Showing 18001 words to 21000 words out of 164763 words
jingina yay da bango ya lumshe ido zuciyarshi yamai so having wani iri yakeji da baitabaji ba in his life, kasa daurewa yayi yabude idanunshi dawani irin sauri yaja kofar yabude yafita daga dakin harda dan gudunshi he wanna see her one last time, yafita bude kofar reception din yayi ya tsaya akan stairs din wajen daidai lokacin Faruk yabude mata bayan motan zata shiga da sauri ya kwala mata kira. "Amatullah!" da sauri daga ita har Faruk suka waigo, hada ido yayi da ita kirjinshi nawani irin suya ahankali yasakin mata wani irin murmushi mai ciwo ya daga mata hannu alamun bye, da sauri ta dauke kak ta shiga cikin mota tana watsa da bakin hijabin ta Faruk yarufe kofan ya juyo yamai murmushi ya dagamai hannu ya shiga gaban motar mai taxi din yaja motar suka tafi sukabar haraban asibitin, motar yabi da ido zuciyarshi namai wani irin rawa rawa har saida yadena hango motar ya lumshe ido, ahankali yabude idon ya sauka daga ya wuce ya shiga motarshi ya kifa jikin kujera yakai kusan 3min kafin yadago yatada motar yaja yabar asibitin da kyar.
Ihun daya cika gidan dashi yasa Mami ta farka daga baccin datake firgigit da salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un, Abie, Abie" firgigit magidancin da akalla zaiyi shekaru 60 shima ya farka yana kallonta yanda Mami ta firgice tana kokarin zira slippers yasa shima sauka daga kan gadon kafin ma yasa nashi bathroom slippers din har Mami tafice daga dakin da sauri tafita tai dakin tabude dake facing nasu, wutan dakin akashe sai ihu yake yana kuka, da sauri Mami ta kunna wutar dakin tai kan gadon, yana kwance sai ihu yake yana juye juye yana kuka idanunshi a rufe, da sauri takarasa jikin gadon ta zauna tana bubbugashi. "Son, Son, Aadil, Aadil" da sauri baban nasu ya karaso ya zauna ta wuraren kanshi yasa hannu yadagoshi ahankali yana kiran sunanshi shima. "Aadil" ganin bai bude idoba har lokacin wani irin kuka yake yasa yanuna ma Mami bottle water shi da ake ajiyemai a gefen bed dan yana tashi yasha ruwa cikin dare, da sauri Mami ta dauka tabude, hanunshi ya mika mata ta xubamai ruwan kadan yashafamai a fuska yana kiran sunanshi. "Aadil, Aadil" bude idanunshi yayi yana kallon ko ina nadakin yana jujjuya idanunshi, da sauri Mami ta matso kusa dashi takama hanunshi tace "am here Son, menene? Mekake so eh? Mekema ciwo tell me" tashi yayi daga jikin Abie yafada jikin Mami yasaki kuka ya rirriketa kanshi narawa yana kuka sosai, shafamai kanshi dataji yay zafi ta shiga yi tama kasa magana sabida yanda gabanta ke faduwa, tsugunnawa Abie yayi agabansu bayan ya sauka daga gadon ya shafa kanshi yana kallon fuskarshi yanda yake kuka ashagwabe, cikin lallashi yace "is okay, are you missing Aabid, zance yadawo gobe okay" fashewa yay da kuka sosai harda shesheka yarike Mami gamgam yana girgiza kai, shafa kanshi Mami tayi ta dagoshi handkerchief dinshi Abie yamika mata ta karba ta sharemai wuyanshi da fuskarshi tace "menene? Mafarki kayi? Why are you crying like this, tell me menene" cikin kuka sosai kanshi na rawa yace "s...she..she" da sauri Mami tace "she? Wace she? Menene kuma she Aadil?" fashewa yasakeyi da kuka yace "Mami I want to see her take me to her, Abie" ya kalli baban su yana kuka sosai yace "Abie take me to her" da sauri Mami tace "wane Aadil? Wazamu