Showing 27001 words to 30000 words out of 164763 words
nayi, jekiyo wanka kiyi Kari na kaiki da kaina na fadi ma malamin ku abinda kikeyi" zaro ido tayi tana kallonta kafin tace "ni bazaki bini school ba".
_🌹IN BANI 🌹_
_Maman Abd Shakur_
15.....
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number 07012181461_
_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461_
Wuce ta Kaka tayi tai dakinta tace "aikuma sai mugani danko ubanki bai isa yahanani kaiki makarantan nan yauba" tai kwafa ta shige dakinta, tashi tayi ahankali tanaji kaman tai kuka ko kadan bataso taje makarantar nan ta tsani zuwa makarantan, mutanen ajinsu sukai dari da hamsin, batason zuwa, dakinta tawuce ta shiga ta shiga bayi dan Kaka tace takaimata ruwan zafi, sirka ruwan tayi sanan tayo wankan bayan tabata kusan 10min a bayin dukdan kartaje school, saida Kaka tazo ta buga kofan tace "jama'a wai bazata fito daga bayin bane, ke kinsan karfe nawa kuwan? Zainaba fa harta tafi abinta, Ihsan ma ta tafi tata makarantan, ke kina nan bayi kina kwainane, wlh koki fito kona fado cikin bayin nan yanzu kuw..." bude kofan tayi tafito Kaka ta matsa gefe tana kallonta, turo baki tayi tawani kumbura taje gaban sip tabude sip din kaman zata balle kofan tsabagen masifa Kaka dake tsaye a inda take tana kallonta tace "wlh kika ballamin sip sai ubanki yabiyani atoh" dogon bakin hijabinta taciro da wani doguwan rigan atampa ja ta ijiye tadau mai ta shafa sanan ta dago ta kalli Kakan dake binta da kallo, akule tace "ni kifita zansa kaya" tsaki Kaka taja tafice tana cewa "kidaiyi sauri ga kokon ki nan afalo, shima kokon dan Allah zanbaki" shiryawa tayi cikin doguwan rigan dayay looking so simple yet elegant a jikinta ta zauna kan gadon tana bude eyeliner dinta tadau madubi taja asaman idonta as usual, bakaramin kyau tayiba ta maida ta rufe ta ijiye, lipgloss tasa abaki tafesa dan simple bodyspray dinta da Abba ke siyoma dukansu duk karshen wata body fantasy na vanilla sanan ta maida kayan kwalliyan tadau channel sandals dinta baki ta saka ta daure igiyan takalmin, bakaramin kyau yama yar farar kafarta ba kaman wata kafar jaririya sanan tadawo tadau jakarta da littatafan ta ke ciki ta rataya jakan akafada kanta ba dan kwali gashin ta daya tsufa sosai sai lilo suke tadau hijabinta tarike a hannu tafita daga dakin, falon ta shigo inda Kaka ke zauna a kasa tanacin dumaman tuwonta acikin tukunyan kasa tai hanyar fita daga dakin Kaka tace "dawo nan kici abincin ki mutafi" makemata kafada tayi da sauri Kaka tacire hanunta daga tuwon ta tashi hakan yasa tawani irin kwasa da gudu tafita daga dakin, cin karo tayi da Ya Faruk yana sanye da white jallabiya tai baya luuu zata fadi da sauri ya tarota tafada jikinshi arude daidai lokacin Kaka tafito da sauri ta kalli Kakan ta tashi daga jikinshi takoma bayanshi ta labe jikinta narawa ahankali tace "Ya Faruk please karka bari Kaka takaini school wai lecturer dinmu zata fadamawa ya dakeni" daga bakin kofa Kaka ke kallonsu tace "ina jinki muna fika, haka nace eh sainasa malamin ku ya dakanmin ke bar ganin Farukun soja ubanme zai iyamin" juyawa yayi ya kalleta fuskarshi