Showing 6001 words to 9000 words out of 164763 words
tana azkar, Ihsan ta karba tasaka takabbarta sallan itama.
Tana cikin lazimi Anty Lami tabude kofa ta shigo, hada ido sukayi hakan yasa tai dan murmushi akunyace tace "ina kwana Anty Lami" hararanta tayi tace "dole kiyi murmushi tunda kin gudo nan kin kwana baki kwana cikin jama'a ba, itakuma wanan data biyoki duk kuka kwana anan kun kyauta ai, tunda kun tashi in kugama kufito mukarasa jeren komi" maida kofan tayi tarufe tafice.
Ihsan na idar da sallan suka fita daga dakin, aiki suka farayi suna gyara gidan dan karfe hudu ne boat cruise party su, babban boat abokanan ango sukai hiring na Nire prest company, Zainab da kawayen Ayush din sai maganan party suke dan a arewa basu tabajin anyiba, sai wuraren one suka gama da sauri ta gudu dakinsu Ihsan ma tabiyota salla sukayi Ihsan ta debo musu abinci suka ci dan bataso takara fita dan gidan yacika da baki matan abokanayen shi ga makeup artist din da aka dauko dazata musu makeup suna gamaci tahau gado Ihsan tabi bayanta sai bacci.
Wuraren uku na rana Anty Lami ta shigo dakin taci gayu cikin wani hadadden lace baki daja dayay mata kyau sosai, baki tabude tana kallonsu yanda suke bacci abinsu kafin ta karaso wajen gadon ta daka musu duka a firgice dukansu suka tashi bayi ta nuna musu cikin fushi tace "tashi kije kiyo wanka right dis minute kisa ashobin ki ki fito amiki makeup, ke Ihsan tafi bathroom din dayan dakin kiyi wanka" da sauri Ihsan ta sauka daga gadon ta wuce dan bataso tai missing party nan for anything bata taba ganin party da akeyi a jirgin ruwaba ba kuma akan ruwa ba, kallon Hamida tayi dake sosa ido tace "wuce kema" ahankali kaman zatai kuka tace "Anty Lami ni bazani ba zan zauna gida tareda ke" cikin tsananin fushi Anty Lami ta nunata da yatsa tace "koki tashi kije kiyo wanka yanzun nan kiyi la'asar kije amiki makeup ki shirya kutafi ko wlh na saba miki Hamida, yanzu nafara yarda da maganan mamanki iskancin ki is too much stand up and get out of my sight my friend" da sauri ta tashi sabida tsawan data daka mata, bayi ta shiga tayo wankan tadauro alwala Anty Lami tagani a zaune ga trolley ta ta shigo mata dashi ahankali ta tsugunna tadau hijabin ta tasaka tai la'asar tana idarwa Anty Lami ta nuna mata sea blue ashobi ta wanda shine theme din party anmata wani hadadden gown, daukan rigan tayi tasaka Anty Lami ta tasata agaba takaita falo inda mata kenan dayawa anata makeup sunnar dakai tayi Anty Lami tasa aka fara mata, raurau tai da ido zatai kuka da kyar ta iya hadiye hawayen har aka gama mata makeup din, duka matan falon kafeta da ido sukayi sabida wani irin shegen kyau da tayi kaman ita tai kanta, hadadden takalmi Anty Lami tabata navy blue tasaka tabata glasses dinta tasa bakaramin kyau tayiba yanda ake kallonta yasa jikinta yafara rawa, horn da aka fara musu ana cewa su fito dan abokan ango tun uku da rabi suka taho yasa ta mike da sauri zata tafi daki hanunta Anty Lami tarike tana hararanta tace "wuce dan ubanki saikinje wlh, Zainab" ta kwalama Zainab dake kokarin sa hill dinta taci gayu sosai kaman itane amaryan kira, da sauri takarasa sa takalmin taje inda Anty Lami take tace "gani Anty Lami" murmushi Anty Lami tamata sabida kyan datayi tace "samomin gyale ta yafa dan bazata saka hijabin nanba yau" fashewa da kuka tayi jin ance bazata sa hijabi ba, bakaramin kular da Anty Lami abin yayiba tace "wai ke lamarin nan naki baza'a kaiki asibiti ba kuwa?" tabe baki Zainab tayi tace "Anty Lami wlh haka take ni dama kinbarta ta zauna a gidan inba hakaba wlh kuka zataje tana mana tana sunnar dakai tana neman inda zata labe saikace barauniyar datai sata a kasuwa, yar kauye kawai" hararanta Anty Lami tayi tace "kekuma dena cemata yar kauye wuce ki samo gyalen danace" ta kalli Hamida dake share hawayen cikin muryan