Showing 54001 words to 57000 words out of 164763 words
Lami ce tadan zamo daga kujera tana murmushi tace "ina kwana Kaka" wani irin mugun kallo Kaka tamata kafin ta kalli Abba dayay shiru yana kallonta asanyaye tace "Sama'ila me wayan nan sukazo yi gidan nan da sassafen nan? Ince ba yarinyar nan suka kawoba" ahankali Abba yace "itace Umma tanama ciki amma duk ba abinda muke tunani bane, ashe taimakon yaron tayi, yaron kuma baima da lafiyan kwakwalwa, kinsan komu munga haka mun zaci pretending yake ashe da gaske ne baida lafiyan kai ne, jiyama saida iyayen yaron sukazo suka yima su Alhaji Ibrahim godiya, yanzu komi yawuce Umma" wani matsiyacin kallo Kaka tamai tace "idan kai yaro ne sunzo sun wanke ma kwakwalwa bayan Hamida taje ta shirga musu karya ka yarda niba yarinya bace, sanan abinda babba ya hango yaro ko yahau bishiyar kwakwa bazai hango ba, na kori Hamida daga gidan nan kuma ta koru ne, billahillazi la'ilaha illahuwa duk wanda yace zai nunamin ban isaba sainaje naci abincin gidan kajinka na mutun maka a wuya Sama'ila kana jina" tai maganan tana gyara kullin zaninta ta kwalama Hamida kira daga nan inda take tsaye. "Hamida! Hamida, dan uwaki kifito daga dakin nan kafin nazo dan wlh idan kika bari na shigo dakin nan sainai miki ruwan zabori aka, kifito nace" tagumi Mama tayi kawai tana kallon Kakan cikeda mugun takaici, Anty Lami ne ta tashi tace "Haba Kaka ki mata afuwa ki yafe mata mana idan kika korata daga gidan uban ta to ina kikeso taje? Tanada wani ubanne?" nunata Kaka tai da yatsa tace "kinga Lami lamiso kinga ina ganin mutuncun kiko karki kara kiran Hamida diyar Sama'ila, nariga nacireta daga yaranshi karki kara, Hamida!" ta kwalama Hamida kira da mugun karfi daidai lokacin wasu yara suka shigo guda biyu. "salama alaykum wai ana neman megidan awaje, ance ana sallama damai gidan" tashi Abba yayi ya kalli baban Ra'is yace "ina zuwa dan Allah" yawuce yafita, hakan yasa Abban Ra'is yace "Kaka kima Allah ki yakuri ki zauna ki saurareni haba Kaka ta" shiru tayi ganin yadan cika mata ido ta zauna akan kujera ta daure fuska tace "ina jinka yimaganan tun ina ganinka da gashi" sake kwantar dakai yayi yace "yauwa Kakana, wlh yarinyar nan ba iskanci tayiba taimakon mutumin nan tayi na rantse miki bari nabaki labarin yaron kiji...." nan yafara koro mata labarin har karshe zai cigaba da magana Abba yay sallama ya shigo ya kallesu dukansu yace "tareda baki nake ku gyara, iyayen yaron nanne sukazo" tashi Baban Ra'is yayi yace "masha Allah gasunan Kaka kyaji gaskiyan zancen daga bakinsu ai" fita Abba yayi tareda Baban Ra'is ko minti biyu basu dauka ba suka shigo da manya manyan baki sunci manyan kaya, Baffa, Suleman da Abie da idanunshi yay mugun jajir yau yana cikin tashin hankalin da rabonshi daya shiga irinshi tun ranan da aka haifi Aadil, gefe daya Aadil ne rai ahannun Allah yana sambatu yana kiran Hamida yana asibiti ansaka mai oxygen, gefe daya kuma Ozo ne dayace mai karya sake yabari Aadil yay aure, kanshi yadau zafi bana wasaba binsu Baffa kawai yake amma hankalin shi baya jikinshi baimasan me akeyiba, sai Mami da itama idanunta har kumbura sunyi tsabagen kuka saikuma big Mum dake biye da Mami, dawani babban Abokin Baffa wanda yake limamin jumma'a na masallacin dan ja, malam Kabir duk suka shigo dakin aka zazzauna, Mami daurewa kawai take tama kasa zama akan kujeran da kyau Kaka dai saibin manyan mutanen take da kallo danji tayi falon yadau wani irin sabon kamshi, Anty Lami ne ta tashi taje kitchen da kanta ta kwaso lemukan kwali tafito dasu a ijiye a tsakar falon sanan tadawo gefen Mama ta zauna tana kallon yanda su Abba ke gaisawa da mazan ana gaishe gaishe.
