Showing 51001 words to 52064 words out of 52064 words

Chapter 18 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt

06 Mar 2025

2598

.?"


Sun kuyar da kai Maher ya yi haɗe da geɗa kai ,


Alamar "Eh."


Ɗan kara juyowa Daada ya yi ya kalli Nailah ita ma kana ya ce .


" Nailah kina son Maher ?"



Ai ina jin haka na miƙe ina murmushi haɗe da barin ɗakin.


Su Nihal suka ɗinga tafi suna faɗin ,



"Yeeee! tana so tana so tana so tana so."


Haka suka ɗinga waƙa .


Murmushi jin dad'i dukansu suka yi kana suka tashi suka bar ɗakin.



*Washe gari*


Yanke shawara su Abie suka yi da a d'aura auren anan kafin su koma ƙasar Nigeria .


Kasan cewa gobe ne za'a fara dawowa ya sa yau bayan sun i'dar da sallahr azahar aka daura auren Maher da Nailah ,


Saboda Maher gobe zai koma ,


Cikin farin ciki suka koma hotel d'insu ,ranar karamin party suka haɗa iya su eh su ,


Sun ci sun sha ,


Bayan sun gama suna cikin hira aka yi nocking umarni Suraj ya je ya buɗe .



Wani ɗaya daga cikin matuƙan jirgin ne ya gani tsaye a baƙin ƙofa hannunsa rik'e da wata farar ta karta .


Gaisawa suka yi da Suraj ya mika masa takartan ya ce ya bawa Maher, godiya Suraj ya yi ya Koma ciki .


" Waye ne Suraj ?"


Daada ya tambaya .



"Wallahi wani ɗaya daga cikin matuƙan jirgin ne ya zo ya kawo takarta ya ce a bawa Bro Maher ."


Suraj ya faɗa yana mai miƙa Maher takardan .



Murmushi Maher ya yi kana ya ce .


" Suraj ba sai ka bani takardan ba ,dan na san me a ciki, kawai ka bawai Abie ya ajiye ,na san tunda na samu Nailah komai zai dawo daidai ,kuma aikin ma zan koma in sha Allah ".


Ya faɗi yana mai miƙewa dan zuwa fara shirya kayansa .



Da kallo aka bishi har ya fita .



Karɓan takardan Abie ya yi kana ya ce .


"Allah ya sa shi ne ya fi zama alkhairi ,tunda ba tire shi daga wajan aikin aka yi ma da sauƙi ,in sha Allah ,in ya nitsu komai ya dawo normal zai koma in sha Allah ."


Allah ya sa Daada ya faɗa.



*Washe gari*


Maher ya koma gida bayan ya.


Ya bar su Abie, da kuma kewar masoyiyarsa .



Washe gari shi ma Suraj ya wuce Nigeria ya bar su Abie.



Bayan kwana uku da tafiyarsu Maher , Daada da su Momma suka yanke shawara wuce ƙasar Dubaï siyan kayan ɗakin Nailah ,nan ne Abie yake shaida masa su ma can za su ,dan bikinsu Nihal ya gabato ,dan haka za su je su siya musu kayan daƙi ,daga nan za su badawa Maher kayan laife ,a haka dai suka tattara suka wuce Dubai .



*Kaduna Nigeria*


Maher kwana ɗaya ya yi a Abuja ya dawo Kaduna.



Ranar da ya dawo gida ranar yaci karo da abun haushi ,na ƴar aiki da aka kawowa Safina a matsayin wacca zata dinga musu girki.



Bai yi magana ba sai da ya yi wanka ya canza kaya ya sauko k'asa da niyar cin abinci ya karasa dinning ta zo ta buɗe abincin da niyar zuba masa .


Ya kalli abincin ya ɗago ya kalle ta kana ya ce.



" Waye dafa wannan abincin Safina ?"



"Wannan waca irin
tambaya ce Maher bayan ka fi kowa sanin cewa masu aiki ne suke min girki ."


