Showing 120001 words to 123000 words out of 164763 words
suka tafi maid din sai kallonta take mota suka shiga driver yajasu koda sukakai gida lokacin ana kiraye kirayen sallan magrib.
Daidai zasu shiga gidan Aadil da Aabid na fitowa zasu tafi masallaci, hada ido sukayi da Aadil daya bita dawani irin kallo kaman zai hadiyeta, saukar da kanta kasa tayi da sauri gabanta na faduwa suka shiga gidan, hanunshi Aabid yaja yace "wanan kallo haka aisaika cinyeta da ido Dil" dan murmushi Aadil yayi a kunyace ya dauke kai, murmushi Aabid yayi nothing beat his brother's happiness awurinshi, shiyasan Aadil nama Hamida son dashi kanshi baisan iya son dayake mata ba, masallaci suka wuce da sauri ganin antada sallan.
fitowa sukayi daga motar sukai part din Mami, a falo suka tarar da Mami kan dadduma ta idar da salla ta kishingida da kujera, murmushi tayi ganin Hamida tare da maid din sun shigo, kanta akasa takaraso kusada Mami ta zauna akasa kanta akasa tana wasa da bakin hijabinta tace "ina yini Mami" hanunta Mami ta karba tana kallo tace "iyye daughter na anyi kyau, wanan lalle ja haka badai kyauba, ya kan an gyarashi shima?" gyadama Mami kai tayi tana kokarin cire hijabin dan ta nuna mata Mami tace "barshi basai kin budeba kin gaji tashi kitafi shashinki kiyi wanka kiyi bacci kihuta abinki, bari Mard tabiyoki da abincin ku, nasa anmiki slicing fruits make sure kinsha kinji daughter na" gyadama Mami kai tayi tace "to Mami na" tamike tsaye maid din kuma tai dining ta kwaso big warmers din guda biyu tabita dashi har shashin su, a dining ta ijiye abincin sanan ta shigoma Hamida da manya manyan jakunkunan kayanta guda uku sanan tamata saida safe tafita dan murmushi Hamida tayi dudda she's so happy da kayan amma fargaban Aadil yasa takasa murnan yanda yakamata, a gurguje tai bathroom wanka tayi sanan tai salla wani maxi doguwan rigan bacci tasa na silk daya tsaya mata a guwiwa pink yabi fatarta sosai yanada open neck, ta chusa gyararen gashinta dake kamshi sosai cikin net, ta feffesa jikinta da turarukan ta sanan tafito dining ko ina na kamshin turarukan ta, warmers din kan dining ta bude taga tuwon shinkafa ne da miyan egushi akayi, sai sliced fruits dakeda sanyi sosai acikin wani while ceramic bowl, kasa cin tuwon tayi dudda ya burgeta sosai tadau fork tasa a bowl din tafara shan fruits din, sosai tasha dan sun mata dadi, kadan kawai tarage tabude fridge tasaka sanan tawuce falo kayan ta tatare ta gyara wurin takoma falo tadauko wani blanket daban tadawo falo ta kwanta kan kujera ta lulluba da bargon ta lumshe ido danta gaji sosai yautaci kuka kanta sai sassara mata take ko 20min batai da kwanciya ba bacci yay awon gaba da ita.