Gyaran murya Baffa yayi zai fara magana, Mami takasa daurewa ahankali ta zamo daga kan kujera ta saukar da gwuiwanta kasa ta hade hannayenta biyu alamun roko tana kallon matar da kamanin ta da Hamida yasa tagane itace mahaifiyar Hamidan tace "dan Allah, dan Allah ba danniba, ku dauki Aadil a matsayin danku kunsan duk abinda zaisa yaron nan farin ciki ya taimaki rayuwan shi, kome yakeso zaku iyayimai koma menene abin dan samun lafiyan shi" da sauri ta share hawayen daya zubo mata, zatai magana saikuma wani irin kuka yazo mata tafashe da kuka sosai tsabagen yanda zuciyarta kemata wani irin rawa, da sauri Mama da Anty Lami sukace "subhanallahi, hajiya dan Allah kidena kuka" cikin wani irin kuka Mami ta girgiza musu kai ta kalli Abban Ra'is da Abba ta kalli Kaka data kafeta da ido sanan tasake kallon Mama har lokacin hannayenta ahade tace "dan girman Allah badanni ba bakuma dan halina ba, alfarma nake nema dudda nasan mai girma ne, mai kuma wuya babu wanda zai dauki yarshi yabama mai kwakwalwan yara, amma dudda haka da Allah nake hadaku Maman Hamida da baban Hamida, ku dubi girman Allah, ku taimakama d'ana kubama d'ana Aadil auren Hamida karya rasa ranshi dan darajan All...Allah" tafashe da kuka sosai kowa na dakin saida kukanta yataba ranshi har Kaka, da sauri Mama ta dagata tama kasa magana Baffa yace "ku shiga ciki mu maza zamuyi maganan mu anan" tashi Big Mum tayi da Anty Lami da Mama suka wuce da Mami dake wani irin kuka sosai ciki tana sambatu bama tasan metake cewaba.
_🌹 IN BANI 🌹_
Maman Abd Shakur
33...
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_
_in kinason novel dinan, zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card 300 for those da basu da account ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_
Tsaki tayi tana kokarin warware daurin zaninta tace "wa kuwa, Hamida mana" wani irin taka birkin dayayi saida ta tsorata tasaki namijin goron hanunta tadafa kirji tana kallon ko ina tana zare ido tace "innahu min sulaymana, wa innahu Bismillah rahmani rahim, kai meya faru haka? Kasheni zakayi?" da kyar ya iya gangarawa gefen hanya yay parking yajuyo ya kalleta yace "wace Hamidan?" hararanshi tayi har lokacin kirjinta nawani irin masifaffen bugawa batadawo daidai ba tace "dan ubanka kana neman kasheni a hanya sanan kuma kana tambayata wace Hamida, tunda munada wata Hamida ne bayan wanda kasani ai shikenan nidai tada mutafi ka kaini gida akwai shirye shirye agabana" Kasa koda kunna motar yayi yajuyo yana kallon Kakan, hararanshi tayi tace "nidai yanda nake cikin farin cikin nan bazan bari bakin cikin ka yabata mini raiba, kaga tafiyata ka jika motarka da ruwan bunu ka tsoma tayoyin motar aciki kasha ka cinye shege mai kama da ifiritu tsabagen bakar mugunta" tabude motan tafita tana surutu ta tare keke napep ta shige tana ballama motar Faruk harara kaman idanunta zasu zazzago kasa.
