Showing 102001 words to 105000 words out of 164763 words
tunanin Hamida data dagulamai lissafi gabaki daya. Ko kadan baimaji shigowan Aabid ba saidai karan ajiye mug yaji akan table din gaban kujeran hakan yasa ya dago kai ya kalli Aabid din daya ijiye mug din yana nazarin shi, zama yayi kusada Aadil din yana mikamai wayar dayake hanunshi yace "are you sure you are okay Twin" gyadamai kai yayi ahankali batare daya iya furta wata kalma ba, dafamai kafada Aabid yayi yace "stop thinking about the past Aadil, karungumi kaddara duk yanda tazoma you have us and u have your beautiful wife, matarka yarinya ce tagari, kagode ma Allah kawai and move on okay we are all here to support you, this is a second chance Allah yabaka make use of it, ga wayanka nan Mami tabani nakawo ma" karban wayan yayi ya rungume a kirjinshi yana kallon Aabid din wasu siraran hawaye suka zubo ta gefen idanunshi da sauri Aabid yarikeshi cikeda damuwa sosai kaman zaiyi kuka yace "kaga tell me wats wrong with you, you are driving me crazy Dil, am so worried" girgiza mai kai Aadil yayi yace "i don't know Bid, bansan meke damuna ba, but deep down inaji ajikina kaman zan mutu anytime soon" chak Aabid ya tsaya yana kallonshi ko kyafta idanu bayayi maganganun shi ya mugun dakanmai zuciya bana wasaba, kallonshi Aadil yake ganin yanda yayi yasa yabude baki zaiyi magana asanyaye Aabid ya daura hanunshi kan bakin nashi yana kallonshi cikin daure fuska yace "are you mad eh Aadil?" yay maganan yana kaimai duka a kafada idanunshi natara hawaye, yace "are you mad eh? Mesa kakemin maganan mutuwa? And wayafadama yanzu zaka mutu Allah shine masanin gaibu, i just got you back karka karamin maganan mutuwan ka idan kasake bazan karama magana ba kaji ko" yay maganan hawaye na gangaromai daga ido gyadamai kai Aadil yayi yana kokarin tsayar da hawayen dake fitomai daga ido rungumeshi Aabid yayi yamai kiss a goshi yace "koma mekakeji u are not alone, we going to go through it together Aadil, kaine kadai dan uwan daya ragemin yanzu banson in rasaka" ahankali Aadil yace "me too Bid" "let's go out, zomuje muyi many many things outside and have fun zakaji dadin jikinka, tashi jeka shirya kazo" kallon fuskar Aabid din yayi ahankali yamika ma Aabid din hannu hakan yasa Aabid din yabi hanunshi da kallo kafin yasa nashi acikin hannun ya kalli Aadil din kaman yanda yake kallonshi, a natse Aadil din yace "meke damunka? Something has been bothering you i can feel it a zuciyata kana cikin matsala wat is it wat is the problem? Your problem is our problem ko Bid we are one, you've been thinking tun jiya banso kamin karya just tell me menene? Meke damunka?"
Girgizamai kai Aabid yayi yana danne zuciyarshi dankar ya fahimci komi game dashi, ahankali yace "bakomi kaina keta ciwo last night saisa nai wani iri" kafeshi da ido Aadil yayi dan bai yarda da maganan shi ba ko kadan hakanan zuciyarshi taki natsuwa taki aminta da maganganun, ganin yanda Aadil din ke kallonshi yasa yatashi da sauri yay bathroom yana tafiya ahankali yace "lemme shower kaje ka shirya kaima" yabude kofar bathroom din ya shiga yarufe, binshi da kallo Aadil yayi dan yanda yayi yanzu yakara tabbatar mai da wani abune ke damunshi ba ciwon kaiba da sauri yatashi sabida yanda yaji zuciyarshi taki natsuwa ya shiga duba dakin, pillows din gadon ya daddaga amma baiga komiba, side drawer ya bubbude nanma baiga komiba, wayar Aabid din daya gani akan gado ya dauka yana budewa yaga ba password hakan yasa ya shiga dube duben wayan amma baiga komiba harzai ajiye wayan yaga watsapp message ya shigo daga Dr Sham "get well soon" da sauri ya shiga watsapp din yabude Dr Sham din, maganan Aabid ya gani kafin reply din Dr Sham " _na am fine now Dr i took d drugs"_ da sauri ganin baida lafiya ne da gaske yasa yay scrolling sama dan yaga meke damunshi, idanunshi ne ya sauka akan maganan Dr yace _"you haven't told me the problem, Hussain u are too young to be suffering from heart disease!"_ wani irin faduwa gabanshi yayi ganin heart disease da sauri ya zauna kan gadon yana dafe kirjinshi dake bugamai way too fast, ya shiga reading chat din ahankali daya bayan daya.