lallashi tace "haba Hamida na, mai kama da mamanta, kinga kyan da kikayi kuwa? Bama wanan ba bakiso kije kiga jirgin ruwa yau, kintaba ganin jirgin ruwane ai saidai a tv a film irinsu tatanic, amma yauko zaki shiga cikin jirgin ruwa akan ruwa za'ayi party jirgi na tafiya, dena kuka kinji kije abinki inkin dawo kibani labarin abinda yafaru, kinga karma kibata kwalliyan ki" tai maganan tana share mata hawayen datakeyi daidai lokacin Zainab tafito dawani hadadden navy blue gyale ta warware ta yafa mata a one side aiko tai masifar kyau, murmushi Anty Lami tayi tace "iyye Allah nagode ma wanan kyau irin na yarana haka muje na rakaku wajen" rike hanunta tayi suka fita har wajen tasasu a mota Hamida kaman zatai ihu sabida tashin hankali gabanta har faduwa yake tsabagen tsorata sai sunnar dakai take tana kare fuskarta da gyalen jikin nata, daga musu hannu Anty Lami tayi tana dariya dan abin Hamidan ma looks funny dan yanzu yaga maganan zainab datace tana abu kaman barauniyar datai sata akasuwa.
Tashi motar tayi itakuma ta koma cikin gida tana girgiza kai tace "Hamida, Hamida hmmm Allah dai ya kyauta".
Gabaki daya she's not comfortable, gashi sai tafiya suke kaman bazasu kaiba chan lekki sukaje sukai parking a parking lot na Nire prest Boat activities, suka fiffito kafin su karasa waterfront din dukansu suna kallon katoton baban Boat din da akai decorating da flowers seablue, ga mutane maza damata suna kida na tashi, karasawa sukayi suka shiga kirjinta wani irin bugawa yake kaman zai tsage da sauri tarike hanun Zainab hakan yasa zainab ta kalleta daidai lokacin dayake duk angama shiga jirgin yafara gudu a ruwan, da sauri ta rike Zainab gam bakinta har rawa yake tace "An..Anty Zainab wlh am scared, please banaso wanan katon jirgin I don't like water" hararanta Zainab tasake yi dan sosai take jin haushin halin Hamida tace "aisai kiyi tsalle kifada ruwan, look back kiga yanda mukai nisa da wurin da muka bari yanzun nan, jirgi tafiya yake, idan kuma you can swim back there bismilla" girgiza mata kai tayi hawaye zai zubo mata tace "to please hide me kinji, am shy and am feeling somehow, mutane sunyi yawa" tsaki Zainab tayi kafin tajata by fire by force sukai sama jirgin asalin party floor din, ihu Zainab tayi ganin wurin yanda yahadu taciro wayarta zatai selfie tace "Omg this is paradise" Ihsan ma ihu tayi tana tsalle karasawa inda akai arranging kujeru sukayi kida natashi yan mata suka fara rawa, janta Zainab tayi tace "dalla chan zomuyi rawa yar kauye kawai karki kofsani" fizge hanunta tayi da karfi dan sosai kanta yafara juyawa yanda taga mutane dayawa awurin ga karan kida dake tashi ga duman music dahar kwanyanta takeji suna wani irin cika mata kunne kunenta yay wani dumm, duk inda ta juya saita hada ido dawani ko wata ana kallonta, cikin tsananin tashin hankali ta iya bude baki bama tagani da kyau tace "Anty Zainab" sosai idanunta suka fara juyawa hakan yasa ta daura hannayenta kan fuskarta tarufe fuskan kozata dena hada ido da mutane yan rawa na bugeta suna ihu, tai nan tai chan da sauri tace "Ihsan, Anty Ayush, somebody please help me, jiri nake gani" daidai lokacin kuma aka rage kidan wai amarya da ango zasu shigo, ahankali ta janye hanunta daga kan fuskarta ta bude idanunta dake juyawa, gani tayi mutane na komawa kan kujeran wajen suna zama, da sauri kanta na juyawa sosai tafita daga wurin tai baya tana tafiya kaman wacce bata da lafiya, da sauri Ihsan ta tana Zainab dake selfie tace "Anty Zainab kalli Anty Hamida ina zata?" batare data kalleta ba tana selfie ta tace "shareta Ihsan kema kinsan zataje neman inda zata boyene me tsoron mutane, nidai banda lokacin damuwa da lamarin ta am going to have fun and take pictures na nunama yan dept dinmu evidence munyi biki a boat akuma kan ruwa" tai dariya tanajan Ihsan tana hoton da ita.
