Showing 84001 words to 87000 words out of 164763 words
Aadil din yakama kunenshi kaman zaiyi kuka yace "dan Allah kayi shiru Aadil, i promise kome kakeso i will do it for you i promise, but dan Allah kai shiru kaji, kukan ka zai karasa kasheni, idan da kasan matsalolin danake ciki ayanzu haka daka tausayamin, kadena damuwa da wanan shegiyar yarinyar yar matsiyatan wanda ubanta ke saida kaji, kaji da kullum anacin sama da arba'in a gidanku gasunan him a frozen fridge, babanka nada kudi Son, kome kakeso zan makashi, kome kakeso daganan har zuwa bangon duniya inada kudin zansa akawo ma, barima kaga nakawo ma kudi kome zakayi dasu kayi" tashi yayi kaman mahaukaci yafita daga dakin baiwani jimaba yashigo dakin yana jan wani babban ganamasgo dake nan zin din a kulle yana kallon Aadil din dake kuka yanamai murmushi, zama yayi abakin gadon kusadashi yasa hannu ya zage zip din ganamasgon uban kudi dake nan dollars note suka bayyana cike a jakan, wani irin murmushin dadi Abie yayi yajuyo ya kalli Aadil din dake kuka yana kallonshi ya lashe baki kaman tsohon maye, yasa hanunshi da sauri ya ciro wraps din dollars note din guda hudu dake kyalli yawani bubbuga kudin together agaban fuskar Aadil yace "kasan menene wanan My son?" yay maganan yana wani irin murmushin jin dadi yace "this is money Boy, manny, hausawa sukace milamila, kaga kudin nan na ganamasgon nan" yay maganan yana karkatamai ganamasgon da kyar sabida nauyinta dan acike take da kudi yace "duka kudin nan nakane kai yanda kakeso dasu nabaka, kai bacci akansu kayi bari dasu duk yanda zakai dasu, kaganni nan your Abie have money Aadil, plenty plenty money enough to buy all this kano kai Nigeria ma gabaki daya, kudin Abie ka basa karewa duk sati sati nake samin kudin da zan iya cika irin manyan ganamasgon nan guda goma sha biyar dasu, inhar you are a good boy kanajin magana na zan karoma irin ganamasgon kudin nan guda biyar kaji my son, my handsome boy kaji ko" makemai kafada Aadil yayi cikin fushi ya fizge kudin hanun Abie ya cillar dasu chan har suna tsalle suna fita daga dakin wasu kuma sukai wurin TV, cikin kuka sosai da muryanshi data dishashe yace "take me back to Mami, Mamiiiiiii, My Hamidaaaaaaa" yaja sunan Mami da Hamidan yana kuka kaman zai sume, tagumi Abie yayi yana tsinema Hamida aranshi yana tunanin wani dubara kuma zaimai ganin har wurin dayan dare Aadil kuka yake jikinshi yay zafi idanunshi kaman jan gauta yasa hankalinshi yatashi ainun, babu kallan dabaran dabai maiba amma sam Aadil Hamida yake kira hakan yasa Abie ya yanke sharawan kaishi wajen Ozo gobe dama gobe sunada meeting karfe taran dare, da kyar yasamu wani wahalallen bacci ya kwasheshi hakan yasa yadau bargo ya lullubeshi dashi ya zauna agefenshi yana tunane tunane, bayan kudi arayuwan nan d next abu dayake so da duka zuciyanshi is Aadil, maisa Allah yake testing dinshi da abu mafi soyuwa agareshi Aadil and Money?.
