Showing 99001 words to 102000 words out of 121577 words

Chapter 34 - TURKEN GIDA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

22 Sep 2025

3085

na koma falo na haɗa masa tea na zuba masa ɗumamen tuwon da na yi jiya da daddare miyan allayu zama na yi sai da ya gama ci muna yi muna hira bayan ya gama na tattara komai zuwa kitchen sai ya biyo ni ya na faɗin" Je ki huta bari na yi "
Ina jin haka na daka tsalle na rumgume shi na bashi sumba a baki kafin na ce" Yaron kirki Yallaɓan Sadiya."
Kaina ya dankwanfar ya na faɗin" Sai na fasa."
Da sauri na ce" Na tuba ranka ya daɗe ka yi mini rai."
Yana dariya ina dariya ban kuma iya zuwa na huta ba saman cabinet ɗin kitchen ɗin na haye na zauna yana wankewa ina karba ina jera su a muhallinsu.

  Anan ne ma ya ke ce mini yanzu ya girma iyalai sun fara taruwa ba girman shi ba ne a ka ga yana aiki
Ni ko sai na buɗe baki na ce" To mi ye a ciki? Ko ƴayan ka sun gan kana aiki ba abin kunya ka yi ba ka na koyi da sunnar ma'aikin mu ne kuma daman da shi muke koyi "

"Uhm daɗin baki ko?

Ya faɗa ya na kallona da sauri na ce" Haba Yallabai ai tsakanimu ba daɗin baki sai dai gaskiya da gaskiya."
Na faɗa ina masa yar dariya sai kawai ya kalleni ya girgiza kai kafin ya ce" To ke ina wani aikin da kike ta zuzutawa? Tun auran mu tare muke aikin nan ban daɗe da daina yi miki girki kina kwance ba."

Sai na buɗe baki ina kallon shi, ban rufe ba ya cigaba da faɗin" Kuma hatta renon su Jidda tare muka yi shi to ina aikin da kike ta kira?
Sai na rufe bakina na kasa mgana sai da ya yarfa min ruwan wanke wanken da ke hannun shi yana faɗin" kin kasa mgana ne?
Sai na kauda kai ina faɗin" To na ga abin ya koma gori ne gwara a bar mganar."
Dariya ya yi yana ƙokarin sake mgana na yi saurin cewa" Yallabai yau ba za ka fita ba ne?

"Zan fita mana. Zan je office akan mganar aikin nan na kaduna ki yi min addu'an Allah ya sa ta faɗa za mu samu alheri in sha Allahu.'"

Da sauri na ce" In alheri ne Allah ya tabbatar in babu Allah ya kawo na alherin."

"Amin Amin Abar ƙauna ta."
Ya faɗa ya na min wani kallo sai nima na tsume ina masa kallon soyayya. Sai kawai Yallaɓai ya ce a hankali" Ko mu je mu yi ɓarnan ruwa ne mu dawo?
Da sauri na ce" A'a. Fita fa za ka yi nima zan je Gwammaja."

"To mu haɗa wankan mana ba shikenan ba."

"Ba ko shiken nan ba.'

Na faɗa ina haran shi, dariya ya fara yi min kafin ya ce" Me ke damun ki ne? Allah kin fara zama raguwa."

Ko magana ban yi masa duk irin ƙokarin da nake yi wai na fara zama raguwa.

"Na ƙosa ki sami ciki irin na Baby. Ko banza ki yi ta nema na ni kuma da sunan taimako ina shan Shagalina."

Kafaɗansa na kaima duka ina faɗin" Ba Amin ba."
Shi kuma ya na min dariya har ya na maƙale murya yana tsokanata.

"Yallaɓai na. Uhm
Uhm.."

Kunya ta kamani na saka tafukan hannuna ina rufe fuska shi kuma ya na mini dariya. In na tuna lokacin har kunyar kaina na ke ji abu kamar cin tuwo na maida shi, ba na gajiya ni dai kawai a yi kuma da an gama sai na ji a lokacin nake son abin gaskiya ba zan so na samu ciki irin na Baby ba.

