Showing 45001 words to 48000 words out of 121577 words

Chapter 16 - TURKEN GIDA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

22 Sep 2025

3056

ya ƙare kuma Yallaɓai bashi da kuɗi.

Ajiyar zuciya na sauke kawai a raina ina fatan kafin komai ya ƙare Allah ya kawo wata mafitar. Tunanin yin Tuwo ya kawo mini acikin raina sai na duba naga ina da kuɓewa ɗanya da Gwaggo ta ba ni wacce ta taho da ita daga Yashe ne sau ɗaya na yi amfani da ita tunda Yallabaina ba ma'abocin cin tuwo ba ne sai bayan lokaci lokaci haka.   Ban yi kai tsaye ba sai da na koma ɗaki na kira Yallaɓai na na ce masa yau Tuwo na ke so na yi ko yana so na dafa masa wani abincin ne?

  "Sadiya na daɗe ban ci tuwo ba. Ina marmarin shi."

Amsar da ya bani kenan. Sai na yi mirmishi kafin na ce"To zan ɗora tuwon yanzu. Ka taho min da ƙashi ko Nama wanda zan yi miyan dashi."
Sai ya amsa min da toh, tunda yau ba Rano ya je ba Office ya je.

  Da ƙarsashina na koma kitchen na ɗora ruwan Tuwo a saman Gas. Yara kuma na yi tunanin su sha wani abun kafin na gama girkin, ina cikin tunanin su sai na ji buga get na san sune tunda shidda saura a lokacin. Ni na je na buɗe musu kofa har Salisu ya tafi bayan ya sauke su. Tare muka shigo cikin gida da su ina tafe riƙe da jakar Baby da lunch box ɗin ta.

  Bayan sun sauya kaya na ce su zo su sha ko goldemorn ne tunda corflex ya ƙare shima sai kwali kafin in gama abinci Baby ce ta biyo ni kitchen ɗin ta na faɗin" Umma me kike dafawa?
Kai tsaye na ce"Tuwo."

"Tuwo?

  Ta faɗa ta na kwabe fuska. Sai ta bar ni ina ta mata dariya daman na san ba ta son tuwo sai na lallasheta na cewa ina da sauran miya zan ce ma Yallaɓai ya taho da buredi sai ta ci dashi jin haka yasa  ta yi tsallen murna. Ko kafin mangariba na gama Tuwo tunda na shinkafa ne har na mulmule a leda Jidda ce ma ta taya ni ɗaurewa a ledan muna yi ina nuna mata in da ba ta yi dai dai ba ta na gyarawa.

  Miyan na ɗora daman na yi greting ɗin kayan miya daddawa daman ina da dakakkiya ban mantawa Inna Mariya ta aiko mini dashi. Sai na ɗan zuba ruwan da yawa saboda ban san lokacin da saƙon Yallabai da zai iso ba. Tare da yarana muka yi sallah a ɗakinsu na zauna muna karanta azkar tare sakamakon na daɗe ban yi musu karatu ba ya sa na ce kowacce ta ɗauko Qur'ani mu yi karatu.

  Na biya ma Jidda na ta Baby ne muke yi lokacin da Yallaɓai ya shigo ɗakin na yi mamakin ganinsa yau da wuri haka. Ya na tsaye bakin kofa sanye da wani farin yadi kansa da hula ta zanna mai kalan aikin jikin yadin. Mirmishi a saman fuskarsa ga leda a hannunsa ɗayan hannun kuma key ɗin mota da sai wayarsa.

"Sannu da zuwa."

  Na faɗa ina kallon shi lokaci ɗaya nima ina maida masa martanin mirmishin. Baby ce ta tsshi ta isa wajensa ta na masa oyoyo Jidda kuma daga zaunen ta ce"Sannu da zuwa Abba."
Ya amsa lokaci ɗaya yana ce ma Baby" Kar ki ɓata jikin ki." Ya faɗa ya na nuna mata ledan hannun shi.
Miƙewa na yi na isa wajen shi ina faɗin" Ban ɗauka za ka dawo yanzu ba. Na ma za ta Musabahu za ka aiko."