Dawowa daga masallacin sukayi around 8:56 suka shigo gidan, zaiyi part dinsu Aabid ya ballamai harara yay pointing din shashinsu yace "go to your house, Allah ko innai aure kafin ka ganni haka chab saidai idan na fito salla, zanci amarci sosai bana wasaba kaganni nan, zanci amarci na bama da tsinke ba da toothpick znci" ware ido Aadil yayi cikeda isgili yace "kadinga mene to? Me toothpick zaima?" hararanshi Aabid yayi yatura bayanshi yace "gud night jor, greet our wife, Allah bamu alkhairi" ahankali yace "Ameen" Aabid yajuya ya shiga part dinsu shikuma yay hanyar part dinsu baida burin daya wuce yasa Hamida a idanunshi, ahankali yamurda door handle ya shiga cikin dakin wani cool sassanyar kamshi ya daki hancinshi, kafe Hamida dake kwance kan kujera ta lulluba da bargo harkai yayi da ido yayi heart dinshi na beating fast wani irin force kaman magnet na pulling dinshi to her, cold feet dinshi yadaga yafara tafiya haryakai wurin dogon kujeran, tsugunnawa yayi agaban kujeran yana kallonta ahankali yasa hanunshi yaja bargon kasa kadan haka ya bayyanar da fuskarta tareda wani kamshi dayamai sallama dake tashi daga jikinta, kafe fuskarta yayi da ido tai wani haske bau lips dinta sunyi pink sosai da dogon hancinta da tip dinshi yay ja kaman wacce take mura, net din data saka akai ya zamiye yay baya hakan ya bayyanar da black gyararren gashinta dake kamshi, gashin gaban goshinta sun kwanta lub, she was looking breathtaking and very innocent kaman ka dauketa ka gudu yanda heart dinshi ke bugawa yasa yakai bakinshi ahankali yama kumatunta Light kiss sonta na ratsa kowani jijiya na jikinshi, tashi yayi yaja bargon jikinta ya ijiye a gefe yanabin dogayen santala santalan fararen cinyarta da kallo kafin ahankali cike da dabara ya dauketa a hannu zaiyi bedroom da ita, firgita tayi tabude idanunta cikin bacci ta kallai, hada i[2/17, 2:37 PM] +2347066933957: .
_IN BANI_
_Maman Abd Shakur_
Baccin ma kadan ya iyayi sabida yanda yay bacci zaune akasa kanshi akan gado, dago kanshi yayi ahankali ya kalleta bacci takeyi sosai abinta blanket din yadan zamo fuskarta ya bayyana, fuskarta har wani shining yake tsabagen gyaran dataji, hulan net din kanta yadan zame kasa ta kudundune tarike bargon data lulluba dashi gam lips dinta looking pink sosai, tashi yayi ahankali yahau kan gadon batare daya yarda yay making any sound ba yana kallon fuskarta, ahankali yay kissing forehead dinta ta hanyar bata light peck dan motsi tayi da ido hakan yasa ya janye ya tsaya chak yana kallon fuskarta he loves Hamida love dashi kanshi baisan iyakan yawanshi ba, dudda da ace Aabid bai yarda ba, dama shahada dane kawai zaiyi yabarmai ita dan babu abinda bazai iyayima dan uwanshi ba but yasan at the end of the day sai ciwo ya kamashi sama ma dana Aadil din dan Hamida is connected to every vein and artery na jikinshi, without Hamida he can not function, without her he cannot live, he just pray and hope zata yafemai inba hakaba baisan yaya zai kasance ba, kara fuskarshi yayi saitin nata yanajin yanda take saukar da ajiyan zuciya cikin bacci ahankali ya lumshe ido murya chan kasa yace "i love you Amatullah, pls kiyafeni" tashi yayi yafita daga dakin zama yayi akan kujera a falo ya ciro wayarshi dake aljihun riganshi yana dube dube kafin ya shiga gallery, hotunan shi da Hamida ya shiga gani dasukai a dining daban daban, tsayawa yayi chak yana kallon yanda yake dilalar da miyau ga Hamida zaune kan jikinshi idanunta sunyi jajir tana kuka, wani hot iska ya fuzar heart dinshi na tafarfasa with fire of her love, swipe yayi yashiga next hoton saiyaga video ne da sauri yay playing video kuka yaga Hamida nayi sosai ta rungumeshi tana cemai i just want you to be fine Aadil, inason Aadil dina ya warke kadawo kaman kowa, ta sharemai bakinshi daya bata ta rungume shi sosai da sauri ya kifa wayan a kirjinshi hawaye na gangarowa daga idanunshi, Lord wani kuskure yaje ya tafka? Kome zaiyi wat ever it takes saiyayi dan ya tabbatar Hamida ta huce, how could he? He treated the woman dat stays with him despite all his flaws, ta aureshi ta kula dashi tsakani ga Allah taji tausayinshi sanan ta soshi, how could he even raise his hand on her how could he? This is the biggest mistake of his life, koma ba itabace baida any right or wat so ever yay treating woman like that meyasameshi wat happen to him, kiran assalatu dayaji anayi yasa yatashi, alwala yaje ya dauro yadawo falon ya shimfida dadduma yay nawafir bayan ya gama yatashi yaje shashinsu yatada Aabid suka wuce masallaci.
