Showing 24001 words to 27000 words out of 164763 words

Chapter 9 - IN BANI BOOK COMPLETE BY M SHAKUR.txt

M.Shakur   

26 Oct 2024

25014

kumbure kumbure hakanan yay bacci awurin.








Biyar saura daidai yafito daga dakinshi yana bugan kamshi yasa kananun kaya, Baffa yasamu zaune akan dadduma a falon yana jan charba, komawa daki yayi yadauko daya daga cikin tulin keys din motar Baffa yafito yadawo falon yazo inda yake yace "am going Oldman" shafa addu'a yayi ya kalleshi yace "kaje da driver karka tafi har airport da asuban nan kai kadai, bari ma tsaya nakira Sulemanu da Muhammad subika" kwankwaso yarike yace "waini yarone Baffa, ni gaskiya bawanda zaka kira, airport dinne ban saniba ko banda karfin kare kainane" yanda yake maganan cikin jin haushi yasa Baffa cikeda lallashi yace "a'a maida wukar, idan wani abu yasaman min ku mutuwa fa zanyi, naji kaje to amma kai tuki ahankali kaji, kadanje da driban kaji yaron kirki" to yace yafita daga dakin da sauri dan he's so eager yaga dan uwanshi, wajen motoci yayi yashiga motar yay warming sanan yay horn aka budemai gate yaja motar yafita daga gidan, minti kusan 20 ya dauke shi yakai airport din ya tsaya agaban arrivals yana jiran yaga fitowa su yana duba wristwatch din hanunshi no rolex.
Kaman daga sama yahango Mami cikin shiga ta alfarma tasa doguwan riga irinta larabawa tana rike da handbag sai Abie dake rike da hanun Aadil dake tafiya ahankali idanunshi sunyi jajir sun kumbura alamun yaci kuka yakoshi acikin jirgi gefensu kuma wani mutumi ne dake tayasu tura laugage dinsu a cart da sauri ya juya ya boye dan bayaso su ganshi, bayan motoci yadinga bi harya kai karshe sanan yaje ya kutsa ta cikin mutane ya zagayo ta bayansu suna cikin tafiya yazo ta daidai saitin Aadil dake tsakiyan su yasa hanunshi yarufema Aadil ido tabaya, ihu Aadil yayi yana turo baki dan dama acike yake daga Mami har Abie da sauri suka juya suka wanda yarufema dansu ido, ganin Aabid ne yasa duk sukayi murmushi duk sukai shiru. Cikeda masifa dakuma shagwaba Aadil yay ihu yana buga kafa akasa yace "open my eyes, leave me eyes alone" yay maganan ya daura hanunshi akan hanun Aabid din yanaja ihu yasakeyi yace "Mami My eyes" da karfi ya fizge hanun ya juyo cikeda fushi dan yaga waye ya kullemai ido Aabid yay wani irin ihu cike da tsantsan murna ya rungumeshi yace "oyoyo you this fight fight yaro" cikin wani irin murna Aadil yasakeshi yana murmushi dake lobar da two sided dimple dinshi yana ware manyan fine lulu eyes dinshi yace "Bid" wani irin tsalle yayi kaman yaro karami kanshi na rawa sosai yanajan riganshi yace "Bid, Bid, Bid, Aa...Bid" shima tsalle Aabid din yayi cikin tsananin farin ciki da mugun son dan uwanshi yanajan white long sleeve high neck Givenchy shirt da Mami tabashi yasa sabida sanyin jirgi yace "yes..yes, my one and only twin Bro, rascal, yes is me, hug me" cikin wani irin bala'in murna da rabon shi da irin murna haka tun Aabid nanan yawani irin fada jikinshi ya kankameshi sosai yana gogamai fuskanshi awuya yana murmushi sosai yana tsalle da kafa, rungumeshi back Aabid yayi yana shafamai baya Mami data gaji da tsayuwa ta ballamai harara tace "tunda bakuda ranan gama oyoyo oyoyon Abie mutafi mudai sa samemu a parking lot" da sauri Aabid