kaika wurinta? Who are you talking about" fashewa yayi dawani irin kuka yana jan rigan Mami cikin kuka sosai yace "shee" hawaye Mami ta share tana gogemai nashi tace "kaga Aadil dan Allah kadena kukan nan is not good for you, u had a dream I guess, bamusan waye she ba, but zamuyi addu'a ko my Son" make mata kafada yayi yana kuka sosai yana wani irin nishi yana make mata kafada yana tura Mami yana komawa baya ganin haka yasa Abie yahau gadon yana kamashi ganin yana neman buga kanshi yace "Aadil come, a ina she din take to mukaita wurinta? Why are you looking for her, dena fushi zamu kaika wurinta, fadamin who is she eh my Boy?" cikin wani irin kuka yana kallon Abie da idanunshi dasukai ja yana lumlumshe ido yace "she, Abie She, she, Abie I want to see her" da sauri Abie yace "to dena kukan zaka ganta, zamuje but saikasha magani sai muje wurin she, zakasha ai ko?" da sauri ya gyadama Abie kai yana dafe kanshi dakemai wani irin ciwo yana lumlumshe ido kanshi na kokarin tunano mafarkin daya gamayi yanzun nan, fuskar Hamida yagani tazo dakinsu ta tsaya abayan labule shikuma yana kan gado yana buga game din race awaya, dan bude labulen tai kadan ta kwalamai kira tana dariya sosai. "Aadil" da sauri yadago kanshi amma saita koma bayan labulen baiga fuskarta ba, make mata kafada yasakeyi yaki tasowa yacigaba sake lekowa tayi tana dariya sosai takirashi. "Aadil" da sauri yadago kai da gudu takara buya abayan labule, ahankali ya ijiye wayan yatashi daga gadon kanshi na rawa yana sanye da clean white t-shirt danshi mayen white ne baya yadda yasa wani kaya ko Mami tabashi inba white rigaba, da wani fine common flag 3quater daya tsayamai agaban gwuiwa kadan, kafanshi sanye da slippers white yataho kanshi na rawa bakinshi na zubar da miyau yanadan lankwasa kai yana leken labulen yana turo baki kaman mai shirin yin fada yana hararan labulen kaman dan yaro yace "who...who are you?" makemai kafada tayi tacikin labulen tace "oh'oh find me and know me Aadil" cigaba da tafiya yayi harya karaso jikin labulen yana hararan labulen yasa hannu yaja labulen da karfi da gudu tana dariya sosai tajuya zata gudu ya damko hanunta dan juyowa tayi kadan ta kalleshi one side din fuskarta yagani tana sanye da glasses fari, zaiyi magana yaga ta fizge hanunta ta gudu da gudu shima yabita amma koda yafito harya sauko kasa bai ganta ba hakan yasa yadinga kuka cikin mafarkin yana nemanta.
_Wanan littafin is a pure, clean, sweet, mesmerizing, warm, twisted love story dabaku taba ganiba, trust maman Shakur kullum sabon Salo nake kawoma makaranta littatafai na_ .
Alhamdulillah anan nakawo karshen free pages din littafin _IN BANI_
In kinason cigaba da karanta littafin nan mai suna _IN BANI_ danjin yanda zata kaya Zaki tura 300 ta account number na 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na sainai adding dinki a group din danake posting.
Zaki iya turo katin MTN ta watsapp number na kaman haka 07012181461, for any enquiry you can contact me through my watsapp number 07012181461. Thank you lovelies. I love you and I appreciate your support.
_🌹IN BANI 🌹_
_M. Shakur_
11...
Suna kaiwa airport yabiya musu kudin komi suka jira kafin suyi boarding flight dinsu, tana rike da hanun nun Faruk gam tana bobboye fuska, ahaka harsuka iso kano saukowa sukayi suka shiga taxi dazai kaisu gida.
