Showing 48001 words to 51000 words out of 52064 words
Chapter 17 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt
ina kyautata zato babu abunda zai samu na shi auren in sha Allah! dan haka kawai ka bashi taba ya je Nigeria ya samu ya yi magana da yarinya ,ya ganta a zahiri ta ma ta ganshi a zahiri ,su ƙara tatt'aunawa akan maganar auren ,daga nan kai ma sai ka yi bincike in ka ga ƴar gidan mutunci ce sai a yi komai a gaba ,in suna so ma ko nan da wata daya ma za'a iya d'aura musu aure ya ɗauki matarsa su tafi tunda can ne yake aiki .“
Ajiyar zuciya Abie ya sauke kana ya buɗe baki ya ce .
" Toh shi ke nan, in sha Allah! Hakan za'a yi , Allah ya tabbatar da alkhairi ."
Dukansu suka amsa da Ameen .
Kana Abie ya sauya magana zuwa na Maher .
Kallon Maher dake ta faman satar kallon Nailah ya yi, kana ya juya ya kalli Alhaji Mai Nasara ya ga shi ma idonsa akan Maher yake .
Kara juyowa Alhaji Aminu ya yi ya sake kallon Maher a karo na biyu kana ya buɗe baki ya soma magana .
" Maher! Maher!! ."
Alhaji Aminu ya kira Maher , kiran farko da ya yi masa bai ji ba ,sai a na biyu ya ji ya ɗago yana sunna kai ƙasa haɗe da buɗe baki ya amsa .
" Na'am Abie ."
"Kai! ma ya maganar da grandpa ɗinka da ya yi a wancan watan da ta wuce ,ka ce a baka wata biyu zaka gyara ta ,ta canza d'in né ko ya ya ?"
Baki ya buɗe da niyar yin bawa Abie amsa sai ya dakatar da shi ta hanyar cewa .
"Ko ta yake ba sai ka bani amsa ba ,dan jikinka ya riga da ya bani amsa ,kuma tunda na zo nan ina karantar yanayinka ,kallo ɗaya za'a maka a fahimci cewa kana cikin damuwa, kuma abokin aikinka ya same ni shekaranjiya ya faɗa min sanadiyar damuwar da kake ciki saura ƙiris ka kashe al'umma ."
"Subhanallah! Al'umma fa kace Alhaji Aminu ?"
Alhaji Mai Nasara ya tambaya .
Kallon Alhaji Mai Nasara Abie ya yi kana ya ce .
"Kwarai kuwa al'umma , saboda ka san tsarai ɗuk sanda wannan jirgin ya faɗi mutane deyewa za su iya rasa rayukansu ,dan ba iya mutanan jirgi kaɗai za su mutu ba ,har waɗan da basa ciki ma ."
"Sabbas haka ne ,
Amma ɗana wannan wana irin damuwa ce take damunka har haka ka kasa magance shi, kake so ka kashe kanka da al'umma ?"
Alhaji Mai Nasara ya tambayi Maher .
Maher bai yi magana ba ,
Alhaji Aminu ne ya ce .
" Matarsa ce take so ta kashe min shi tun lokacin mutuwarsa bai yi ba ."
Alhaji Aminu ya faɗa cikin takaici da ba'kin ciki .
Tunda suka fara magana nake jin su, jikina ya yi sanyi sosai ,ga kuma abunda na tuna a baya ,
"Tabbas laifina ne ."
Na faɗa cikin raina ina mai fashewa da kuka .
Abunda ban sani ba, shi ne,a she maganar zuci da na yi ,ya fito fili.
"Laifin ki kuma ƴata?"
Alhaji Aminu ya faɗi .
Da sauki na dago na kallesa ,irin yana yin kallon da yake min ne, ya tabbatar min da cewa maganar da na yi a cikin zuciyata ta fito fili .
Ba tare da na masa ba na miƙe cikin kuka na bar wajan ,ina jin suna kira na, amma ko waiwayowa ban yi ba ,ballantana a sa ran juyowa ta .
Kallon su Nihal Abie ya yi kana ya ce .
"Maza ku tashi ku bi bayanta ."
