Showing 45001 words to 48000 words out of 52064 words

Chapter 16 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt

06 Mar 2025

2944

,ta karasa shiga cikin gidan .


Da yake su Nadia sun fi zama a sakar gida ne ya sa yau ma ta tarar da su zaune a sakar gidan suna shan iska .



Maman Nadia na kwance hawan jininta ya ɗan ta shi , Nadia kuma tana zaune a gefenta tana mata fifita da maficin dake hannunta .


Jin shigowar mutun ba sallama ne ya sa Nadia ɗagowa don ganin waye , idonta ne ya sauka akan Safina take shigowa cikin gidan tana tauna cingan ji kake ƙass, ƙass,ƙass .



Har ta karaso gaban tabarman da suke zaune .



Kallon ta Maman Nadia dake kwance ta yi kana ta ce .


"Baiwar Allah dawowa kika ƙara yi ?"



Bin bayanta Sufyanu ya yi , ya tsaya bayanta yana jiran ya ga mai zata yi ,dan wannan karon in ta yi wani abu bazai taɓa ƙyaleta ba ,haka yake ji .



" Eh Mama, ohhh ko da yake ke ba uwata ba ce ba ce, eh na dawo Mamar wasu ."


Ta yi maganar .


Haɗe da juyowa ta kalli Nadia ta ce .


"Na zo na yi miki kashedi na karshe ,in ba ki ji ba zan aikita miki wanda tafi ta da ,dan haka ki fita har kata da na mijina ,ki yi rayuwarki in yi tawa in ba haka ba zan ɗauki mummunar mataki wanda daga ke har iyayenki ba zai taɓa muku dad'i ba ."


Tana kaiwa nan ta juya ta fita ,


Juyowa shi ma Sufyanu ya ya sake bin bayanta .


Haɗe da kara waya a kunnensa kana ya ce .


"Yellabai bata musu komai ba ."

"Okay, saka wayan a hasfree akwai abunda nake son faɗa mata ."


Da toh Sufyanu ya amsa kana ya saka waya a hasfree ya sha gaban Safina .


Dakanar da tafiyan Safina ta ya yi kana ta buɗe baki ta fara magana .


"Malam matsa a gabana na wuce ".


"Ni ne nake magana ."


Ta ji Maher ya faɗa a cikin wayar Yayan Nadia .


Kallon wayar ta yi kana ta ce .


"Maher! Kai ne ?"


" A'a ba ni ba ne ,ke ce."


Ya bada amsa , haɗe da cigaba da cewa .



" Safina wai me ye sa kin fiya taurin kai ne ,yanzu sai da kika sake zuwa gidan nasu ko ,toh bari ki ji na gaya miki ,daga yau idan kika kara tako kafarki gidansu Nadia zan ɗauki matakin da bazai taɓa miki dad'i ba ,karki ga saboda kina yi ina kyaleki ne za ki ce za ki iya yin ɗuk abunda kike ga dama ,


Na gaya miki ,in kika sake zuwa gidansu Allah! daga can gidanku za ki wuce ."


Maher na kaiwa nan ya katse wayan.


Kallon wayan Safina ta yi ,ta ga an kashe kiran ,maida dubanta ta yi kan Sufyanu kana ta yi kofa ta juya ta bar kafar gidan .


*Gidansu Nailah*



*Da misali karfe huɗu na yamma*


shirya kayana nake ,dan yau da daɗɗare bayan sallar magrib jirginmu zai ta shi zuwa ƙasa mai tsarki , saboda duƙ shekara muke zuwa aikin Haji gaba ɗayanmu hadda kakata , sai wannan shekara kam ta ce mu je ita jikinta babu dad'i ,shi ya sa wannan shekaran mu kaɗai zamu tafi .


Sai wajan karfe biyar na yamma na kammala shirya kayana ,


Ɗakin Mommana na nufa don zuwa shirya mata ita ma tana kayan ,dan na Dadana kam Mommana ce zata shirya masa .




