Showing 1 words to 3000 words out of 52064 words

Chapter 1 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt

06 Mar 2025

2595

SANADIN RABUWARMU book1by Sakina Isma'il [02/01, 12:26] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)



________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V

________________________________________________



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝


*Book one free*


Alhamdulillah! Ina miƙa godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya bani dama fara wannan littafin nawa mai suna SANADIN RABUWARMU !kamar yanda na fara shi a sa'a, Allah ubangiji ya bani ikon kammala shi ma a sa'a,tare da nasara.


Jinjina ga kungiyarmu ta Jajirtattu💪 Allah ya kara haɗa kawunanmu.



Wannan littafin sad'aukarwane ga ɗuk way'en da suka rasa ɗaya daga cikin makusantan su,irin su iyaye ko dan uwa ko miji ko kuma mata,


Allah ya jikan iyayenmu,ya kuma kai haske kabarin su,mu kuma idan tamu ta zo ya sa mucika da kyau da imani ameen 🥹🤲



Na sad'aukar da wannan littafin zuwa ga mahaifiyata abun alfarina kuma farin ciki , Allah! ya jikinki da rahama ya kuma kai haske kabarinki much love Mammina 🥹




Page 1️⃣




Bismillahi rahmani rahim



Kwance take saman bed dinta kamar kullun tana aikin da ta tsaba yi, ma'ana aikin danna waya.
Dan yanzu danna waya ya zama kamar sana'arta ,saɓanin da kuwa danna waya sam bata gabanta .


Amma yanzu kam zata iya cewa ma wannan waya ita ce rayuwarta, kuma ita ce komai nata.


Ta yi nesa sosai akan chat d'in da take yi,kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa chat d'in ba karamin dad'i yake mata ba.


Saboda murmushin da take yi a kai -a kai.


Tana cikin chat ta ji kamar motsi a palo,ba shiri ta kashe data hade da saka wayan silent kana ta tura wayan karka shin pillow ta miƙe ta diro daga kan bed din kamar damusa,kai in kaga yanayin yanda ta yi sai ka d'auka ba mace ba.


Sai a lokacin na kare mata kallo.


Tana da kyau dai- dai gwargwad'o,fara ce sosai,tana da hanci ba laifi,sai dai karshe hancin na da fadi wannan ne dalilin da ya sa ba'a gane fasalin hancin nata,sai bakinta dan madaidaici,da kuma jan lips,yanayin lips ɗin nata ya yi kama da masu shaye -share,saboda jan da lips din nata ta yi ya yi yawa.



Tsaye ta yi a bakin shigowar palon tana kallonsa yana tire takalmin socikin dake kafarsa.


Jin idon mutun na yawo a jikinsa ne ya sa shi ɗago sexy eyes d'insa ya ɗora su akanta, kallon ta ya fara yi tun daga sama har kasa.


Sai da ya kara mata kallo saf kana ya d'auke idonsa, haɗe da miƙewa.


Kana ya nufi step din har ya fara taka matattakalar benan sai ya ji ta ce "Sannu da dawowa."


Ɗan dakatar da taka matattakalar ya yi kana ya kara juyowa,ya d'au kusan second goma yana kallonta,ita kuwa Safina har ta fudda rai maganar shi.


Sai can ta ji ya ce " Anya Safina tunda na bar gidan nan kin yi wanka kuwa.?"


Shiru Safina ta yi bata amsa ba.


Jin shiru da ta yi ne ya tabbtar masa da bata yi wanka ba tunda ya fita, kai kawai ya girgiza haɗe da juyowa ya ida sa hawa benan.


Cikin sanyin jiki ta juya ta koma dak'inta tana shiga dak'in bata tsaya ba darek ta wuce toilet bata fi mintuna biyar da shiga ba ta fito d'aure da karamin tawel a kirjinta.


Gaban mirror ta karasa ta ja karamin kujeran dressing mirror ta zauna,ta d'au mai ta shiga shafawa jikinta.



Sama -sama ta shafa mai,hade da fesa turare.


Bayan ta gama ta miƙe ta karasa gaban wardrobe dinta ta bude ta d'auko semple riga mara nauyi ta saka da wula, ta fifa ta bar dak'in ta nufin sama.



Tana zuwa ta turo kofar a hankali ta shiga ta maida k'ofar ta rufe ta karasa cikin palon.