Haka dai Yallaɓai ya gama wanke wanke sai na ce ya cika ladanshi ya wanke wajen ya goge mini kitchen ɗin harara ta ya yi ya ce" Shi wannan ɗin ba ni da lada ne ko ba ki gode ba ne? Da sauri na ce" Na gode. Allah ya ƙara girma mai girma Tafidan Rano."
Kaina ya shafa ya na faɗin" Rayuwarki ta yi albarka ɗiyar ga."

Ni da shi muka saka dariya gabaɗaya. Haka nan ya haƙura ya tayani muka gyara kitchen ɗin muka goge sannan muka koma ɗaki Yallabai  dai sai da ya aikata abin da ya ce wato mu ka haɗa wanka Musbahu na ta kiran shi baƙi sun iso amman shi ya na gida yana shagali.

  Tare muka fita bayan mun shirya na rufe gida bayan na ɗaukan ma Baby dogon wando kawai suna da kayan sawa a gidan Nene domin wani lokacin in sun je sun kwana ba duka kayansu suke dawowa da shi ba, ni kuma ba na damuwa saboda irin haka suna wucewa daga makaranta ba ni da haufin kayan da za su sauya.

Yallaɓai na sauke ni a Gwammaja ko shiga bai yi ba ya wuce office ya ce mini sai ya dawo
A can na samu Hauwa Munnira ce ba ta kariso ba. Gida cike da dangin Maman Farko sannan a bangaren ƴaƴa kuma su Anty Zulaihat da Nasara sune kan gaba su da su Anty Bahijja. Anty Zuwaira kuma da ya ke yar sabga ce ba ta zo ba ƙila sai yamma. Suwaiba, Jamila  da Hindatu duk suna nan  Safiya ma haka Hafsat ce tana Abuja ba ta ƙariso ba matar Muhammad Sani an ce sai Jumma'a za su taho tare da mijin nata.
Ummu Salma ma da ke aure a Bauchi da wuri ta zo, na zo ba daɗewa Jawahir ta dawo daga makaranta sun samu hutun sati biyu.

A ɗakin Nene na sauka. Tunda nan ne ɗakin Uwar mijina. Ana mganar abincin da za a yi su Anty Bahijja suka ce a yi tuwo da shinkafa sai alale sannan za a yi zoɓo duk da akwai lemuka da ruwa da aka sauke sai Nama da aka ce za a kawo naman sa da na rago za a gyara a soya domin a yi amfani da shi ga baƙi masu zuwa. Sai can bayan azahar sai ga Muninira Halima ma sai bayan la'asar ta zo. Mu surukan gidan muka gyara wake tunda an farke shi ya fara ƙwari bayan mun gama an kawo kayan miya da yawa ni dai daman yar laushi ce su Hauwa na bari da gyaran kayan miya ni dai na gyara albasa Munira na yi min tsiya gyaran albasa kaɗai ne aiki a wajen? Na ce shi ne na ga zan iya. Hauwa dai an yi dama dama cikin gyaran kayan miya ina zan iya. Ba zan yi ba ada dai kam na yi amman ban da yanzu.

Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya zo muka koma gida washegari ma Alhamis mun koma ranar nama aka gyara aka soya sai kum an tafasa kayan miyan da aka nuƙo. A ranar baƙin Rano suka iso har da Gimbiya a ciki ban ɗauka ma za ta zo bikin ba amman sai na ji ana mganar har da cuku cukun transfer ɗinta ya kawo ta bikin.
Sai can da mangariba ne ma muka haɗu muka gaisa. Baby dai ta kawo mini chaculate ta ce Anty Gimbiya ta ba ta, ba tun yau ba tana son su Jidda ba kyauttukan da ba ta yi musu tun tana gida ko bayan auranta da suka je honeymoon da mijinta Paris ta siyo musu kaya masu kyau da yarari.

