Showing 39001 words to 42000 words out of 164763 words

Chapter 14 - IN BANI BOOK COMPLETE BY M SHAKUR.txt

M.Shakur   

26 Oct 2024

25012

yace "i love you Hamida, and we will marry just like Mami and Abie right?" shiru tayi takasa magana jikinta yay wani irin shegen sanyi tundaga yatsar kafarta, lumshe ido yayi yasake budesu ya kalleta araunane kafin yasakin mata wani irin kuka, ta tsani taga yana mata kuka, sosai kukan shi ketaba mata rai, da sauri ta gyadamai kai tace "yes" wani irin ware mata manyan eyes dinshi yayi yace "yes Hamida my wife, she will marry me like Abie and Mami na yay" yay maganan yana mata fari da ido yana juyawa, tsayawa tayi tana kallonshi sosai taji tana wani irin tausayin shi to wai mutunmin dayake da lafiyan shi meya dawo dashi hakane? Meya maidashi haka? Hanunta taji ya fizgo yace "lets go, bazamu koma dat mugu house bako" ahankali ta karbe hanunta daga rikon dayamata suka cigaba da tafiya, batamasan inda zasuba gashi ko naira daya batadashi tafiya kawai suke yana mata surutu yana kirga hanunshi yana nuna mata yana murmushi, sosai yake wani irin farin ciki yana murna sabida tacemai yes sai tsalle tsalle yake akan hanya yana kallon fuskarta, duk in sukazo wuce bishiyan fulawa saiya katso yabata, karba kawai take tana murmushi amma matsalan datake ciki yawuce tunaninshi.




Gidan data boye jiya sukaje, atare suka shiga yana tsalle tsalle, pure water data gani awurin tadauka da sauri ta bude tai alwala, Aadil dake tsalle tsalle shima yazo da sauri ya tsugunna yana kallonta sai leken fuskarta yake, turo mata baki yayi yace "me too zanyi alwalan" zaro ido tayi ganin saura dan kadan ruwan, mikamishi tayi da sauri ya karba yana murmushi yace "thank you my wife" yafada yana nuna kanshi yana wani irin fikifiki da idanunshi dimples dinshi na lotsawa, tashi tayi da sauri batason tana kallonshi inyana mata irin abubuwan nan dan wlh wani irin kyau da kwarjini yake mata bana wasaba, karasawa dan filin dakin tayi ta gyara kasan wajen da hanunta sanan ta yafa dan kwalin kanta da kyau ajikinta ta kabbarta salla sai alokacin taji zuciyarta yarage mata nauyin dayake mata na kunci da azaba sosai, yay wani fayau kaman an kawad da damuwanta, salla tayi tai addu'a Allah ya bayyanar da yanuwanshi burinta kawai bai wuce yaga yan uwanshi yatafi gidaba ita saita tafi gidan Anty Lami yayar Mama, zuwa yayi shima ya tsaya a gefen ta yafara sallan murmushi kawai tayi tacigaba da addu'oin datakeyi.