_"i used to be a bad boy Dr, inabin mata, ina shan alcohol sometimes su kadaine abinda nakeyi idan rage tunanin dan uwana barin ma idan yana tsaka da ciwo, kullum kuka nake in rasa kwanciya hankali sainaje nasha giya sanan zan manta, my brother, my twin brother is not okay almost every every month saiya kwanta a asibiti, my brother is my life ina sonshi sama da komi aduniyan nan idan kacire iyayen mu, wata rana a Lagos nahadu da yarinyar da i fell for her at a glance, My Jewel! My Amatullah!"_ chak Aadil ya tsayar da karatun jin sunan Amatullah ahankali ya furta sunan Amatullah, dan yaji su Mum sun kira yarinyar nan na dazu Amatullah, cigaba da karatun yayi..
_"my Hamida!"_ tsayawa Aadil yay chak kanshi yawani irin sara yana ganin flash din fuskar Hamida a idanunshi tanamai murmushi tana kiranshi "My Aadil, stop crying to" dafe kanshi yayi ganin yasoma tuna da yacigaba da karanta message din da kyar.
_"I saved her lokacin datai drowning a ruwa, Dr Sham i love her, i just fell for her naturally, inasonta sosai with all the fiber in my body with all my soul, i love Hamida with all my mind, my heart and soul, and right then bayan nakaita asibiti i confess my love for her cus i understood she was d one for me, mine, dudda she was afraid of me i get to understand that she's a girl that hardly get comfortable around men lemme say mutane ma in general, bayan mun rabu, yan uwanta sunzo sun tafi da ita i was dreaming about her, babu randa zanyi barci na farka banyi mafarkin my Jewel ba, unfortunately my brother as well fell in love, he fell for her as well, funny right yanda twin brothers fell for mace daya, cikin ciwonshi bama tareda ya ganta ba tun amafarki yafara sonta"_ tsayar da karatun Aadil yayi kanshi na saramai komi na dawomai kadan kadan ya dafe kanshi dakemai zafi sosai kaman an kunna wuta.