Sai gaf da magriba na kammala shirya wa Mommana kayanta ,wanka na shiga shaf -shaf na yi ,dan su oredi sun yi nasu ,ni kaɗai ban yi ba .



*Bayan magrib*


Dadana na dawowa daga masallaci abinci muka ci , bayan mun gama dreve da su Security's ɗinmu suka rakamu airport ,



Lokacin da muka karasa airport karfe shiɗa da rabi ta ɗan wuce kaɗan ,


Muna zuwa aka yi mana duk abunda akewa mutun kafin ya shiga jirgi ,bayan angama muka shiga jirgi .


Da misalin karfe 8 na dare jirginmu ya ɗaga zuwa ƙatsa mai tsarki .







*Fulalin Jajirtattu ce ✍️*





*More comment more typing ✍️*





Share fisabilillah 👏 my lovely fan's 🥰
[26/02, 16:21] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________


Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/FpkwDV3VSsHAei7kZz518c

________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V


________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*


*Gargaɗi*

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️2️⃣8️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*



*Cikin jirgi*



Iyalan Alhaji Aminu ne a cikin jirgin zuwa ƙasa mai tsarki domin gabatar da aikin haji.


Nihal ce ta kalli Nihilah kana ta ce .



" Nihilah wancan kamar Jamilah Mai Nasara ce."


Ɗan kallon inda Nihal ta ke kalla Nihilah ta yi, sai idonta ya s'auka akan Nailah dake zaune tare da iyayenta .



" Lahh wallahi ita ce, da ma tana nan ?"



" Toh ni za ki tambaya ?


Ni ma rabon da na ganta tun lokacin da muka yi kandi ban sake ganinta ba ,kuma da ma kinsan da shegen iyayi ba ta son mutane ."



" Wallahi ni ma tun lokacin ban kara ganinta ba sai yau, wallahi ni kuma ba laifi muna ɗan yin hira da ita ,kin san ƙawar ƙawata Madina ce ,toh in ina zaune da Madina tana zuwa ta same mu, mu ɗan yi hira , ɗuk da ba wani hiran kirki ne da ita ba , amma in ina yi da Madina takan sa baki jefi -jefi , bari ma ki gani na je na yi mata magana ."



Nihilah ta faɗa tana mai miƙewa .


Kallon ta Alhaji Aminu ya yi kana ya ce .


"Nihilah ina za ki yi kuma ?"


"Abie ƙawata da muka yi makaranta tare da ita na gani ,shi ne zan je wajanta ,dan tunda muka yi kanti ban sake ganinta ba sai yau ."



Nihilah ta bawa mahaifinta amsa , haɗe da juyowa ta nufi inda su Nailah suke .


Alhaji Aminu har ya buɗe baki da niyar yin magana sai ya ga tuni Nihilah ta yi gama ,sai ya maida bakinsa ya rufe ya bi ta da kallo .


Nihilah kuwa wajan Nailah ta nufa tana zuwa ta yi sallama .



"Assalamu alaikum!


Ɗagowa Nailah dake zaune kusa da Mommata ta yi kana ta amsa da .


"Wa'alaikum salam! Sai kuma na yi shiru ina kallon Nihilah, tunanin inda na taɓa ganin fuskar nake amma na kasa tuna komai .


Fahimtar hakan da Nihilah ta yi ne ya sa ta sakin murmushi haɗe da buɗe baki ta ce .


" Baki gane ni ba ko?'


Kai Naila ta geɗa haɗe da cewa .


"Eh wallhi ban gane ki ba , amma kamar kawai inda na sanki ,sai dai na yi, na yi na tuna na kasa ."


"Eh wallahi za ki iya manta ni gaskiya tunda rabon da mu haɗu zai iya kai shekara biyar haka ."


"Haka ne gaskiya , toh har yanzu baki tunamin inda na sanki ba ."


Murmushi Nihilah ta saki kana ta ce .


