Showing 12001 words to 15000 words out of 52064 words

Chapter 5 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt

06 Mar 2025

2588

in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️8️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*



A tak'aice dai tun ranar Layla ta koma hannun 'yan fulani.


Su kuwa Alhaji Mai Nasara ba su suka tuna da Layla ba sai da suka gama fita dajin da suke gaba ɗaya suka shiga gari,lokacin dare ya yi dan har an yi i'sha ma.


Suna ganin hasken fitilu can gaba da su kaɗan suka sauke ajiyar zuciya a tare.


Kallon Hajiya Sumayya Alhaji Mai Nasara ya yi kana ya ce "Alhamdulillah! Ga wani gari can mu karasa sai mu samu inda zamu huta kafin safe mu ga abunda Allah zai yi."



Alhaji Mai Nasara ya yi maganar,yana mai yin gaba.



Kallon Alhaji Mai Nasara Hajiya Sumayya ta yi kana ta ce"Alhaji ina Layla take.?"



Ai Alhaji Mai Nasara na jin haka ya dakatar da tafiyan da ya fara yi, ya juya ya kalli Hajiya Sumayya haɗe da juyowa ya kara dawowa inda take,kana ya ce" Ban gane ba Hajiya,kina nufin kin bar min ƴata a can.?"



Ba tare da ta bawa Alhaji Mai Nasara amsa ba ta fashe da kuka,cikin kuka take faɗin" Wayyo Allah na ƴata Alhaji na bar ƴata a hannun fulali Alhaji zan koma na je ta karɓo ƴata."


Ta faɗi haɗe da juyawa ta fara tafiya da niyar koma wa wajan da suka baro.



Da sauri Alhaji Mai Nasara ya sha gabanta haɗe da riƙo hannunta, ɗan kallon ɗan kallon Alhaji Mai Nasara Hajiya Sumayya ta yi kana ta ce "Please Alhaji ka sake ni na koma na je na d'auko ƴata,bazan iya barta a hannun wasu ba, gashi ko yayeta ban yi ba."



"Ba inda za ki dear, kawai ki zo mu karasa cikin wancan garin da nake gani mu zauna,in mun zauna mun nitsu sai mu nemo mafita, amma komawarki can a wannan lokacin ba shine mafita ba sai dai mu kara jefo kanmu cikin wata matsalar daban,



Saboda kina gani d'azu ma waɗan da muka ga ni a can,amma shine za ki wani cewa za ki koma ?


Zo mu je."

Ya faɗi yana mai kamo hannunta kana ya ja ta suka bar wajan.


Bayan sun karasa cikin garin da basu san ko wana gari ba,dan karamin gari ne.


Wani bishiya ya gani suka karasa wajan suna shirin zama sai Alhaji Mai Nasara ya hango wani masallaci, ɗan kallon Hajiya Sumayya da take shirin zama ya yi kana ya ce "My dear taso muje wancan masallacin zai fi nan tsaro."


Kai ta geɗa cikin sanyin jiki ta kara miƙewan ɗauke da ƴarta.


Kallonta ya yi lokaci ɗaya wani tausayinta ya kama shi sosai.


Hannu ya sa ya karɓo babyn ya riƙe mata kana ya kamo hannunta ita ma suka nufi masallacin.



Bayan sun karasa mallacin ta cikin masallacin akwai bangaren mata ya ce ta shiga ta yi alwala ta yi sallah,kai kawai ta geɗa masa kana ta karbi Baby Naila ta shiga ciki.



Shi kuma ya nufi cikin masallaci.


Sallah ya yi,ita ma ta yi sallah bangaren mata.


Bayan ya idar da sallah ya fito ya nufi inda ya ga wata mai saida ƙosai da koko can gaba da masallacin ya karasa,kallon Alhaji Mai Nasara mai saida ƙosai ta yi,suna haɗa ido da Alhaji Mai Nasara mai ƙosai ta tashi daga kan kujerar da take zaune ta ta durƙusa har k'asa ta shiga gaida Alhaji Mai Nasara.



Cikin sakin fuska Mai Nasara ya amsa ,ga kuma mamakin da yake yi a cikin zuciyarsa.


Dan bai d'auka akwai waɗanda suka san shi a cikin wannan k'auyen ba.



"Tashi ƙosai nake so."