Bude idanunta tayi sabida karan kiraye kirayen tada salla, addu'an tashi daga bacci ta karanto kafin ta tashi zaune tana kallon ko ina na dakin, tashi tayi ahankali ta shiga bayi brush tayi sanan ta dauro alwala bayan tagama abubuwan dazatayi tafito zani ta daura ta zira hijabi tai salla tai azkar kafin ta dauko Al Qur'ani ta karanta, sai wuraren bakwai ta rufe tai addu'oin dazatayi ta linke dadduman da zanin jikinta ta tafita tadauko broom tazo ta gyara dakin nasu fes har zuwa falo da kitchen dako ina, turaren wuta ta kunna ta turare gidan sanan tadawo falo kayan da maid ta ijiye mata ta shiga fitowa dasu english wears ne gabaki dayansu sexy ones, inviting english wears shiru tayi tana tuna maganan da Anty Ayush tamata lokacin da aka kawota tace "ta dinga saka english wears tana matsu tana tsukewa, ta dinga gayu tanacin kwalliya akoda yaushe, sanan ko ina na jikinki na kamshi yana sa miji haukacewa akan matarshi" da sauri ta tashi harda dan gudunta ta dauko wayarta daga bedroom tadawo falon ta zauna tai maza tai dailing number Anty Ayush ringing kusan uku Anty Ayush ta dauka kafin ma tai magana Anty Ayush tai ihu tace "Hamida kece kika kirani ko mafarki nake mara son mutane" dan murmushi tayi tace "ina kwana" "kwana kuma munan Nigeria yamma ne, anyway fine ya kike, ya jikin ki kin warke?" gyadamata kai tayi kaman tana wurin tace "eh naji sauki" "Mama tacemin mijinki yaji sauki ya warke rass kingani ko you are such a blessing to his life and his family Alhamdulillah, Alhamdulillah, mun godema Allah, Allah yakaramai lafiya yakuma tsareki, yanzu yadawo normal saikuma fara zaman aure na kwarai na hankali dole kidena wanan banzayen wawayen halayan naki kinji little sis, you are not more a yarinya second to auta Ihsan, yanzu ke matar aure ce, dama dazu nacema Mama ta turamin number ki na Egypt dannai magana dake, ya kuke ciki yanzu daya warke ya? Yagode miki did he love you more?" shiru tayi batace komiba idanunta akasa kunya takeji dan gani take kaman tana gabanta."talk to me mana Hamida kinji am your sister koba hakaba" gyadamata kai tayi tace "uhm" "yauwa to tell me how did he react?" ahankali muryanta nadan rawa tace "sai jiya ya ganeni nikuma bana sonshi yanzu na tsaneshi he's a very bad person Anty Ayush he said such bad and hurtful stuff to me...." nanta fada mata abubuwan daya mata sama sama, murmushi Anty Ayush tayi ta tashi daga kan gado tazauna da kyau dan ta lura har yanzu yarinta nacin Hamida sosai wani abunma harda rashin kawaye da rashin wayewan kai ke damunta, ahankali tace "listen to me Hamida, duka abubuwan dayamiki is a normal thing, put yourself in his shoes kema zakiyi haka maybe sama da hakan ma idan kika farka daga ciwon shekaru talatin, trust me is a miracle ma yagane su Maman su da yan uwanshi, don't forget kin shigo rayuwanshi a last stage din rashin lafiyan shi, dole ba lallai dama yaganeki ba idan ya warke yan uwanshi has been with him tun yana yaro, yaro yarone amma ai kinga yasan his family gabaki daya ko'a ina yake so same thing yasamai shima, but am still proud of what you did to him jiya, you are a woman dole ki koyama mijinki how to respect and treat you, like bakebama duk wani woman dazai hadu da ita nan gaba in his life, he can't say sorry shikenan ki yafemai no! Take your time and make him understand your worth okay, yanzu ai kinada sexy kayako?" ahankali tace "eh" "yauwa good, dama kin cemin yanzu safiya neko am sure baidawo daga masallaci ba, ki gyara ko ina na gidanki kisaka turare, jekiyi wanka kici gayu sosai kisaka very sexy kaya dat will get him to salivate kiyi kwalliya mai kyau sanan sai ki shiga kitchen kihada muku breakfast, mind you Hamida