Palon ya yi kyau ma sha Allah! Ɗuk da ba a kintse palon yake ba amma ya yi kyau,


Komai na palon fadi ne,dan Maher yana son farin abu sosai,


Sakamak'on rashin kulawa da palon bai samu bane ya sa carpet din da kujerun tashi daga fari ya koma wata kala daban, shi ba fari ba shi ba ash ba.



Bedroom d'insa ta nufa,tana zuwa nan ma ta turo kofar ta shiga ta maida shi ta rufe,kana ta karasa cikin dak'in.


Babu kowa a ɗak'in sai kayansa da taga ya tire ya ajiye akan bed da alama wanka ya shiga.


Karasa gaban bed ɗin yi ta,kana ta zauna akan kujerar dake manne da dagon.


Cikin dak'in ma dai ba karamin kyau ya yi ba.
Dan kallo ɗaya zaka wa kayan ɗak'in ka tabbatar da kayan kasar waje ne.


Dan kuwa wardrobe ɗin kaɗai ma abun kallo ne,saboda gaba dayanta glass ne sai sakiyar sa kad'ai ba glass ba,haka ma gadon shima gefe da gefensa glass ne.


ga wasu irin hotunan flawe da aka man na a saman gadon.


Abun dai ba'a cewa komai, ɗak'in ya yi kyau matuƙa.



Gadon kamar yanda aka yi bacci aka tashi da safe haka yake ba'a gyara ba.


Kuma ko a jikinta,a haka tazo ta zauna.



Fitowa ya yi daga wanka d'aure da tawel sai wata ɗan karanmi tawel ɗin dake hannunsa yana ɗan goge lafiyayyan sumar kansa baƙi wulik dake ɗan subar da ruwa saboda wanke shi da ya yi.


Saboda tsabar gyara da yake samu wani irin kyalli da tsantsi yake yi.


Bai lura da ita a cikin ɗak'in ba, har ya karasa ciki.



Ɗagowan da zai kenan ya ganta zaune a kan bed.


Cikin mamaki yake kallon ta,


Murmushi ta sakar mishi, ɗauke kai ya yi ya karasa gaban dressing mirror ya ja kujerar dressing mirror ya zauna kana ya juya yana kallonta,kana ya ce "Safina baki wanka ba kika d'au wani kayan kika saka."


Cikin mamaki Safina take kallon Maher,kamar baza ta yi magana ba,sai kuma ta ce "Haba Maher kana gani na fess -fess ka ce ban yi wanka ba."


Da mamaki Maher yake kallon ta,dan shi har ga Allah! Ya ɗ'auka bata yi wanka ba,



Shanye mamakin sa ya yi kana ya ce "Yanzu Safina kina nufin da barina palon har kin koma ɗak'i ki kin yi wanka ?"



"Eh na yi."


Ta bashi amsa ko a cikinta.


"Amma dai da ruwa kawai kika yi wankan ko? Dan na tabbata da a ce da sabutu kika yi baza ki gama da wuri haka ba."


"Haba Maher wai me ye sa kake min haka ne.?"



"Okay sorry kin yi da sabulu kuma kin fita,oya ta shi kije ki haɗa min abincina kafin na gama shiryawa, dan wallahi yinwa nake ji."



Da toh ta amsa,kana ta miƙe ta fita,dan zuwa haɗa masa abincin sa kamar yanda ya bukata.


Da kallo ya bita da shi har ta ɓace mai.


Kai ya girgiza,kana ya juya ya d'au mai ya shiga shafawa.



*Da daɗɗare*


Kamar kullun ita take riga Maher kwanciya yau ma dai hakan ce ta kasan ce,


Dan kuwa tun wajan 10 ta kwanta kamar mai bacci,nan kuwa ba bacci take yi ba ,ta dai rufe ido ne kawai kamar mai bacci.



Shi kuwa Maher ɗuk sanda Safina zata yi baccin karya bai taba ganewa ba.


Dan shi kullun d'auka yake baccin gaske take yi.




Ya daɗe yana aiki a cikin laptop d'insa sai wajan 11 da rabi ya kashe ,
kana ya mike ya je rurrufe ko ina haɗe da kakkashe fitilu,ya dawo ɗak'in ya kara gudun AC ya kashe fitilun ɗak'in shi ma,kana ya karasa ayan ya yi addu'ar bacci ya kwanta.