Alhaji Mai Nasara ya faɗi yana kallon matar.


Cikin mamaki Mai ƙosai ta shiga kallon Alhaji Mai Nasara dan ta tabbata mutun kamar Alhaji Mai Nasara bazai ci ƙosai irin nasu ba.


Kamar Alhaji Mai Nasara ya san tunanin da take ya ce " Karki yi mamaki ni ba irin waɗannan mutanan da kika sani ba ne,


Kawai matsala ta ɗaya bani da kuɗi a inda nake, sakamak'on wasu 'yan fashi da suka kamamu a hanya dan daƙer ni da matata muka tsira,

Saboda sauran ɗuk suna can."


Wani bawan Allah ne da yake zaune can gefe yana cin ƙosai ne ya yi magana kamar haka.



" Ko dai su ne waɗanda na ga an kama a can wajan gonan nakin nan dama can ne yawanci suke ɓuya."



Ai Alhaji Mai Nasara na jin haka da tsauri ya karaso inda wannan bawan Allan yake zaune kana ya kallesa ya ce "Tabbas nan wajan,amma a ina kaga ni.?"


"Wallahi a TV gidanmu na gani d'azun nan an nuno."



"Na tabbata tunda har an haska a TV toh baza'a rasa ganin shi a social media ba."


"Tabbas Alhaji."


Ɗan saurayin ya sake fada.

"Please kana da data a wayarka.?"


Alhaji Mai Nasara ya sake tambayar saurayin.


"Eh ina da shi Alhaji amma bashi deyewa sosai ,500mb ne kawai na siya d'azu."



"Please bani wayanka na gani zan baka ka siyo wata."


Da toh ɗan saurayin ya amsa,kana ya kunna data ya miƙawa Mai Nasara waya.

Karɓa Mai Nasara ya yi kana ya shiga YouTube ya shiga duba wa.


Ai kuwa yana cikin duba wa ya gan shi.


Kunnawa ya yi ya shiga kalla.


Tun lokacin da aka kama su aka saka su a cikin mota har i zuwa sanda aka kira ambulance aka kwashe Usman da amaryarsa aka tafi da su asibiti,dama police tension d'in da aka kaisu duka an nuno.


Ba tare da ya karasa kallon sauran ba ya kashe masa datansa.


Daga jannunsa sama ya yi ya shiga yi wa Allah godiya,


Bayan ya kammala miƙa godiyarsa ga Allah,ya sake duba wayan da ke hannunsa,wata number ya saka ya danna kira,ana ɗagawa ya faɗa masa shine haɗe da cewa gobe a turo masa mota bayan ya tambayi mutan wajan sunan garin da suke ya faɗawa yaronsa kana ya katse wayan.


A jiyar zuciya ya sauke kana ya danna number Usman sai da ya kusa sinkewa sannan aka d'auka.



"Usman ne ?".

"Eh ni ne,kamar muryar abokina nake ji ?"


"Tabbas ni ne Usman."


Cikin dauriya Usman ya miƙe zaune daga kan dagon asibitin da yake kwance,ya kalli gefensa inda amaryarsa take kwance sai girgiza kai take tana runtse ido kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa ba karamin azaba take sha ba,saboda yanayin yanda take girgiza kainta tana cize labe.


Ba dan komai ya sa aka haɗa su ɗaki daya ba, Usman ne ya nemi haka.


Wani irin cize labe ya yi a lolacin da ya gama kallonta.


Kana ya ci gaba da yin magana " Amma Mai Nasara kana kuna ina aka nemeku aka rasa,yanzu haka ma 'yan sanda da sojojin da suka taimake mu suna neman ku."


Baki ya buɗe da niyar faɗawa Usman inda suke sai kati ya kare,gajeran tsaki ya ja,kana ya shiga kallon wayan,dan shi tunda yake kati bai taba karewa a wayarsa ba, in yana waya,saboda kullun yake sakawa ko bai kare ba,dan a yanzu haka ba yana da kati a cikin wayarsa da 'yan fashi suka karbe kusan na 50k



Wannan saurayin kamar ya san tunanin da Alhaji Mai Nasara yake yi,ya ce "Alhaji ka yi haƙuri kuɗin dama nera amsin ce kawai a ciki,na ma yi mamaki da na ga ka kira har mutun biyu bai kare ba."