Da kyar take tafiya tasa hannayenta tasake rufe fuskarta da sauri tafita daga wurin kanta na juyawa tai chan gaban jirgin wurin ba mutane tana kulle ido dan ko kadan bataso ta kalli ruwan dasuke kai da yanda ruwan ke gudu, ihu dataji na jama'a dakuma wani irin duma da sautin music da aka kara kaman zai fasa mata kunne yasa taji duka kanta na juyawa tana ganin jiri sama da dazu kanta na juyawa sosai da sauri ta zare hannayenta daga kan fuskarta ta kalli sama idanunta na kankancewa, sosai saman ke juyamata hakan yasa tafara juye juye itama tana mikar da hannu trying to hold on to something da kyar cikin layi tace "Ma...ma" bayanta ne taji yabugu da karfen jirgi gakida dake tashi ga kanta dake juyawa, wani irin mika tayi kanta yay bayan karfen idanunta suka juya tana kallon ruwan da yanda jirgin ke gudu sosai wani irin iska na walwal da gyalenta dake lilo shima, kara mika tayi hakan yasa glasses din idanunta suka fita daga fuskarta suka fada ruwan yanda take bangara idanunta na kafewa sosai ya rinjayi karfinta kafafunta suka daga tai cikin ruwan itama takai tsundum!.
_🌹IN BANI 🌹_
_M. Shakur_
5.....
Hakanan Ihsan taji tanajin wani irin, zuciyarta taki natsuwa sai kawo mata Anty Hamida take aranta da sauri ta kutsa kai tafito daga dance floor din tabi hanyar dataga Hamidan tabi tana kalle kalle har itama takai gaban jirgin amma bata ganta ba, babu ma alamunta awajen da sauri tace "to ina taje" sosai taji tanajin wani iri a zuciyarta tashiga wani irin damuwa hakan yasa ta juyo ahankali tana tafiya tana tunani, yar budurwa da saurayinta data gani a wajen takarasa wajensu tana murmushi kafin ma tai magana saurayin yace "cute girl wakike nema anan ki koma ciki karki fada ruwa, small girl doesn't suppose to be here" murmushi tamai tace "please Uncle have you seen my sister Anty Hamida anan?" da sauri dagashi har budurwanshi sukace no, hakan yasa tajuya tana magana ita kadai tace "to a ina kikaje kika boye Anty Hamida?" komawa hall din tayi but still she's not herself karasawa wajen Zainab dake rawa abinta tayi tarike hanun Zainab da sauri Zainab ta kalleta, ganin idanunta sun cika da kwalla yasa ta duko dakai cikin daga murya dan karan waka yay yawa tace "Ihsan leave me alone, if you are hungry dau plate ga wajen abinci chan serve ur self ne babu mai hanaki, kici duk abinda kikeso, am having fun please karki daman da rigiman ki auta pls" sakinta Ihsan tayi cikin fushi tai gaban hall din chan inda Ayush ke zaune da handsome mijinta agefenta sunyi kyau sosai, tana ganin Ihsan suka mata murmushi da sauri ta karasa wajen kaman zata fashe da sauri Ayush tarike mata hannu tace "menene auta?" hawaye ne ya gangaro daga idanunta tace "banga Anty Hamida ba nabi inda tayi banganta ba" dan shiru Ayush tayi tana kallonta hakan yasa mijin Ayush yadan duko dakanshi yace "menene Baby" ahankali tace "wai bataga Hamida ba" shiru yayi saikuma yace "bari nasa a