Showing 45001 words to 48000 words out of 164763 words
da ita Aabid yama dukan nan dayafi mata sau dubu akan Aadil mara lafiya wanda baimasan zafin kanshi ba, yaron da kullun suna hanyar asibiti dashine yama wanan dukan rashin imanin, share mata hawayen daya kasa daina zuba Abie yayi tsabagen bakin ciki da kuncin datakeji, kana Abie shima kasan ranshi abace yake, janye hanunshi yayi daga fuskar Mami bayan yagama share mata hawayen yace "is okay, barshi" ya dago kai yama Aabid din wani irin mugun kallo yace "wuce katafi abunka" kasa daga kafa Aabid yayi yafita daga dakin ko motsi yakasa saima kanshi dayakai kasa, cikin wani irin ihu Mami taja belt dinshi dake gefenta ta wurgamai belt din yafada kanshi tace "ance ka wuce kafita daga dakin nan, kozaka hada damune kadaka eh zalim?" dan dago kai yayi ya kalli Mami zuciyarshi namai wani iri da sauri yajuya yafita daga dakin kaman zai tashi sama yay tsakar gida ya shiga mota yaja motar yabar gidan da shegen gudu.
Ahankali tafito daga bayan verse din tana kuka sosai ta tsaya abakin kofan so kawai take taga Aadil din da zuciyarta ke mugun kwadayin ganinshi.
Gogemishi jinin gefen bakin Abie yayi yadan bude ido kadan yana kuka ahankali ya rirrike Mami, kiss Mami tamai a goshi jin yanda jikinshi yadau wani irin zafi sosai kaman an sakashi a oven, tsugunnawa Baffa yayi shima yana kallonshi yamika mai hannu alamun yazo kaman yanda akema yaro yana kallonshi, ahankali Mami tadaga kanshi daga jikinta tace "zakaje wajen grandfather, oya go" wasu irin hawaye ne suka bulbulo ta gefen idanunshi yana wani irin nishin kuka da karfi kaman mai asma dan abun nawani irin sosa mai rai, cikin muryan kuka sosai yace "Bid beat me Mami" yay maganan wasu sababbin ruwan hawaye na zubomai daga ido, dasauri Mami tawani irin rungumeshi tsam tsam tana jijjigashi sosai Aadil weak point dinta ne sosai, batason abunda zai taba innocent boy dinan, tunda tahaifi Aabid baitaba bata mata raiba irin nayau, sosai take jijjiga kanshi a kirjinta tana bubbuga bayanshi jin yanda yake wani irin kuka tace "is okay, ya isa kaji, mekamai yadake ka? Karka sake kashi" cikin kuka sosai yanayi kaman zai suma yace "Bid hate me Mami" da sauri Mami ta girgiza maikai tana neman yin kuka dan daurewa kawai take tasa hannun riganta ta sharemai fuska tace "no, no no, dont say that, Aabid bai tsanake ba, yana sonka sosai ko Baba" ta tambayi Baffa dake kallon Aadil din, gyadamata kai Baffa yayi yace "Aabid na sonka sosai kaji dan kirki" girgiza musu kai yayi zaiyi magana saikuma yafashe da kuka sosai tafada jikin Mami, tashi Baffa yayi da sauri dan wani irin zafin dukan da Aabid yamai yakeji yajuya yay hanyar kofa yana dogara sandarshi, ko kadan bataji alamun tafiyan mutum ba sabida kukan datake sosai tana sharewa da bayan hannu, yanda Aadil keta maganganu yanatasa zuciyarta nawani irin karaya jitake kaman ta daukemai ciwon dukan, bude kofan Baffa yayi arude tai baya tana kuka sosai ta saukar da kanta kasa tana kokarin tsayar da kukan datake data kasa, binta da kallon mamaki Baffa yayi wearing a smile akan fuskarshi kafin ahankali yace "bakuwa kin tashi ya karfin jikin?" gyadamai kai tayi tadan dago kanta ta leka Aadil ta gefen Baffa dake tsaya abakin kofan, hangoshi tayi jikin Mami dake kallonta asanyaye da Abie daidai lokacin Aadil din yabude idanunshi dake buduwa da kyar sun kumbura sunyi jajir ya kalleta innocently, lumshe ido yayi ya budesu ya miko mata hannu daga inda yake da kyar tsabagen zazzabin dake cinshi, dawata irin murya dabata da kara sosai yakira sunanta yana mika mata hannu yace "My H..Hamida" fashewa tai da kuka sosai tana share idanunta da bayan hannu tana kallonshi yanda taga fuskarshi ya kumbura da lips, takasa koda motsi daga inda take ta daura hannayenta akan bakinta tana