Murmushi Alhaji Mai Nasara ya saki kana ya shiga miƙawa saurayin wayarsa.


Yana cikin miƙa masa sai Kiran Usman ya shiga wayar.



Ai da sauri ya ɗaga yana mai faɗin "Sorry Usman wallahi kuɗin wayar ce ta kare."



"Allah sarki ba komai,yauwa ya sunan garin da kuke?".


Faɗa masa sunan garin ya yi ɗuk da bai san ƙauyen ba amma ya ce zai faɗawa 'yan sandan gobe a zo a dauke su.


Godiya Alhaji Mai Nasara ya yi wa Usman,kana suka yi sallama ya katse wayan.



Miƙawa saurayin wayarsa ya yi haɗe da yi masa godiya.


Hannu ya zira cikin aljihun wandonsa da niyar d'auko agogonsa dake ciki da ya saka d'azu a Gombe da ya tashi yin alwala.



Yana zira hannunsa ciki zai dauki agogon sai yaji banɗir ɗin kuɗi a ciki.


Fito da su ya yi harda agogon,yana mai cewa "Ashe jiya ba ɗuka kuɗin na yi liƙi ba, akwai ragowa."


Ya faɗa yana mai sakin Murmushi kana ya tire dubu biƴu ya miƙawa mai kosai ya ce ta bashi kosai na dubu ɗaya da koko na dubu ɗaya.


Cikin murna mai kosai ta amshi kuɗin ta zubawa Alhaji Mai Nasara kosai da koko na 1k ,1k kana ta miƙa masa,


Karban kosan ya yi kana ya tire dubu biƴu ya miƙawa wannan saurayin da ya yi waya da wayarsa.


Cikin murna saurayi ya karbi kuɗin haɗe da yin godiya.


Bayan ya karbi number saurin ya ce zai nemeshi,in sha Allah idan ya koma gida,kana ya juya ya bar wajan ya nufi cikin masallacin bangaren mata ya shiga ya miƙawa Hajiya Sumayya kosai da kokon kana ya faɗa mata wannan labarin mai dad'in da ya samu akan kama 'yan fashin nan da aka yi,ta yi murna sosai.


Bayan ya gama faɗa masa ya kara da cewa gobe 'yan sandan zasu zo su ɗauke su.


Ta yi murna sosai da jin haka,


Yana gama faɗa mata ya yi mata sallama ya wuce bangaren maza.



Washe gari kamar yanda Usman ya faɗa hakan kuwa ta kasan ce,dan bai fi karfe 10 am aka zo aka dauke su.

Da suka fita daga cikin garin nan ne Alhaji Mai Nasara yake shaida wa 'yan sanda batar ƴar su Layla nan suka yanke shawaran zuwa garin,sai dai ina sam basu gane wajan ba,jiki babu ƙwari suka bar wajan.


Hajiya Sumayya kam kuka kawai take yi.


Gombe suka koma suka je suka duba Usman da amaryarsa haɗe da yi masa jajen abunda ya faru nan ne suka sanar masa da maganar batar ƴar su Layla shi ma ya taya su jaje.


Kasan cewar masu kuɗi ne ya sa suka yanke shawara tafiya kasar wajan,a duba kafar Usman dama matarsa duka.


Babu bata lokaci suka nemi jirgi suka tafi tare da 'yan uwansu guda biƴu.


Na bangaren Usman dana bangaren amaryarsa.


Shi kawunsa ne,ita kuma amarya Ƙanwar mahaifiyarta ce.


Sai da suka tafi su ma su Alhaji Mai Nasara lokacin ya samu Security's ba tare da bata lokaci ba suka koma (Kano)suna zuwa (Kano)darek airport suka wuce ba tare da sun koma gidan su Usman ba, suna zuwa babu ɓata lokaci suka samu jirgin da zai kaisu (Kaduna) nan take suka hau sai (Kaduna)



*Bayan wani lokaci*


Bayan sun koma (Kaduna) kuka sosai aka yi akan batar Layla,tun suna zuwa nemanta har suka haƙura suka barwa Allah.


Haka ma bangaren Hajiya Sumayya ita ma ta miƙa lamuranta ga Allah.



Su Usman da amaryarsa kuwa sun warke garau,daga kasar America suka wuce (Dubai)su kawu da ƙanwar mahaifiyar amarya ɗuk an samo musu jirgi sun koma Nigeria.