Jinginar da bayanta tayi da bango ta daura kanta akan guiwowinta tai shiru idanunta sun cika da kwalla sosai, alamun mutun dataji akanta yasa tabude ido ahankali, hada ido tayi da Aadil daya leko da kanshi yana wani irin kallonta, ganin yanda hawaye yacika idanunta yasa duk yabi ya damu, zama yay a gefenta ya daura hanunshi akan kadadarta yawani irin dago kanta daga jikin kafafunta da karfi, kallonshi tayi shima kallonta yake ya daure fuska sosai, akumbure yace "why do you want to cry?" dan lumshe ido tayi da sauri tana kokarin ture hanunshi daga kafadarta takasa sabida yanda yarike ta gam, jiyayi kanshi yadau zafi da sauri ya fada jikinta yakai fuskarshi saitin nata, arude tabude idanunta dake gab da zubar da kwalla tace "Aadil kadena stop, kasakeni" makemata kafada yayi yakai hanunshi ya daura akan saman idanunta yana leka idanun kaman maison gano wani abu, murya chan kasa yace "you want to cry" girgiza mai kai tayi zuciyarta namata rawa sosa tace "n...no Aadil am not cr..crying, kaga....ni" saikuma tasaki kukan da karfi sosai sabida yanda zuciyarta kemata zafi, bamatasan tasaki kukan ba kawai kukan ne yazo uncontrollably, Kaka ta koreta daga gida batada gida ina zata, rudewa Aadil yayi sosai dan yatsani yaga ana kuka barinma na Hamida dayakeji har kasan zuciyan shi, wani irin rungume yayi yasata ajikinshi yana jijigata muryanshi shima narawa sosai yace "d...on't cry, i will call police for them, they will arrest them, they beat you and injury you i will go with police and beat all of them, stop crying Hamida" yanda yake maganganu dabama ta ganewa dan dukya rude muryanshi narawa sosai yana breaking kaman shima yana shirin kukan yasa tai shiru tana tureshi tana kokarin tashi daga jikinshi, make mata kafada yayi yana kallon idanunta dasukai jajir sun kumbura sosai, hanunshi dake rawa sosai yakai kan fuskarta yay cupping face dinta yana share mata hawayen dake kan fuskar yana yana turo baki kaman zai fashe da kuka yace "i will beat them for beating you, stop crying, don't cry again kinji" gyadamai kai tayi ta hadiye duka kukan datakeji tamai murmushi tace "am fine" ahankali yana kallon idanunta batare dayasaki fuskarta ba yace "are you sure?" gyadamai kai tayi tama kasa magana kirjinta na bugawa sabida wani irin kallo dayake mata daya bambanta dana koda yaushe da sauri ta runtse idanunta gam tafara kokarin fita daga jikinshi, make mata kafada yayi yasata a kirjinshi ya kankameta yay shiru kirjinshi nawani irin bugawa, shikanshi baisan meyakejiba kawai yanaso yacire mata damuwan datake cikine, ganin ko motsin kirki takasa yasa dan bebata daman ba yasa tai shiru gabanta na faduwa tana sauraron yanda jikinshi kewani irin daukan zafi heart dinshi na beating da karfi and fast fast...






***
"Mami, Mami na" da kyar ta iya bude idanunta dasuka mata nauyi sosai tsabagen kukan datake sha ta kalli Aabid daya rame shima duk yay wani iri hanunshi rike da mug din hot tea yana kallon mahaifiyar nashi dake kwance kan gado ta lulluba da bargo, kaman zaiyi kuka yace "Mami please tashi kisha tea kinji Mami na, please sweet Mum" girgiza mai kai tayi muryanta narawa sosai tace "bazan iya shaba, bansan ina Aadil dina yakeba, bansan ko yasamu abinci yaci ba, am sure my baby is hungry yanzu haka, bansan wani hali Aadil dina yakeba, tayaya zan iyacin abinci bansan wani hali my poor innocent boy yake cikiba" hanunta Aabid yakamo yarike zaiyi magana Baffa da shigowan shi dakin kenan kusan shi yamafi kowa damuwa ya nunata da Sanda cike da masifa yace "tashi ki karbi shayin nan kisha, kashe kanki zakiyi tunda yaro yabata babu abinda kika sama bakin salati, tashi ki karbi shayin nan kisha Maryama kona mugun saba miki wlh" cikin kwantar da murya Suleman yace "ya isa Baba muje kahuta kaima bakajin dadin, yanzu nida Abdullahi zamu koma police station din da Hussain" wayar Aabid ne yay ringing da sauri yaciro wayar daga aljihu ya kalli screen din, da sauri yadaga kai ya kalli Abie dake kusa dasu Baffa yace "Inspecta ne" da sauri Mami ta yunkura ta tashi zaune tanajin wani irin masifaffen ciwon kai tace "dauka hala anga Aadil dina ne" da sauri yay picking call din yakai wayar kunenshi daga tachan bangaren inspecta yace "yallabai..." da sauri Mami da jikinta har bari yake tace "sa, saka a speaker Son" zare wayan yayi daga kunenshi yasa a speaker yace "i can hear you inspecta kace mene?" "yallabai jami'an tsaro damuka baza a kowani anguwa ne muka sami wani information da safen nan dayasa muke bukatar kuzo kuyi comfarming ko shine" da sauri Mami ta fizge wayar daga hannun Aabid tsabagen yanda jikinta ke bari tace "inspecta anga d'ana?" anatse inspecta yace "abinda yasa nake neman ku kenan anga wani amma shi gaskiya ga dukkan alamu ba kidnapping dinshi akayiba kaman yanda muke zargi ba, dawata mace muka ganshi yanzu haka suna under our watch suna wani uncompleted building da ba'a gamaba awata sabuwar unguwa, na zuba jami'an tsaro da yawa a anguwan tayanda bazasu fitaba harsai kunzo kun tattance idan shine na hoton dakuka bamu, dan gaskiya wanan yay datti sosai yay budu budu kaman mahaukaci ko takalmi babu akafarshi kawai nadai ga dan kamaninsa da wanan saurayin daya kawo case din offis ne saisa mukace bari mukira" da sauri Mami ta share hawayen dake zubo mata tace "i...ina...inane wurin?" "zan tura muku address din yanzu" ya katse wayar saukowa Mami tai daga gadon tai baya luuu zata fadi sabida rashin karfi babu abinci acikinta tun jiya da sauri Aabid ya riketa, Baffa ne yace "ki zauna agida bari mu muje" fashewa tayi da kuka tace "Baba dan Allah zanje" share mata hawayen Aabid yayi yadau mayafinta ya yafa mata yace "muje grandfather muje da ita" fita dukan su sukayi harda big mum, Kafin ma su shiga mota har inspecta ya tura musu address din location din suka shiga manya manyan jeep dinsu kusan guda uku sukaja suka sukabar gidan.