Sosai taji hankalinta yawani irin kwanta data gansu a anguwan su sai murmushi take tana kallon anguwan su, ta mirror Faruk ke kallon fuskarta yanda take murmushi tana kallon hanya, suna parking a kofar gidansu da sauri tabude kofan motar tafita, Mama ce kadai a tsakar gida da matan dake zuwa musu wankau, wani irin murmushi tayi ta kwala mata kira. "Mama" da sauri Mama ta juyo jin muryan Hamida, wani irin gudu Hamida tayi taje tafada jikinta tana dariya ahankali yanda takeyi, cikin jin dadi da tsananin farin ciki Mama tawani irin rungumeta tace "kedawa yene Hamida?" tai maganan tana cirota daga jikinta dan taji tsoro ganinta kaman an jehota, ko kadan batasan Abba yacema Faruk yaje yadaukota ba jiya da daddare ba, tana jikinta rungume da ita tace "Yaya Faruk yazo yadauko ni fa Maman mu" daidai lokacin Faruk ya shigo gidan rike da jakanta, murmushi Mama tayi tace "to aisai kije ki gaishe da Kakan ku kizo" tasaketa tana kallon Faruk dake karasowa wajen rike da jakanta tace "sannu soja shine ta barka da jakan ko" ahankali ya ijiye jakan agaban Mama kanshi akasa yace "ina kwana Mama" sakin Mama Hamida tayi tai hanyar sasan Kaka, ahankali ta turo kofan ta shiga tana kallon ko'ina tai sallama cikin daga murya Kaka tace "Hamida, Hamida, aini tun ranan dazaki tafi nace saikinsan mekika yi, sai kinsan me kikayi, me kika shirya, saikinsan kirsa da kisisina dazaki hada ki dawo garin nan, Hamida anya bazan kiramiki malamai azo amiki rukiyya ba inaga aljanu gareki fa" dan turo baki tayi tasami waje ta zauna nesa da ita tana wasa da bakin hijabin ta kaman bada ita ake magana ba, zaro ido Kaka tayi tace "nikika maida mahaukaciya ina magana kinmini banza" daidai lokacin Faruk ya shigo dakin, watsa mata harara yayi yace "ke tsohuwar nan kin cika ihu, please inada ciwon kai yau kiyi shiru pls" yay maganan yana karasawa wajen fridge din dake falon, binshi da kallo Kaka tayi baki abude hakan yasa Hamida tarufe bakinta da hijab tana dariya chan kasa kasa, juyowa Kaka tayi ta kalleta ranta abace tace "dan gidanku dariya kike mini" da sauri ta girgiza kai still tana dariya chan ciki gudun karta ji tana kare bakinta da hijabi daidai lokacin shima Faruk yadawo rike da bottle water ya zauna a gefen Kaka zai bude bottle water, duka ta dakamai abaya da sauri ya kalleta cikin fushi yace "auch waike old lady nan me haka kike dukana agaban yara" kaman Kaka zatai kuka ta nuna kanta tace "kafara kirana da wanan yaren yahudancin ko Faruku, to wlh bari ubanku yadawo saina fadamai cin mutunci dakuke shigowa har Sasa na kukemin, ku tashi kufita, kutashi kufita nace, kuma bani ruwan gorana saurayin Zainaba ya kawomin su kusan katan biyar, bani" tafada bacin rai tana mika hannu zata karbi ruwan, tsaki yayi yadaura kafa daya kan daya yanashan ruwan shi ahankali Kaka tasaki baki tana kallonshi tace "ai shikenan kasha wuta shege dan buhun uba" fashewa da dariya Hamida tayi dayasa Faruk saukar da ruwan daga bakinshi ya watsa mata wani mugun kallo da sauri ta tashi tafita daga dakin da gudunta yabita da kallo, hararan kofan Kaka tayi tace "ja'irar yarinya, ai wlh Faruk banso kaje ka daukota ba, so nayi jiya da Sama'ila nama maganan kace aiki zaka, baga tanan ba rass bataima kama da wacce tafada ruwaba" juyowa Kaka tayi ta kalleshi daidai ya ijiye ruwan akasa tace "kaje wurin Maman kane yau?" girgiza mata kai yayi yana yatsine fuska, yace "sai anjima da yamma yanzu aiki zan tafi" washemai baki tayi tana kara matsowa kusa dashi tana murmushi tace "Faruku na wai har yanzu ba'ayi albashin bane, kamin alkawarin dubu ashirin fa" hararanta