_"maganan shi alokacin shine take me to she! She! Bid she! Ranan daya fara ganin Hamida was randa yafita shida Mami, dayaga Hamida saida yaja accident ahanya yafita yabita har gidansu har aka koresu ita da shi, atare mukazo muka gansu with the help of police dats d second time danake ganin Hamida, the way naga my brother hugged her touching her yana mata shagwaba playing with her saida yasa naji kaman an chakamin kibiya azuciyata, da kyar na iya na daure inata kallon Hamidan da at that instant nagane akwai strong connection and bond tsakanin ita da my twin dan she's always free with him, bazaka tabajin maganan Hamida ba sai tana tareda Aadil, her smile her teeth saitana tare da Aadil, bakajin maganan ta tana surutu saitana tare dashi, we took them both home kasan ranan danai worst mistake?"_ ya tambayi Dr yacigaba
_"ranan danaga yana kokarin sama Jewel chocolate abaki yana mata all sort of things tanamai murmushi tana lallashin shi sosai zuciyata tai baki i was madly jealous, i don't know Sanda nai raising hand dina on my brother inacemai yadena kiran Hamida his wife, banyi considering nashi ba banyi considering condition dinshiba namai duka sosai sabida kishi ina dukanshi yana kuka inajin zafin yanda nake dukanshi ajikina nima but i couldn't help it, ranan i cried my life out for beating him najamai ciwo har saida akai admitting nashi a hospital, daganan from how things were going saina fara lallaba kaina ina lallashin kaina inason Hamida but my brother needs her more har akazo akasa ranan lallaba kaina nakeyi battling with depression dan i was seriously depressed ni kaina bansan lokacin danai ma Hamida wanan strong so dinba, banfadan ma kowa halin danake cikiba ranan daurin aure kasa daurewa nayi nabar garin straight to wurinka a hospital a Lagos sabida ciwon danakeyi harkai admitting dina bayan naji sauki na koma gidana a VGC nakira Vanessa nafara all sort of things just to stop thinking about Hamida, my brother's happiness is everything to me Dr Sham, Hamida is blessing to his life saisa na daure, karka damu ciwo baya kisa saidai idan lokacin ne yayi i will be fine zan cigaba da shan magungunan daka rubutamin"_ yanda gaban Aadil ke bugawa kanshi na vibrating abin yadawo kaman ana tariyo mishi lokacin dayay haukan yana ganin komi daya faru yasa ya shiga dube duben dakin har ya jawo side drawer yaga wata yar box bude box din yayi nan yaga drugs din heart dayawa fashewa yayi da kuka sosai ya taushe baki komi nadawo mai yace "no no no, najama dan uwana ciwo" daidai lokacin Aabid yabude bayi yafito tsayawa yayi chak ganin Aadil idanunshi sunyi jajir yana rike da magungunan shi na ciwon zuciya yana kallonshi hawaye na zuba, da sauri yay wurin Aadil din yana rike da magungunan yanunamai magungunan cikin fushi yace "mesa kamin karya Bid why did you lie to me?" saukar da idanunshi Aabid yayi kasa yakasa magana chakumeshi Aadil yayi idanunshi sunyi jajir yace "you lie to me Bid, you are sick ka boyemin, you think i cannot take care of you? I can't give you wat you want and i will judge you ko? Aabid!" yakira sunanshi kaman zaiyi kuka hakan yasa Aabid ya dago kanshi ya kallai, ahankali Aadil yace "you love Hamida! Nasan komi, Kanason Hamida tun ranan daka fara ganinta, kanason Hamida sosai kazaci bazan iya barma Hamida ba? Now i remember everything, natuna komi, Aabid i remember yanda kake kula dani, I remember yanda kake rike dani kana tareda ni tun ranan da aka fara sakamu a nursery school a UK, i remember yanda kake kuka koda faduwa nayi akasa, i remember yanda idan banda lafiya bazaka ci abinci ba ni ciwo kaima ciwo sabida ni haryau kana suffering from ulcer, i remember yanda kake amfani da rigan jikinka ka sharemin miyau danake dilalar wa, i remember yanda nakeda saurin fushi i will not talk to you but u will stick around kanamin murmushi harsai nadawo normal, i remember yanda kake sona nida kai were inseparables, Hussain i remember each and every single memory of my past, duk abinda kakeso aduniyan nan sainama shi you are all i have, kaine jinina, kanina, dan uwana, abokina, abokina rayuwata and komi nawa, zan iya sadaukar ma da komi aduniyan nan, am leaving Hamida for you, zan saki Hamida!" yafada hawaye na rolling down his cheeks yana kallon Aabid din dake kallonshi.
Good morning readers, like i said ni makarantana nakema rubutu and am at your service after all you guys paid for it.
Please vote da Aabid da Aadil wanne yafi dacewa da Hamida, wanne kuke so? This book is love o, romantic love story, so feel free kufadamin, thank you.
Aadil ☑
Aabid ♾
Wanan page din harda na jibi nahada muku, jibi bazanyi typing ba, love you🥰 don't forget to vote and lemme hear reasons dinku.