Bai wani jima da kwanciya ba bacci ya yi awan gaba da shi.



Tana jin s'aukewar numfashinsa ta saƙi murmushi dan ta tabbatar ya yi bacci,kana ta jawo wayarta ta hau Facebook.



Ganin sa a online ne ya sa ta s'auke ajiyar zujiya kana ta tura masa Hy.


Bai fi one minute ba ya tura mata da "Oyoyo my queen,tun dazu nake ta jira ki na ɗ'auka ma kin yi bacci."



"A'a Habibi idona biƴu kawai dai ciwon mara ne ya sani a gaba tun dazu shi ya sa ba ban hau online da wuri ba sai yanzu."


"Subhanallah! sorry dear,amma kin sha magani.?"



Ta ga ya kara tura mata.


Murmushi ta ɗan saƙi haɗe da gyara bargon da take lullube da shi,ta rufe kanta sosai ta kara rage hasken wayan,kana ta shiga yi masa reply kamar haka.



"Ban sha ba my dear."


"Me ye sa baki sha magani ba my love? Gaskiya ya kamata ki sha magani ki dena wasa da lafiyarki,kin san lafiyarki shine komai nawa."


"Ciwo na ba na magani ba ne ba my love".



Dan gyara kwanciya Suraj ya yi kana ya ɗan yamutsa sumar kansa kaɗan ya shiga mata reply.


"Toh my queen,in ba na magani ba na mene ne ?".



"Aure nake so,ina bukatar na miji a kusa da ni,wannan ne kad'ai maganin ciwon maran da nake fama da shi."



"Woww!yanzu na gane abunda kike nufi,


Karki damu in sha Allah! Kwanan nan zan zo (Nigeria) ina zuwa zan zo na ganki daga nan in na koma sai na turo iyayena a zo a nema min auren ki,mu samu mu mallaki juna mu wuta da wannan chat din haka."


Ai Safna na jin Suraj ya yi maganar zuwa da kuma aure ta ji kirjinta ya buga dib -dib!! Har sau ɓiyu,ba shiri,ta ce" Habibi ka yi haƙuri bari na kwanta yau maran nan na min ciwo sosai gobe zamu karasa maganar."


"Okay sorry my dear, Allah ya baki lafiya,ki kwanta, please ki kulanmin da kanki sosai kin ji.?"



"Okay my love good night,i love you so much."


Safna ta faɗa.


"I Love you more my heart."


Shi ma Suraj ya faɗi.


Murmushi Safina ta saki kana ta kashe data ta s'auka daga online ɗin.



A jiye wayan ta yi kana ta kwanta.


Lokacin har sha 12 ta ɗan wuce.




Bata daɗe da ajiye waya ba ita ma baccin ya yi awan gaba da ita.



















*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*






*More comments more typing*✍️






Please sharen fisabilillah 👏
[04/01, 14:12] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________


Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/K0ug6sIXtuyFaEI3q27XDx

________________________
________________________



Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V


________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*




Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.

Ban yadda wani ko wata ta juya min labari ba.
Haka ban yadda a karanta min labari a YouTube ba tare da neman ijinina ba, pl a kiyaye, dan in anyi min haka zan ɗauki mata ki,tunda hakki nane.



Page _2️⃣



Bismillahi rahmani rahim


*Washe gari*



Har ya tashi ya yi wanka ya shirya ita bata tashi ba,haka ma sallar asubaha,ya tashe ta har ya gaji ya kyaleta,


In da sabo dama ya saba da halin Safina.
Bayan ya kammala shiryawa ya fito palo, dinning table ya nufa yana zuwa ya ja kujera ya zauna.


Kana ya saka hannu ya shiga babbuɗe kulolin da suke kai.


Dankalin turawa da ƙwai ya gani,rufe kulolin ya yi kana ya shiga ƙwallawa mai aikin su kira.



"Nadia! Nadia !!."

Can cikin Kitchen na ji wacca aka kira da Nadia da amsa da na'am haɗe da fitowa da sauri,ta karaso gaban sa,sai da ta durƙusa har kasa kafin ta ce " Gani Ranka ya daɗe."



"Tea." Ya faɗi a tak'aice ba tare da ya kalle ta ba.


"Gashi can yanzu na zuba a flas zan kawo sai ka kirani."


"Okay kawo."


"Ya kara faɗi."


Dan shi baya iya dogon magana.


