Showing 21001 words to 24000 words out of 164763 words
ciro wayar yana kallon screen din, dan juyowa yayi ya kalleta yace "Baba ne" da sauri ta share hawayen datake yi tana mishi alamu daya dauka, daukan wayar yayi cikeda girmamawa harda dan dukar dakai yace "barka da safiya Baba" daga tachan bangaren tsohon da akalla xaikai shekara 80 yace "da Abdullahi nake magana ko?" yay maganan a natse kuma dadaddaya kaman yanda tsofaffi ke magana, cikeda girmamawa yace "eh Baba nine" a natse yace "to, to, to Masha Allah, ya kuke? Ya sana'ar taka tachan?" murmushi yayi yace "Alhamdulillah Baba, sana'ar munakan yi kuma ana samun riba daidai gwargwado" ahankali yace "masha Allah, Allah ya taimaka, Maryama fa?" murmushi yayi yace "gatanan Baba bari nabata wayan" ahankali yace "tsaya tukunna" cikeda girmamawa yace "to Baba" dan shiru yayi kafin ahankali yace "ina Hassan da Hussain?" kallon Mami yayi suka hada ido sanan ya maida hankalinshi kan wayan yace "Alhamdulillah suna lpy, Hussain na Nigeria yanzu haka yana Lagos ya...." cike da fada yace "Hussain na Nigeria shine baizo gidaba? Abdullahi dagakai har Maryama inda kusan bazaku iya bama jikokina yan biyuna tarbiya mai kyau ba dakun banisu na rainesu sun girma sun taso anan wurina, amma yaro ace yana kasar iyayenshi munan bamamu da labari yana gari, kenan inda ban kirakaba da bazaka fadi mini ba" cikin kwantar da murya yace "kayakuri Bab..." da sauri yace "bannemi wanan daga gareku ba, yau kwanan shi nawa?" ahankali yace "kwanan shi tara Baba, wani assignment yajeyi a Lagos amma dama..." katseshi yayi ta hanyar kiran sunanshi. "Abdullahi" da sauri cikeda girmamawa yace "na'am Babana" ahankali yace "kafadama Hussain yakamo hanya yazo kano yauyau dinan gidan kakanin shi banason naji wata magana, sai magana nabiyu dayasa na kira" yadanyi shiru yana hutawa, a natse yace "ina Hassan, yaya jikin nashi?" dan juyawa yayi ya kalli Aadil dake bacci har lokacin yace "Alhamdulillah Baba, jikin nashi da sauki" cikin dan kakkausar murya tsohon yakira sunanshi. "Abdullahi" ahankali yace "na'am Baba" shiru yayi nawurin minti biyu kafin yace "kaima kasan nabaku lokaci mai tsawo, na tsaya sanan na zuba muku ido ina kallon ku dakai da Maryama, nasan ku nasan halinku na yaran zamani, sanan bankuma tauye muku hakkin ku ba a matsayin ku na iyayen yaraba, na barku babu kasashen duniyan nan dabaku zaga da Hassan ba tun yana dan mininin shi neman mishi magani, to kanajina?" da sauri yace" eh Baba ina jinka" cikin yar shakakkiyar muryanshi ta tsofaffi yace "masha Allah, abinda nakeso daku shine, ka tattaro yinaku yinaku ka kawomin jikana nan kano, ku kawomin shi nan kano afara mishi maganin gargajiya, zamu jaraba mugani abinda Allah zaiyi, bazan zuba muku ido ku karar min da rayuwan jikana a hanyar asibiti ba, burina shine ya warke namai aure naga tattaba kunnena kafin mai afkuwa ta afku wato mutuwa, ku kawomin jikokina Kano zan nema mishi magani da kaina, ku kawomin su, ku zaku iya komawa indanta Hassan ne zan daukomai babban nurse ko Nani dazai dinga kulanmin dashi" yay dan shiru yana Tari da sauri yace "sannu Baba" saida tarin ya lafa sanan yace "kuyi shirye shiryen dazakuyi, ku kwasan mai duk wani abu dayake so gudun karya muku kuka a jirgi inya gaji da zama, ku hada komi kutaho Nigeria gobe, kufadima Hussain ina jiranshi shikuma yauyau dinan" ahankali yace "to Baba" "yauwa ka gaidamin da Maryama" "to Baba zataji" ahankali yace "Allah yamuku albarka dukan ku, Allah yabama Hassan lafiya, Allah ya kiyaye hanya yakawoku lafiya" da sauri yace "Ameen Baba" "yauwa to, nabarku lafiya" ya katse wayan. Ahankali ya zare wayan daga kunenshi ya juyo ya kalli Mami data gamajin komi, ahankali yace "anjima kihada mai kayanshi komi da komi, I will sort out d booking" gyadamai kai tayi tace "to Alhaji Allah yabada