ba'a shiga kitchen batare da anyi wanka ba, karki zama cikin matan dake cewa saisun fito daga kitchen sanan zasuyi wanka, a'a! ana so mace ta shiga kitchen tsaf tsaf looking super neat then saikiyi amfani da afron in zaki fara aiki, kihada breakfast, Bayan kin gama zaki iya sakeyin wani wankan, idan yakara baki hakuri kicemai kin hakura but take ur time kijamai aji, kimai kissa, kimai different things dat will drive him, ki hargitsamai tunani, ki tadamai sha'awa, kimai yanga da shagwaba, kisa ya mutum miki kinji kece zaki koyamai everything, now tashi kije kiyi wanka ki shiga kitchen kici gayu sosai kafin yadawo, will be calling you everyday inabaki new new tips, bye baby sis mai kama da Maman mu", murmushi tayi a kunyace tace "bye Anty Ayush agaida uncle Navy" "aikece Uncle navy din, kiri kiri kun radama babyna uncle navy saina fadamai" dariya duk sukayi ta katse wayar.
Tattare kayan Hamida tayi ta je ta jerasu a wardrobe kafin ta shiga bayi ko wankan nayauma special tayishi sanan tafito daure da towel tazo gaban madubi ta shafa mai tsaf sanan taja stool tazauna ta shafa powder tasa kwallin dake karama kwayar idanunta kyau, gyara giranta tayi tai carving dinshi kafin tadau wani pink lipstick tashafa akan pink lips, small fici ficin lips dinta yadauki shinning sosai, drawer mirror tajawo nan taga sarkoki daban daban da dankunnayen da Mami duk tasaka mata, wani simply necklace ta dauko irin wayanda ake sawa da English wears, wani dainty necklace ta dauko dakeda two pendant first pendent din mai siffar moon daidai wuyanta zai tsaya saina biyun mai shape din heart ya sauka acikin cleavage dinta sabida tsawon chain din wajen, bakaramin kyau yama wuyanta ba yawani irin haska farin neck dinta, round portable earing tasaka kafin ta mika hanunta tadau hair brushes ta warware gashin kanta ta hanyar girgiza kanta gashin ya warware, brushing kan dake hadadden kamshi tayi tadau wani black ribbon dake cikin drawer ta kama gashin tai ponytail, long jelan gashin yazubo down freely yana lilo, yanda tai parking gashin yakarama fuskarta kyau bana wasaba, tashi tayi takarasa gaban wardrobe din tabude tana kallon jerin english wears din takai almost 2min kafin tasa hannu ta jawo wani white black strips pocket sashes nine's pant dawani black girly t-shirts mai short v-neck ta ijiye kan gado, black bra da black pant taciro ta shirya tsaf kayan sun mata kyau bana wasaba farar mace acikin bakin kaya, gaban madubin taje ta tsaya tana kallon yanda v neck rigan ya bayyanar da tudun kirjinta chain din sarkan wuyanta dayabi cleavage dinta sai haska wurin yake yakara haskaka black rigan jikinta, pink lipstick da round earing din datasa ya haska round fitted face dinta tai wani irin kyau, turarenta ta dauka ta feffesa na twilly da cabotine floralie, dakin da ita kanta suka dauki kamshi maida komi tayi ta ijiye a maijiyar su sanan ta zura white bathroom slippers dinta tabude kofa tafito tai kitchen wandon yakama curved hips dinta sosai tafito figure 8 dinta chachas, kitchen ta shiga tana kalle kalle bata taba girki ba aciki, store ta wuce ganin Irish yasa tadebo a tray tafito ta ijiye sanan ta bude fridge taciro one round cabbage dakuma green and yellow ball peppers, da 2 big red onions, taciro 5 eggs, taciro mozzarella cheese sanan ta rufe fridge din, ta bude cupboard taciro black pepper, garlic powder, tafito da salt, curry, oil da maggi, da chilly flakes tarufe, gaban coffee machine taje thanks to tataba ganin Mami nayi nan tasaka tabar wajen tadawo tafara pilling irish din danso take tai light healthy breakfast potatoes and cabbage omelet, tasha gani Mama nayi abincin is healthy and good for breakfast Abba naso.