bincikata" ya kalli Ihsan din dake share hawaye yay murmushi yace "cry cry Auta, bari nasa anemo miki ita tunda you are missing her dama gashi kunfi kama" yana maganan ya juyar dakai yama wani abokinshi dake sanye da kayan security alamu da hannu yazo yana zuwa yace "Man please ga Ihsan anemo mata Hamida duk inda, am sure ta buya a jirgin nan ne somewhere just help her find her" ya kalli Ihsan yace "follow him kinuna mai Hamidan inkin ganta" washemai baki tayi tabishi da sauri suka fita daga wurin tanamai surutu tace "Uncle dukna duba saman nan bata, muje kasane" murmushi yamata dan d girl is so cute yace "okay fine girl muje" kasa sukayi dan duba dakunan dake kasan.....
Wani irin tumble tayi ta shige chan cikin ruwan takai kafin wani wave mai karfi na ruwa yay sweeping dinta with force gaba dawani irin mugun gudu, sanan ruwan yawani irin wuntsulota sama kanta yafito space wani irin nishi tayi tana daga wuya. "iy..yyuuu" tabude baki tana wuntsila kafa da hannu sama tana juye juye tana kokarin bude idanuwanta da ruwa duk suka shiga, da kyar ta bude idanun tana juye juye amma bata hango jirgingu ba tadai ganta a tsakiyan ruwa, gaba ruwa baya ruwa, gefe ruwa ko ina ruwa, gashi sai kasa kasa take kaman ruwan najanta ciki ta nitse, ruwan har habanta, da kyar cikin tsananin tashin hankali gwanin ban tausayi tace "Ma...m" wani irin wave na ruwa yakara zuwa kaman ana aikoshi yahau kanta yay sweeping nata away with force fiye da nada gabaki daya kawai tasadakar ta mutu dan tama kasa bude ido tana kokarin bude baki danta iya numfashi ruwa na shigan bakinta ga ruwan so salty, gawani irin ruwa dake shiga hancinta da kunnuwanta taji kanta yay dumm, yanda take kasa kasa kasa tana bubbuga kafa tana fighting da ruwan dataji gabaki daya yawani irin matseta ya shaketa ya murdeta sosai kaman an kulleta da chain yasa fishes din ruwan duk suka rude suna neman wurin guduwa......
_Elagushi Beach Lagos_
Zaune yake agaban Beach yana kallon ruwa, he's d sunset type, there's something about sunset that gives him goosebumps, tun yana yaro when ever he's outside d yamma he always stare at the sun idan yana faduwa, saisa yau ya shigo beach da yamma just to have fun and watch the sun set.
Sanye yake da summer beach pant dayadan wucemai cinya kadan ya dameshi yabi kakkauran cinyarshi, jikinshi ba riga sai fadaddan huge full kirjinshi irin na maza masu work out, idanunshi sanye da ocean cabaretti sunglasses daya wani irin fitar da dogon hancinshi kaman karas, ga wani round black tabon salla agoshin shi daya karama fuskarshi kyau sosai, gashin kanshi dakeda dan yawa jike yake da ruwa dan ruwan ma diddiga yake yanabin gefen fuskarshi alamun daga cikin ruwan yake hanunshi rike da abinda akafi sani a beach da Aqua de coco (danyen kwakwa da aka fere saman akasa straw aciki) ahankali yake sipping coconut water har lokacin yana kallon beach din cool breeze da feshin ruwa na fesomai.