Kai suka geɗa kana suka miƙe suka bi bayan Nailah da sauri .
Bayan tafiyar su Nailah kallon Hajiya Sumayya ya yi kana ya ce .
"Hajiya ko kin san dalilin da ya sa Nailah ta ce laifinta ne ? "
" A'a Alhaji ni ma bansani ba ,dan ka san Nailah da zurfin ciki,
Wata rana ko na ganta cikin damuwa ko wani abu ma in na tambayeta cewa take ba komai ."
"Okay! shi ke nan ,ki samu anjima ki same ta ki tambaye ta ."
"Toh Alhaji in sha Allah! zan yi hakan."
Hajiya Sumayya ta sake faɗi .
Kallon Maher Alhaji Aminu ya yi kana ya ce .
"Maher jinina ya na bani cewa ka san dalilin kukan Nailah , dan haka ka faɗa min ."
Miƙewa Maher ya yi kana ya kalli Abie ya ce .
" Abie ku tambaye ta ita zata gaya muku dalili, dan ni ban san komai ba ."
Yana kaiwa nan shi ma ya juya ya bar wajan .
Ganin ya tafi ne ,ya sa Alhaji Mai Nasara cewa.
" Ai mu ma mun gama ,mu tashi mu tafi kawai ."
Kai ɗuk suka geɗa haɗe da miƙewa ,bayan an umarci Suraj da ya biya sai ya same su a waje ,ya amsa da toh ,su kuma suka juya suka fita .
*Nailah*
Ina fita na tari taxi ina koƙarin shiga su Nihal suka kara so ,ba tare da na kalle su ba ,na shiga motar su ma babu ɓata lokaci suka antaya cikin motar .
Sai da muka ɗan yi tafiya kaɗan kafin mai taxi ya tambayi inda zamu .
Ban yi magana ba , Nihilah ce ta faɗa masa .
Bayan mun iso na sauka na miƙawa mai taxi kuɗinsa kana na yi ciki .
Su ma suka mara min baya .
Muna shiga cikin ɗakinmu na samu waje na zauna kana na yi shiru .
Su ma su Nihilah kara sowa suka yi suka nemi waje suka zauna, kana Nihilah ta shiga tambaya ta .
" Friend me yake damunki ne .?"
"Babu ."
Na bata amsa .
"Ina akwai wallahi! Dan haka kawai ba za ki yi kuka ba ."
"Ku bamu waje mu yi magana ."
Suka ji an faɗa a bayansu .
Ɗuk juyowa suka yi suka kalli wajan ,a cikin kuwa hadda ni .
Maher ne tsaye a bakin kofar shiga ɗakin ya harɗe hannayensa biyu yana kallon su .
Miƙewa Nihilah da Nihal suka yi suka fita suka bar ɗakin .
Bayan fitar su ya maida kofar ya rufe kana ya karasa wajan da take ya zauna ya fara magana kamar haka .
"Nailah!"
Ba tare da na amsa ba ,na fashe da kuka ,kamar wanda yake jira .
Cikin kuka nake faɗin .
"Please i'm sorry, wallahi ban kyauta maka ba , dan na tabbata da a ce wancan lokacin ban yi maka wulakanci ba da ni ce a matsayin matarka a yanzu ba ƙawata Safina ba ,dan Allah! ka yi hakuri ka yafe min ."
Baki ya buɗe da niyar yin magana suka ji magana a bayansu an ce .
"Ai dama na san da akwai wani abu a ƙasa dan haka kawai ba za ta yi kuka ba ."
Alhaji Aminu ya faɗa ,
Juyowa ɗuk suka yi, suka ga gaba dayansu ne .
Abie, Daada Mommy Momma da su Nihal tsaye suna kallon su .
Karasowa ɗakin duƙ suka yi, suka nemo waje suka zauna .
Yauwa muna jinku , yanzu sai ku faɗa mana sauran maganar dan ba ɗuka muka ji ba ."
Cewar Momma take kallon Nailah ,da kanta yake a sunkuye .
"Shi ke nan ,kai Maher sai ka faɗa mana ,kuma kar ka kuskura wannan karon ka ce min baka san komai ba ,dan in ka faɗi hakan zan yi mummunar saɓa maka ."