Yanka all abubuwan data fito dasu tayi ta zubasu a different small small bowls bayan ta wanke su ta tsaftace su, sanan tai hitting small amount of oil a pan tazuba sliced albasa kafin ta zuba diced potatoes din....
Shigowa cikin gidan sukayi atare, Aabid na lura dashi tun a wurin karatu a mosque dansun shiga wani class din da akeyi a masallacin bayan asuba kullum ana koyar da manyan maza duk wanda is interested can join karatu inda wani babban malami balarabe ke koyar dasu, hanunshi Aabid yarike yaja plastic chair dake gaban shashin su ya zaunar dashi ya zauna adayan yana kallonshi yace "wat is the matter with you rascal?" shiru Aadil yayi bayaso yamai karya kuma yanajin nauyin fadamai, murmushi Aabid yayi ya bugi kafadarshi cikin zolaya yace "Hamida na fushi dakai ko?" da sauri Aadil ya kallai irin kallon ya akayi ka sani dinan, dariya Aabid yayi yace "ai nasan za'arina, konine sainai fushi dakai baka kyautaba wat you did, and kaima kasan abinda kamata yanzu dai is left for you kasan yanda zakayi ka lallabata kashawo kan matarka welcome to married men world twinny" yafada yana dariya sosai harda rike ciki, hararanshi Aadil yayi kaman ya bugeshi yakeji shiru Aabid yayi yana daura hanunshi akan bakinshi yana kallon Aadil din ganin yana shirin mai kuka yace "yakuri, yakuri to am adding salt to your wound ko, zokaji yanda akema mata idan suna silly fushin su kaine me weapon fa, kanada abubuwan yaki ajikinka ne zaka tsaya kana sanyi, duk yanda mace takai ga fushi akwai yanda ake calming dinta down, kawo kunenka kaji yanda zaka lallasota" da sauri Aadil yamika mai kunenshi wasu maganganu Aabid yagayamai baisan lokacin dayay wani murmushin keta ba Ya lumshe ido tareda cizan lips dinshi ranshi fess, dariya Aabid yayi yana mikewa yace "kaje ka kusa sumar ma da Mami daughter count me out wlh, no be me talk am" yay maganan yana kokarin bude kofa yace "am sleepy, ayi lallashi lafiya basaikazo gaida Mami ba zance mata zaku shigo tare anjima da daddare" harara Aadil ya watsamai yabiyoshi zaije wajen Mami da gudu Aabid yarufe kofan ta ciki harda saka kwado Aadil ya murza kofan jin akulle yasa yay kwafa yajuya yay hanyar shashinsu baida burin daya wuce yaga fuskar Hamida ba smiling at him, tun kafin yakarasa part dinsu wani hadadden kamshin girki da kamshin menene dabai saniba ya daki hancinshi wani irin yunwa yaji yanaji atake yanke, ahankali yabude kofa kamshin girki dana turaren wuta yama hancinshi oyoyo, lumshe ido yayi yabude cikin jin dadi, shiga dakin yayi ya maida kofar ya rufe yana kallon ko ina na dakin fess fess wani sonta yaji yakarayi dan he hates dirty and hancinshi nason kamshi bana wasaba karasowa cikin falon yayi yana kallon TV dake aiki shi kadai tashar CNN, zare jallabiyar jikinshi yayi yana tafiya ya ijiye akan kujeran dining yarage dagashi sai singlet da boxer na Calvin Klein harzaiyi