adan daure yace "put on your hijab" da sauri tasaka hijabin dayay mata kyau sosai yafito da hasken fatarta, hulan hijabin har goshinta yace "let's go" ficewa sukayi Kaka tai kwafa tace "wlh zaku gamu danine dukanku munafukan banza" takoma daki, waje sukayi bahalin tacemai zataje ta gaida Mama da Baba yabi yadaure fuska motarshi yabude ya shiga itama ta shiga dayan side din lokacin kusan karfe tara yaja motar har BUK, sosai gabanta keta faduwa tana kallon ko'ina har gaban department dinta ya kaita na Islamic studies sanan yay parking dan dagokai tayi ta kalleshi suka hada ido, ahankali tace "thank you" 3k yaciro daga wallet dinshi yabata yana kallonta yace "make sure you eat" gyadamai kai tayi ta karbi kudin murmushi tayi tace "thank you" ta bude marfin motan tafita, binta yayi da kallo yanda take tafiya a mugun natse kaman tana tausayin kasa kanta akasa as usual tana kakkare fuskarta da hijabi, hijabin nan har kasa dan ko kayan datasa aciki ba'a hangowa, saida ta kule mai sanan yadan fuzar da iska wayarshi dake ringing ya kalla ganin Ammi ne yasa yadau wayan yakai kunenshi. Daga tachan bangaren cike da masifa matar tace "where are you Son, kacemin you're having headache bazakaje aiki yauba ina kaje this early morning eh Umar Faruk?" shiru yadanyi batare dayace komiba dan ya tsani karya, kuma baya karya, dan ya tsani anamai ihu aka, ahankali yace "sorry Ammi na" cikin fada tace "Faruk kullum kullum saika nunamin ban isa dakai bako son? Am sure kaje gidan wan Baban kane, am sure kaje kai wanan mai aljanun makaranta ne sabida kai hired driver dinta ne ko, Faruk wats wrong with you? Narabaka dasu kakiji, tun baban ka nada rai wanan mayyar wicked Kakan taka tasa aka sakeni dan haka nafa and am going to say it again, jinina bazai kara hada wani abu da wanan family ba, tun wuri kacire yarinyar nan aranka inba hakaba wlh fushin dazanyi dakai wanan karan saiyafi na wanda nai dakai ranan dakaje Lagos ka daukota stubborn boy, and come back home rightaway Dr na jiranka" tai tsaki ta katse wayan, ahankali ya zare wayan daga kunenshi kirjinshi namai wani irin zafi, he don't know where all this hate is coming from but one thing is for sure yasan idan har abinda Ammi ke fada gaskiya ne, Kaka tasa aka saketa dan Kaka batai laifi ba dan ko kadan Ammi batada kirki yana ganin yanda takema yan aiki wani zubin ma shiyake hanata, yasan mahaifiyarshi sosaisosai. Yakai kusan 5min a wurin yana tunane tunane sanan yaja mota yabar wajen yadau hanyar gidansu.
Faruk yaron kanin mahaifin su Hamida ne, shika dai suka Haifa shikadai ne kuma jikan Kaka namiji, inda Baban su Hamida yahaifi yara bakwai dukansu mata, baban Faruk ya rasu a plane crash ne, his Mum is from a rich wealthy family, bayan rasuwan baban Faruk Faruk yadawo hanun Abba da Kaka, rashin mutunci Ammi tazo tai dasu Kaka akan abata danta, in other to maintain peace yasa Abba yacema Faruk yakoma wurinta but dudda haka kullum yana gidansu, weekend yana yawan zuwa gidan kajin Abba yana tayashi aiki dan sana'ar baban su Hamida kenan saida kaji da Kwai and he's making it Alhamdulillah Allah ya sanya mai albarka a sana'ar.