Asali ma shi magana ba wani damusa ya yi ba sai in ya zama dole yake yi,ko a office.


Ba'a wani d'au lokaci ba, Nadia ta kawowa Maher tea,kana ta ajiye akan dinning table haɗe da d'auko glass cup zata zuba masa tea ɗin ya daga mata hannu taɓe baki ta yi haɗe da ajiye cup din ta juya ta bar wajan ta koma kitchen,



A kitchen take faɗin "Ummm! Mutun na tausaya maka kai baka gani,kar Allah ma ya sa ka bari a zubamaka tea ɗin,ta karashe magana tana mai haɗa kayan wanke -wanke da ta yi anfani da shi kana ta soma wanke su.



A palo kuwa,tea ɗin ya zuba kana ya soma sha.


Bai wani sha deyewa ba ya ajiye cup ɗin, kuma bawai tea din ne baya so ba a'a,kawai dai bai cika son abincin masu aiki ba ne,yanzu ma dole ne ya sa shi ya fara ci.


Dan ya yi magana har ya gaji akan bawa masu aiki na masa abinci amma taƙi,a karshe ma cewa ta yi ita gaskiya bazata iya ba,in zai ci abincin mai aikin ya ci in bazai ci ba kuma ya je ya nemi restaurant mai kyau da hankalinsa ya kwanta dashi ya dinga zuwa yana cin abincin a can.


Bayan ya goge bakinsa da tishu ya miƙe ya tattara wayoyinsa da key ɗin motarsa da jakar aikinsa ya rataya ya juya ya fita.



Yana fita ya nufi inda farar motarsa ya ke ya shiga bayan sun gaisa da Baba mai gadi ya buɗe masa gate ya cilla hancin motarsa waje.



Tuƙi yake yana tunanin nemawa kansa mafita,dan ya gaji da irin abubuwan da Safina yake masa.


A haka dai har ya karasa gidan su,dan akwai meeting na family yau.



Kasan cewa ba wani jimawa zai yi ba ne ya sa shi yin parking motarsa a waje bai shiga da shi ciki ba,kana ya karasa karamin gate ɗin ya yi nocking.


Ba'a wani d'au lokaci ba mai gadin gidan ya zo ya buɗe.



Ganin Maher ne ya sa mai gadi durkusawa har ƙasa yana gaishe shi, haɗe da yi mai barka da zuwa.


"Baba miƙe."


Ya faɗa fuska a haɗe,dan shi ya sani yaga babba yana durkusawa yaro.


Sai da yaga Baba mai gadi ya miƙe kafin ya fara magana " Yauwa daga yau sai yau karka kara suguna kana gaishe ni,ka dinga gaisheni daga tsaye kawai tunda ka girmeni."


Yana kaiwa nan ya yi cikin gida, Baba mai gadi ya bi Maher da kallo yana murmushi.


Allah sarki bawan Allah! ɗuk Ƴaƴan Alhaji kai ne mai hankali, way'encan na isa na gaida su a tsaye ?
Ummm ! Wallahi ban isa ba."



Baba ya yi magana a lokacin da yake zama akan bencinsa,kana ya ɗauki radionsa ya ci gaba da sauraran labarai safe da ake yi a freedom radio.




Turo kofar palon mahaifin nasa ya yi, bayan ya tire sociki dake kafarsa,kana ya karasa ciki.


Sai da ya yi sallama suka amsa tukun kafin ya karasa shigowa cikin palon.



Wanene Maher?

Sunan mahaifinsa Alhaji Aminu Mustapha,
Alhaji Aminu Mustapha babban tsohon ma tuƙin jirgi ne, a yanzu ya yi ritaya, Allah ya daɗe da yiwa Mahaifiyarsa rasuwa sai dai mahaifinsa kad'ai ya rage a raye,su uku ne iyayensu suka haifa,shine babba,sai kuma wanda yake binsa Muhammad Auwal wanda yake aiki likita a garin(Zaria)sai ta uku wanda yake bin Muhammad Auwal mai suna Ai'sha, Ai'sha na kasar India tare da mijinta,dan a can yake aiki,a yanzu haka ma a wajanta Suraj yake zaune, ɗuk da ya so kama haya,amma Ai'sha da mijinta sun hana shi,wannan ne dalilin da ya sa ya haƙura da neman gidan haya ya zauna a gidan yayarsa.