Kai Maher ya geɗa kana ya fara magana .
*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*
*More comment more typing ✍️*
Share fisabilillah 👏my lovely fan's 🥰
[01/03, 09:26] Sakinaabubakar120: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭
Story & Written ✍️
By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)
________________________________________________
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
________________________________________________
Page ▶️3️⃣0️⃣
*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*
Kai Maher ya geɗa kana ya fara magana .
*Shekara ɗaya da suka wuce*
Abokina Kamal ya kawo min ziyara gida ,bayan na raka shi zai hau motarsa ya tafi gida ne ,ya yi, ya yi ya tashi motar amma yaƙi ,a karshe dai ni ne na koma ciki na d'auko key ɗin motana na kai shi .
Toh muna hanyar maida shi gida ne ya ce mu biyo wata unguwa wajan wani Malamin shi mu yi gaisuwa ,da farko na ce masa mazan je unguwar ba ,sai daga baya da ya lallaɓa ni sannan na yarda na raka shi unguwar ,bayan mun yi gaisuwa muka fito da niyar hawa mota ,idona ya sauka akan 'yan mata ɓiyu sun fito daga gidan ,ban d'auka akwai ƴar gidan a cikin su ba ,dan dukansu ba su yi kama da ƴaƴan talakawa ba ,ba tare da na damu ba na yi gaba kuma dama can nesa da gidan kaɗan muka yi parking ɗin motarmu .
Sanda idona ya sauka akan dayar 'yan matan wacca bata da jiki sosai ,lokaci ɗaya na ji soyayyarta ta shiga cikin zuciyata ,ba tare da ɓata lokaci ba na karaso inda suke da sauri ,dan dayan tana koƙarin shiga mota .
Saurin karasowa wajan na yi na kama murfin motar na rik'e .
Dagowa ta yi ta kalle ni daga sama har k'asa ,kana ta soma magana cikin masifa
" Malam lafiya ka rik'e min murfin mota .?"
Murmushi na sakar mata ,wanda da wuya yan mata su name shi a wajena ,dan ba kasafai nake murmushin ba .
Sai da na sakar mata Murmushi tukun kafin na buɗe baki na soma magana .
" Sorry, na rik'e miki murfin mota ,magana ce mai mahimmanci nake so mu yi, dan Allah ki taimaka ki bani ko da minti ɗaya ne ,na faɗi abunda ke cikin zuciyata ."
Dan guntun murmushi ta yi kana ta ce .
" Ba sai ka wahalar da bakinka ba ,na san bai wuce ka ce kana so na ba ."
Murmushi na sake saƙi kana na ce .
" Wallahi kamar kin san abunda nake son faɗa ,dan Allah ki....
Bai karasa ba ta dakatar da shi ta hanyar faɗin .
"Kaga Malam ,karka wahalar da zuciyarka ,ni bana sonka baka yi min ba sam ,dan haka ka sakar min mota na tafi ."
Kamal da tun dazu bai yi magana ba ne ya ce.
"Haba baiwar Allah! Ta ya ya kamar Maher ki ce bai miki ba ,bayan ƴan mata deyewa suna son shi yaƙi amincewa da su sai ke ,wallahi tunda nake da Maher ban taɓa ganin ya yi wa wata ƴa mace magana ba sai ke ."
Taɓe baki Nailah ta yi kana ta ce .
" Toh ka sani shawara ya koma wajansu ya zabi ɗaya daga cikin su ,dan su ne suka dace da shi ba ni ba ."
Tana kaiwa nan ta fisge murfin motarta ta faɗa ciki ,ta kunna ta ja shi da karfi ta bar wajan ,ko sallama ba ta yi wa ƙawarta ba .
Abunda Nailah ta yi wa Maher ba karamin ɓata ran Maher abun ya yi ba .
Safina da tun lokacin da suka fara magana bata tanka ba ne ta tanka .
Cikin kwantar da murya ta kalli Maher haɗe da cewa .
"Dan Allah bawan Allah ka yi hakuri, ni ban san me ke damun Nailah ba, sam bata son samari su raɓe ta, Kamar mai aljanu ."