**
Dan lekowa tayi daga inda ta labe ganin yatafi babu yasa tafito ahankali tana tafiya da sauri da sauri wani kantin taje dayake safiya ne ba mutane sosai, take away abinci merai da lafiya tayi guda biyu tabiya kudi ta karba tafito tafita daga school din gabanta na faduwa sosai, kasa samin Keke tayi hakan yasa tafara tafiya akasa tana kakkare fuskarta, saida tai nisa sosai tamugun gaji da tafiya takai junction din wani layi keke napep ta tare ta shiga tace "old railway" "hajiya dari uku" ahankali kanta akasa tace "muje" tada keke napep yayi suka shiga hanya, sukayi tafiyan kusan 15 minute yakaisu wurin, ahankali ta sauko taciro dari uku tabashi batare data kalli fuskarshi shi tajuya ta shiga wajen tana kallon kan kujeran da Baba yake zama yanajin yar radio shi ganin bashi yasa ta karasa wajen, takeaways din ta ijiyemai ta ta wuce ciki hango wasu samari tayi kusan biyar ko shida zaune a inda ta saba zama suna kokarin kunna wiwi da sauri ta juya kafinma su lura da ita, cin karo tai dawani abayanta idanunshi jajir da alamun yasha yai tatil yace "ke waya kiraki nan?" kwalama sauran dabama su lura da ita kira yayi yace "babaa jimana, tawaye ne tazo? Ba munce babu wacce zai kira tashi nanba yau" da sauri amugun rude tai gefenshi zata wuce yatareta yace "ki tsaya mana baby nakira miki su, hala wajen Sani kikazo dan nasan mayen da shegen iya zabo zafafan mata" arude tana dan waigen bayanta jin sahun mutane suna zuwa ta kwalama tsohon dake gadin wajen kira. "Baba, Baba" daidai lokacin sauran sun iso wajen fashewa sukai da dariya dayan yace "Baba wai me gadi kike kira? Ke yarshi ce?" daya daga cikin su yace "kaima jibeka dawata magana ina Baba mai gadi yakeda kyan haifan irin wanan lu'u lu'un?" daya daga cikinsu yace "kodai me zuwa bashi kayane?" kulle bakinsu sukayi suna zaro ido irin na isgilanci atare sukace "tsoho yaji chakwai" fashewa tai da kuka ta duka a tsakiyan su tana kwalama Baba kira. "Babaa" daya daga cikinsu yace "ankai Baba kauyen su Baba ba lafiya muma fanshi Baba yau, kingan mu mushida kici har ki koshi ko yan mata" yay maganan zai kama mata hannu boye hanunta tayi ajikinta tafashe da kuka, hijabinta ya fizgo ya mikar da ita tsaye fasa wani irin ihu tayi a mugun tsorace ta bugamai kafarta hakan yasa yay baya yasaketa yana tsaki dan yaji zafi da sauri sauran sukayo kanta tawani irin kwasa da gudu tana kuka wanda ta hambaran yawani irin tadiyota tafadi akasa hancinta ya shiga cikin dan kasan yashin dake wurin.
_🌹IN BANI 🌹_
Maman Abd Shakur
16....
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461_
Kafafunta yajawo tafasa ihu sosai tana kuka ta dibi kasan wajen da hannuwanta biyu ta juyo da kanta cikin kuka, watsa musu kasan tayi a idanu hakan yasa ya saketa da sauri yay ihu shida sauran suna sosa ido suna kokarin budewa sun kasa, dawani irin sauri ta tashi tadau jakanta taruga aguje suka biyota, fitowa tayi tana gudu sosai tana kuka, black hijabin ta gabaki daya ya baci da kasa tana gudu suna binta....
Anatse Mami ke tuki taci gayu sosai tasa wani hadadden exclusive atampa brown da yellow dayay mata kyau tayafa wani babban mayafi brown tana tuki, gefenta kuma Aadil ne yana zaune agaba yana wasa da fingers dinshi yana counting dinsu one, two, three, yana sanye cikin wani Fendi white t-shirt daya kama jikinshi sosai, hanun rigan are dark brown, yana sanye da dogon brown pant yasanya white sneaker na Fendi, wrist dinshi daure da agogo na rolex gashin kanshi a kwance yana kara bubbude manyan idanunshi yana magana kasa kasa yana counting yatsunshi sai wani hadadden kamshi dake tashi ajikinshi, murmushi Mami tayi tadan kalleshi ta maida hankalinta kan tukin datake yi tana tunani Aadil kenan, Ball fa suke bugawa a compound shida Aabid Baffa kuma na zaune acikin bukkan dake compound din yana kallonsu yana murmushi, yana ganin Mami tafito rike da car key gidan BigMum zata yafashe da kuka ya yarda kallon zai bita shine ta taho dashi.