Akofar gidansu aka sauketa tafito tana soka hannu a lalita tace "nawane kudin ka Malam?" "dari biyu ne Hajiya" hararanshi tayi tazaro dari dakuma naira hamsin tace "dari da hamsin zan baka yaro tsadarka tai waya nagadai ba wuyan fetur akeyiba" ta mikomai kudin karba yayi ganin tsohuwa ce yace "to shikenan Allah sa musu albarka" Ameen tace tajuya tabude gate ta shiga cikin gidan, Mama tagani a tsakar gidan da Baba dabasu dade da dawowa daga rakiyan Anty Lami da mijinta ba, dauke kai tayi tai kaman bata gansu ba tai hanyar sasanta, da sauri Abba yabita yace "daga ina kike Umma?" "inda ka aikeni" tafada atakaice tana kokarin bude kofar sasanta, zai biyota ta juyo fuska adaure tace "karka sake ka shigomin sasa ka wuce kacema Haleema a shirya gobe zanyi baki, manya manyan baki kuwa, sanan kabata kudi tai cefane, sanan katuromin Hamida yanzun nan ina jiranta" tana maganan ta rufo kofarta ta wuce ciki abinta, shiru Abba yayi yanabin kofar da kallo kafin ahankali ya saukar da ijiyan zuciya ya juya ya shiga dakinsu dan Mama tabar tsakar gidan, labulen falon ya yaye yaga Mama na kokarin shiga corridor yace "kirama Kaka Hamida zan tafi gidan kaji ni" ahankali takaraso inda yake tsaye tana kallonshi ganin damuwa karara sosai akan fuskarshi, hanunshi takama ahankali takai kan bakinta ta sumbaci hanun kadan tace "karka damu Umma zata sauko okay" gyadamata kai yayi yakai hanun nata kirjinshi ya rungume yana kallonta nayan sakanni kaman yanda itama take kallonshi asanyaye cikeda tausayin shi, saida yadanji dama dama sanan yasaki hanunta ahankali yace "thank you best wife, natafi" murmushi tayi tace "Allah kaika lafiya yakawo kasuwa best husband" kiss yama forehead dinta sanan yawuce yatafi itakuma takoma ciki, dakinsu tabude ahankali suka hada ido da Hamidan da har lokacin bata cire hijabi ba tana zaune kan gado kirjinta bai dena dukan uku uku ba, sai harba ido take kaman wacce tai kisan kai, Ihsan na gefen ta tana homework sai Zainab data gama gyara waken ta turesu gefe ta bude wani littafi tana dubawa, duk dagokai sukayi suna kallon Maman banda ita data saukar da kanta da sauri kasa tana wasa da yatsunta ahankali, da sauri Ihsan ta ajiye byron ta sauko daga kan gadon tace "Mama biscuit din dakikace zaki bani" hanun Ihsan tarike tace "muje yana dakina" sanan ta kalli Hamidan dataki dago kai tace "inkinga dama kije Kaka na kiranki" tana fadin haka tai gaba abinta, Zainab ta gimtse dariyan dake cinta saida taga Mama ta wuce sanan tasaki dariyan da sauri Hamidan ta kalleta da idanunta dasuka cicciko da kwalla, hararanta Zainab tayi tace "Allah ya tsagamin baki sainaki dariya ni" sauka tai daga gadon da sauri Zainab ta tashi itama daga kasa tana kallonta tace "wai ba cewa Mama tayi Kaka na kiranki ba eh hajjaju" harara ta watsama zainab din da manya idanunta tawuce tafita daga dakin ahankali tai sasan Kaka.
Ahankali ta shiga falon da sallama tana kallon ko'ina komi nadawo mata kaman wata matsoraciya, daidai Kaka tafito daga uwar dakan ta rike da wani turmi da tabarya na karfe, shigowa falon tayi ta ijiye turmin a tsakar dakin ta kalli Hamidan tace "kin wani tsaya hala nadawo aljana ce ko kike kallona da katun katun idanun ki kaman kwan lantarki, bazaki shigoba" shigowa tayi dakin Kaka kuma tadau ledojin data fito dasu tana budewa tana dubawa tace "yauwa saiwar ce" ta dago kai ta kalli Hamidan data zauna achan gefe tace "tashi ki cire hijabin nan kije fridge ki daukomin nono da kofi da chokali kizo nan" tashi tayi ta cire hijabin ta ijiye akan kujera taje fridge ta dauko nonon dakeda sanyi ta maida fridge din ta rufe ta kawo ta ijiye kusada ita sanan taje ta dauko kofi ta chokali takawo da sauri Kaka ta ijiye dakan ta karba ta zuba nonon a kofi ta zuba wasu magunguna aciki ta juya sosai sanan ta mika mata tace "yauwa shanye wanan kafin gobe suzo su kawomin kudaden saina dauko miki yar buzu tazo ta fara miki gyaran jiki dan wanan fatar taki fatar manya ce dole kiji gyara, ungo" ahankali ta karba tana kallonta dan ko kadan bamata gane metake cewaba ganin bata mata fadaba yasa taji zuciyata tai sanyi tai maza ta shanye batare data damu da dacin maganin ba.