sa'a" juyowa sukayi dukansu suna kallon Aadil din dake bacci ahankali Mum tasa hannu tana shafamai kai kafin tadan kwanta a gefenshi tana shafamai kai tana kallon fuskarshi, Allah kadai yasan yanda takeson Aadil dinan, zata iya bada duka abinda ta mallaka a duniya inhar zai warke, shafa fuskarshi tayi tana kallonshi hawaye ya gangaro mata daga ido ahaka bacci yay gaba da ita hanunta akan fuskarshi, kafesu da ido Abie yayi feeling guilty, babu irin tunane tunanen da baiyi ba, blanket din gadon yaja ya lullubesu dashi yatashi yafita daga dakin yarufo musu kofa yafita, dakinshi ya shiga ya zauna gaban study dinshi ya kunna laptop dinshi yaje sight din emirate airlines, booking yamusu yay making payment aka turamai booking reference din ta email dinshi sanan ya rufe laptop din yay shiru yana kallon wani babban zoben dake kan yatsarshi yakai kusan 10min yana kallon zoben sanan yasake daukan wayarshi, dailing number Aadil yayi amma baishiga ba hakan yasa yatashi ya kwanta akan gado.
***
Shafashi dayaji anayi yasa yabude ido daga wani irin nauyayyan bacci daya samu ya kwasheshi around 4 nadare tunda jiya dayadawo daga asibitin da aka kwantar da Hamida yakejin wani irin kunci, sosai zazzabi yarufe shi jiyan nan, ahankali ya daura idanun akan fuskar Vanessa dataci gayu sosai tai makeup a fuskar tana daure dadan white towel, kwanciya tayi akan kirjinshi tanama kirjinshi kiss murya chan kasa tace "handsome baccin ya isa haka okay, your temperature is normal yanzu, am so lonely Aabid how are you feeling now?" lumshe ido yayi yanadan cije lips yakira sunanta achan kasan makoshi yace "Vanes...sa" dago kanta tayi tace "yes Handsome menene? something seems off about you tun jiya dakadawo, kodai yarinyar nan is a witch ne dama she's too fine" bude idanunshi yayi duka yadaura akanta yana mata wani irin kallo da idanunshi dasuke cike da bacci a gajiye yace "watch your tongue" yay maganan yana kara lumshe idonshi danko kadan baison hayaniya ko motsi zaiyi sai Hamida tafado mai arai, anytime daya kulle idanunshi ita yake gani, ta tsayamai arai, ta tsayamai a thought, ta tsayamai akomi ma, baitabajin yanda yakejin nanba akan any girl, pink lips dinshi Vanessa takafe da ido kafin ahankali ta daura fuskarta kan nashi tana kallon lips din tana breathing heavenly takira sunanshi dawani irin low sweet voice. "Aabid, talk to me handsome, what's the matter uhm?" tai shiru tana kallon fuskarshi amma baiyi magana ba, kiss tamai akan fine soft lips dinshi light one, bude ido yayi kadan ya kalleta batare daya cemata komiba, murmushi tayi tai cupping face dinshi tace "lemme make you feel better" zaiyi magana ta daura yatsar ta akan lips dinshi tana wani irin mai sexy kallo tasanya dayan hanunta ta warware towel din jikinta tai flinging dinshi, lumshe ido yayi da sauri dan she's so tempting, yasan dayana school he and Vanessa dated for a very long time, but yanzu ya girma he really wants to change, baya sonta but she's just a girl a d tun yana school ta makale mai dudda ba same course suka karantawa ba, kuma ba same school sukayi ba, lokacin dasuka haduma masters yakeyi ita tana degree dinta a New York film academy, another thing dayasa yake kara kulata is because bata kula any guy bandashi dan yanada mugun kishi, yarinyar na sonshi sosai bana wasaba, they had sex couple of time dan akwai wasu abubuwa datake mai da koyaya yaso karyayi saiyayi but yanzu he really wants to change, yasan a Islam abin is a sin haramun ne saisa yaketa son yay aure but baitaba ganin wacce yakeso ba, wacce tamai ta kwantamai arai baitaba ganiba, yaje kano sau da dama all his cousins, duk yanmatan garin dayake gani ko sha'awa basu bashi balle yamaji yana sonsu, sai akan Hamida dayaji he loves every single thing akan yarinyar, yaji his whole world is revolving akanta.