Ahankali takira sunanshi. "Son" dan juyowa yayi ya kalleta da manya manyan idanunshi yadan daga cikakken gyararren giranshi sama kaman na tamace yana kallonta, itama dan kallonshi tayi ta maida hankalinta kan tuki tace "wat are you counting Son" turo mata baki yayi kafin ya maida kanshi kan hanya yana lankwasa kan yana cizan wet lips dinshi batare dayace mata komiba yafara counting motocin gabansu. Dawani irin mugun gudu Hamida tafado kan titin tana waigen baya saura kiris Mami ta bigeta ta gitta, dan batakai ga taka birki ba ta buga salati. "subhannallahi wanan lafiyanta kuwa" wani irin ganin gittawan ta yayi kaman flash of light, dasauri yakara ware ido yabi bayanta da kallo harta karasa tsallake titin da gudu tana waigen baya tana kuka tana share fuskarta da hijabi dan gani tayi kaman suna binta, da sauri cikin wani irin rudewa kirjinshi nawani irin bugawa kaman zai tsage yasaki lips dinshi daya rike da hakori tun dazu dayake wasa yana waigenta ta baya dan sunriga sun mata dan nisa, arude yay pointing saitin Hamida yana kyafkyfata ido kaman mai stammering yace "s...s...she Mami" wani irin juyawa yayi batare daya damu tafiya suke akan titi ba ya tuge sitbelt din jikinshi yawani irin bude kofan motan iska yaja kofan, kofan ya bude gaba daya ya daki wani mai machine dake tafiya, salati Mami tayi arude dan bama ta lura dazai bude motar ba saida taji wani irin iska, kafin kyaftawan ido yafita daga motan kanshi na rawa sosai yawani irin fadi akasa sosai dan da wuya in baiji ciwo ba, ihu Mami tayi tawani irin taka brake din motarta duka tana kallonshi kar wani abin hawa ko babban mota yatakeshi before you know it motar dake bayan Mami dat was on speed tazo da gudu ta bugi boot din motan Mami danta taka burki ne unexpectedly ta tsaya, motar Mami tai gaba kan Mami dayake ta lekone tana kallon Aadil arude kanta yawani irin bugu da starring, cikin ikon Allah mota bata bugeshi ba, da sauri batare daya lura da Mami bama yatashi yana waige waige kanshi na rawa sosai yana yarfe hannu danya bugu sosai akafa baima damu da mutanen dake salati ba ana kallonshi ana kallon mai machine dayay hatsari da two cars ya shiga gudu yana hango Hamida datamai nisa sosai yana yarfa hannu yafashe da kuka yace "she noo, don't go" yacigaba da gudu, gajiya yayi sosai kaman zai suma yafashe da kuka yana kallon titin dan baitaba gudu hakaba a rayuwan shiba, wani mai machine ne dayazo wucewa ya tsaya yana kallonshi cikeda mamaki yace "malam amma mutuwa ne kake kuka haka miyau na zuba" cikin kuka sosai yamai pointing Hamida dake shirin yin kwana tai nisa sosai yace "she" kallon inda yake nunamai yayi sanan ya kalleshi ganin yanda yake kaman mara lafiya sanan wanda yake nunamai itama gudu take yasa yakawo aranshi halama mai gudun shi take nema itama, tausayi yabashi hakan yasa yace "hauna kaikah wurinta to" tsayawa yayi yana kallon machine din yana kuka hannu mai machine din yamika mai da sauri yarike shi ya dafa shi sanan ya iya hawa kan machine din, mai machine din ya kunna yaja machine din, rikeshi yayi a tsorace yana kuka, adaidai bakin layin lokacin harta shiga layin mai machine din ya tsaya yace "sauko ka bita bazan shiga layin nanba, machine dinan daga wajen wanki na karbota yanzu haka, layin nan duk chabalbali" lekoshi yayi da kai yana kallon fuskanshi dan baicika gane manyan hausaba, ahankali mai machine din yace "come down" saukowa yayi yana kallonta yana kuka da karfi ya kwala mata kira. "sheeee" arude Hamida dake gudu har lokacin tana kuka sosai tafada wani uncompleted building ta tsugunna tana kuka sosai tana addu'a Allah yasa basu ganta ba, tabude jakanta arude ta shiga neman wayanta tanaso takira Ya Faruk amma bataga wayanba hala tafadi awurin, tafashe da wani sabon kuka tana kare fuskarta ta hijabi ta.
