuf zaune a gefen gadon su Jidda.
Sanye yake da jallabiya. Tun bayan dawowarsa sallar asuba ya kwanta ban ma san ya tashi ba.
Tsayawa na yi sororo ina kallon shi kafin na yi mirmishi na ƙariso ina faɗin"Har ka tashi?
Miƙewa ya yi ya zo gabana ya buɗe min hannuwansa na faɗa ya rumgumeni yana faɗin" Ina kwana Sadiya ta."
Na amsa ina sakin sa kafin na ce"Na ga barcin ka ya yi nisa shi ya sa na ce su Jidda kar su tashe ka, su tafi kawai."
Ya na tsaye ya harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ni kuma sai na duka ina saka musu brush ɗin su a cikin jakan da na haɗa musu kaya.
"Kayan me ye wannan?
Ina duƙe na ce" Kayan su Jidda ne.
"Na zuwa ina kuma?
Sai da na ɗago sannan na kallesa kafin na ce"Gidan Anty Maimuna. Wancan satin kasan ba su samu zuwa ba."
Sai a lokacin ya ce"Oh. Na tuna ko jiya da na je gida Nene sai da ta yi min magana. Wai Anty Maimuna na ta faɗa."
Ina kallon idanuwansa na ce"Wai faɗan me?
Taɓe baki ya yi kafin ya ce"Ban sani ba, amman ta tambayeni me ya hanasu zuwa wancan satin na ce ma Nene ban sani ba."
Baki kawai na saki ina kallon shi, wai bai sani ba, Me ya sa Yusuf ya ke yi mini haka ne? Yadda ya ga ina kallonsa ne ya sa ya fara dariya, ya matso ya riƙeni na matsa baya ina haɗe rai kafin na ce"Ba ka sani ba ko? To ai ya yi kyau."
Ina gama faɗin haka na juya na bar masa ɗakin. Wai ni haka maza suke ko nawa mijin ne haka? Sau tari wasu laifuffukan da danginshi ke kallona da shi har da laifin shi, sai a yi abu kuma ya san dalilin faruwan shi amman in suka tare shi da maganar sai ya ce bai sani ba, kuma na yi masa ƙorafi har na gaji ya kasa dainawa, in na yi magana sai ya ce ai bai sani ba ne, ko game da zuwa sha'anin dangin shi, gajiya suka yi suka ƙyaleni, da suka fahimci ba ma su kaɗai ba hatta nawa dangin ba kasafai na ke shiga ba, ganewan suka yi ko gajiya suka yi da abu ɗaya suka kyaleni ban sanin musu ba.
Kitchen na koma, daman yara saboda yau jumma'a ne drink suka tafi da shi da Bicuit, sai tea da suka sha da biredi kafin su tafi, doya na fara ferewa zan soya mu sha tea da shi, ina feran doyan ya shigo kitchen ɗin yana faɗin"Fushi kika yi?
Banza dashi na yi, saboda ya ba ni haushi, burin sa na yi ta laifi a idon danginsa shi kuma ya na jin daɗi.
Zuwa ya yi ya rumgumeni ta baya. Lokaci ɗaya yana ɗora kansa saman kafaɗana bayan ya rankwafa.
"Sorry, kin ji ko?
Taɓe baki na yi kafin na ce"Ba dai da man so kake yi ko da yaushe na zama mai laifi a wajen ƴan'uwanka ba? To ai shikenan."
Matse cikina ya yi da hannayensa da ya saƙalo ta cikina. Sannan da ƴar murya ya ce" To ai na ce ne ban sani ba, kin sani da yawan mantuwa."
Mirmishin gefen baki kawai na yi, ba tare da na yi magana ba ya yi ta taƙalan mgana da ni na yi masa gim daga e, sai a'a kawai na ke amsa masa, sanin halina ya san in raina ya baci haka na ke yi sai ya sake ni yana faɗin" Bari na je na yi wanka. Zan je Rano."