Maher da tun da ta fara magana bai kalleta ba ne ya kalleta .
Lokaci ɗaya ya saki murmushi, kana ya buɗe baki ya ce .
" Na yi miki kina so na ?"
"Haba yellabaï, wa zai ga saurayi irin ka ya ce baka yi mata ba ?"
"Allah ko?"
Maher ya faɗa.
"Sosai ma kuwa, dan ita kanta kawar tawa na yi mamaki da ta kasa karban ka a matsayin masoyi ."
"Okay yanzu sauri nake yi , sa min numberki ."
Karɓan wayar Maher dake miƙa masa Safina ta yi kana ta saka wa Maher number d'inta .
Bayan ta gama saka masa number d'inta miƙa masa wayarsa ta yi ,kana ya yi mata sallama suka shiga motarsu suka bar layin nasu .
Cikin farin ciki Safina ta juya ta koma cikin gidansu .
Tun kafin ta karasa cikin gidan nasu ta shiga kwallawa Innarta kira .
" Inna! Inna!! Wai kina ina ne ? Ki fito na samo miki labari mai dad'i ."
Haka take faɗi har ta shiga cikin gidan ,ganin Innarta bata fito ba ne ya sata nufar cikin ɗakin , 'yan zaman makoki dake zaune a tsakar gida suka bita da kallon mamaki har ta shige cikin ɗakin nasu .
Babu sallama ta shiga cikin ɗakin nasu ,ta kalli Innarta dake zaune cikin ƴar karamin ɗakin nasu , wanda bata da girma sosai, shi ya sa mutanan dake ciki suke ta faman share gumi lokaci zuwa lokaci , ɗuk da fifitar da suke yi da mafici bai hana su jin zafi ba .
Kallon Safina Inna ta yi ,cikin takaici ta buɗe baki ta ce .
"Ke! yanzu Safina kina da hankali kuwa ? Ta ya ya za ki shigo ɗaki babu ko sallama kuma kina ganin mutane a ciki ."
"Haba Inna farin ciki ne ya sa na manta sallamar ."
"Okay na ji, farin cikin me kike yi ? Bayan kina ganin jiya- jiyan nan Allah ya yi wa yayanki rasuwa ."
" Toh shi ke nan Inna tunda bakya son labarin da na kawo miki na bari ."
Ta faɗa tana mai miƙewa .
Kallon ta Inna ta yi kana ta ce .
"Shi ke nan, koma ki zauna ki faɗa min dalilin murnar taki ."
Washe baki Safina ta yi kana ta koma ta zauna ta fara bata labarin yanda suka yi da Maher da kuma numberta da ya karɓa ya ce zai kira ,har da yanayin haduwarsa da irin motar da yake hawa ,da kuma irin wayar da yake rik'ewa .
Bayan ta kammata bawa mahaifiyarta labarin ta ɗago ta kalli ɗakinsu daga sama har k'asa ,kana ta kalli mahaifiyarta ta ce .
" Kin ga Inna in har na samu na aurin wannan bawan Allah ,kakata ta yanke saƙa wallahi ,dan daga gani in na shiga gidansa zan huta ,
In sha Allah na kusa tafiya na bar muku wannan kurkukub d'in naku ."
Salati Inna ta hau yi , haɗe da tafa hannu ,sai da ta gama salatin tukun kafin ta ce .
" Anya Safina kina jin tsoron Allah kuwa ?
Anya lokacin da na haifo ki asibi ba canza min ƴa aka yi ba kuwa ?
Dan sam halayenki basu kama da na 'yan gidan nan ba .
" Haba Inna ta ya ya za ki dinga fada haka ....
A haka dai ranar Safina ta wuni tana shirme kala -kala .
*Maher*
Kallonsa Kamal ya yi kana ya ce .
"Maher ya na ga ka karɓi number ƙawarta ?"
" Eh da ita zan rama abunda waccan yarinyar ta yi min ,dan raina ba karamin ɓaci ya yi ba ,ba dan bana taɓa cikin mace ba ,da wallahi na wanka mata lafiyayyan mari a lokacin da take min rashin kunya ."