***
Wuraren shidda na safiya Mami ta bude ido, ganin yanda ta makara gari haryadan soma wayewa yasa tai bathroom agurguje, wanke baki tayi sanan tafito daga bayin daure da alwala, dadduma ta shinfida tai sallan bayan ta idar tai azkar sama sama ta mike da sauri dan zuwa tada Hamida, ahankali tabude kofar dakin bakinta dauke da sallama tana kallon yanda Hamidan ta kudundune kan dadduma tana bacci tana sanye da hijabin Mami, maida kofar Mami tayi tarufe takaraso cikin dakin tana kallon fuskar nata ganin yadan washe shaidan hanun Abie, tsugunnawa tayi agabanta takama hanunta tadan bubbuga tareda kiran sunanta. "Amatullah" saida takira sunan kusan sau uku sanan taji tabude kodaddun idanun nata dake cike da bacci, ahankali Mami ta mika hannu ta dagata zaune tana kallon fuskarta tace "kinyi sallan subhi?" girgiza kai tayi tana sosa ido, hakan yasa Mami tace "but naganki da hijabi akan daduma" cikin siriruwar muryanta dake cike da bacci tace "nakasa bacci ne shine natashi naita salloli" "sorry bansan kin kasa bacci ba ai danazo, tashi yanzu kije ki dauro alwala kiyi sallan kinji" gyadama Mami kai tayi Mami ta taimaka mata ta mikar da ita ta tashi ta shiga bayin itakuma Mami tawuce tafita daga dakin danzuwa fadinma masu aiki abinda za'a dafa, fitowa tayi tai wani irin mugun yaushi gabaki daya tunanin Aadil take jiya takasa bacci hakan yasa ta tashi ta dinga salloli tanamai addu'a ita kadan batasan lokacin data fara damuwa da Aadil hakaba, batasan lokacin daya shiga ranta hakaba, share hawayen dasuka zubomata tayi tasa hijabin Mami ta kabbarta salla, bayan ta idar tai azkar sanan tafara neman Al Qur'ani, akan drawer Mami taga wani hakan yasa ta dauko ta zauna tafara karatu har sai wuraren tara da rabi ta ijiye nan tasamu tadanji dama dama zuciyarta yadan yimata wasai. Tashi tayi ta linke dadduman ta cire hijabin ta ta linke ta ijiye sanan ta shiga gyara dakin gadon da baiwani yamutse ba ta gyara tsaf sanan ta zauna akan gado, shigowa Mami tayi tareda wata yar aikinta data riko tray ta nunamata idan zata ijiye tawuce tafita, ahankali tace "ina kwana Mum" murmushi Mami tayi tace "kintashi lpy daughter na, taso kiyi breakfast nabaki magani kisha kinji" gyadama Mami kai tayi ta sauko daga kan gadon kaman yanda Mami ta umurceta tahada tea tasha da su chips da egg da aka kawo mata tama kasa cinyewa dan sunmata yawa Mami takawo paracetamol takara bata tana murmushi dan sosai takeso ta danne damuwanta kotabama yarinyar strength but itama tunanin Aadil da Abie takeyi bana wasaba.
Sawa Mami tayi akazo aka fitar da tray din ta zauna kusada Hamidan tana janta da hira kadan kadan Hamida ke amsawa sallama akayi big Mum ta shigo dakin cikeda damuwa tace "meya faru sis? Ina Abban su yakai Aadil?" dan murmushi Mami tayi tana kokarin rike kukanta, ahankali Hamida tace "ina kwana Mummy" murmushi Big Mum tayi sosai tace "sannu daughter ya kk" tashi tayi ta kalli tace "lpy lau" ta kalli Mami tace "zanje nai wanka" gyadamata kai Mami tayi ganin yarinyar daurewa itama kawai take tace "dau hijabina kisa karki fita ahaka" hijabin ta dauka tasaka sanan tafita daga dakin tai shashinsu, ahankali tabude kofar shashinsu ta shiga tana kallon ko ina, kafin ta tadaga kafa kaman mai koyan tatata tai hanyar bathroom dinsu bude kofan tayi ta shiga idanunta suka sauka akan some few chocolate dake kasa wanda Aadil yakawo mata jiya, wani kuka ne yazo mata da sauri ta rufe fuskarta da hijabi tanayi kafin tafada kan gadon taja rigan Aadil din datagani akan gadon ta rungume sosai tanajin kamshin shi tana kuka ahankali tace "come back Aadil kaji, come back to me kaji My Aadil, inaso na kula dakai and watch you koda yaushe atare dani kanamin that ur cute smile and talk, i miss you so much" tafashe da kuka ahaka bacci yy gaba da ita sai wuraren azahar ta tashi gyara gadon tayi sanan ta shiga wanka.
50......