Haba Safina, ta ya ya kwana da kwanaki bana gida amma ranar da zan dawo ma baza ki tsaya ki dafa min abinci ba ,sai dai ki bawa wancan ƴar figigiyar yarinyar ta yi min girki ."



Ya faɗa bai tsaya jiran ansarta ba ya miƙe.


Kallonsa ta yi kana ta ce.


"Ina kuma zaka .?"


"Inda kika aike ni ."


Yana kaiwa nan ya bar gidan .


Yana barin palon wajan motarsa ya je ya shiga ya kunna, mai gadi ya buɗe masa ƙofa ya ja motarsa ya bar gidan, ya nufi gidansu ,yana zuwa gidansu a waje ya yi parking kana ya fito ya nufi cikin gidan .



Bayan ya shiga ba kowa a palon, zama ya yi ya kwallawa mai aiki kira.


Bayan ta zo ya ce ta kawo masa abinci, da toh ta amsa takoma kitchen ta zubo masa abinci ta kawo masa ,


Karba ya yi ya ɗiba ya kai baki ,yana dandanawa ya ji danɗanon abincin bai masa ba ya ajie abincin ya ɗauki ruwa ya sha ya miƙe ya fita ,



A waje suka haɗu da Suraj ya fito daga ɗayan part ɗin .


"Bro yaushe ka zo?"


"Yanzu na zo kuma tafiya zanyi .


Ya basa amsa.


"Okay, muje na ga Auntyna mu gaisa , duk da bata da mutunci ya faɗa yana mai saƙin murmushi.


"Okay, amma zan biya restored tukun kafin na tafi gidan.


Nan ma dai Suraj ya ce su je.


Fita suka yi ,sai da Maher ya tsaya ya ci abinci .



Bayan sun gama suka fito za su hau mota suka ganshi shi ma zai shiga ciki.


" Wa zan gani kamar Nasir Abbas?"


Maher ya faɗa.


Kallon wajan ya yi yana mai saƙin murmushi kana ya ce.


"Wallahi ni ne Maher wata sabon gani dama kana duniya?"


"Wallahi ina nan kwana deyewa."



"Eh wallahi ka yi aure ba gaiyata sai dai na ji labari a waje ."


Nasir ya faɗa.


"Sorry."


Kawai Maher ya faɗi yana mai shiga mota .


" Ba komai na san gida zaka koma mu je na ga amaryar taka ."


"Okay."



Kawai Maher ya sake faɗi



Shiga motocinsu suka yi suka bar restored ɗin.



*Gidan Maher*



Bayan sun sauko daga cikin mota suka nufi cikin gidan.



Kujera ya nuna musu da su zauna bari ya je ya kira ta ,


Kai suka geɗa kana ya nufi ciki don zuwa kiran Safina.



Zune take tana chat da Suraj yana ce masa yaushe za su haɗu ta ce bata Kaduna ta ɗan yi wata yar tafiya ne amma jibi zata dawo, ya ce Allah ya shi ke nan.


Tana cikin chat da shi ta ji Maher ya shigo.


Da sauƙi ta ɗago ta kalle shi.


"Ki zo ga abokina da ƙanina a palo sun zo ku gaisa ."


Ya faɗa yana kaiwa nan ya juya ya bar ɗakin ya koma palo.


Dubansu ya yi ya ce.



"Yauwa gata nan zuwa ."

Suka amsa da toh.


Bayan fitar Maher miƙewa Safina ta yi ta saka hijab ta fito.


Suna zaune suka ji takun takalmin mutun.


Dagowa Suraj da Nasir suka yi suka zubawa wajan da suke jin takun ido suna jiran su ganta.



Fitowar Safina yake da wuya, Suraj da Nasir ya miƙe .















Alhamdulillah nan na kawo karshen book 1


Sai mun haɗu a book 2 bayan sallah.


Allah ya sa mu fara azumin lafiya mu gama lafiya, ya kuma sa mu yi ibada karbabɓiya Ameen







*Fulalin Jajirtattu ce ✍️*






*More comment more typing ✍️*







Share fisabilillah 👏 my lovely fan's

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login