  Kai ya girgizamin kafin ya ce"Kawai na ga ba wani aiki ne shi ya sa na ce bari na dawo gidan kawai.'
Ya faɗa ya na miƙamin ledan na karɓa lokaci ɗaya ina kallon Baby da ke riƙe da hannun babanta."

  "Je ku gama karatun Baby."

  Kumatunta ya shafa kafin ya ce"Je ki. In an gama karatu ki zo ki karɓi tsarabanki."
Jin haka yasa ta wuce da gudu ta na dariya muka bita da kallo gabaɗayanmu cikin ƙauna gaban Jidda ta koma ta zauna ta ɗauki Qur'aninta ta na karantawa da karfi.
Ni da Yallaɓai muka fita ina gaba ya na bin bayana shi ya rufe musu ƙofar.

  Tare muka shiga har kitchen ina buɗe naman.
"Ko da na je duk sun gasa sai wannan na samu na 3k ne zai isa?
Yallaɓai ya faɗa ya na sunkuyo da kansa ta ɓarayin wuyana. Kai na jinjina kafin na ce" Zai yi mana. Miya ce ba yawa sosai."
  Sai da na saka naman duka a cikin miyan ina juyowa Yallaɓai ya rumgumeni ta baya lokaci ɗaya ya na faɗin" Yau ko ɗan hug ɗin oyoyo ba a yi min ba ko?
Ina mirmishi na ce"To ka jira ka ga ban yi maka ba ne? Na faɗa ina wucewa wajen sink in da na buɗe famfo na tara hannuna ina wankewa shima sai ya sunkunyo da kansa ta wajen wuyana lokaci ɗaya ya zuro hannayensa duka biyu ya kama nawa yana murzawa a tare ruwa na zubar mana.

"Nima a wanke min hannun mana Sadiya ta."

  Ya faɗa cikin raɗa sai na yi yar dariya na karɓi hannun ina murza masa na wani lokaci kafin na kashe famfon ƙaramin Towel ɗin da ke kitchen na ɗauka ina goge masa hannunsa. Nima na goge nawa hannun sannan na yi masa rumgumar da ya yi min ƙorafi shi kuma ya ɗago ya sumbaci goshina.

   Ta falo muka fita na ɗauko masa wayarsa da key ɗin mota muka wuce cikin ɗaki. Wanka ya ce zai yi amman da ruwan sanyi saboda garin akwai zafi zafi mun fita damina an fara zafin nan na fiddan dawa. Shi ya shiga wanka ni kuma sai na koma kitchen ina duba miyata da na saka mata kalolin maggi. An kira isha'i Yallaɓai bayan ya fito wanka ya saka Jallabiya ya tafi masallaci ni kuma da yara muka yi a gida. Da zai shigo ne ya shigo da ice cream ɗin da ya siyo ma Baby ita kuma Jidda wani bickit mai madara mai ɗan karan daɗi lokacin har na kaɗa miyata na gyara kitchen ɗin ina jin shigowarsa na faɗa wanka.

  Har na gama shiryawa yana falo tare da yara. Ni kuma sai na tsuke cikin riga da wando. Wando ya kamani ta sama amman ya na da buɗewa ta ƙasa rigar ma tana buɗewa ta ƙasa. Wandon baki ne rigar fara sai na yi amfani da bakar hula a kaina ban fesa turare jiki kuma na shafa humra har da jan baki na saka na yi ɗas da ni ina fitowa falo wajen ya ɗauka da kamshi. Jidda na kira ta tayani ɗaukan kaya zuwa Dinning. Baby ta samu ice cream tuni ta manta da mganar Biredi ni kaina na manta ban kira Yallaɓai ban ba a lokacin.

  Gabaɗayanmu muka haɗu a saman dining ɗin ban da Baby da ke can falo ta na kallo. Da kaina na saka ma Yallabai guda biyu na zuba masa miyar da ta ji naman rago Jidda ma ta saka ɗaya ta ce ya isheta nima dai ɗayan na saka saboda na ci abinci a gidan Halima.