yayi yace "jiya agabana Abba yabaki dubu talatin wai mekike yi da kudi ne haka?" sake matsowa kusada shi tayi kaman zatai gulma tace "na rantse maka Faruku adashi nakeyi, tara kudin bikin Hamida nake" wani irin kallo yamata yace "wace Hamidan?" baki tabude tace "kagamin iskanci munada wata Hamida agidan nanne bayan wanan hamidan data fita daga dakina yanzu?" cikin daure fuska yace "yaushe tai saurayi?" sake matsowa tayi kusa dashi kaman wacce ke shirin yin gulma tace "a'a kaima dai kasan ko mashinshini Hamida batadashi ko, amma so nake kabani kudin dukna hada naita zubin adashi ina tari, inama bikin ta tari, kasan Hamida yar wajena ce, itace mai sunana fa, kaga shegen fadan nan danake mata wlh sonake ta chanza ne dan batayi gadon halina ba, bataci sunana da aka bataba, amma dazaran ta chanza zamu zo mu fara shiri sosai, nama tuna bari naje sasan su hado kayanta zatayi tadawo shashin nan ma yau dinan" shiru tayi tana nazarin yanayin fuskanshi yanda yay kini kini darai, tace "kaikuma lafiyan ka naga kai wani iri" yatsine fuska yayi yace "am fine" ya mike tsaye yana gyara kayan jikinshi yace "natafi aiki" tashi tayi tace "muje na rakaka, kadan tahomin dayar bakan leda kaji inzaka dawo, tunda su Zainaba da Ayush sukabar gidan da yunwa nake kwana Faruku" hararanta yayi yanaji kaman ya bugeta kiri Kiri sai Kaka tabude ido tana karya, dariya tayi sosai ganin yanda yake kallonta tace "bawai yunwan abinci ba na kayan kwadayi, idan kadawo kaza bani kudin aiko? Bazanyi barci ba zan jiraka" hararanta yayi yajuya zai fita hanunshi da damke tace "dan ubanka saika bani danma ina lallabaka" kaman zaiyi kuka ya kalli yanda ta damke well ironed uniform dinshi yace "naji inna dawo zanbaki, ki saken to" sakinshi tayi tana dariya ta dungure mai kai tace "ja'iri barima ubanku yadawo yau zan mishi maganan aurenka ne, wlh koka fito da mata kona je kauye nahadaka dayar aminiyata Iyami" tsaki yayi tsabagen takaici baima tsaya yabata amsaba yawuce yafita daga sasan da sauri tabi bayanshi amma har yay wajen gate hakan yasa tai tsaki ta wuce part din su Hamida.
Da sallama ta shiga falon su Hamida tagani zaune a falon tanacin indomie data dafa da boiled egg tana kallon zee world tana ganin Kaka tai murmushi tana sunnar dakai, hararanta Kaka tayi tace "aikin kenan ki zauna ke kadai awuri babu kowa shine burinki a duniya miskilan banza, ni ina mamarki?" daidai lokacin Mama tafito daga kitchen rike da tray data debo wake dan gyarawa zatayi tana ganin Kaka tai murmushi tace "yau Umma a shashin mu" da sauri Kaka tace "eh nazo ne, kihada ma yarki kaya sasana zata dawo" turo baki Hamida tayi tana tauna abincin dake bakinta ahankali Kaka ta kalleta tace "ahap ai saidai ki mutu ingayamiki yarinya, yaushe zasu koma ma makarantan yama sunan hutun da sukaje?" murmushi Mama tayi tana karasa shigowa cikin falon tace "mid semester break" da sauri Kaka tace "yauwa shi yaushe zaku koma ke?" tai maganan tana kallon Hamidan dakecin abincinta, dan turo baki tayi tace "ranan Monday" kwafa Kaka tayi tace "saura wanan karan ma ki kwaso zero zero a makarantan kaman na wanchan karan, wlh cema Sama'ila zanyi bazai kara kashemiki koda sule biyar a makarantan ba, aure zamu miki, inyaki kuma nida kaina zan aurar dake" da sauri ta kalli Kaka, gyada mata kai tayi tace "eh kinjini da kyau, wlh aure zansa amiki inhar wanan karan ma kin fadi kaman wanchan tunda kedai bazaki saki ranki ki jona mutane kikoyi abuba, ba nannan zainaba ke zuwa makaranta karatu ba banda ke, malami na koya muku abu kina kakkare fuska kikasa kallon allo, yoto menene amfani