kuka, wani irin tausayin shi takeji bana wasaba, sosai Baffa ke kallonta yana karanta wasu abubuwa tattare da ita kafin ahankali ya juyar da kanshi ya kalli Aadil din dake kuka ahankali yana kiran sunanta agalabaice yana mika mata hannu yana lumlumshe ido kaman mai shirin yin bacci, ahankali Baffa yasake juyowa ya kalleta yace "ki shiga ciki mana yarinya kin tsaya anan" gyadamai kai tayi tana share hawayen datakey, Mami ma murmushi tayi tana kallonta tama kasa magana, ahankali tafara tafiya Baffa ya matsa mata ta shigo dakin Abie yay shiru yana kallonta harta karaso tsakiyan dakin ta tsugunna ata gefe tana kallon Aadil din tana kuka, wani irin tashi Aadil din yayi daga jikin Mami ya rarrafo da kyar yakaraso inda take ya tsaya gab da ita yana kallonta, fashewa tai da kuka sosai tana kallon fuskanshi, fadawa yayi jikinta yasaki kuka sosai itama kuka tasaki tana girgiza mai kai, ahankali ta ciro kanshi daga jikinta tai cupping face dinshi tana kallonshi, lumshe mata ido yayi hawaye suka zubo, murya chan kasa ta kuka yace "Bid beat me" yasake sakin mata wani kukan, girgiza mai kai tayi takai hanunta ahankali ta sharemai hawayen dake zubowa tace "stop crying okay" make mata kafada yayi yawani narke mata hakanan yaji yanajin wani iri farinciki sosai, ahankali tana kuka sosai dan kawai tasashi murna tace "where is my chocolate?" ware manyan kumburarrun idanunshi yayi yace "i don't know, I've lost it wen Bid was beating me" gabaki daya tama manta dasu Mami na wurin burinta kawai yay shiru yadena kuka yadawo normal Aadil daya iya damunta, hararanshi tayi ta murguda mai baki tace "find it" wani irin bude ido da baki yayi yana kallonta saikuma ya leka nose dinta kaman ba shine yaci duka yanzun nanba yace "ur nose is a robotic nose" murmushi tayi sosai daya bayyana dimple dinta da sauri ya daura hanunshi kan hancinta yaja yana dariya yace "do it again, saikin kara yimin" dariya tayi ta fizge hancinta shima yay dariyan yana clapping hands dinshi, Mami, Abie da Baffa duk sukai shiru suna kallonsu kowa da abinda yake kawowa aranshi daidai lokacin Suleman yazo wajen, hanunshi Baffa yaja batare daya bari ya shiga dakin ba suka bar wajen yace "Baba har yarinyar ta tashi ne" gyadamai kai Baffa yayi suka karasa falon Baffan, zama Baffa yayi akan kujeran zaman yi yay dan shiru nayan sakanni, shiru Suleman yayi dan yasan inhar Baba na tunani bayason anamai magana, dan ajiyan zuciya ya sauke ya kalli Suleman yace "Sulemanu" da sauri yace "na'am Baba" gyara zaman shi yayi yace "inaso kamin binciken yarinyar nan, wanan bakuwan data taimaki Aadil, inaso nasan wacece ita, sanan inaso nasan iyayenta dakomi nata daga nan zuwa gobe" gyadamai kai Suleman yayi yace "shikenan Baba angama, amma Baba mezakayi da information dinta haka?" shiru yayi saikuma yay murmushi yace "time will tell, kaidai kamin abinda nace".
_🌹IN BANI 🌹_
Maman Abd Shakur
26....
Agaban wani babban club Aabid yay parking yabude mota yafito kanshi harwani irin zafi yakemai kaman zai tarwatse tsabagen bacin ran dayake ciki ya juya ya shiga ciki, gaban counter yaje ya zauna ya kalli waiter dake aiki a wurin yana kokarin serving wasu samari dake kallonshi yace "meza akawo ma Sir?" dan bude ido yayi kadan ya kalleshi kafin ahankali yace "rum" da sauri guy din yadauko wani kwalba yabude yazuba awani dan karamin kofi zai mikomai, hararanshi Aabid yayi da jajayen idanunshi kaman wuta yace "give me the whole bottle" mikamai bottle din yayi ya fizge da sauri ya kafa abaki ya kurba yana yatsine fuska yacigaba dasha saida yay kusan rabin goran sanan ya janye daga bakinshi yana zaro manya manyan idanunshi kanshi kaman zai fashe tsabagen chajin daya dauka, da kyar yay relaxing bayanshi ajikin kujeran ya lumshe ido yakafa goran rum din abaki yana tunane tunane.