" Toh yanzu da ka ɗauki number kawarta me zaka yi da shi ,kuma ta ya ya zaka rama abunda wancan din ta yi miki ?".
"Aurenta zan yi ."
"Ƙawar?"
"Ƙwarai ma kuwa ."
"Toh kana sonta ne da kake son auren ta ?"
"Ko bana son ta zan aure ta ,dan na tabbata in ta shiga gidana zan fara son ta."
Jinjina kai kawai Kamal ya yi , bai kara cewa komai ba har suka karasa ƙofar gidansu , Maher ya sauke sa ya tafi ,bayan ba yanda baiyi da shi ya shiga ba ,ya ce shi sauri yake bazai shiga ba ,da haka dai Kamal ya kyale Maher ya tafi .
*Bayan uku*
Maher ya saba da Safina sosai , Safina ta faɗa soyayyar Maher , ɗuk da Mahe har yanzu baya jin komai game da ita amma yana biye mata su sha hira ,
A haka dai aka je gidansu Safina aka nemawa Maher auren Safina ,ba dan komai ya sa Abie ya yedda da Maher ya auri Safina ba ,sai don mahaifinta ,dan yana da kirki da mutunci, kuma ya san hakan ma yarta ,
Wannan dalilin ne ya sa ya yedda ,
Bayan wata ɓiyar aka d'aura auren Safina da Mahe suka tare a gidansu mai kyau .
a lokacin da Safina ta je ta sanar wa da Nailah aurenta dama wanda zata aura ,sosai ta taya ta murna , dan ita tama manta da wani Maher sai da Safina ta tuna mata ,
Tare da ita aka yi komai na shirye shiryen bikin Safina ,dan kayan daƙi da akawa Safina ma ita ta faɗawa mahaifinta ta yi mata kayan daƙi da kujeru .
Ranar da aka daura auren Safina ta ce kai amarya ,toh tun ranar dai bata kara zuwa gidan Safina ba .
Ƙannen Safina sun sha zuwa , amma wulakanci kala -kala Safina take musu ,in sun zo ta hana su zama akan kujera ta ce kar su shafa mata talauci ,wannan dalilin ne da ya sa yaran suka dena zuwa ,
Ita da Mahe kuwa ,bai fi wata biyu da aure ba suka soma samun saɓani ,
Saboda da farko hakuri yake da kazantarta ,sai daga baya ya ga abun ba mai karewa ba ne ,ya gaya mata da ta gyara amma ta yi banza da shi ,wannan ne dalilin da ya sa suke samun saɓani har izuwa wannan lokacin basu dena samun saɓani ba .
Bayan ya kammala basu labari ya dago ya kalli iyayensa kana ya ce .
" Wannan shi ne dalilin da ya sa na auri Safina ,amma har yanzu ba wani sonta nake ba , dan na yi na yi na kasa ."
Ajiyar zuciya ƴan ɗakin suka sauke kana Abie ya ce .
" Gaskiya Maher ka yi kuskure ,ta ya ya zaka auri wacca baka so saboda kawai ka rama abunda ƙawarta ta yi maka ."
"Wallahi Abie ranar da Nailah ta yi min hakan raina ba karamin ɓaci ya yi ba , shi ya sa na yanke wannan hukuncin ,sai daga baya kuma na yi da na sanin auren na ta ."
Ya mare maganar yana mai sunkuyar da kai ƙasa .
Ni kam kwalla na kara sharewa kana na dubi Maher na shiga bashi haƙuri a karo na biƴu .
" Dan Allah Yaya Maher ka yi haƙuri da abunda na yi maka ,wallahi na san ban kyauta maka ba , amma wallahi ni ma ban san sanda nake yin haka ba , saboda a duƙ lokacin da saurayi ya furta min kalmar so sai na ji na sane shi ."
Na kare maganar ina mai cigaba da share kwalla .
" Ba komai Nailah komai ya wuce ."
Maher ya faɗi .
"Alhamdulillah! Ma sha Allah ."
Daada ya faɗa , haɗe da kallon Maher ya ce .
"Maher har yanzu kana son ƴata Nailah