yasakeshi yana dariya handkerchief dinshi yaciro daga aljihu yakai fuskarshi yana sharemai fuska da wuya yace "su Mami are jealous banyi hugging dinsu ba saikai My Dil" washemai baki Aadil yayi yana kallonshi, gama gogemai yayi shima ya goge wuyan nashi sanan yarike mai hannu yace "let's go kaga grandfather, kagaji ko" gyadamai kai yayi batare dayay magana ba dan sosai yaji yawani irin gaji gabanshi sai faduwa yake, hanunshi yakama sukai wajen Mami da Abie dake hiransu saida yafara bude motar yakai Aadil gaba ya zaunar dashi sanan yadawo ya saka akwatinan su a bot yarufe yadawo gaba ya shiga yana waigen su Mami da Abie yace "welcome Abie and Mami hope you all had a smooth flight" yakarshe maganan yana kallon Aadil dayay shiru yanata kallon waje, kunna motar yayi yaja saida suka fara tsayawa a wani masallaci sukai sallan asuba sanan suka dawo motar sukaja sai gida, horn yayi aka bude gate din yaja motar ciki gidan su, Yayin Mami ne da bigMum Dakuma Baffa dayafito daga daki rike da sandarshi kashe motar yayi Mami tafita da sauri ta karasa ta rungume yar uwarta Abie ma fita yayi, juyo dakai Aadil yayi ya kalli Aabid yana daddure fuska yace "who are all this people?" dan shiru Aabid yayi yana kallonshi dan wani zubin idan Aadil yay magana kaman wani Boss wani zubin kuma kaga kaman yaro dan shekara 3, ahankali ganin rigima yakeji kaman bashi yagama murna dazuba yace "gidan su Mami da Abie ne anan suka girma, and ko last year big eid ba anan mukayi ba kaman tane?" yatsine fuska yayi yace "take me back to our house I don't like here" hanunshi yakamo da sauri yace "iskancin naka yatashi ne rascal? Okay let's do this look" dan juyo dakai yayi ya kalli Aabid din idanunshi suncika da hawaye sosai suna shirin xubowa, ahankali Aabid yace "how about we just stay here sabida we want to be good children muma su Mami biyayya but kullum kullum am gonna be taking you out kana ganin cool places muna zuwa yawonmu how did you see d idea? Idea yamaka?" shiru yayi kafin ya daura hanunshi akanshi yana yatsine fuska, da sauri Aabid ya matso yataba kan nashi yace "menene ciwo yakema?" gyadamai kai yayi hawaye na xubowa da sauri yace "sorry sorry, tashi muje kaga Baffa sai muje daki kayi wanka kai bacci" fitowa yayi yazagayo ta side dinshi ya budemai kofa, fitowa yayi ahankali yana kallon Baffan su dayagani yana dogara sanda yana karasowa inda suke shima kakan nasu wani irin kallon Aadil din yake wani abu ya tsayamai awuya yaro har yaro amma ba lafiyan kwakwalwa, da sauri Aabid yaja hanunshi kafin kakan nasu yakaraso yace "Dil zokaga old man mai gilas" dariya kakan nasu yayi yadaga sandarshi zai bugama Aabid cike da wasa yadan matsa gefe yana dariyan isgilanci, ahankali ya daga hanunshi yana wani irin kallon Aadil dake kallonshi yana kokarin tunashi ya shafa kumatun shi har zuwa sajenshi yace "Hassan barka da zuwa, menene idanunka sukai ja haka kagaji ko?" gyadamai kai yayi ahankali, murmushi Baffa yayi yace "muje kahuta" ahankali yake tafiya Aabid a gefenshi sukai babban falo inda har ancika ko'ina da abinci, kin gaida kowa Aadil saima kuka daya saki shizai koma gidansu sai lallabashi ake yakiyin shiru, Baffa yacema Aabid yawuce yakaishi dakinsu yay wanka abiyosu da abincin.
_🌹IN BANI 🌹_