Komai ya wuce a wajan Usman da amarya ɗuk da abun da ya faru da wuya su manta ta cikin sauki,amma Alhamdulillah!.


Sai da suka sha amarcinsu sosai kafin su dawo gida Nigeria.



A haka rayuwa taci gaba da tafiya har Naila ta yi girma ta zama budurwa ba'a sake ganin Layla ba, ba'a kuma san inda take ba.


Kuma ko sau ɗaya ba'a taba faɗawa Naila wannan labarin ba.


Dan a tunaninta ta dauka ita kaɗai iyayenta suka haifa,bata taba sanin cewa ita 'yan ɓiyu ce ba.



Amma sai dai abun mamaki lokaci zuwa lokaci takan yi mafarkin Layla.


Ikon ubangiji kenan.


Wannan shine labarin Naila da iyayenta.



Ɗagowa Hajiya Sumayya ta yi idonta ya yi jahur saboda kukan da ta yi,dan ɓatar Layla ya dawo mata sabuwa.





*More comment more typing ✍️*




Allah in bakuwa comment sosai zan rage yawan typing 🙄



Dan haka ina son naga ruwan comment da zai tashi kaina 🥹




Sharen fisabilillah 👏





*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*
[21/01, 11:37] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V

________________________________________________


Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ


________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*


*Gargaɗi*

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️9️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*


Rungume mahaifiyata na yi,cikin sanyin murya na ce "Sorry Momma, Allah sarki sis ko kina ina haka? Allah ya sa muna da rabon ganin juna kafin Allah ya ɗauki ran ɗaya daga cikin mu."



Na faɗi cikin wani irin yanayi.


"Me haka Mamana? Kar na kara jin irin wannan maganar ya fito daga bakinki,in sha Allah! za ku haɗu kuma ku rayu tare."



"Allah ya sa Momma."

Naila ta kara faɗi.


Ameen Hajiya Sumayya ta amsa.


Kana ta ce.

Maza tashi ki shiga ki yi wanka da brosh ki zo ki yi breakfast,in kuma a ɗaki za ki yi sai na saka Asiya ta kawo miki."



Asiya ƴar aikin su ce.

"Noo Momma ta kawo min tea kawai ina da lecture wajan 2am bari nayi sauri na shirya na wuce in kin fita ki faɗawa Asiya ta faɗawa Ado ya wanke min motata please."



Shi ke nan za'a kawo miki tea ɗin da bread dan bazai yu ki sha iya tea kawai ba,bayan fita za ki yi,kuma na tabbata acan d'in ma in kin je ba zuwa za ki yi ki siyo abunda za ki ci ba,

Maganar wanke mota kuma ba jiya -jiyan nan aka wanke miki ba,wana irin wankewa za'a yi yau kuma.?"



Ɗan turo baki na yi gama kana ina mai cewa "Haba Mommana, Allah motan ta yi ƙura please ka faɗa masa ya wanke min."



"Ke! ungo nan baza'a faɗa masa ba,an gaya miki bashi da aikin yi ne irin ki ?"


Ni dai dan Allah Momma ki faɗa masa, ai aikinsa ne, kuma ana bashi albashi dan haka ni banga wani aibu ba anan dan na ce ya wanke min mota."


"Toh babu wani mota da za'a wanke yau in za ki shiga ki yi wanka ki shiga in kuma ba za ki shiga ba ki zauna."


Hajiya Sumayya ta faɗi haɗe da miƙewa ta yi bakin kofar fita ɗakin.



Da kallo na bi bayan Mommana har ta fita,baki na turo gaba haɗe da juyowa na nufi toilet don yin wanka.



*Maher*



Yana fita gidan wani abokinsa ya nufa.


Kafin ya karaso ya kirasa a waya dan tabbatar in yana gida kar ya je bai sameshi ba.


Nan ne ya kirasa ya tabbaye shi yana gida?ya ce yana nan,ya ce gashi nan zuwa.


Da yake gidan abokinsa babu nesa da gidansa sosai ne ya sa bai fi mintuna15 biyar ba ya karasa ƙofar gidan, parking ya yi a waje dan ba wani daɗe wa zai yi ba,ya buɗe murfin motar ya nufi karamin gate ɗin gidan, nocking ya yi mai gadi ya zo ya buɗe.