"Sadiya ta. Kin yi kyau.''

Haka Yallaɓai ya faɗa yana kallona da mirmishi a saman fuskarsa. Fari na yi masa da ido kafin na ce"Thank you Yallaɓan Sadiya."
Jidda na cin tuwon ta ba ta ɗago ba amman ta yi mirmishi. Yallaɓai ya kalleta kafin ya ce"Hajiya Nene ko Umma ba ta yi kyau ba?
Da sauri ta ce" Ta yi kyau sosai Abba." Ya na ƴar dariya ya ce"To ai shi ne na yaba kuma sai na ga kamar ta cancanci tuƙwaici ko?

  Jai ta gyaɗa masa ta na mirmishi ina jin su ban ce komai ba sai da na ji ya ce"Kar ki damu zan ba ta kyakyawan tuƙwaici"
Ɗagowa na yi ina hararanshi kafin na saka kafata na taka masa kafa sai ya janye yana dariya. Jidda dai ta gama cin tuwonta ta ɗauki filet ɗin ta bar mana Falon sai da ta fita na kalle shi kafin na ce" A gaban Jiddan ka ke mganar tuƙwaici?

Kai ya gyaɗa kafin ya ce"To miye a ciki? Ai ba ta san irin tuƙwaicin da kike karɓa ba madam"
Wani kallo na yi masa da ya sa sai da ya ƙware yana shan ruwa na yi masa gwalo ina dariya amman sai da na saka hannuna ta bayansa ina shafawa ganin ya sarƙe da yawa. Wani ruwan na sake zuba masa na bashi ya sha sannan ya ɗan lafa masa.

  Kallona ya yi kafin ya ce" Ki riƙa bari sai mun shiga ɗaki sai ki yi mini wannan kallon kin ji ko?

Ina dariya ban yi mgana ba shi kuma ya ce" Saboda tsaro ba."

  Murguɗa masa baki na yi shi kuma sai ya kaɗa kai kafin ya ce"Murgaɗa da kyau za ki yi bayani ne yarinya in na fara gyara miki service ɗinki har da garambahul."
Marairaicewa na yi ina faɗin" Mai jan mota ya tokare boda yau Yallaɓai."
Kai tsaye ya ce"ko jan jirgi ne yau sai na gyara miki service ɗin ki."
Dariya na yi shi kuma yana faɗin" Yi dariya da kyau."
Ni ko na ce to kuka zan yi? Ya na min wani kallo ya ce" A'a shi wannan ki bari sai anjuma."

  Kafarsa na taka ina faɗin" Yallaɓai cikin shagwaɓa "
Da sauri ya miƙe yana faɗin" Yau wannan shagwaɓar taki ba amfanin da za ta yi miki "
Tiolet ɗin falon ya shiga ya wanke bakin shi da hannunshi bayan ya fito ya wuce kan kujera ya zauna ya dauki remot ya kunna TV ni kuma sai na tattara komai na maida kitchen ɗin ina gyara wajen daga can zaune Yallaɓai ya ce.

"Ki zo mu yi hira. Hiran saurayi da budurwansa."

Ina mirmishi na ce"Sadiya da Yusuf ɗin ta ba."
Kai ya jinjina kafin ya ce" ko dai Yallaɓai da Sadiyarsa? Na ce ai duk ɗaya.
Sai da nima na wanke hannuna da bakina sannan na leƙa su Jidda na ce tara ta yi su kashe kallon nan su je su kwanta in suna da aikin makaranta su ɗauko su yi kafin su kwanta. Jidda ta amsa min da toh sai na rufe musu kofar na dawo wajen Yallaɓai shi kuma sai ya miƙa min hannu na taho ya yi min mazauni saman cinyarsa ina zama ya kishingiɗa nima sai na lafe kaina saman ƙirjinsa ina wasa da tsillin gashin wajen tunda ya cire jallabiyar daga shi sai dogon wando shi kuma sai ya cire min hula yana wasa da gashina gefe ɗaya kuma yana min susan kunni dukkanmu mun yi shuru muna jin bugawar zuciyan juna ga ƙaran tibi da iskar fanka na ƙaɗawa.