Grabbing dinshi dayaji tayi down there yasa ya saukar dawani irin ajiyan zuciya ya ware Ido ya kalleta, da kyar ya iya yay fighting yanda yakeji dan he so want it shima bana wasaba, hanunta yarike cikin rashin karfi ya girgiza mata kai yace "stop it" fashemai tai da kuka ahankali tace "please Aabid, I want you badly handsome, nakasa saurayi Aabid, nobody can f*ck as good as you, please my love, okay I understand you said having sex without marriage in your religion is a sin right" tai maganan tana share fuskarta da bayan hannu ta kalleshi, gyadamata kai yayi yana mika mata bargo danta rufe kirjinta dake dancing a face dinshi, karban bargon tayi tarike tareda hanunshi tace "okay let's get married handsome" lumshe ido yayi ya girgiza mata kai yace "I cannot get married to you" da sauri tace "why?" bude idanunshi yayi ya kalleta ahankali yace "because I don't have feelings for you" fashemai tayi da kuka tafada jikinshi tana girgiza mai kai tace "please love dont say that kaji My Aabid, am begging you" zaiyi magana wayarshi tai kara alamun shigowan message ahankali yamika hannu yadau wayar da sauri yabude sakon ganin daga Abie ne, yana gama karantawa ya ijiye wayan wani irin murmushi yayi yace "Kano!" tashi yayi daga kan gadon, drawer gefen gadon yajawo, bundle din kudi yaciro nayan dubu daidai guda biyar ya ijiye mata yana kallon yanda take goge idanunta da hannu yace "get ready and leave, am going to my grandparents house, my parents are coming to Nigeria tomorrow, take care okay will call you" juyawa yayi ya shiga bayi tabi bayanshi da kallo kafin ta kalli kudin daya ajiyemata tafashe da wani kukan sanan ta tashi ta kwashi kudin ta wuce tafita ta shiga next room ta shirya tsaf tsabagen yanda takeji haushin shi ko jiranshi tamai bye batayiba tadau jakanta tafita tana kumbura kumbure.
Yana fitowa shafe shafenshi yayi yana murmushi, yasan halin kakan shi hakan yasa ya shirya cikin wani white soft yard da akamai dinki jumper, bakaramin kyau kayan sukamai ba, kallon wardrobe din yayi yana kallon kayanshi he's so lazy, baida karfin dazai wani hada kayanshi a akwati banda hakama yanada kaya achan kano, hakan yasa yaje gaban madubi turaruruka ya fesa yana kallon kanshi a gaban mirror yanda farin kayan yawani irin haska shi ya shiga kayan dam yay wani irin shegen kyau, ahankali yana murmushi yace "am coming Jewel saina nemoki koma a ina kike agarin kano, ur husband is coming Mrs Aabid" murmushi yasakeyi ya zira takalmin shi na Gucci yadau wrist watch dinshi ya daura, wayarshi ya dauka yafita daga dakin yafara sauka kasa yana danna waya yana order Uber, ya sauka kasa yana wani irin kamshi dukya cika gidan da kamshin turaren shi, kitchen ya shiga yahada coffee a mug yafito zama yayi kan kujera yanashan coffee kafin Uber yazo yana cikin sha mai Uber yazo, tashi yayi yaje ya ijiye mug din a kitchen yafito ya kulle gidan, mai gadin yabama key yamai sallama tareda mai kyauta sanan yawuce yafita gate ya shiga motar Uber yajashi har airport yana zuwa yay komi Azman airline zaibi to Kano, ya karbi boarding pass dinshi yawuce upstairs ya shiga departure lounge bai wani dadeba akai announcing boarding dinsu, tashi yayi yawuce yaje yay boarding jirginsu yadaga, 1: 25 jirgin su ya sauka a Airport din kano, wani irin murmushi yayi yafito yana kallon ko ina rabonshi da kano almost a year kenan, yasan inda yafadama grandpa yana hanya da yanzu airport dinan yacika da motoci anzo daukan shi, he's so eager yaga Aadil gobe, karasawa yayi yashiga taxi yacema mai taxi din "New GRA zaka kaini".