Haka Kaka tarike ta a Sasan batare data bari tafita ba, tabata wanan tabata wanchan har bayan magrib sanan tasata taje tayo wanka, wanka tayi ta shirya cikin doguwan riganta na atampa sanan tasaka hijab tafito tai sasan su.
Falonsu ta shiga, babu kowa sai kamshin turaren wuta dayake yi, ahankali tawuce ciki ta tsaya agaban dakin Mama, sallama tayi chan kasa tanajin wani irin tsoro aranta, daga taciki Mama tace "waye, shigo" bude kofan tayi kaman wata matsoraciya ta shiga tana zare ido hada ido sukayi da Mama dake tsaye gaban wardrobe tana maida wasu kaya dake kan gadonta ciki, kallonta tayi kafin ta dauke kai tace "rufemin kofana sauro, meya kawoki kuma?" mayar da kofan tayi ahankali tarufe sanan tajuyo ta kalli Maman data mayarda hankalin ta kan abinda takeyi kaman batasan da ita a wurinba, jitayi jikinta yadau rawa wani irin kuka yazo mata ta tsani taga Mama na shashareta kotana fushi da ita, abin na mugun damunta arai bana wasaba, batasan lokacin dataje da gudu tawani irin rungume Mama ta baya ba tafashe da kuka sosai tace "Mama kiyakuri dan Allah kiyafemin kinji bazan karaba, wlh, wlh, biyoni yayi, tsoro naji nayi ihu Kaka tazo ta dakeni tahadani da Abba koya Faruk saisa naki fadi, am sorry kinji Maman mu" tasaki wani irin kuka dayasa Mama sakin kayan hanunta kasa ahankali ta lumshe ido tanajin kukan nata akowani jijiya na jikinta, kasa daurewa tayi ta juyo ahankali, hakan yakara bata dama tafada jikinta sosai tasaki wani irin kuka dayake cinta kwana da kwanaki tana shesheka tace "dan Allah ki yafemin bazan karaba, am sorry" ganin yanda take kukan yasa ahankali Mama ta dago kanta daga jikinta ahankali takai hanunta ta share mata idon tana girgiza mata kai tace "ya isa haka kukan" gyadama Maman kai tayi wasu hawayen na sake xubowa, hanunta Mama takama takaita gefen gado ta zaunar da ita sanan ta zauna itama a gefen ta, ahankali tai cupping fuskarta da duka hannayenta takira sunanta chan kasa. "Amatullahi" ahankali akuma natse ta amsa da "na'am" dan Mama bata taba kiran asalin sunan ta hakaba, murya chan kasa Mama tace "wacece mahaifiyar ki?" ahankali tace "kece Mama" zama Mama ta gyara tace "maisa baki bani matsayin ba? Kinada wata kamata ne aduniyan nan?" girgiza mata kai tayi, "kinada wacce zata soki regardless, wacce zatai understanding naki kaman nine a duniyan nan?" sake girgiza mata kai tayi ahankali hakan yasa Mama tace "to mesa baki fadamin matsalar ki? Mesa baki gayamin kowani hali kike ciki? Inaso kifadamin yau mecece matsalar ki tell me everything, tell me anything, tell me the whole thing Amatullahi and your mother will listen to you, mesa bakison mutane? Mesa baki attending lecture mesa? Mesa u are not free da kowa, eh? Talk to me Hamida ina jinki, i want to know your problem" hawaye ta share ahankali sanan ta girgiza kai tace "nima i don't know Mama, kunya nakeji idan naga mutane dayawa sun taru sai naga anata kallona saina dingajin kunya saikuma nafara jin tsoro idan banvar wajenba sai nafarajin kirjina na bugawa sosai, kaina yafaramin wani iri, kafufuna sufara rawa, nafara ganin jiri, inji kaman kallonsu na shakemin wuya, numfashi na nafita da kyar, banson zuwa lectures sabida yan ajinmu kullum nunani suke yi wai nice maicin 3 