_Asalin su_
Alhaji Muhammadu Gambo Sawaba (Baffa) shararren business man ne mai kirki bana wasaba, ga taimakon mutane, talaka, marayu da mabukata, babu inda zaka shiga afadin garin kano ka ambaci sunanshi daba'a sanshi ba, matanshi biyu a duniya Rukayya da Maimuna, Rukayya itace ta haifi yaranshi maza guda uku, sai Maimuna wacce itace ta haifi Mami da Big Mum, yarane dasuka taso cikin gata da kulawa kome sukeso shi mahaifinsu ke musu kansu ahade. Kullum akwai direban dake kaisu school yaje yadauko su, lokacin islamiyya ma yakaisu yadauko su.
Kafin mahaifiyarshi ta rasu, akwai lokaci ta tattaro yinata yinata ta dawo birni gidanshi da zama tareda wani marayan yaron makwabcinta a kauye mai suna Abdullahi (Abie), Abdallahi yarone mai natsuwa da hankali wanda akalla zai girmi babban dan Baffa Suleman da shekara daya ko biyu. Tunda tadawo gidan da zama da Abdullahi ta damkama Baffa shi tacemai tanaso yarikeshi amatsayin danshi, gashinan amana, iyayen shi sun rasu, karya bambamtashi dasu Sulemanu, tabashi shine sabida koda tafadi ta mutu tasan yana hanunshi da zama, Baffa baimata musu ko jayayya ba ya karbi yaron dan yaron badai natsuwaba, nan Suleman da Abdullahi suka shaku suka zama abokan juna suna zuwa makaranta tare both boko da islamiyya dudda sun fishi aji.
Bayan wasu yan shekaru sun gama makaranta alokacin Baffa kuma yanso yay retire saiya daura Suleman baban daddanshi shugaban kampanin shi duka ukun, yasa sauran yaranshi maza biyu da Abdullahi duk a kampanin yabasu office suna aiki ana biyan su duk karshen wata makudan kudi, abin bakaramin ciwo yama Abdullahi ba yaso ace shine zai Baffa yabama shugaban kampanin dan yafi Suleman kai a business, banda haka yanada mugun sha'awan yaganshi yazama shugaban kampani, hakanan ya tattara ya watsar da zancen amma abin na nan ranshi ras duk idan yatuna har kuka yakeyi a boye yace wato sabida shi ba danshi bane saisa baibashi shugaban kampanin shiba ko bakomi shima zaiyi kudi wataran, ana haka wani irin soyayya ya kullu tsakanin Abdullahi da Mami bana wasaba, Allah ya dauramai wani irin soyayyan Mami bana wasaba.
Akwai ranan da Baffa yay order wasu hadaddun motoci toyota camry alokacin ana yayyin su yabama duka yaran nashi daidai as end of the year prayer gift amma banda Abdullahi yacemai shi tashi bata isoba, kuma harga Allah bata iso bane dan Baffa yaso yay surprising dinshi ne yatabaji yana hira da Suleman yacema Suleman shi yanason babban mota arayuwan shi jeep na burgeshi hakan yasa Baffa yaso yay surprising nashi kodan jarumtar shi a kampani yabashi shi jeep amma sai tashi bata isoba dan ba'a gama yima motar custom duty ba harsai next week, nan fa bayan komi yadan lafa Abdallahi yasaci hanya yafita daga gidan yatafi kampanin su yadinga kuka yanajin bakin ciki sosai yana zagin rashin kudi da zama a karkashin wasu, dafashi yaji anyi da sauri yadago kanshi wani inyamurin gateman dinsu ne yagani yana sanye da hadadden suit baki, murmushi yamai yace "kasoma gane basu sonka ko Sir? Kawai amfani suke da talent dinka suna making money a kampanin nan" da sauri ya kalleshi yace "ya akayi ka sani?" murmushi yayi ya kalli ko ina na wurin kafin yaciro wata yar Kati daga aljihun wandonshi ya mikamai yace "inhar kanaso yau yau dinan rayuwarka ta chanza from this poor man dakekeci a gindin wasu kana musu boyi boyi kaima kai kudin bala'i, kudin da sunema zasu rokeka, inhar kanason money and fame, kanason dukiya, kanaso kafada aji kahana ahanu, kanaso kadawo yaro mai gari a hannu to ka kira number nan da kagani ajikin katin nan, Ozo zai biyama bukataun ka, zakai kudin ban mamaki, kudin dasu kansu saisun koma suna rokon ka kudi.