_This novel is for sale karki karanta in baki biyaba_


_in kinaso novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card ta watsapp number na sainai adding dinki a group din danake posting_






_Maman Abd Shakur_




14.....

Fadawa yayi kan katon gadon dakin ya rungume filon, ahankali Aabid yamaida kofar yana kallonshi dan idan lafiya yake yanda yaganshi dinan murna zaitayi yana tsalle yanajin dadi, takawa yayi yakarasa gaban gadon ya tsugunna yana shafa gashin kanshi ahankali ya juyo da kanshi ya kalli Aabid dake kallonshi idanunshi sun cika da kwalla sosai hakanan yaji baida sukuni gabanshi na faduwa sosai, ahankali Aabid yace "menene, are you sick Aadil talk to me" fashewa yayi da kuka again yatashi yafada jikin Aabid din, gyara zama Aabid yay a kasan shima ya rungumeshi back yanajin wani irin kunci sabida yanda dukyay wani suku suku, ahankali yace "shiiiiii, menene tell me meke damunka? your stomach?" girgiza mai kai yayi yarike hanunshi yana kallonshi yana turo baki, handkerchief yakara sawa ya gogemai bakinshi yace "kanka ke ciwo?" girgiza mai kai yayi, ahankali yana kallon idanunshi cikeda damuwa shima kaman zaiyi kuka yace "in kirama Mami to?" makemai kafada yayi yana kuka still, ahankali yace "tome kakeso kanaso kasani kuka ne nima?" gyadamai kai yayi da sauri yana Kuka ahankali, murmushi Aabid yayi ya dungure mai kai yace "zaka fara ko, tashi muje kayi wanka" ahankali murya chan kasa yanadan lumlumshe ido yace "she" da sauri Aabid ya kalleshi yanadan ware ido yace "she?" gyadamai kai yayi yace "uhm she" shiru Aabid yayi yana kallonshi ahankali yashafa kanshi yadanyi murmushi dan no one understands Aadil kaman shi, their emotions are so connected da at time he feels wat Aadil is feeling, ahankali yace "alright tashi muje kayi wanka to" dagashi yayi ahankali yamike tsaye, wani irin faduwa gabanshi yayi hakan yasa yay baya zai fadi da sauri Aabid yarike shi yace "Aadil!" rikeshi yayi gam suka kalli juna da sauri yawani irin dagoshi ya rungumeshi yace "are you okay Aadil? Come" ya kaishi kan gado, zaunar dashi yayi yaciremai hadadden takalmin kafarshi da safa ya ciremai rigan jikinshi ya barshi da singlet daya bayyanar da fadaddan kirjinshi dakeda wasu irin kwantattun gashi, kwantar dashi yayi yace "anjima kayi wanka rest, are you hungry?" girgiza mai kai yayi yana runtse ido da karfi, hanunshi Aabid yarike yana kallon fuskarshi dukya damu, ahankali Aadil yamika dayan hanunshi yakamo dayan hanun Aabid din yashiga wasa dasu yana kirga yatsunshi bakinshi na motsi yana murmushin dake karamai wani irin bala'in kyau shikadai, dan ajiyan zuciya Aabid yayi yacigaba da kallonshi yana kallon yanda yake maganganu chan kasa yana wasa da hannayen yana lumlumshe ido har bacci yay gaba dashi ahaka shiru Aabid yayi yana kallonshi batare daya karbe hanunshi daga nashi ba, bude kofan da akayi yasa yadan waigo Mami ce da big Mum suka shigo, maida kofar sukayi big Mum ta kalli Aabid tace "lafiya dan gidana?" dan ajiyan zuciya yayi yace "I don't know big mum but Mami wat is wrong with Aadil? Baida lafiya ne" zama Mami tayi abakin gadon tana kallonshi tace "lafiyan shi lau oho nidai banmasan yazance ma ba, yanata cemana she she tun jiya fa, wai mukaishi wurin shi, I don't know waye she din" kallon Mami yayi sanan ya kalleshi yanda yake baccin shi a natse ga dogon black eyelash dinshi kaman na mace yace "Mami kunfita dashi daga gidane bayan nai tafiya? Could it be yaga wata ne" da sauri Bigmum tace "dayake so ko Aabid? Hala saisa yake ta damun ku yanaso yaganta" dan murmushi Mami tayi tace "kai Anty tayaya yaro da baida lafiya ace yaga wata yanaso ai is impossible, IQ yarafa Aadil kedashi tayaya ma zaiso wata? Maybe kawai mafarki ne, mafarkin dayayi ne" da sauri Aabid yace "no Mami bahaka bane, look at it like this, yes IQ yara Aadil kedashi and yara tun suna kanana zakiga wasu yaran sunada ability to love, mutane nawa sukayi aure da sun fara soyayya ne tun basusan kansu ba tun suna wasan kasa? Is very possible, inhar Dil was able to connect with me, Mami, Abie, and kome nacemai yayi zaiyi, ya soni yay understanding dina, inhar bananan he will be crying and he feel my absence then I think ya..." da sauri bigmum tace "yafara son wata ba, tunda ai lafiyan shi kalau da baya zazzabi, amma dukya duburce, shi kanshi yarasa gane kan meyakeji, yarasa sukuni, yanata cemutu ku kaishi wurinta, wlh Maryam son wata yake" shiru duk Mami tayi tana kallon su daga ita har Aabid din maganganun suma dariya yabata tadan murmusa tace "boko ce tamuku yawa wlh inba hakaba tayaya Aadil ku kalli fa Aadil, look at Aadil fa me bambancin shi da yaro dan shekara 4-5, saidai ya nunamai iya magana da gane magana, dakuma iya karanta abu, tayaya ma Aadil zaiso wata ne jama'a, dan Allah kubar maganan nan is totally impossible" da sauri Big Mum tace "kajiki fa Maryama wani irin abar magana, so fa dakike gani rahama ce inbaki saniba, sanan so magani ne, kikasan ko ta sanadin sonta ya warke?" dan tabe baki Mami tayi ta buga tagumi tana kallon Aadil din tace "ba irin cutarnan so ke warkarwa ba Anty, so bata warkan da cutan datafi shekara talatin da, inhar asibitocin kasashen duniyar nan basu iya sunsa ya warke ba banjin so yanada wani tasiri ba, am sure hala yaga yarinyar dawani abu dayake so musaimai ne nawasa kokuma wani abun dayake so yananu mana saisa ta tsayamai arai" ahankali Aabid yana kallonshi yace "Mami nidai yanzu yaushe zamu koma na nemomai she din dayake so yagani, am sure he saw her somewhere a UK ne" Mami tace "ai Allah kadai yasan ranan komawan mu Son, Baba yace nemama Aadil maganin gargajiya za'ayi sanan kaikuma aure zakayi kafin kabar garin nan" dan murmushi yayi ya juyar da kanshi ya kalli Aadil, dariya bigmum tayi tace "wanan murmushi haka Aabid daga gani kanada budurwa ko" shiru yayi yana murmushi, Mami ta harareshi tace "miskilin banza kadai fito da ita inba hakaba in Baffa yasamo ma mata baruwana wlh dole ka aura" ta tashi daga kan gadon tace "Yaya mutafi".