Tafiyan wurin 25min yakaisu anguwan, parking sukayi agaban junction din anguwan nan inspecta da sauran yaranshi suka fito daga inda suka boye, fiffitowa daga mota sukayi inspecta yakarso wajen yace "muje".....








Yanda yake wani irin shishigewa jikinta yana numfashi da sauri da sauri yasa ta tureshi tace "stop" make mata kafada yayi da idanunshi dasukai ja sundan kankance kaman zaiyi kuka yace "am sleepy" matsawa gefenshi tayi da sauri tace "to sleep ga fili nan" make mata kafada yasakeyi hawaye ya cicciko a idanunshi yace "i want to sleep on your body" yay maganan yana matsowa kusada ita gabaki daya idanunshi sun chanza kala, da sauri ta mike tsaye adan tsorace ganin yanda ya chanza, kadangare tagani abango da sauri ta matsa baya tace "wayyo lizard" kallon bangon yayi kafin ya fizgo riganta tabaya juyowa tayi da sauri ta kallai tamai pointing lizard din tace "come let's play with lizard, kadangaren babba ne sosai ko" tashi tsaye yayi shima batare daya saki riganta ba ya kalli lizard din sanan ya kalleta yanda yaga tana kallon kadangaren tana komawa baya alamun tsoron kadangaren take yasa yaturata da karfi yace "lizard catch her" ihu tayi sosai takoma bayanshi da gudu ya kyalkyace dawani irin dariya yana clapping hands dinshi yace "Hamida my wife is afraid of lizard" kaman daga sama idanunshi suka sarke dana Mami data fara kunno kai dakin.
_🌹 IN BANI 🌹_






Maman Abd Shakur




23 & 24


_This novel is for sale karki karanta in baki biyaba_


_in kinason this novel, xaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_




_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_










Ware manyan fararen eyes dinshi yayi yana wani irin cute smile yace "Mami" daidai lokacin sauran mutanen duk suka iso sukai turus ganinshi tsaye yana kallon Mami dasu dasuka karaso wajen, dan duhun data gani dan sunyi blocking ray din rana dayake shigowa ta kofan yasa ahankali tadan leko da kanta daga bayanshi, mutanen data gani yasa da sauri ta komar da kanta bayanshi ta labe.