"Ni ce ƙawar -ƙawarki Madina Jabir ."


"Ohhhh! Tabbas yanzu na tuna ki Sis , I'm sorry, wallahi d'azu ban gane ki ba sai yanzu da kika faɗa min , ku ma kwana kin baya da Madina ta zo gidanmu muna hira sai da na tambayeta ke ,ta ce min kina nan ."


Nailah ta faɗi tana Murmushi ."


"Allah sarki! Kuma wallahi kwanakin baya na je gidansu ba ta faɗa min ba ."


"Ina ga ta manta ."

Na sake faɗin .


Kallon gefena na yi ,kana na maida dubana kan Nihilah na ce .



" Hasana Aminu ga iyayena ku gaisa ."



Kallon su Mommana da Daada Nihilah ta yi kana ta durƙusa har ƙasa ta ce.




"Ina wuni Mommy ? "


Cikin fara'a Hajiya Sumayya ta amsa da lafiya lau .


Haka ma Alhaji Mai Nasara ,



Bayan ta gama gaida su ta kalli Nailah kana ta ce .


"Jamilah bari na koma wajan iyayena ,sai mun s'auka ."


" Toh Nailah ,samun numberki ."

Karban wayar Nihilah ta yi, ta sakawa Nailah number wayarta ,kana Nailah ita ma ta ba ta number d'inta , suka yi sallama ta koma wajan iyayenta .



Bayan Nihilah ta koma wajan zaman su ,ta bawa Nihal labari yanda suka yi da Nailah .



*Saudia Arabia*



*Da misali karfe 2 na dare*


Kasan cewa ƙasar deyewan mutane ba su cika baccin dare ba, sai da safe suke wuni suna baccin su ne ya sa ko ina mutane kamar rana .


A wannan lokacin ne iyalan Alhaji Aminu da Alhaji Mai Nasara suka sauka ƙasar Saudia Arabia ,


Bayan sun s'auka daga ciki jirgi ne , Alhaji Mai Nasara ya ga Alhaji Aminu, kallon Hajiya Sumayya ya yi kana ta ya ce .


"Madam zo mu je ga wani abokina can na hango tare da iyanasa ,mu je mu gaisa da shi, dan rabon da na ganshi an jima ."


Kallon wajan da yake kalla Hajiya Sumayya ta yi kana ta ce .


"Nailah! wancan ba kawar nan taki ba ce ,da ta zo wajanki a cikin jirgi .?"


Kallon wajan na yi kana na ce .


"Laaaa! Wallahi Momma ita ce bari na je ."


Ban tsaya jiran me Momma za ta ce ba na yi gaba abuna .


Da sauri na kara sa wajansu kana na ce .


"Husaina Aminu!".


Dakatar da tafiyan ɗukkansu suka yi ,a ciki kuwa har da Alhaji Aminun da ya ji an haɗa hadda sunansa a ciki ,juyowa suka yi a tare ,idanuwansu suka sauka akan Nailah ,


Ni kuwa ban wani damu da kallon da suke min ba na karasa kusa da su ,na kalli Husaina Aminu na ce .


"Mun sauka lafiya .?"

Husaina Aminu ta amsa da lafiya .


Kallon Hasana Aminu na yi kana na ce .


"Hasana ya gida kwana deyewa ? Dama ke ba kya magana , Sis ɗinki ta fiki magana ."


" Haba Jamilah Mai Nasara , yanzu ni za ki ce bana magana ? Ke dai kawai ki ce saboda ke da Sis dita halinku ɗaya ne na tsiwa shi ya sa kuke gani na a matsayin mara surutu ."



Murmushi kawai na saƙi kana na kalli Alhaji Aminu (Abie) na ce .


"Daddy ina wuni .?"


Murmushi Alhaji Aminu ya yi kana ya ce.


" Lafiya lau ƴata ya makaranta ,ina fatan ana koƙari ko ?"


Kai na geɗa haɗe da cewa .