_🌹IN BANI 🌹_
Maman Abd Shakur
13....
_This novel is for sale karki karanta in baki biyaba_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card ta watsapp number na sainai adding dinki a group din danake posting_
Agaban wani babban gida yasa akai parking, gidan babban gaske ne dan yay girman wani anguwan, fitowa yayi daga mota yabama mai taxi kudi, masu gadin gidan dake sanye da kayan security ne suna ganinshi suka washe baki. "laaaa jikokin Alhaji ne, barka da zuwa oga" murmushi yamusu ya gyadamusu kai dan baijin yin magana suka budemai gate ya shiga, babban gidane dakeda fadi sosai gawani hadadden water treatment plant a tsakiyan compound din dayay kaman round about ta gefe kuma wajejen parking cars ne inda cars sunfi kala goma apake awurin, gawasu irin hadaddun design din flower dayabi ko ina na tsakar gidan babu kowa atsakar gidan kasancewa babu kananun yara a gidan inbadai jikoki sun zo kokuma anyi hutun school shine zakaga yara cike a gidan, da saurin shi yakarasa shiga ciki yay shashin kakanshi bude kofan part dinshi yayi babban falone dayasha hadaddun manyan kujeru sai carpet mai bala'in kyau da taushi dake shimfide akasa, wani tsohone azaune yasha manyan kaya dadan rawani akanshi idanunshi sanye da glasses nakara karfin ido, yana zaune akan wata lumstatsiyan kujera hanunshi rike da jarida yana dubawa gefen kujeran dayake zaune kuma yar sanda ce ajingine awajen wanda daga gani kasa ita ke taimakamai ya tsaya yay tafiya, manyan mazane guda uku a falon zaune akasa wanda suke yaranshi Uncle Suleman, Uncle Muhammad, sai last namijin shi Uncle Mustapha, sai mace guda daya wacce take yayar Mami tana sanye da hadadun kayan kamansu daya da Mami mai suna Asma'u, sunfi kiranta da Big Mum, itama tana zaune a falon suna hira suna shan slice fruits dake wadace agaban su, ahankali yay sallama ya shiga falon yana dan sosa keya dan yasan shima laifine, dukansu dagokai sukayi suna kallonshi cikeda mamaki Uncle Suleman wanda yake babban yayan su yace "kaga daman zuwa yanzu Hussain aika kyauta" kaman zaiyi kuka yakaraso cikin dakin yace "sorry Uncle" cikeda masifa Uncle Muhammad yace "bazaai sorry ba, shine baka fada ka shigo hanya ba kadauko taxi daga Airport kataho wat if something happen akai kidnapping dinka ahanya eh?" sake dan turo baki yayi yana kallon Baffan daya janye jaridan daga fuskarshi yana kallonshi yanamai wani irin calm love look irin na kakanni da jikoki, a sanyaye yay murmushi yanadan sosa keya ya ware hanunshi yatafi wajen tsohon. "oyoyo Grandfather oyoyo Oldman dina" karasawa yayi zai rungumeshi tsohon yadau sandar gefenshi yana nunashi dashi cikeda masifa yace "ka zonan kaga yanda zan kwaleka da sandar nan" da sauri yakoma baya ya zauna kusa da Anty Asma'u dasuke kira da big Mum kaman zaiyi kuka yace "Big Mum kinga grandfather zai bugamin wanchan ugly sandan nashi ko" dariya duka yaran sukayi tsohon yanunamai sandar cikin jin haushinshi yace "kana Nigeria kusan sati biyu saiyau zakazo dan baka da mutunci bakasam mahimmmancin yan uwanka bako, kullum da tunanin ku nake kwana nake tashi aika kyau" kallon Uncles dinshi yayi dake kallonshi cike da so yace "Uncles am sorry kunji, Big Mum am sorry wani assignment fa nazo yi dama nace saina gama zanzo, kema kinsan bazan iya zuwa Nigeria