*******
Tana zaune afalonsu suna kallon wani hausa film tareda Zainab da Ihsan da dazu da safe suka dawo daga Lagos, Mama kuma na daki Kaka ta rafka uban sallama daga bakin kofa batare data shigo ba ta kwalama Hamida kira. "Hamida, Hamida ai kinajina kikai shiru ko, oya fito mutafi kulle kofata zanyi na mikar da hakarkari" kaman zatai kuka ta kalli Zainab dake kusa da ita, hararanta Zainab tayi sanan tamata gwalo murya chan kasa gudun jar Kaka taji tace "wuce kitafi dakin Kaka dake warin daddawawiya" tafashe da dariya Ihsan ma natayata tace "Anty Zainab harda warin busashen kubebbewiya" suka kwashe da dariya dukansu Zainab harda sauka daga kan kujera tsabagen dariya Ihsan kuma taboye fuskarta a cinya tana dariya, wasu hawaye ne suka cika mata ido ta tashi, wayar ta dake kan kujeran ta dauka cikin fushi sanan tajuya zata fita daga dakin saikuma ta juyo ta kalli yanda suke mata dariya tadau filon kujera ta jefa musu da sauri Zainab ta chabe filon tana dariya harda hawaye tace "byebye daddawee" wani irin fashewa tai da kuka sosai da sauri Kaka dake bakin kofa tatura kofan ta shigo tana kallonta tace "ga aljana tazo ko takiraki kizo ki kwanta dole kiyi kuka" cikin kuka ta nuna Zainab tace "Kaka sunefa sukemin dariya wai dakinki na warin daddawa" da sauri Kaka ta kalli Zainab dahar lokacin ke dariya takama habanta tana shigowa dakin da kyau tace "rubabbiya haka kikace, dakina ne me warin daddawa?" da gudu Zainab ta tashi tai hanyar corridor dan tasan bakaramin aikin Kaka bane ta durma mata dundu, bin bayanta Kaka tai da kallo tace "aida kin tsaya nagadai ubanki ma anan yake karin safe bai taba cewa dakin uwarshi yana wariba" ta kalli Ihsan data kife kanta a cinya tana dariya tace "kekuma uban me kikeyi kanki akan cinyan ki wari kikeyine kike shinshinawa?" dariya Hamida itama dake kuka tafita daga dakin da sauri tana dariya tai hanyar sasan Kaka da gudu karo taci da mutum hakan yasa tai baya da sauri ganin Ya Faruk ne yadaure fuska kaman bai taba dariya ba yana sanye da da shirt da jeans ya watsa mata harara da sauri ta sunnar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta ahankali tace "sorry bangan kaba" dan kallonta yayi na kusan 1min sanan yafara tafiya yazo zai wuce saikuma ya tsaya ta daidai inda take ahankali yace "gobe zakuyi resuming school get ready I will drop u off" gyadamai kai tayi da sauri kirjinta na bugawa da sauri ta wuce ta shiga cikin gidan tabude dakin Kakan ta shiga, dakinta da Kaka ta gyara mata tabude kofa ta shiga dan gadone guda daya sai sip irin normal sip dinan data tayata jera kayanta aciki kwanciya tayi kan gadon tana kallon wayanta dake hanunta rabon data danna wayan tun suna Lagos, gyara kwanciya tayi ta lulluba da bargo ta kunna datan wayan nan yan few messages suka shigo saikuma message na massenger, zaro ido tayi kafin ahankali kaman mai tsoron wani abu ta shiga messenger taga new messege from Aadil Abdullahi, sosai taji gabanta yawani irin fadi takai kusan 2min tana kallon sunan dakuma profile picture account din dayake na rubutu an rubuta Unique ajiki ahankali tai sliding in tabude message din.