Gaida shi ya yi Maher ya amsa can ƙasar maƙoshisa,


Dan yanayin yanda ya amsa ɗin ma na tabbata mai gadi bai ji ba.


Mai gadi kuwa da ido ya bi bayan sa har ya shige cikin gidan.


A bakin kofar palon ya tsaya ya yi nocking babu jimawa aka zo aka buɗe.


Wani matashin saurayine wanda kan su zai yi ɗaya da Maher,dan bazai wuce sheraku 35 haka ba shi ma kamar Maher ɗin.


Haba Maher wai kai ɗuk sanda ka zo gidan nan kamar wani baƙo ka wani tsaya a waje kana nocking maimakon ka shiga ciki kai tsaye?."


Isham ya faɗa.

Saboda ban da hankali ina zuwa gidan mutane na antayo ciki babu neman izini ko wani abu,kasan dai hakan ba daidai bane,kuma wannan tsarin sam ba tsari ba ne,na san me kake yi a ciki tare da Madam ne da zan antayo muku babu neman izini, toh ni ba haka nake ba."


Maher ya yi maganar,fuska a haɗe kamar bai taɓa yin dariya ba.



"Toh na ji Ustaz,mu shiga daga ciki toh."


Isham bai tsaya jiran amsar Maher ba ya kamo hannunsa suka shiga cikin.


*Bangaren Safina*


Ba ita ta tashi daga bacci ba sai wajan 1am ta ta shi,wanka da brosh ta shiga ta yi ta fito ta shirya cikin riga mara nauyi ta saka wula a kanta,kana ta fito palon don yin breakfast,dan tama manta sa cewa Nadia bata nan.



Tana fita palo ta kalli dinning table taga wayam ba komai.

"Kutumar uban can ashe yarinyar nan bata nan, alkur'an in kin dawo gidan nan sai na koreki kuma yau -yau ɗin nan zan nemo wata bazan iya ba."



Ta faɗa kana ta juyowa fuuu kamar zata tashi sama ta wuce kitchen.


Yanzu ma dai indomin ta kuma defawa ta haɗa tea mai kauri ta dawo palon ta zauna ƙasar carpet ɗin ta soma ci.


Bayan ta gama ta mike ta koma ɗakinta,plate kuwa a inda ta ci nan ta bar ta ta wuce ɗaki.



Wayarta ja ta dannawa wata number kira,ana ɗagawa ta fara magana kamar haka.


"Hajiya ina wuni ya gida."


Ta can bangaren Hajiya dake zaune a ɗakinta ta saƙi murmushi haɗe da cewa "Lafiya lau Alhamdulillah! Safina ya kuke?"


"Wallahi Hajiya muna lafiya,dama jiya ƴar aikina ce ta tafi bata sanar min ba,kuma ban san inda ta tafi ba,shine take so in ba damuwa ki yiwa wannan matar magana ta kawo min wata yau in ba'a samu yau ba ko gobe haka."



"Shi ke nan zan yi mata magana,amma gaskiya yau lokaci ya kure da a ce tun safe kika kina ni ma da sauki amma yanzu kam ko na kira baza'a kawo miki yau ba sai zuwa gobe idan Allah ya kaimu."

"Toh ba damuwa Allah ya kaimu goben."

Hajiya ta amsa da ameen kana ta ce.


"Amma Safina ina wancan mai aikin ta tafi.?"


"Wallahi Hajiya ban san inda ta tafi ba,ni dai fita na yi na dawo gida na tarar bata nan,


Na nemeta sama ko kasa banganta ba."


"Okay shi ke nan,sai an kawo miki goben,bari na kashe."


"Toh shi ke nan Hajiya na gode sosai."


Hajiya bata ce komai ba ta katse wayan.


Bayan ta kammala waya da Hajiya kwanciya ta yi akan gado ta kunna data ta shiga yin chat da samarinta.


Saƙo na farko da ta ci karo da shi shine na Nas,shiga ciki ta yi ta shiga karantawa,


My love na gode sosai,kin ciyar da ni dadi ina sonki sosai,kuma na yi miki alkawari ɗuk wiya ɗuk rantsi ina tare da ke,bazan taba rabuwa dake ba.



Wannan sakon na jiya ne.


Sai kuma wata ta kara gani da ya tura mata d'azu da safe kamar haka.


My love,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login