Sai da na ji ya ambaci Rano sannan na ɗago ina kallonsa kafin na ce"Uncle Abba bai kira ka ba?
Kai ya girgiza kafin ya ce" Ya kirani amman bai yi mini maganar ba, amman in mun haɗu zan tuna masa."
Kai na jinjina, ba tare da na yi magana ba shi kuma ya fice daga kitchen ɗin, bayan ya rufo mini ƙofar. Na bi shi da kallo kawai, a baya ne ba na ƙaunar na ji ya ce zai je Rano duk da tushen shi ne, saboda GIMBIYA, amman tunda yanzu ta yi aure ban damu da yawan zuwan shi ba, in na yi duba da irin ayyukansa na kwangilan gine gine in an samu yana zuwa ko Uncle Abba ya yi masa hanya, tun da shi har gobe ya na garin Rano kuma a nan ya gina ƙaton gida duk da bai yi aure ba.
Gun bayan lamarin da ya faru tsakani na da Ma'u da yadda Alhajinmu ya goya mata baya. Tun da na dawo gida ban wani saki ba, ko Jidda sai da ta ce Umma ko ba ki da lafiya ne? Gabaɗaya zuciyata ba ta mini daɗi, ballatana da gabaɗaya ƴan gidanmu suka goya ma Ma'u baya, Yaya Hamza ne kaɗai bai shiga maganar ba shi daman sai a yi abu goma bai saka baki ba, mutum ne mai fahimta shi ya sa ko a baya nake ƙaunar Yaya Hamza saboda hallayarsa ɗaya ne a cikin dubu. Shi da Yaya Auwalu za a daɗe ana abu ba su maida kai ba.
Yaya Abubakar har sake kirana ya yi, bayan na ɗauka zagina ne kawai bai yi ba akan Ma'u. Su Yaya Murja kar a ji labari. Yaya Aina har cewa ta yi za ta iya yanke ni akan Ma'u.
A group ɗin Gidanmu an fi kwana uku maganar kawai ake tattaunawa. Ban san ina suka samu cikakken bayanin abin da ya wakana tsakaninmu da Alhajimu ba, sai ga shi Yaya Murja na maida yarda aka yi, to har na yi mamaki Ma'u ce ta faɗa mata ta na jin daɗi haka. Yaya Aina har ta na cewa gwara da Alhajinmu ya yi min haka ƙila zan shiga tairayina.
A mganar nan mutane biyu ne suka ce nima ya kamata a duba maganata ƙawar Ma'u ta yi magana domin tozarci. Yaya Balki da Amina. Sauran kuma duk iyalan Ma'u ne, shi ya sa nima na sauya musu matsayi. Rahila dai ba ta saka baki ba wannan karon, domin ta san halina wallahi sai na yanketa. Sai na yi amfani da shawaran da na yanke a cikin zuciyata akan na shiga na yi magana na ƙara ba ma Ma'u hakuri a gaban kowa kamar yadda take yi min amman munafuki shi daman a koda yaushe yana shirye ne.
Sai kawai ta rigani shiga ta yi magana, hakuri ta ba ma kowa sannan ta ce a bar maganar daga karshe ta yi tagging ɗina kafin ta ce"Komai ya wuce, zumunci da ni da Sadiya har aljannah ko ƴar'uwata?
Ban yi wani mamaki ba, sanin ba tun yau ba Ma'u ta kware a iya acting ba sai nima na fito muka yi acting ɗin a tare, kai tsaye na ce"Kowa ya yi hakuri mun daidaita barakan dake tsakaninmu da ƴar'uwata Asma'u."