_Antyna! People like you are rare a duniyan nan, thank you so much, and i dedicate this page to you, thank you ones again for taking care of me_
Shiryawa tayi tsaf cikin wani free gown na atampa red and black, color yay mata kyau sosai ajiki, batasa ko kwalli ba danji tayi gabaki daya tagaji da komi, fita tayi taje kitchen ta dauko broom tadawo ajiye broom din tayi akasa ta gyara gadon tsaf dabai wani baciba sanan tadau tsintsiyar tafara sharan dakin just to while away time dan dakin ba datti, baban zoben silver color dakenan kaman na azurfa data gani a tsakar dakin yasa ta tsugunna tana kallon zoben, daukan zobe tayi da hannu da sauri ta kalli zoben jin zoben da shegen nauyi a hannu kaman tadaga wani babban abu, hakan yasa tace "me Aadil yakeyi da wanan zoben mai nauyi haka" ajiye zoben tayi agaban madubi tana tunani dan bata taba ganin zobe a hannun Aadil ba, kodai bata lura da kyau bane, no babu zobe a hanun Aadil ko daya.
Share batun zoben tayi daga ranta tadau broom din tacigaba da sharan ta share ko ina na gidan ta turare gidan da turare sanan tadauko wayarta tazauna akan kujera tai yan danne danne ganin duk batajin dadin maganan Aadil sai zuwanmata yake arai yasa takoma bedroom ta dauro alwala tasa hijabi ta zauna tafara karatun Al'qurani har lokacin la'asar tayi ta ijiye tai salla tana idarwa ta daura karatun danko kadan bamatajin yunwa har magrib ta tashi ta shiga bayi ta dauro alwala, sallaman Mami dataji yasa tafita tana zura hijabi, murmushi Mami da idanunta sukai wani iri tayi tace "jekiyi sallan ki mun shigo muduba kine dama" gyadakai tayi taredayin murmushi tajuya takoma ciki, Big Mum tace "yarinyar badai hakuri ba, ga dauriya dudda abin na damunta she's trying to hide it, muje muyi sallan muma" bude kofa sukayi suka fita daga dakin.
Sallan magrib tayi tacigaba da karatun har lokacin isha'i......
Wuraren takwas saura Abie yasake dawowa dakin ya kalli Aadil da tun safe yake kuka yaki shan daidai da ruwa agidan Abie hankalinshi duk yabi yatashi dan yasan yanajin yunwa kuma Aadil baison yunwa ko kadan nan da nan zakaga yanama kuka dazaran yaji yunwa, zama yayi gefenshi rike da bowl of fresh sliced fruits kaman zaiyi kuka yace "tashi to kasha saina kaika wurin Hamidan, idan bakasha ba bazan kaikaba" kallon Abie yayi da sauri yana tashi zaune yace "My Hamida?" gyadamai kai Abie yayi yay murmushi yace "yes but only if u have this fruits, you haven't eaten since when we get here" fizge bowl din yayi ya debo fruits din da fork yakai baki yasha yana murmushin kuka Abie na binshi da kallo yanajin son dannashi na ratsashi, sau uku yasha yamika ma Abie yace "am okay" tsabagen yanda ya kosa yaga Hamidan, kallon fruits din Abie yayi dudda baiwani ci wani abuba but at least is something, yasashi yasa wani abu a cikinshi tundama dabaran tai aiki haka zai dingamai kullum yanamai wayau yanasashi yaci abinci, kayan dayakawo mai ya nunamai yace "tashi to kasa mutafi" jumping yayi from bed yanajin wani irin mugun ciwon kai yasaka kayan yay tsalle tareda murmushi yace "let's go to My Hamida Abie" tashi Abie yayi yakama hanunshi suka fice daga dakin har zuwa compound yabude mota yasashi ciki sanan ya shiga gaba yaja motar suka fita daga gidan, tafiyan wurin minti talatin sukayi yay parking agaban gidan gonanshi dake wanan kyauyen, parking yayi yafito yabudema Aadil din fitowa Aadil yayi yana kallon gidan yace "My Hamida is here Abie?" yes Abie yace yakama hanunshi sukai ciki yaciro key yabude kofan ya shiga sitting room din dayay kura sosai kafin yayi hanyar dakin tsafinshi dashi, key yaciro yabude