Can da dare ma tare na ganta da su Jidda da yaran Naja'atu. Sai ranar jumma'a Ango ya iso gida. Sai ihun ango ƴan uwa ke yi masa yana kamewa kusan Soja da tsare gida a ranar ma Tariq ya zo shi da Faridarsa. Muhammad Sani da Nafisa tun da safe suka iso shi Jafar ma da matar shi Nauwara ma sun iso ranar duk da Kaduna za a ɗaura auran amma dai ya zo gida shima.
zuwa kuma yamma komai an kammale shi.
Za a yi waina amma an ba da ne a yi sai dai Tuwon da miyan anan gidan za a yi shi kuma Alalen Anty Bahijja ta ce namu ne mu surukai mu za mu yi tsakani ga Allah ta na son ɗora mana wahala. Hauwa da Muniira na bar ma jagoracin su da ya ke a nan gidan suka kwana ni kuma gidana na koma na kwana na ce musu in sun ga ban zo da wuri ba kar su jira ni su fara aikin daman sun san halina ba da wurin zan zo ba. Jidda nan ta kwana tare da yara sa'aninta ita kuma baby ta na tare da Gimbiya Yallaɓai ke faɗa mini ta kira shi a waya ta faɗa masa ta tafi da Baby gidan Naja acan za ta kwana.

Da safe sai da na sha barcina na gajiya. Yallaɓai ma a gida ya barni na dai shirya shi cikin wata dakakkiyar shadda mai ruwan ƙasa har da babban riga hula da takalminsa bakaƙe haka ma agogon fatan dake hannun shi na fesa masa turare na bishi da Allah ya kiyaye ba da motarsa ya je ba shi. Da shi da Tariq motar Uncle Abba za su bi zuwa Kaduna.
Motar shi kuma Muttaƙƙa zai tukata zuwa Kadunan shima ɗaurin aure 11 ne na safe tun takwas suka ɗau hanya.

Ni ina gida ma sai wajen goma da rabi na fita. Rahila ta kira ni ta ce za ta zo na ce sai ta zo domin ni ban gayyaci kowa ba Yaya Balki ma da ta yi mini mganar muna da biki ba gayya na ce ni ban yi gayya ba.
Sai dai in sun zo domin Allah Gwaggo daman ta ce sai bayan biki za ta je Allah ya sanya alheri.
Ma'u daman na san za ta zo balle Uwar ɗakin nata ne yan gaba gaba. Ko da na je su Hauwa sun gama alale Munnira na ta harara ta na ce su yi haƙuri na tsaya shirya Yallaɓai ne.

"Au to me Yallaɓai? Mu ma ai muna da mazajen da za mu shirya amman ba mu je ba sai ke mai Yallaɓai a 'a yallaɓiya"
Munira ta faɗa ta na mai ƙara ɓalla minibharara.
Ina dariya na ce" To ai ban hanaku ba. Da kun tafi kuma"

Hauwa ta ce" Mu tafi Anty Bahijja ta tsire mu ko? Daman da ba ki zo ba ta ce Munirra ta ɗau girman tun da ke ba ki daraja girman da Allah ya ba ki."
Ina dariya na ce" Ran Munirra ya daɗe. Zan zama mai yi miki biyayya."
Kafaɗata ta daka tana dariya. Hauwa ke faɗa mini Nafisa ba ta da lafiya ta na ta amai ba ta yin komai ba na ce yanzu haka ciki gare ta. Nauwara kuwa gidansu ta gudu har na zo ba ta dawo ba.
  Shashen Marigayi Hajiya Karima muka gyara muka zauna tunda sauran duk ya na cike da jama'a Shashen Nene duk mutanen Rano ne Hajiyar Tafida ma da safe ta iso. Ni daman na yi wanka na a gida Jidda na nema na bata kayan da za ta saka da takalmi da mayafi saura na Baby ne an ce ba su dawo ba. Faridan Tariq kuma suna da ƴan uwa acikin gari can ta je ta kwana bayan ta dawo itama muna tare. Sameena ma sai a ranar ta so ashe ba ta nan ta je can Niger wajen dangin mijinta duk muna tare da su anan ɗakin.