[2/17, 2:37 PM] +2347066933957: ...
Ahankali take bude idanunta dasuka mata nauyi sosai jikinta ko kadan ba karfi gabobin jikinta sun mata tsami sosai, bude idanun tayi gabaki daya ta daura shanyayyun idanunta akan makeken agogon bangon, tana fitar da numfashi ahankali ahankali da baki bata feeling jikinta ko kadan, motsin da kunnuwanta sukaji yasa tajuyo da kanta ahankali, sauka idanunta sukayi akan fuskar Aadil dake kwance agadon dake dayan bangaren dakin akwai dan gab a tsakanin su, motsi yake sosai batare daya bude idoba sai motsi dayakeyi idanunshi na rawa suna shirin su bude, lumshe idanunta tayi asanyaye takara budesu ahankali tasauke su akan fuskarshi, wani irin sanyi taji ajikinta bana wasaba, ahankali ta matsar da hanunta da kyar zuwa baki bakin gadon datake kai tai pointing Aadil din da hanunta tana lumshe ido batare datai koda kwakkwaran motsi ba, bude ido Aadil yayi gabaki daya yana kallon dakin yanabin ko ina da kallo, yakai kusan minti biyar ahaka kaman mai nazarin wani abu kafin ahankali yatashi ya zauna yana kallon drip din da ake karamai yadan yatsine fuska sabida ciwo da jikinshi kemai sosai yana shafa hanun nashi dan wurin karin ruwan namai zafi sosai, lumshe ido tasakeyi ahankali tanajin wani irin murna har cikin ranta ganinshi atare da ita dat means he's fine bai mutu ya barta ba, bude bakinta dayamata nauyi sosai tayi zatai magana wani atishawa mai karfi yazo mata tayi, da sauri ya waigo ya kalli bayanshi jin karan atishawa tsayawa yayi chak batare dayace komiba yakafeta da ido, wata yarinya yagani fara sosai kan gadon, tana sanye da wani pink rigan asibitin akwai bandeji biyu a jaws dinta tana kwance gashin kanta ya barbarzu kaman na yar buzuwa ta kafeshi da ido kaman mayyar dataga yaron dazata lashe, murmushi tasankin mai daya bayyanar da cute dimples dinta ganin ya ganta yajuyo yana kallonta, yatsine fuska yayi akasalance ya dauke kai ganin yarinyar tanamai murmushi tana wani irin kallonshi kaman zata hadiyeshi daidai lokacin aka bude kofar dakin za'a shigo, atare dukansu sukabi kofar da kallo, Big Mum ce ta shigo dakin tareda Baba Suleman suna hira batare da sunma lura dasuba. "eh saida na tabbatar tasha maganin Yaya sanan nafito, saida nahada da yimata alkawari zan kirata a video call taga fuskokin su sanan ta yard...." shiru tayi batare data karasa maganan ba ganin Aadil zaune abakin gado ya kafesu da ido yana kallonsu, dukansu kamewa sukayi tsaye suna kallon Aadil din daya kafesu da ido bayako kyaftawa, da wani irin sauri Big Mum tai wurin gadon ta zauna kusa dashi cikin murna tadaura hanunta akan fuskarshi tana shafawa tace "Aadil, Boy katashi, yaushe katashi ya jikin?" hanunshi ya daura akan nata dake kan fuskarshi yadan lumshe ido ya bude ahankali kafin cikin wani cool calm voice yace "Big Mum ina Mami na? Ina Bid?" chak daga Big Mum har Baba Suleman suka tsaya suna kallonshi ganin for the first time in life sunga Aadil yay magana batareda kanshi yay rawa ba batare da miyau ya zuba daga bakinshi ba and magana ba childish magana daya sabayi ba yana turo baki a shagwabe yana fari da ido yana lankwasa kai yana make kafada, tashi Big Mum tayi tafada kasa cikin so much happiness tai sujjada kafin ta tashi tafashe da kuka sosai tana kallon Aadil din dake binta da kallo, kawai takasa holding