kofan yana rike da hanun Aadil suka shiga dakin dayay mugun duhu Abie yamaida kofan yarufe, rikeshi gam Aadil yayi yace "where's My Hamidah Abie this place da duhu" sakata Abie yasaka nasama dana kasa yace "don't worry u will see her now" yana rike da hanunshi yakarasa a duhun nan ya tsaya inda uniform dinshi suke yasaki hanun Aadil dake shirin yin kuka ya cire kayan jikinshi yasaka jan rigan tsaf sanan yana rike da hanun Aadil ya laluba yaciro ashana yay gaban dakin ya tsugunna ya kunna candles din wajen dake tare da gumaka da sunkai guda goma haske ya gauraye dakin, ihu Aadil yayi sosai ya rirrike Abie ganin mutane da sunkai guda goma shabiyar a tsaitsaye a dakin suna snye da jajayen kaya saikuma wani dake zaune gaban dakin fuskarshi kaman na biri idanunshi jajir dakaman jan wuta, runtse ido Aadil yayi gam ya rirrike Abie yace "Abie this is not My Hamida this is ojuju calaba, this is gorilla, am scared Abie" wani irin tsawa Ozo ya dakama Abie tareda buga karfen hanunshi akasa yace "kayi latti Tursoso sanan wayace kataho mana da wanan meeting iye" da sauri Abie yasa guwiwanshi akasa hakan yasa Aadil binshi, jikinshi narawa sosai yace "Great One Ozo tuba nake, tuba nake, inada dalilin kawoshi amma saika bani izini zan fadi" rike Abie Aadil yayi gam kanshi na juyawa idanunshi arufe, cikin murya mai kama data jarirai Ozo yace "fadi" ajiyan zuciya Abie yasauke yana addu'a Allah ya daurashi akan Ozo wanan karan kaman koda yaushe, ahankali cikin natsuwa yace "OZO na, Ozo mu, Ozo na kowa mai bamu kudade, Ozo mai bamu fame, Ozo the great one, zuciyata ta gaza natsuwa, zuciyata na cike da tsoron azaban ka dakuma hukuncinka, banzo koda da wasa nakara karyama doka ba dan banmanta abinda kaceba inhar na kara saba doka ban kiyaye sharadi ba bloodline must go dole saikunsha jini, saisa na shiryoshi takanas takano Ozo the great nazoma dashi, sonake ka shafemai gaba, sonake ka sideta ka shafeta tass ta yanda ko sha'awa bazaimaji ba balle harta mike yay kokarin saduwan, Ozo gashinan so nake ka shafeta dan kamashi nayi yana shirin saduwa da makirar yarinyar da aka auramai, Ozo inada matsalan jaraba kuma ina kyautata zaton yagado ni dan Aadil baisan komiba amma yana kebewa da mace gabanshi tafara mikewa, Ozo ka taimakamin nasan am asking too much nasan kuma you've always been granting my requests, Ozo kamin afuwa kataimaka min ka shafemin gabanshi ko hankalina ya kwanta nasan koshekara miliyan zaiyi da ita bazai taba karya dokaba dan baida gaban dazaiyi saduwan dashi, shikenan barata Ozo the the great" shiru dakin akayi kaman ba'ayi hallita awurin ba members duk kansu akasa ana jira aji abinda OZo zaiyi dan sosai sukejin haushin Abie, su Ozo baya daga musu kafa haka basu isa su karya dokaba sai Tursoso, babu dokan da Tursoso bai karyaba, duk ansha jinin yaransu na fari amma banda na Tursoso, wani irin tsawa Ozo yayi da saida dakin ya girgiza. "Tursoso!" zabura Abie yayi yamike tsaye Aadil kuma yasaki fitsari ya kankame Abie yana kuka. "Abie my Hamida" tureshi Abie yayi yana kallon Ozo, cikin fushi Ozo yace "Tursoso kan wanan yaron ne kaketa sabamin doka tun randa ka haifeshi ko, toyau zan zuke jininshi agabanka yamutu" ihu Abie yayi ya rungume Aadil tareda sakeyin kneeling cikin wani irin masifaffen tashin hankali yace "Ozo kayakuri natuba, natuba karka kashemin shi, to naji, naji basai ka shafe gaban nashiba, koda kashe yarinyar zanyi dandai nahanashi saduwa da ita zanyi Ozo the great kagafarceni karka tabamini Aadil dina Ozo" yanda yahaukace yana rokan Ozo yasa Ozo ya gyara zama yanamai wani irin kallon