Alhaji Aminu na da ƴaƴa 5, Maher,Suraj,sai Nihal da Nihilah, Nihal da Nihilah su ƴan tagwaye ne, Maher shi Mahaifiyarsa ta ɗaɗe da rasuwa ,dan a lokacin da Allah ya yi wa Mahaifiyarsa rasuwa ma bai fi shekara biƴu zuwa uku ba a duniya,a hannun matar mahifinsa ya taso,shi ƙad'ai ya yi aure a cikin su,sauran ɗuk basu yi aure ba.


Dan shi Suraj yana kasar waje ma yana aiki ,bayan ya gama karatu acan ya samu aikin, yanzu haka shine babban likita a garin (Delhi India)


Yana son dawowa (Nigeria) amma sun hana shi , saboda ya ƙware sosai wajan iya duba marsa lafiya,amma yana zuwa lokaci zuwa lokaci,
Su Nihal ma suna matakin karye a jamiya.
Kuma ɗuk sun samu mazajen aure,suna yin degree za'a musu aure.


Shi kuwa Muhammad Auwal,matansa ɗaya da ƴaƴa biyu, Muhammd (Imran)
Wanda yaci sunan mahaifinsa,sai Fatima (Basma)
Fatima na da shekara 14 yanzu,shi kuma Imran na da shekara 20 .


Ɗuk sati suna family meeting,suna tatt'aunawa akan abubuwan da ya shafi rayuwar su,da kuma tambaya in akwai wanda yake da damuwa ya faɗa a bashi shawara.


Wannan shine tak'aitattacen tarihin Maher.


Sauran kuma zaku ji anan gaba.



Bayan ya gaida kowa dake cikin palon tare da amsa gaisuwan ƙannansa ne ya nemi waje ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun palon.


Ɗagowa Alhaji Baba ya yi,watoh kakan su Maher,wanda ya haifi mahaifin su.

Kallon jikokin nasa ya yi ɗaya bayan ɗaya,kana fara buɗe taro da addu'a.



Bayan ya gama addu'a,kana ya fara magana kamar haka,


"Yauwa kamar yanda ku ka sani a ɗuk karshe wata muna meeting,kuma ba dan komai ya sa muke yi ba,sai don jin matsalar juna domin magancewa tare,



"Kai Maher wannan zaman da aka yi yau naka ne."


"Ni kuma Alhaji Baba.?"


Ya faɗa yana nuna kansa.



"Eh kai! Ɗuk da ka boye mana damuwarka,da kuma matsalan da ka ke fuskanta a gidanka,amma su ƴam ɓiyu sun zo sun faɗa min komai."


Wani irin juyowa ya yi ya kalli inda su Nihal da Nihilah suke,suna haɗa ido suka yi saurin sunkuyar da kai ƙasa,ga kirjinsu da yake bugawa da sauri -sauri, dan sun san yau kam kashin su ya bushe a wajan sa.


Magana Alhaji Baba ya ci gaba da yi " Kullun in muka tambayeka zaka ce mana ba komai,bayan kuma mu munga komai ɗin a jikinka,da kuma fuskarka,



Amma a haka muka kyaleka,


In baka manta ba kwanakin uƙu da suka wuce su Nihal sun kai muku ziyaran bazata,anan ne suka ji kana wa matarka Safina magana tana mayar maka da marna ni,kuma bayan haka ba'a tsaya iya nan ba,sun tabbatar min da cewa ɗuk abunda ya shafi gidan yar aiki take yi hatta gyaran ɗaki bayan fitarka mai aiki ta tura ta je ta kyara maka,ta kuma tattara gajeran wantunan ka da su singlet ta bawa yar aikin ku ta wanke,



Wannan aikin ɗuk ita ya kama ta yi,amma bata yi ba,dan haka na baka wata ɗaya ka nemo mata ka kara aure,dan bazan lamunci irin wannan abun ba."



Alhaji Baba ya kare magana.


Cikin sanyin murya ya buɗe baki ya ce" Alhaji Baba,bana son mata sama ɗaya a rayuwata na sani mata sama da ɗaya,amma tunda ka ce haka zan yi,


Amma kafin nan so nake ka karamin ko da wata ɓiyu ne,in sha Allah! Zan yi ƙoƙarin ganin cewa na gyara ta,in kuma bata gyaru nan da wata ɓiyu ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login