Sama'ila yay ta bata kudi akanki har shekara hudu? Kema kinsan naso keda Zainab da Ayush dakuna gama sakandire a aurar daku amma kuma sainazo na hakura da Sama'ila ya nunamin yanaso kuyi karatu amma kam wanan karan bala'i zanyi dashi dan wlh bazan bari dan kudin dayake samu a saida kaji, saida kajifa jama'a yazo yana batasu akanki ba, dan asarace, da'ace nine yabama uban kudaden danasan menayi dashi kuma Allah kaimu mondan, ni nan dakaina zan kaiki har Bayeron incema malamin ku wlh yazane min ke tunda dai kinki maida hankali kiyi karatu" tai shiru tana kallon Hamidan data daura hannu a fuska tana share hawaye, tsaki tayi ta kalli Mama data zauna kan kujera tafara gyaran wakenta ita yanzu bala'in Kaka baya damunta dan tsufa ce yamata yawa, cikin masifa tace "ai cewa nayi kibar gyaran waken nan kitasa keyanta taje dakinsu ta ciro kayanta daga sip dinsu, na Zainab da Ihsan kawai zaku bari a sip din ta tattaro tadawo Sasa na, nariga na share dakin dazan bata tastas, Allah kuma yakaimu Monday zakiga nizan kaiki makarantan na rantse miki saina sa malamin ajinku yamiki bulala goma hala hakan zaisa kifara karatu, kici jarabawa da kyau, kigafa tunda sukai hutun nan banga tabude littafiba fa, kullum tana nanike adakin su daga taci saita bacci sai shegen bacci kaman kaza, ki ajiye kwanon wanan tsutsan kampanin duksu kesaki bakida kyan gani, yarinya taci tuwon dawa da miyan kalkashi abinci mai Gina jiki bazata ciba sai tsutsan kampani" murmushi Mama tayi tace "Kaka indomie ce ba tsutsan kampani ba" cikin daga murya kaman zata fasa gidan tace "injiwa Haleematu" ta nuna plate din tace "ke bakiga yanda abin take a lankwashe ba, wani irin ziza ziza da ita, tsutsa ce saisu busar saisu barbadeta da fulawa fa asaka a leda a sayar" ta kalli Hamida dake share kwalla tana tauna indomie bakinta ahankali tace "ba dake nakeba dan gidanku, tashi kije mamar ki ta tayaki hada tulin kayan ki, dama gobe su Zainaba zasu dawo sa sami sarari adakin suma" tashi tayi ahankali tai hanyar corridor inda dakinsu yake, ajiye waken Mama tayi ta tashi tabita tana murmushi kasa kasa Kaka tabisu da harara kafin takarasa tadau plate din indomie tafice dashi tana hararan abincin takarasa wajen bolansu zubar da indomie tayi sanan ta wuce chan pampo ta ijiye kwanon ta wuce Sasan ta.
_🌹IN BANI 🌹_
_Maman Abd Shakur_
12....
Tashi Abie yayi yadauko maganin shi da yawancin inya fara surutai haka shi ake bashi ya dauko da sauri yadawo kan gadon ya dagoshi yana mikama Mami maganin yace "tashi kasha to saimuje wajen She" gyadama Abie kai yayi yana kuka ahankali yana yatsine fuska, zuba maganin Mami tayi ta mikamai ahankali yabude baki ya shanye maganin da kyar kullum yake yarda yasha amma yau yasha da kanshi, yanasha ko two minutes baiyiba bacci yay gaba dashi, gyaramai kwanciya Abie yay da kyar yaja bargo ya lullubeshi ya tofamai addu'a yajuyo ya kalli Mami dake share kwallan dake xubo mata, tasowa yayi ahankali yadawo bakin gadon kusada ita hanunshi yasa ya rungumota batare dayay magana ba, ahankali ta saukar da kanta kan kafadarshi wasu sababbin hawayen na gangaro mata kumatu tace "Abie why this? Why we? Why our Son? Shekaru talatin da biyu kenan muke fama, Abie please kafadamin what else dazanyi da yaronmu zai sami lafiya, banda burin daya wuce nabude idanuna naga Aadil kaman kowani namiji aduniyan nan, kaman dan uwanshi, Abieee" taja sunanshi cikin kuka, kiss yama forehead dinta yanadan shafa bayanta shima idanunshi sunyi ja, zaiyi magana wayarshi dake aljihun jallabiyar shi ta shiga ringing, riketa yay da hannu daya yasa hannunshi a aljihu ya