tsana yace "ina zobenka Tursoso?" da sauri Abie ya kalli yatsunshi ganin babu zoben dakemai aman kudi yasa yarude tsoro yamugun kamashi yace "Ozo, Ozo" yama rasa maizaice dan baisan inda ya jefar da zoben ba baitaba cire zoben daga yatsunshi ba koda da wasa cikin inda inda yace "Ozo hala nabarshi abayi danaje wanka ne amin afuwa" wani kallo Ozo yasake mai kafin cikin kakkausar murya yakira sunanshi azafafe. "Tursoso!" da sauri Abie yace "na'am Ozo da great one" "yarinyar nan tadamemu, tahanamu sukuni, tun jiya da daddare take konamu, kaje kafitar da ita daga gidan nan kanajina, kafitar da ita daga gidan nan da daddaren nan, i repeat kafitar da ita daga gidan nan inka sabamin zaka hadu da fushina dabaka taba ganin irinshi ba" cikin tsoro da fargaba Abie yace "to Ozo" wani jini Ozo ya mikomai a kwarya yace "ga sacrifice dinka jinin first born da ifufuwa" tashi yayi ya duka gaban Ozo ya karbi kwaryan yakafa abaki ya shanye jinin tass sanan ya ijiye kwaryan gaban wani gunki, Ozo yace "dau dandanka kuwuce kutafi kufitar da yarinyar nan daga gidan nan now, now, nowwwwww" yana fadin haka Ozo yabace daga dakin sauran yan dakinma haka, uniform din Abie ya chanza ya kashe candles din sanan yabude kofan yafita baima tsaya kulle kofan ba yanda Ozo yamai warning haka yasan abinda Hamidan tayi babba ne yafita da sauri yana rikeda Aadil da har lokacin idanunshi ke akulle mota yabude yasashi bude ido yayi sanan yasaki kuka sosai Abie baibi taka shi ba dan tashin hankalin dayake ciki yafi karfinshi ya shiga gaban mota yatada motar yaja dawani irin fitinannen gudu yabar wajen........
Sai bayan ta idar da isha sanan tai shafa'i da wuturi ta tashi daga kan dadduma ta linke ta tube kayan jikinta ta linkesu dan basuyi dattiba ta maida wardrobe taciro rigan baccin dazata saka ta ijiye akan gadon tana tunanin Aadil, bathroom tabude ta shiga ahankali tana share kwallan daya zubomata, brush tafarayi sanan taja shower cap tasaka sanan tafara wanka da ruwan zafi sosau, tadan dade tana wankan sanan tafito tadau towel pink tadaura daya kusan kaimata guwiwa ta daura ta zare shower cap din daga kanta ta ijiye tana kallon fuskarta, share hawayen dasuka zubomata tayi danko kadan jitakeyi bataso tafita daga bathroom din batare dataga Aadil ba azaune kan gado yana washe mata baki ba, lallasan kanta tayi kafin tajuya tana tafiya kaman wacce kwai yafashewa aciki ta murda door handle tabude kofa tafito daga bathroom din tai gaban mirror ta tsaya tana tsane fuskarta da towel din, karan dataji na faduwan abu kwan yasa ta juya ta kalli kasa dan tasan bata taba komiba tome yafadi, zoben dazu tagani akasan dakin harzata dauke kai saitaga kaman zoben yakara girma fiye da dazu da sauri tasake kallon zoben tana ware manyan idanunta, gani tayi zoben yay girma kaman anhuramai iska da sauri ta dafe kirji tace "innalillahi wa innailaihi raji'un" kaman daga sama taga kwalliyan dake gaban zoben yakara girma saitaga ya dare yarabe biyu yabude baki yay katoo sosai, wani karamin paper tagani yafito daga bakin zoben yafadi akasan dakin saitaga paper yay wani irin girma shima taga yakoma kudi dubu daya sabuwa dal, wani irin faduwa gabanta yayi jikinta yafara rawa bakinta yafara rawa tana kokarin furta addu'a takasa, gani tayi bakin zoben yafara fiffito da kananun papers din dayawa suna zuba akasan dakin suna komawa yan 1, 1k note sababbi dal dal, wani irin ihu tabuga afirgice. "Mamaaaa!" tai wurin kofa da mugun gudu tabude kofan tafita kaman wacce ta zare tana ihu. "Mamaaa, Mamaa" ta kwalama Maman su kira ta kwasa da mugun gudu tai hanyar gate