  Karfe sha ɗaya da mintina goma Nasir ya kira Munnira ya ce an ɗaura aure acan ma cikin gida an kira su Anty Bahijja sai suka fara guɗa suna ta iface ifacen murna. Sai wajen sha biyu muka sake wanka muka saka ankom mu. Ni na yi kitso amman ban yi ƙunshi ba saboda wacce ke yi min kunshi ta yi tafiya kuma wacce ta yi ma su Hauwa na ga kunshinta bai yi min ba sai ban yi ba.
Mu aka bari da wahalan raba abinci shi dai na yi saboda Mimisco ce ta kirani da kanta ta yi mini mgana shi ya sa na yi abin da ta ce.

Kafin bayan azahar kowa ka gani ya ci kwalliya sannan wasu sun ci sun sha ko na ce ana kan cin da sha ɗin. Sai a lokacin su Baby suka dawo an saka mata wani leshi mai duwatsu dogowar riga sai da na natsu na fahinci anko ne irin shi ne a jikin Gimbiya da Naja'atu da ƴayanta sun kuma saka musu ƙananun hijabi a saman kansu har takalmin su baki mai igiya iri ɗaya ne.  Baby na ta murna ta nuna mini na ce kaya sun yi kyau na kuma yi ma Gimbiyar godiya ta na mirmishi ta ce mini bakomai.
  A she ban sani ba har da Jidda sai can wajajen La'aaar na ga Jidda ta sauya atamfa ta saka kayan itama tana murna ta ce mini Anty Gimbiya ta yi mata na ce ta gode.

  Rahila da Yaya Balki ne suka zo min biki domin ba zan saka Ma'u da ƙawarta a lissafina ba. Ni fa ban ma san ta zo ba sai da Yaya Balki ta ce kafin su fito sun yi waya ta ce musu ta na gidan tun ɗazu na ce ni kam ban san ta zo ba sai da suka ci abinci na raka su ɗakin Maman Farko suka yi mata Allah ya sanya alheri daganan muka shiga ɗakin Nene nan na ga abin mamaki Ma'u da ƙawarta shema'u filet ɗin abincin su cike da kaji da nama sannan suna tare da su Gimbiya da Anty Bahijja ana ta hira ana shewa.
  Tana ganin mu ta tsargu ni ko da gangan na kalleta kafin na ce" Su Ma'u manya maso bare kiƙi dangi. Kin zo amman ba ki iya nema na ba?
Sai ta fara kame kamen ta nemi ni ba ta ganni ba sai tana taɓe baki kafin na ce" Muna shashen su Jawahir tare da su Hauwa."
Nan dai muka gaisa ni dai na kai su ciki su ka gaida Nene da Hajiyar Tafida bayan mun fito na ga sun tsaya suna mgana da Ma'u da shirina na yi tafiya ta. Allah ya so mu ma Mimisco ta ce mu ɗiba komai saboda namu baƙin kuma daman ina nemanta saboda ba a diɓar mana na mazajen mu ba, mun yi waya da Yallaɓai duk da sun yi reception a can akwai bukatar mu ijiye musu abinci.

  Anty Maimuna na tare da baƙin ta dangin mijinta. Sulaihat na gani na ce ina Mimisco sai ta ce mini tana bangaren Hajiya iya sai na kalli Anty Bahijja ina faɗin.

" Anty Bahijja muna bukatar nama sannan da waina."