tears nata back ne, sake zama tayi ta matso kusada Aadil din sosai taima fuskarshi kyakkyawar cupping tace "Aadil, Aadil am I dreaming kaine Aadil, Aadil u are fine kaji sauki wayyo Allah na Yaya am so happy today, kalli Aadil dinmu fa, Alhamdulillah, ya rabb i can't wait to tell kanwata this good news dasu Baffa" tai maganan tana wani irin rungume Aadil dayay shiru yana kallonta kaman mai tunani yanason gano wani abu, karasowa cikin dakin Baba Suleman yayi ya zauna adayan gefen side din Aadil din yana kallon Aadil din today is such a good day hanun Aadil din yakama yarike, hakan yasa Big Mum tace "kagane shi Aadil?" juyodakai yayi ya saukar da manyan eyes dinshi akan fuskar Baba Suleman din ya kafeshi da manyan milky eyes dinshi yana kallo ahankali yace "Uncle" wani irin ihun dadi Big Mum tasakeyi tana goge hawayen datakeyi nonstop tana kokarin ciro wayarta daga jaka da sauri Baba Suleman ya fizge wayan yace "babu wanda zaki fadamawa saidai su ganmu mun da Aadil din kawai, lemme go an call Dr yazo yaduba shi" tashi yayi daga kan gadon daidai zai juya yay wurin kofa idanunshi suka sauka akan Hamida dayagani idanunta biyu tana kallonsu hawaye nafita daga gefen idanunta tana kallonsu da sauri Baba Suleman yace "H...Hamida" yay maganan yana karasawa wurin gadon cikin tsananin farin ciki da sauri Big Mum ta mike tsaye jin sunan da Baba Suleman yakira, karawasa gaban gadon Baba Suleman yayi ya tsaya yana kallon Hamidan ahankali yace "Hamida kin farka?" kafin ma tabada amsa big mum takaraso wajen tana Share kwalla tace "daughter na, Hamida na kintashi" da kyar Hamida ta iya ta gyadamata kai sabida bones dinta dake mata ciwo sosai daidai lokacin Aadil yamike tsaye ahankali yana yatsine fuska ya cizge karin ruwan dake hanunshi ya yar, singlet da 3quater dayagani kan gadon ya dauka yadaga kafa ahankali yay hanyar kofar dakin dayagani wanda ya kyautata zaton na bathroom ne, yanda Hamida tabishi da kallo batare databa Big Mum amsar tambayanta ba yasa Big Mum da Baba Suleman suka juya atare dan suga metake kallo haka, ganin Aadil ne yatashi yana tafiya yabude bathroom ya shiga yasa big Mum tace "Yaya akira mana Dr yakamata yasan sun farka beside Hamida doesn't look good, meke miki ciwo daughter?" fita Baba Suleman yayi dan zuwa kiran Dr, ahankali batare datai magana ba Hamida ta nuna mata fuskarta da jaws dinta alamun su kemata ciwo, a forehead big Mum tamata peck cikin tsananin son yarinyar tace "don't worry zakiji sauki kinji, Maman ki kullum saita kira taji yaya jikin ki, i know she will be very happy idan taji kin farka" shigowa Baba Suleman yayi tareda Dr da nurses guda biyu, kana ganin su kaga larabawa, da farin ciki gabaki dayansu suka shigo suna tambayan ina Aadil Baba Suleman yace "ya shiga bathroom wanka" Dr ya shiga duba Hamida daidai lokacin Aadil yafito daga bathroom din sanye da white single da 3quater ajikinshi yana tafiya ahankali, tafi duka Dr da nurses din suka fara suna kallonshi suna murna ganin patient dinsu yatashi strong and healthy, dan kallonsu yayi kafin ya dauke kai yakarasa yazauna akan wani plastic chair dan yagaji da kwanciya Hamida tabishi da kallo, so kawai take yamata magana koma ya kalleta amma yaki, saida aka gama dubata sanan Dr yaduba shi, babu wata matsala tattare da shi sai rashin kuzari wanda