Sai gashi sun fito suna murna, Yaya Murja ni kaɗai nasan haushinta da nake ji, har da cewa Allah Sarki Ma'u mai hakuri ce daman, ke kuma Sadiya a rage zafin zuciya. Ita da Yaya Abubakar Ma'u kamar ƙanwar uwarsu, ko da ya ke shi Yaya Abubakar akwai tsohuwar soyayya, ita kuma Yaya Murja har da son abin duniya, tunda Mijin Ma'u na da kuɗi ana zuwa ana maula dole ta riƙa zama mai goyon bayanta, ni fa a gidanmu na riga na san halin kowa sannan na yi ma kowa wajen zamansa wallahi.
Har na gama soya doya raina a ɓace ya ke, na kwashi komai zuwa Dinning, sannan na koma Bedroom sai na iske Yusuf suna waya da Uncle Abba sai na ce ya ba ni mu yi magana kan dai maganar fara zuwa na ganin likita asibitin Shika dake Zaria ne. Sai ya ce sun sake magana da Dr. Fadel ya ce in ta bashi lokaci zai kira mu ya sanar da mu.
"Ki kwantar da hankalinki Sadiyan Yallaɓai. Da zaran ta saka lokacin ganin ki zan sanar ma Tafida kin ji ko?
Sai na gyaɗa masa kai kamar ya na ganina sannan muka yi sallama na miƙa ma Yusuf wayarsa. Tiolet na shiga nima na fara wanka ko da na fito baya falon. Sai na samu daman shiryawa a tsanake.
Riga da wando na saka na material Daman ni in dai ba fita zan yi ba, ba na saka kaya masu nauyi.
Kalan kayan maroon ne, sai na yi amfani da bakar hula mai raga raga, kaina har lokacin ban yi kitso ba mai zuwa har gida ta yi mini kitso ta yi tafiya ne, ni kuma ko sake wanke shi a gida ban yi ba, tunda na iya ina da kayan wanke kan, har su Jidda ni nakan wanke musu kai na gyara musu.
Takalmin gidana mai taushi na saka bayan na fesa turare mai ƙamshi na fita zuwa falo Yusuf na jira na mu karya sannan ya fita. Ni na zuba masa doyan sannan na haɗa masa tea ɗin, sannan na haɗa ma kaina na zauna kujeran gefensa.
Ban ɗaure fuska ba amman ban kuma saki fuskar ba, ganin yanayina yasa sai ya rika takala na da magana sai dai in bishi da ido kawai.
"Ko za ki shirya yau ki je ki gaida Nene, in na dawo daga Rano sai na biya ta gida mu dawo tare."
Kai na gyaɗa kafin na ce"To shikenan sai na shirya na je ɗin."
Yana mirmishi ya shafa kumatuna kafin ya ce"To a saki fuskar, shan kunin ya isa haka."
Kalamansa suka ba ni dariya, sai na murmusa, mun cigaba da karyawa mun gama kenan na kallesa ina faɗin"Wata kwangilar a ka samu a Rano kuma?
Ya na miƙewa ya ce"Ban sani ba. Abba ya ce na shigo mu je mu gani."
Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Allah ya sa a dace? To su dai waɗancan masu payment ɗin shuru ko?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Wallahi shuru. Amman ban cire rai ba tun da sun ce ko da yaushe zan iya jin su." Fatan alheri na yi masa amman ban yi ɗoki ba domin ni nasan yanayin aikin shi, sai a yi shekara ana cewa za a biya shuru amman fa aka biya muna warkewa masha Allah tunda kuɗi ne ba kaɗan ba, kuma in aka samu aikin ana yin shi muna shiga hali tunda kuɗin shi zai ɗauka ya yi amfani dashi a karkashin kamfaninsa na HM. TAFIDA AND SON'S LIMITED. office ɗinsa na can hanyar zoo road kan titin Zaria Road.
Ni na raka shi har bakin mota kamar yadda muka saba, ya ba ni 2k ya ce na hau adaidaita zuwa gidansu da ke Gwammaja, muka rabu bayan ya rumgumeni ya sumbaceni, nima na maida masa martani, yana ɗaga min hannu nima ina ɗaga masa