" Eh Daddy kwannan nan ma zan gama in sha Allah!"


" Toh ma sha Allah! Yanzu dai aure kaɗai ya rage muku ,dan aure shi ne mutuncin ' ƴa mace dan haka kina yin digirinki yi auren ki kin ji ƴata .?"



"Ni ma burina kenan ,amma har yanzu babu wanda ta taɓa zance da shi , ɗuk na mijin da ya zo sai ta kore shi ,da har da zagi take haɗa musu, sai da na yi da gaske ta bari ,gwara ka yi mata faɗa ko ta samu ta dena korar su ."



Alhaji Mai Nasara da ya karaso wajan yanzu ya yi maganar cikin damuwa .



Kallon wajan da aka yi magana Alhaji Aminu ya yi kana ya ce .



"Ikon Allah! Alhaji Mai Nasara ashe dama rai kan ga rai ? Washa rabu da na ganka? an daɗe gaskiya ."


Alhaji Aminu ya faɗa yana mai saƙin murmushi .


Wallahi abubuwa ne sai a hankali ,ban cika zama ƙasar ma sosai shi ya sa ,kuma da na zo bana wuce sati uku zuwa huɗu nake kara tafiya , please ka yi haƙuri ."


Ajiyar zuciya Alhaji Aminu ya s'auke kana ya ce.


"Wallahi ba komai ,na san baka cika zama ba ,dan kwanakin baya da na je Kano na haɗu da Usman nake tambayarsa kana nan ? Yake cewa a'a kana ƙasar waje ,baka cika zama Nigeria sosai ba ."


"Allah sarki ."

Alhaji Mai Nasara ya fadi hm, haɗe da miƙawa Alhaji Aminu hannu suka yi musabaha, kana Momma ta gaisa da Mommy .


Nan na gane cewa Alhaji Aminu sohon abokin Dadana ne ,


A tak'aice dai mota ɗaya muka shiga aka kaimu hotel ɗin da zamu s'auka.


Kasan cewa tun kafin su s'auka Maher ya kama musu ɗaki a hotel ɗin da ya s'auka ne ya sa suna zuwa babu ɓata lokaci ya kai su ɗakin su ,


Alhaji Aminu ( Abie)
Da matarsa ɗaki ɗaya,
Sai Alhaji Mai Nasara shi ma ɗaki ɗaya da matarsa ,


Ɗaki ɗaya aka kamawa su Nihal da Nihilah da Nailah .


Dan sun ce tare za su zauna .



Sanda na ga Maher mijin ƙawata Safina, muka gaisa na yi kamar ban san shi ba, ɗuk da kuwa mun gaisa ,amma ban yi abunda zai sa su Momma su gane cewa na san shi ba .




Maher kuwa mamaki ne ya cika shi a lokacin da ya ga 'yan gidansu tare da iyayen Nailah .


Har zai yi shiru sai ya ga bazai iya ba ,dole ya tambaya .



Wannan ne dalilin da ya sa ya kira Nihal ya tambaye ta a ina suka san Nailah ?


Nan ne Nihal ta gaya masa cewa sun yi makaranta ɗaya da ita ,
Haka ma Abiensu shi ma Dadan Nailah sohon abokinsa ne , sun jima ba su haɗu ba sai a jirgi .


Sai a lokacin Maher ya sani .


Bangaren Suraj kuwa , rabin zaman sa a ɗakin iyayensa yake yi , dan kuwa in baya komai can yake wuni , wani lokaci ma har dare yake kaiwa a can ,sai da Abie ya yi mai magana sannan ya daina kai dare sosai a wajan su ,


Ya ce in yana kewarsu me ye hana shi zuwa can Nigeria ya same su ?



Sai ya ce aiki ne ya yi masa yewa shi ya sa bai zo ba ,amma in sun tashi komawa yanzu tare za su koma Nigeria ,shi ne Abie ya ce ,toh ya bari sai sun je can ɗin suwa yi ɗuk maganar da za su yi a can ,dan anan ibada ne ya kawo su ,


Shi ya sa Suraj ya rage zama sosai in ya je wajansu .