Wani farinciki na ke ji. Zuciyata na bugawa da sauri da sauri kamar yadda shima na shi ke bugawa.

"Yallaɓai na."

Na kira sunan shi cikin wani salon da na san ya na kunna shi.

"Uhm."

A saman leɓensa ya amsa min.

"Ina son ka."

"Ina ƙaunarki Halimatuna."

Haka Yallaɓai ya faɗa lokaci ɗaya yana ɗago kaina. Bakinsa na nufa shima sai ya sunkuyomin a tare muka tarbi juna muna sumbatar juna cikin wani shauƙi da muradin junan mu.




*Janafty*
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKWRWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA (MOMMY)*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

*🅿️09*

Mun daɗe muna sumbatar junanmu cikin wani shauƙin da a cikin zukatanmu kawai muke jin tasirin yanayin. Mu ka saki juna lokaci ɗaya kuma muka bi juna da kallo muna sauke numfashi a jejjere.

  Mirmishi ya yi mini nima na mayar masa da martanin mirmishinsa. Tallafo kuguna ya yi ni kuma sai na ƙara maƙale hannuwana a a saman wuyansa jawo ni ya yi na sake lafewa a saman ƙirjinsa ina jin yadda ya ke ɗan sauke numfashi kaɗan kaɗan kamar wanda ya yu gudun tsare.

  "Yallaɓai.."

Na kira sunan shi bai amsa ba sai ya kalleni kafin ya lakace min hanci da hannunsa guda ɗaya yana faɗin" Uhm"
Hannuna na kai saman Sajensa ina shafawa har zuwa ƙasa wajen gemunsa da ya fara fitowa domin yana yawan askewa yana dai barin kaɗan haka ina shafa gemunsa zuwa sajensa ina faɗin.

"Ka san kai ne namiji na farko da ka ruguza dukkan tunanina. Kowa ya san burina na sai na gama jami'a na samu aiki zan yi aure. Amman tashin farko ina haɗuwa da kai ina yar aji ɗaya a jami'a ka susuta tunanina da ya sa na amince da kalamanka na aure ka bayan na yi fatali da mafarkina da burina gabaɗaya."

  Na ƙarishe faɗa ina kallon shi. Shima ni yake kallo kafin ya yi mirmishi ya ce" To ni ɗin wasa ne? Kin ga zangaɗeɗen saurayi jikan mutanen Rano. Kin san in kika bari na suɓuce miki samun kamata ai da wahala shi ya sa kika yi amfani da maganar hausawa da suke cewa in dama ta zo maka ka yi amfani da ita saboda wataƙila in ta suɓuce maka har abada ba lalle ka ƙara samun damar ba"

"Allah ko?

   Na faɗa ina kallonsa da ƴar dariya. Shi kuma sai ya ɗaga min gira kafin ya ce"Kema kin san gaskiya. Samun jarumi kamata a cikin maza ai da wahala shi ya sa kika yi wuf da ni da sauri kafin ki makara. Ko wata ta yi miki ƴar kafa ba."

  Ina dariya ina jan gashin sajensa ya yi shii alamun zafi ya na ƙokarin riƙe min hannu na ce" To me ya sa ka yi ta mini na ci sai da na yi maka kwatancen gidanmu? Kai ma ai kasan in ka bari na subuce maka samun kamata da wahala."
Na faɗa ina masa fari, bakina ya sunkuyo ya sumbata lokaci ɗaya ya na faɗin" Ɗan bakin nan na daga cikin abin da ya fara jan hankalina a kanki. Da yanayin mganarki da takun ki. Kai kin iya jan Aji kin ba ma bawan Allah wahala ranar da na koma gida daƙyar na iya barci. A time ɗin bani da burin aure har sai na samu aiki na gina gida na gina kaina amman tun ranar da na fara ganinki kika ruguza mini wannan tunanin. Ke ce silan da ya sa na yi fito na fito da kowa akan aure saboda ai suna ganin ban kai ba me na tara me na ke da shi sannan a tunaninsu na yi yaro a lokacin ba su san a halin da na ke kwana ba ne shi ya sa.'