Kai tsaye ta ce" Duk wanda aka ba ku fa?
Nima kai tsayen na ce" To na mutane ne wannan, shi wannan da na ke magana na mazajen mu ne da suka tafi ɗaurin aure ne na yi ma Mimisco ma mgana."
Sai gabaɗaya suka kalleni har da Gimbiya.
Sai Anty Bahijja ta riƙe baki tana faɗin" To ma su miji. Mu namu mazajen da suka tafi fa? Ba su da rai ne ?
Ina dariya na ce" Kowa na shi ya sani Anty Bahijja. Ba zan hanaki ki ijiye ma Baban Sulaihat ba. Amma ni kam sai na ijiye ma Yallaɓai duk abin da na ci."

Naja'atu ta buga guɗa kafin ta ce" Kin burgeni Anty Sadiya. Shi ya sa Kawu dai ya fara ajiyan tumbi."
Ina mata dariya na ce" Ai na iya kiwo ne."
Ta ce kwarai kam. Sai aka maida mganar dariya Anty Bahijja ta miƙe ta na faɗin.

"Muje mai Yallabai."

Ta faɗa tana riƙo hannuna sai aka kara saka dariya ni ko sai na rike ta muka fita daga falon muna tafe tana ce mini wai shi Yallaɓan nan ba zai ci abinci acan ba ne? Na marairai ce na ce zai ci amman akwai tafiya kar ya dawo ya na jin yunwa.

A can shashen Hajiya iya muka je ta diɓar min waina da naman na je na kawo kula ta saka mini tana ta min tsiya Mimisco ta kare min da cewa abin da na yi mai kyau ne mata da dama in ana sha'ani sai su manta da mazajen su.
  Ni dai na wuce na barsu ina zuwa na ce su Hauwa sun ci sun ƙoshi suna sakin tusa sun manta da mazajensu to ni na yunƙura na samo ma mazajen namu abinci sai suka fara min dariya nace su gode minibko na fasa ba su Munnira ne wajen gaba gaban gode mini.  Su Rahila da wuri suka tafi kafin mangariba Ma'u kam tana gidan tawagan masu ɗaurin aure da amarya suka dawo. A shashen Hajiya Iya aka safki amarya da tawaganta. Ana yin mamgariba na kira Yallaɓai na tambaye shi ko yana ina? Ya ce min suna cikin gida a ɗakin Musbahu da kaina na yi lulluɓi na kai masa abinci da ruwa da lemu na san daman shi da Tariq da Uncle Abba ne nama daman da yawa na diɓar musu sauran na bar ma su Munirra domin na ga su ba su damu da cikin mazajen su ba.

Yallaɓai sai da ya rumgumeni ya ba ni sumbata a baki kafin ya ce" Allah ga baiwarr ka nan Halima Allah ka jiɓanci lamuranta kamar yadda take jiblɓanta nawa."

Daman sun ce yunwa suke ji.  Suna ma shirin tashi su fita su je su ci abinci a cikin gari ne sai ga ni, Tariq dai ba baka sai kunni ya fara cin nama Uncle Abba kuma sai ya kalleni kafin ya ce" Sadiya na ce wai ba ki da yar ƙanwa ne a gida?
Gabaɗaya suka saka masa dariya nima sai da na dara kafin na ce" Babu Uncle Abba kana so ne sai a duba maka a dangi?

Sai ya ɗau naman kaza ya saka a baki yana tauna kafin ya ce" Ina tunanin haka na gaji da wulaƙancin da yaran nan suke yi mini. Yusuf a gabana bai ji kunyar kama mace ba ina kawun sa."
  Yallaɓai na cin waina ya ce" Ba fa Mace ba. Matata na kama. Kawu kuma ai ban hana shi aure ba ko?. In ka ji haushi gobe a ɗaura ko Tariq?
Ya faɗa ya na kallonshi Tariq ya gyaɗa kai sannan ya ɗaga hannu Abba ya zungure shi da ƙafa yana faɗin" Shege sarkin cin abinci."

  Ni dai gajiya na yi na fita na bar su domin ba za su fasa ba sai dai idan ba su haɗu ba.
Farida dai na faɗa mata ba ta damuwa Tariq na tare da Yallaɓai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login