*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*




*More comment more typing ✍️*







Share fisabilillah 👏 my lovely fan's 🥰
[26/02, 16:21] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________


Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/FpkwDV3VSsHAei7kZz518c

________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V


________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*


*Gargaɗi*

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️2️⃣9️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*



*Bayan kwana biyu*


Yau ne ake hawan arfa ,shi ya sa duk wanda ka gani a ƙasar Saudia maza da mata, har ma da ƙananun yara suke sanye da fararen kaya ,kasan cewa kowa ya san in za'a yi aikin haji ,fararen kaya ake sakawa.



Da misalin karfe 8 na dare ,an yi aikin haji lafiya .


Zaune muke mu duka a wani babban restored dake cikin garin maka ,wanda ake ji da shi ,dan ba kowa ne ma yake zuwa wajan ba, sai masu kuɗi , ɗuk wanda ka gani a cikin wajan masu kuɗi ne .


Tunda muka sha ruwa muka samu masallacin dake cikin restored ɗin muka yi sallah muka dawo muka cigaba da ciye -ciyen mu, ba mu ta shi ba har yanzu ,sai shan hira ake .



Dan gaba ɗayanmu muka zo restored ɗin ,a ciki kuwa har da Maher .


Ni ina hira da su Nihilah Maher da Suraj kuma da iyayenmu suke hira .


Abie ne ya kalli Suraj kana ya ce .



Suraj da alama akwai magana a bakinka ,dan tun dazu ina lura da kai .



Ɗan Sosa ƙeya Suraj ya yi kana ya geɗa kai alamar eh akwai .



"Okay ka yi maganarka kawai ina jinka ,dan dukanmu babu bare anan ."



Alhaji Aminu ya faɗi .


Kai Suraj ya geɗa kana ya buɗe baki ya soma magana .



" Yauwa Abie da ma akan maganar nema min aure ne dan in na je muka gama magana bana son ya wuce wata ɓiyu ."


" Ohhhh! ikon Allah ƴaƴan zamani har da gaya min watan da yake so a yi biki ."



" Shi ke nan na ji ,amma yarinyar yar gidan waye kuma a ina ku ka haɗu ? Ko karatu ta je ƙasar Indian ne .?"




Abie ya jefawa Suraj tambaya .


Maher da tun dazu hankalinsa baya kansu yana kan Naila dake ta faman hira da su Nihal ne ya juya ya zubawa Suraj idanu yana jiran ya ji wacca amsa zai basu .


Suraj kai nake sauraro baka bani amsa ba .



" Abie a social media muka haɗu da ita ,har muka fara soyayya har izuwa yanzu da muke son mu mallai juna a matsayin miji da mata ."


"Babban magana , kai yanzu Suraj da hankalinka da komai kake neman matar aure a social media ?


A ma bar shi kun haɗu a social media ,amma ta ya ya baka taɓa ganinta ba ita ma ba ta taɓa ganinka ba, kuma kuke son ku yi aure ,


Na ga alama daga kai har ita baku san me ake nufi da aure ba ."


Abie ya karashe magana yana mai miƙewa .


Hannunsa Alhaji Mai Nasara ya kama , Abie ya ɗago ya kalle shi nuni Alhaji Mai Nasara ya yi masa da ya koma ya zauna ,zama Abie ya yi ,ya yi shiru .



Alhaji Mai Nasara da tun da Suraj ya fara magana bai tanka ba ne ya buɗe baki ya fara magana .


"Yauwa , Alhaji Aminu bai kamata ka yi saurin yanke hukunci ba , saboda yanzu duniya ta waye , mata da maza deyewa sun haɗu ta social media kuma sun yi aure suna zaune kuma lafiya a gidajansu ,



Ɗuk da a kwai wasu da suka yi irin wannan auren , auren ya mutu ,amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login