  Ya ƙarishe faɗa yana wani sauke nunfashi ni kuma sai na ƙyalƙyace dariya taya ni ya fara yi yana cewa" Allah. Azumi fa na ke yi duk litini da al'amis ai ya kamata su gane ina son aure. Daga karshe dai na fito musu a Mutum na ce ina son na yi aure saboda ina da karfin sha'awa kuma ina tsoron faɗawa halaka. Nene na jin haka tace ku bar Tafida ya yi auran nan Zuwaira shi ne alherin mu gabaɗaya."

  Shi ke tuna labarin a bakinsa amman ni kuma ina hasaso lokacin a cikin idanuwana. Tabbas lokacin an sha gwagwarmaya sosai kafin auran mu amman gashi komai ya zama tarihi. Mun yi aure har da albarkar ƴa'ƴa biyu kuma shekarun sun haura goma sai dai tunawa da abin ya faru kawai a yi dariya ko nishaɗi.   Mun cigaba da hirar baya a tsakanin muna yi muna dariya cikin nishaɗi wata magana da Yallaɓai ya faɗa sai da na sauka ƙasan cafet ina dariya.

  "Lokacin da kika samu cikin Jidda na faɗa ma kawu Abba da Tariq? Kin san me Abba ya ce? Bai ba ni zarafin mgana ba ya cigaba da faɗin" Cewa ya yi wai ashe dai da gaske ina son aure ashe ƙwan haihuwa ne kunshe a cikina da ba a barni na yi auran nan ba da Allah kaɗai ya san in da za kai wannan ƙwan haihuwan."

  Ia riƙe da cikina ina dariya na ce"To sai ka ce musu me?
Domin ni a baya bai taɓa faɗa mini sun yi haka da su ba. Shima ƙasan cafet ɗin ya sauko kusa da ni yana faɗin" Me kuwa? Na ce wallahi ai kun kyauta ma kanku da kuka yimin yaƙi kan aurena da Sadiya. Tariq kuma ya ce Allah ya shiryeka Yusuf ban san yaushe ka lalace haka ba."

  Ina kallonsa na ce" Gaskiya nima na san ka lalace ni ba haka na aure ka ba."
Kansa ya saukar mini a saman kafaɗata yana faɗin" Ke kika lalatani Sadiya. Kika koyar da ni abin da ban sani ba kika buɗe mini baki. Kin san an ce da Namiji ya san mace bakinsa ke buɗewa."
Mintsinin hannunsa na yi ina faɗin" Ni kar ka mini sharri. Na koyar dakai ko ka koyar da ni?
Na faɗa ina kallonsa sai ya ɗago shima ya na kallona kafin ya riƙe mini hannuna guda ɗaya ya matse cikin hannunsa ya na faɗin" To shike nan na ji mun koyar da juna shike nan?
Sai na gyaɗa kai matsowa na yi kusa dashi na matse shi rabin jikina na kan jikinsa ina faɗin" Wai Tarig ɗin sun koma ne?
Yana shafa bayana zuwa ƙuguna ya ce" Ina jin kamar sai cikin Weekend ɗin nan za su koma. Faridarsa ma ta ce na gaisheki ranar na sha'afa ne."

Kai na jinjina ina gyara zaman kaina a saman ƙirjinsa lokaci ɗaya ina faɗin" Yallabai. Kayan abinci fa sun ƙare."
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Bari mu gani zuwa a shiga wannan satin. Sauran da ya rage zai kai mu lokacin?
"A'a gaskiya. Ko su indomie duk sun kare lemun su Jidda na makaranta ba ko rabin katan bai kai ba."

  Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Allah zai rufa asiri. Amman duk kudaɗen hannuna na saka su cikin aikin nan kuma ba a ma gama ba ballatana su yi mana payment amman dai na yi magana da su za su fara ba mu half ɗin in angama aikin sai su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login