banzo wajenki ba, please Uncles kucema grandfather am sorry" duk dariya sukayi gabadayan su, Big Mum ta shafa kanshi tana kallon mahaifin nata tace "amai afuwa Baba bazai karaba" baban yayansu Suleman yace "Baba amai afuwa ai gashinan yazo, muma madan huta da maganan yan biyun ka dakake ta mana" kallonshi tsohon yayi yanajin wani irin sonshi aranshi tun yana saurayi yaso yan biyu yakeson yan biyu amma Allah baitaba bashi ba sai akan jikokin shi akuma kansu saisa yake mugun sonsu, ahankali yamai alamu da hannu. "yaka" da sauri yatashi yaje yana murmushi rungumeshi yayi ahankali yana dariya yace "My old grandfather kajika fadafa duk randa kabugamin sandar nan ai shikenan sai mutuwa" da sauri yadan zaro mai ido yace "kul denamini maganan mutuwa, sainaga yaranka, naga yaran Hassan dinka ma in sha Allah" dariya duka yan dakin sukayi, murmushi shima tsohon yayi ya nunamai gefenshi yace "zauna anan" ya kalli Asma'u yace "Asama akira masu aiki su kawomai abinci, kice suzo sufarajin meyake so tukunna abinda yakeso shi za'a dafa" da sauri tace "to Baba bari na turosu" tashi tayi tafita, ya kalli Suleman babban danshi yace "Sulemanu akiramin duka jikokina duk suzo gida ayi liyafa na kwana uku tunda Hassan da iyayensu gobe zasu shigo suma" murmushi duk sukayi sukace to Baba, yasake kallon Aabid din dake kallonshi kaman zai cinyeshi dan dudda tsufanshi badai kyauba yace "kaikuma tunanin me kake" shafa kanshi yayi ya kwanta akan kujeran yadaura kanshi kan cinyar Baffan yace "nothing old man" gashin kanshi ya shafa yace "wanan karan bazaka bar garin nanba saida mata namaka alkwari kodai kafito da ita kokuma na nema maka dakaina" sosai gabanshi yaji yawani irin fadi hakan yasa yadan lumshe ido yakai hanunshi yadaura kan kirjin yana ganin Hamida a idanunshi. Hanunshi Baffa daya gani akan kirji yakama yana kallon yar karaman yatsarshi yanda yabar kunba a yatsar yace "kumban nan fa Hussaini zama cikin yaran yahudawa ne yasa zaka fara abu kaman su" dan murmushi yayi yace "ina jirane fa jumma'a nayi na yanke ta" daga kanshi yayi daga kan cinyarshi dan ya tsani ganin mutum da doguwan kumba yace "tashi ka daukomin kayan yanke kumba adakina kazo nan na yanke maka ita" tashi yayi yana dariya dan grandfather is just d best ne, he's so caring akansu, ga masifa, ga kirki ga korafi ga naci shidai Baffa babu abinda bai hadaba. Dakinshi ya shiga da komi yake a gyare dakin sai kamshi yake yadauko abin yanke kumban yafito yadawo kusa dashi a shagwabe ya zauna kaman wani yaro yabashi yace "please Grandfather karka ciremin kaji" hararanshi yayi yakama hanunshi yana gyara glasses din idanunshi yashiga yanke mai kumban tass har sauran da basukai wanan fitowa ba saida ya yanke, daidai lokacin masu aiki sun shigo dakin sanye da uniform cikeda girmamawa suka gaishe shi suka tambayi mezasu dafamai ahankali yace "just something light" dan bama yunwa yakeji ba yasan idan yace yakoshi ne bala'i zasuyi da Baffa dan dole saiya sashi aci wani abu zaima iya yabashi da kanshi.
Haka ranan yawuni da grandfather banda masallaci babu inda yabari yafita yaje dudda yaso yabi bigmum yaje gidanta hanawa grandfather yayi, koda daddare kin bari yaje part dinshi yayi yace anan part dinshi zai kwana wani hadadden daki dake kusa da nashi ya shiga yana