Da gudu yay cikin layin clean white sneaker dinshi na shiga cikin chabali, bai damuba burunshi yakai gidan data shiga yaganta, wani irin mugun faduwa yayi cikin ruwan chabalin white rigan shi da wandonshi suka baci sosai, tashi yayi ahankali yana kuka sosai yana kallon hanunshi da jikinshi danko kadan ya tsani datti yacigaba da gudu yakai gaban gidan, da gudu shima ya shiga haryana neman faduwa sabida block dake wajen ya buge kafanshi ya kwala mata kira yana kalle kalle. "shee" amugun tsorace Hamida ta dagokai ta mike tsaye da mugun sauri tana kuka tana komawa baya, tsabagen yanda tai gudu tana haki, ga heart dinta dake beating way to fast yasa har dishi dishi take gani, zaro idanun dabata gani sosai tayi ta kalleshi kaman yanda yake kuka sosai yake wani irin kallonta cikin wani irin low and calm voice yace "uhmm is me" yay maganan yana takowa gabanta kanshi na rawa yanadan dingishi danya buge kafanshi sosai, zaro ido Hamida tayi tana komawa da baya tana ganin dishi dishi tana ganin mutum na tahowa amma bata ganin fuskarshi da kyau tsabagen dishi dishin dayake gani, ahankali take komawa baya yana tafiya ahankali shima yana goge kukan dayake yi yakeyi yana tafiya ahankali yana kallonta yana biyota hartakai jikin bango ta tsaya, karasawa yayi shima har inda take yana breathing fast sosai yana wani irin kallonta numfashin duka na sauka akan fuskarta, wani irin kallonshi take da idanunta that went completely blind tsabagen yanda zuciyata ke bugu shima kallonta yake zuciyarshi nawani irin bugawan da tunda yake baitaba jin yamai irin bugun ba, wani irin nishi yayi yana kara matso ta har kafafunshi na gogan nata, dawata irin murya chan kasa yar karama chan ciki yasakin mata wani irin kuka dako su Aabid baitaba sakin musu irinshi ba yabude hannayenshi ahankali yafada jikinta yana kuka yay cuddling nata so tight not knowing what exactly yakeyi and yake feeling but he just wanna cuddle and cuddle and cuddle her, dip wuta ya daukemata tai wani irin passing out instantly kafafunta suka lankwashe zatai kasa, ahankali yadaga kanshi daga wuyanta yana kuka sosai yana kallonta dukya jika mata wuyan hijabi da hawaye da miyau, binta yay da kallo ta yanda arms dinshi ne are d only things dake rike da ita danda tuni tazube akasa asume, jijjigata yayi ahankali ya fashe da kuka kaman karamin yaro yace "wake up, are you sleeping?".
_🌹IN BANI 🌹_
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na sainai adding a group din danake posting_
Maman Abd Shakur
17....
Goga fuskarshi yayi anata yana kuka sosai yace "wake up pls" yay maganan yana turo baki cikin kuka yana kallonta ganin shiru yasa ahankali ya kwantar da ita a kasan wajen, kwanciya yayi shima gefenta yana kallonta shi kanshi baisan meke damubshi ba, fashewa yasakeyi da kuka yarike hanunta dan wani iri heart dinshi kemai, he's feeling something all over his