_Manage this guys, nai typing duka ya goge, da kyar na iya nai wanan yanzun nan, gobe kuna bina bashin daya in sha Allah_.
_🌹IN BANI 🌹_
Maman Abd Shakur
27....
_Cigaban labari_
Baki yasaki yana kallon gateman cikeda mamaki yama kasa cewa uppan, murmushi gateman yayi yace "kaga tafiyata dama resignation letter na nazo nabasu kai baka ganni ba level don change, nima wani yamin hanya wanan harkan, dazaran ka shirya kaima kawai kiran number kadai zakayi, nina gayama har gidana zakazo kamin godiya sabida gatan danama, sai anjima" yawuce yay gaba yana wani irin tafiya irin na masu kudi dinan Abie yabishi da kallo kasa tashi yay daga wurin sai kallon katin yake yana jujjuyawa har aka kira sallan magrib yatashi yaje yayi yajira har akai isha'i yayi daganan yakoma gida ranan kasa baccin dare yayi sai tunane tunane yakeyi yakira ko kar yakira, shidai harga Allah yanason yyi kudin nan kodan yanuna Baffa baidamu da kudin suba hasalima saidai su sudinga begging nashi, har gari yawaye yatafi masallaci baibar tunane tunane va, arana na uku ne ya yanke shawara zai kiradai kodan yaga me gateman kecewa idan ma karyane yagano, Motar gida daya sabaja yadauka yafita daga gidan ya gangara chan wajen gari yay parking motarshi ya kashe sanan yaciro wayarshi yadau katin ya kwafe number jiki yay dailing number, ringing daya wayan yayi kawai saiyaga wani irin duhu a idanunshi daganan kuma bai karasanin inda kanshi yakeba yadai farka yaganshi a wani jan daki yana sanye da jan riga akwance akasa, saiga wasu mutane sun zagayeshi daga cikinsu harda gateman suna rike da jajayen candle dake ci da wuta suna wasu irin wake wake suna zagayeshi, kasa koda motsin kirki yayi tsabagen yanda jikinshi yahau rawa yamugun tsorata kaman daga sama yaji ankira sunanshi. "Abdullahi yakira Ozo, Ozo ya amsa mishi saki jikinka kafada ma Ozo mekake so" tashi yayi zaune daga kwanciyan ya kankame jikinshi ko ina na jikinshi narawa sosai yama kasa daga kai ya kalli kowa hanunshi nawani irin rawa jikinshi na kakkaurwa yace "dan Allah kuyakuri dama inaso nayi kudine amma yanzu nafasa, banison kudin tsafi dan Allah kumaidani gida" wani irin dariya akayi kaman zai fasa dakin saikuma akai wani irin nishi kaman na zaki. "ba'a kira mana Allah anan ka kiyaye, dazaran mutum yakirani babu gudu babu komawa baya ka shiga ka shiga ne baka isa kafita ba, inda kasan bakaso da tun aranan ka yarda katin baka kiramu ba" hanunshi yakai baki jikinshi narawa sosai yace "natuba, natuba, ayakuri, amin afuwa, wlh banison kudin tsafi" wani irin dariya akayi dake kama da tsawa akace "nine Ozo duk wanda yakira ni yanemi sanan yace yafasa to motar nan dakasan ka kirani aciki, anan yan uwanka suzo su dauki gawanka tsotse jinin ka zamuyi tsaf dama ga jininka nan mai karni ne jinin virgin, daman irin wanda nake nema kenan jinin musulmi virgin" abun dayaji yana zuba daga ka sanshi yasa yabude ido da kyau yaga ashe fitsari yake, "Abdullahi" a firgice yadago kanshi yace "na...na'am" dawata irin murya kaman nayar jaririya yaji ance "step forward" gabaki daya organ din jikinshi karkadawa suke yay nadaman dailing number dayayi ahankali yamike tsaye kafarshi bankarewa sukeyi tsabagen tsoron dayake ciki yana tafiya kaman wani kwashoko yay gaban dakin yakasa daga kanshi haryakai gaban dakin da candles kenan dayawa da gumaka