Ahankali take tafiya sanye da bikini pink tadaura beach hat akan long kitson attachment din dake kanta, tana tafiya ahankali cike da rangwada babu takalmi akafa kafafunta na nitsewa cikin lallausar kasar Beach din, hanunta tana rike da nata Aqua de coco tana sipping kadan kadan ta karaso inda guy din yake zaune, fadawa kanshi tayi ta daura kan akan kafadarshi kaman zatai kuka cikin harshen turenci tace "auch Aabid my feets are aching" shiru yayi kaman baijitaba ya cigaba da sipping aqua de coco shi yana kallon ruwan, ahankali ta sakeshi ta tankwashe kafa ta cigaba da sipping nata saikuma ta ajiye ta sake kallonshi tana turo baki takai yatsanta dake sanye da dogon kumba irin na arna tace "talk to me love, I have a shoot today but I abondon it just for you Aabid" ganin ko kallonta baiyiba yasa ta ijiye kwakwan nata a gefe ta tashi ta zagayo ta gabanshi ta shiga ruwan bayanta yabi da kallo tsugunnawa tayi ta dibi ruwan ta watsamai tana murmushi tace "you must talk, say something Aabid, say something, you must talk" takara watsamai ruwan a kirji, dan murmushi yayi daya bayyanar da cute one sided dimple dinshi daidai lokacin wani ma'aikacin beach din yazo yadan dukkar dakai alamun respect yace "sir your sport water bike is ready" dawani irin murya chan kasan makoshi kaman anyi forcing dinshi yay magana yace "okay u can go" ya juyar dakai yana kallon bike din dake cikin ruwan da aka daure igiya a jikin wani karfe awater front din gudun karya gudu, ajiye aqua de coco yayi yamike tsaye da sauri tafito daga ruwan tabiyoshi da gudu takama hanunshi tace "am going too Aabid let's water dive together since d bike has two seat" dan juyo dakai yayi ya kalleta da baki yanuna mata yaron beach din akasalance yace "then get a life vest jacket, I don't want you to die before your time" dariya tayi tamai kiss a hanunshi tana wani irin kallon shi cike da so tace "so you care for me" tai maganan tana kallon fuskarshi ganin bai kalleta ba yasa tasaki hanunshi ahankali tajuya da sauri taje wajen yaron beach din karban jacket shikuma yay wurin bike din, there's nothing dat gives him more fun koyana nigeria koyana outside inhar yana beach shine riding bike a ruwa, dan tsaki yayi dan beach din Lagos dinma is not as blue as he wants it to be, is too local for his liking, shiga ruwan yayi harya kaima gwuiwa kana ganinshi kaga wanda ya kware da ruwa sanna yahau kan bike din yajuyo yana kallon Vanessa that's coming towards him tanasa life jacket din data karbo akan dan pininin pant da bra na beach dake jikinta bikini, tana gyara beach hat dake kanta, ruwan itama ta shiga tace "yayy am so excited Aabid this ride is gonna be mad fun right baby" gyada mata kai yayi da sauri ta dane ta rungumeshi ta baya ta daura hanunta akan cikinshi tanaji kaman ta cinyeshi dan so, dan yatsine fuska yayi yadan duko yamika hannu yacire igiyan daga bike din ya kunna bike din dawani irin jarababben gudu yana awizo yaja bike din sukai cikin ruwan wave yawani irin dagasu ihu tayi sosai tana kara kankameshi tace "please Aabid we shouldn't go far okay, am a lil bit scared" cikin husky voice yace "and you shouldn't have followed me, just keep quiet and enjoy d free ride am giving you" kiss tamai abaya cike da murna takara kankameshi tace "I feel honored Mr Cute, sharing a ride with you is a privilege, no is an achievement" kara lankwashe murya tayi breeze din ruwan na neman fadin da hat din kanta tace "am so happy you choose me acikin all d hot hot celebrities damukeda shi a nigeria, thank you handsome" lashe pink lips dinshi yayi yawani irin yin awizo