Sake zaro ido Aadil yayi sosai ya kalli Aabid dayay shiru yana kallonshi kaman yanda kowa na dakin ke kallonshi yanda yay mugun butu butu, wandon jikinshi kaman an kwaba kasa akai, kafarnan da babu ko takalmi ajiki tai busu busu, shimin jikinshi ma tai datti idanunshi sunyi suntum sunyi wani iri alamun yaci kuka, fashewa dawani irin Kuka Mami tayi ta shigo dakin da sauri tayo kanshi tace "Aadil, my baby" budema Mami hannu yayi yana wani irin jumping yana murna kaman dan yaro. "oyoyo Mami, oyoyo Mami, oyoyo Mami na" tana karasowa gabanshi yawani irin fadajikinta ya kankameta yana tsalle da kafa hakan ya bayyanar da Hamida dake labe abayanshi ta sunnar dakai kasa tama rasa ma me zatayi har wani soshe soshe take, kallon ta Mami da duka kowa na dakin suke yi barin ma Aabid dayaji gabaki daya numfashin shi ya tsaya chak, Cikin wata irin murya yace "Amatullah" da sauri ta dago kanta ta kalli direction din da aka kira sunanta daidai lokacin Aadil yasaki Mami shima yajuyo cike da murna yace "Mami look at Hamida, my wife" kallon Aabid Hamida tayi saikuma ta kalli Aadil dayay magana yanzun nan wani irin faduwa gabanta yayi bana wasa ba dan bambamcin da ayanzu tagani ajikinsu shine daya tsaf tsaf yake yaci shadda gizna kanshi sanye da hula tangaran, shaddar jikinshi har wani irin kyalli yake yana walkiya sai dayan kuma wanda yake daka daka yana sanye da singlet da dogon wando amma kamaninsu daya tsaf, kasa kallon sauran manyan mazan dakin tayi da tsohon dake sanye da glsass yana rike dayar Sanda tasake sunnar dakai tahade hannayenta dake wani irin bari tana murzawa da sauri da sauri tana numfashi sama sama. Sakin Mami Aadil yayi yaje dawani irin gudu yafada jikin Aabid batare daya lura da yanayin dayake ciki ba yaja hanunshi yace "come, come and talk to My Hamida Bid" yaja hanunshi yakawo shi gaban Hamida da kanta ke kasa har lokacin tana murza hannuwanta yace "Bid see my Hamida" yasaki Bid yajuya da sauri ya kalli Mami daketa binshi da kallo kaman zata hadiyeshi da so yace "Mami see Hamida my wife" da gudu yay wurin Baffa yafada jikinshi wani irin murmushi tsohon yayi ya shafa kanshi yace "Hassan" da sauri ya dago kanshi yana turamai baki a shagwabe yace "Am Aadil grandfather not Hassan" sake bubbude manyan idanunshi yayi yakama hanun Baffan yace "zokaga My Hamida Baffa" da sauri yakawo grandfather wajen, sanan yakoma yana wani irin tsalle yana kallon Abie da idanunshi sukai jajir yanamai wani irin murmushi kaman ya cinyeshi da so yace "Abie come and see my Hamidaaa" yaja hanun Abie yakaishi wurin kafin yakoma ya kwaso duka Uncles dinshi yakaisu gaban Hamida sanan ya tsaya shima kusa da Aabid yana kallon Hamidan da duk suka tsaya suna kallonta babu wanda yay magana cikinsu yana murmushi yace "Bid u see my Hamida, she's my Hamida" wani irin murza hanunwanta Hamida take jikinta nawani rawa, murmushi Mami tayi tace "baiwar Allah a ina kikaga Aadil?" ahankali tadago kanta ta kallesu, wani irin jiri tafara gani yanda duk suke kallonta bakinta har rawa yake tana nishi sama sama tace "i...ina...na...w...wun..." batakarasa gaisuwan ba tai wani irin baya a sume dan kwalin ta data lulluba dashi tai daurin ta wuya ya xame yay kasa arude Aabid ya mika hannu zai tarota yace "Amatullah! " arude Aadil yamika hanunshi zai tarota shima yace "my Hamida" da sauri Aabid yatarota Aadil ya tsugunna ya dafa kafadar Aabid yana kallonta yasaki kuka yana kallon fuskarta yace "wat happen to her Bid?" dagokai Aabid yayi yace "mutafi da ita gida Mami" da sauri Abie yace "munsan tane da zamu kwasheta mutafi da ita gida?" makemai kafada Aadil yayi yana goge kwallan dayake hakan yasa Baffa yace "muje akira likita yadubata koba komi ga Aadil nan yasaba da ita, daga gani ita ta taimake shi, kumuje, yaka Aadil" zuwa wurinshi Aadil yayi yana waigen Hamida da Aabid yadaga, Baffa yarike mai hannu duk suka dunguma suka fita daga wajen, saida suka salami su inspecta sanan suka shiga mota sai gida.