_Hello Anty Hamida_
_Hello Ihsan_
_I want to be your friend too_
_Anty Hamida pls don't beat Ihsan okay, Mami said beating is not gud_
_Me too I don't have friends and my brother said i can be your friends yayy_
_bye Anty Hamidaaaaa_


Murmushi tayi tana kallon chat din ahankali tace "wanan daga gani da kadan zai girmi Ihsan" shiru tayi tana kallon chat din saikuma takara murmushi ta shiga typing.


_I did not beat her, she was just scared_
_take care bye_
Tafita daga messenger ta shiga watsapp ganin batada any message yasa ta sauka ta shiga pinterest tana duba styles and latest arab collection na abayas, messege ne ya shigo da sauri ta sake zaro ido ganin is from Aadil, sosai gabanta yafadi ahankali kaman wata matsoraciya ta danna tabude.


_Anty Hamida where is she?_
_you see Mami and Bid don't want to take me to she, am seeing she anytime I close my eyes_
_I'm sick_
Shiru tayi tana kallon last maganan dan bataga ne da sauran maganun shiba, hakanan taji she felt somehow sabida yanda yace baida lpy, ahankali ta rubuta
_sorry, get well soon_ da sauri ta kashe datan ta kafin takara ganin wani chat din ta kwanta ta ijiye wayan nesa da ita tana kallon wayan maganan sick din ya tsayamata arai sosai ahaka bacci yay awon gaba da ita.


Da asuban farko Kaka ta shigo ta tadata kaman zata mutu da haushi ta shiga bayi ta wanko baki tai alwala tafito tazo tai nawafir sanan ta zauna tafara karatun saida aka kira sallan asuba sanan ta tashi tayi bayan ta idar tai azkarus subhi, ahaka tafara bacci, hararanta Kaka tayi tacigaba da jan katoton charbin hanunta, takwas saura Kaka ta daka mata duka a baya hakan yasa tabude ido da sauri tana kwalalo ido cikin bacci ta kalli Kakan, dakuwa Kaka tamata tace "ba zakije makaranta bane wai? Yi sauri ki shirya nina shirya d'an har wanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login