kanshi akasa. "ka daga kanka" yaji anfadi cikin wani irin kakkausar murya da sauri yadaga kanshi wani kwarangwal yagani agabanshi yamikomai wata yar karaman kwarya da abu keciki ja kaman jini, ihu yayi zaikoma baya yaji kafafunshi sunkasa motsi kaman yataka gum, yafashe da kuka cikin wata irin murya mai echo yaji ance "karba kasha" kasa mika hanunshi yayi tsabagen tsoron kwarangwal din mai jajayen idanu, hanunshi yaji ana kaiwa saitin karyan yadaiga ya karbi kwaryan amma baisan tayaya ba yadaiga hanunshi ya amshi kwaryan yakai bakinshi wani irin yatsine fuska yayi yanajin wani iri amai natasomai haka yaga abun kaman ana controlling dinshi yabude baki da kyar yafara shan jinin hawaye nafita daga idanunshi, ahaka ya shanye na kwaryan tass, wani irin sanyi yaji cikin jikinshi tundaga yatsarshi har cikin kwakwalwanshi kafin idanunshi suyi wani irin ja yazaro su saikuma sukadawo farare, dariya dakin yadauka sauran mutanen sukace "welcome to the family, money and fame duka nakane ayanzu" shiru sukayi sabida wani hadadden zobe da kwarangwal din yadauko yakawo saitin hanunshi, ahankali yamikamai hanunshi yanajin wani irin farin ciki yasakamai ring din jikinshi yay wani irin kara saikuma yadawo daidai, daga sama yaji magana. "welcome to the family Tursoso, kudi saidai idan kaine kace sun isheka, Ga zoban kanan koda yaushe ka bukata zai maka aman kudi, wanan cult din mai adalci ne babu bukatan wani abu babba kuma bamu tsanan tawa kasani cewa duk randa ka haifi d'a namiji, danka nafarko namune, namune, namune " nan yace ya yarda haka yakoma gida ya shiga dakinshi ya kulle ya xauna akan gado yanaso ya gwada ya kalli zoben yatsar tashi yace" kudi", ko gama ambata baiyiba zoben yafaramai aman kudi dahar saida yaji tsoro ya tsugunna yana tumurmusan kudin yana ihu yana murna yana mamaki yanzu wanan duka kudin shine, nan ya tatatra kudin yazuba a ghana masgo kusan biyu ya cika yafara tunanin karyan dazai shigo yafadi cewa ya sami wani aiki ne, wani paper ne yaga an wurgo akanshi da sauri ya chabe yaga job offer letter ne nawani kampanin sport cars ihu yay najin dadi yace thank you Ozo the great one, washe gari ya nunama Baffa sosai duka yan gidan sukaji dadi nan Baffa yace tunda hakanr za'aska ranan bikin shi da Mami kafin yatafi haka aka saka wata biyu yatafi UK abinshi yana fanchakala da kudi yabude wani durmemen kampanin motoci inda har kira motoci akeyi aikuwa fame yasamu dan kusan kowa na UK din saida ya sanshi lokacin bikin shi yakoma ya auro Mami yadawo suna zama na soyayya dan sosai Yakesan Mami yanadai ta addu'a kartasami ciki, bayan shekara daya.
Kwatsam Mami tasami ciki sosai cikin ke bata wahala bana wasaba haka suka cigaba da rainon cikin, cikin nawani irin girma, ko kadan baida kwanciyan hankali dan tun kafin yaga mezata haifamai Allah ya dauramai son cikin bana wasaba sai fargaba yake har bayason ranan haihuwan tazo haka wani Friday night Mami ta tashi da serious nakuda ya kwashe ta sai wani babban asibiti, takai kusan awa biyar da kyar ta sullubo yaranta maza, biyu Hassan akafara shiryawa aka fitomai dashi nannade a towel sosai gabanshi yawani irin fadi yana addu'a Allah yasa mace ce banamiji ba, karban yaron yayi ahankali jikinshi a mugun sanyaye ya kalli yaron ganin namiji ne, yaron gwanin kyau jajur dashi bulbul ahankali ya sumbaci