Wani hadadden daki Aabid ya shimfidar da ita kan makeken gadon dake dakin yana kallon fuskarta, tsugunnawa Aadil yayi gefen gadon yana kallonta shima idanunshi yay jajir, ahankali Aabid yajuyo da kanshi yana kallon yanda Aadil ke kallonta yana leka fuskarta, runtse idanunshi yayi da karfi yanajin ciwo aranshi sosai, daidai lokacin Mami ta shigo dakin karasawa tayi gaban gadon ta zauna ata saitin kafafun Hamidan tana kallon fuskarta tace "ga Dr nan zuwa ya dubata Baba yakira shi, Aabid stay with her karta tashi bakowa" ta kalli Aadil dake wani irin kallonta tamikamai hannu tana murmushi tace "come Aadil, muje kai wanka and change this cloth, kaima Dr zai dubaka inyazo duba friend dinka" make mata kafada yayi yana hararanta a shagwabe yace "she's my wife" shiru Mami tayi tana kallonshi saikuma tai murmushi tace "naji, muje kayi wankan to kafin kafito nahada maka abinci" tashi yayi ahankali kanshi narawa yana kallon Hamidan tashi itama Mami tayi taja bargo ta lullubeta dashi tarike hanun Aadil suka fice suka rufo kofan, wani irin runtse ido Aabid yayi yafuzar da iska kafin yadaura hanunshi kan zuciyarshi yana dukan zuciyarshi yay hakan kusan na 2min sanan yadawo daidai, zama yayi agefen gadon yay shiru yana wani irin kallon fuskarta, dawani irin murya mai rauni sosai yace "tayaya kika hadu da brother na Jewel? I'm the one for you Amatullah" yay shiru yana kallon fuskarta, knocking da akayi yasa yatashi yay wurin kofan bude kofan yayi Dr ne da Baffa suka shigo dakin, Baffa yace "yauwa gatachan likita adubata" karasawa Dr yayi bakin gado yaduba ta sanan yaciro drip daga katon jakan hanunshi yamata fixing yay allura aciki wurin 15 minutes yabata akanta sanan yajuyo ya kalli Baffa yace "fever ne kawai, i guess tsoron kune yasta ta suma, yanzu dai komi lpy dazaran drip dinan ya kare aciremata and yanzu dai bacci take zuwa anjima chan haka zata farka" murmushi Baffa yayi yace "masha Allah itace taga jikana ta taimaka mai, muje kadubamin jika" wucewa sukayi suka fita daga dakin Aabid yadawo ya zauna.


Duba Aadil Dr yayi yarubuta magungunan daza asayomai sanan yamai allura da kyar ya yarda akamai, yaci abinci nan wani baccin gajiya da wahala yay gaba dashi shima.






Saida yay bacci sanan Mami tarufa mai bargo takashe wutan dakin nasu tarage karfin Ac tafito, dakin da Hamida take tawuce ahankali tabude kofan har lokacin Aabid na zaune agefen gadon yazuba mata ido, budewan kofan dayaji yasa yadago kai, murmushi Mami ta sakinmai takaraso ta zauna kusada shi, ahankali yadaura kanshi kan kafadarta ya sauke ajiyar zuciya, shafa kanshi Mami tayi tace "menene Son?" dan murmushin yake ya kakalo mata yace "babu komi Mami na" dagashi tai daga kafadarta ta kalli fuskarshi jin yanda yay maganan danta tabbatar da abinda ke damun shi, lumshe ido yayi da sauri dan yasan tsaf Mami zata gano da damuwa a idanunshi, ahankali kira sunanshi. "Aabid" bude idanunshi yayi ya kalleta, nunamai Hamida tayi da ido tace "you called her Amatullah dazu kasanta ne daman?" shiru yayi yana kallon fuskar Mami kaman bazaice komiba saikuma yace "eh nasanta a Lagos nataba ganinta tafada ruwa nacirota nakaita asibiti daganan bankara ganinta ba saiyau" murmushi Mami tayi tace "Allah sarki, hala saisa itama ta taimaki Aadil maybe tazaci kaine" murmushi tasakeyi tasake jan kumatun shi tace "tashi muje kaci abinci idan ta farka sai a gaggaisa da kyau amata godiya saimu maidata gidansu ko" gyadama Mami kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login