da 5 a CA, duk in naje class kallona suke saisa bana zuwa ajin" ahankali Mama na kallonta asanyaye tace "to ina kike zuwa in baki shiga lecture ba?" murya chan kasa tasake share hawayen daya zubo mata tace "old railway station chan nake zuwa?" cikin wani irin yanayi na mamaki Mami tace "old railway Hamida? Bakisan irin wajajen nan matattaran yan shaye shaye bane?" gyadamata kai tayi ahankali tana kokarin fashewa da kuka tace "sunma biyoni ranan nagudu shine harna hadu da mara lafiyan nan shima yadinga bina har gida" ahankali Mama tai salati "innalillahi wa innailaihi raji'un, Hamida all this suka faru baki fadamin ni mahaifiyar ki ba anya kinmin adalci kuwa?" girgiza mata kai tayi tana kuka tace "am sorry Mama bazan karaba Allah kuwan" shiru Mama tayi tana kallonta kafin tace "dena kukan share hawayen ki" share hawayen tayi wasu na zuba, Mama tace "daga yau kome yasame ki any problem at all, ko wani abu dakikeji lemme be the first person to know kina jina" gyadamata kai tayi ahankali kafin ta rungume Maman da sauri tace "am sorry Mama, kiyafemin" kanta ta shafa tace "nayafe miki ya isa kinci abinci" gyadamata kai tayi ta tashi tace "bari na gyara miki kayan" hijabin jikinta ta cire ta gyara kayan ta jerasu a wardrobe din tass Mama nabinta da kallo tana mata addu'a aranta Allah ya shiryata, yakuma chanzata sanan yabata miji nagari, mayarda kofan tayi tarufe sanan tadawo ta zauna kusada Mama suna hira su biyu ahaka bacci ya kwashe ta gyara mata kwanciya Mama tayi taja bargo tarufe ta tana kallon fuskarta, duk cikin yaranta tafijin tausayin ta kodan sabida itace shiru shiru bata saniba amma hakanan takejin wani irin tausayinta da sonta bana wasaba, Hamida daban takejinta aranta tun ranan data haifota duniyan nan, all children are special but deep down tanaji Hamida zata dawo wani abu nan gaba, inka kalli Hamida innocent dinta zaisa ko cizonta bazaka iyayiba.
Sallaman Abba dataji yasa ta kalli agogo goman dare lokacin dawowan shine tashi tayi takara fesa kanta da turare tabude kofan tafita daga dakin dan zuwa tarban mijinta.
Ranan Kaka batai baccin dareba wani hadadden kwaleman dakinta tayi tana masifa ita kadai. "ja'irar yarinya tatafi bata dawoba sun barni nikadai naketa aiki, ai wlh duk kudin dazasu kawo gobe sisi bazasu ciba nikadai nasha wahalata nizan mori kudina, Hamida tasami gidan hutu miji pagal kaman ita chan su karata sa warkar da juna" tai maganan tana tura kujeran falon ta jikin bango ta tsaya tana kallo yanda dakin yay kyau sosai tace "masha Allah komi yay tsaf tsaf, sun gogu kujerun jibi yanda suke kyalli gobe dazaran sunzo shashina zan kawosu darat ayi magana in yanke musu sadaki, sati hudu zan saka biki, babu kyau jan biki yay tsawo ga yaro ma ba lafiya, yar buzuwa ma kudin ta rabi zan bata sai bayan biki zan cika mata rabin, wayyo Allah na bayana" tai ihu tana kokarin zama akan kujera dan tagaji iya gajiya, ko minti biyu batayi da zama ba bacci yay awon gaba da ita.
_🌹IN BANI 🌹_
Maman Abd Shakur
34 - 35
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 acess fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_
_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 for those da basu da account sainai adding dinki a group din