Showing 42001 words to 45000 words out of 52064 words

Chapter 15 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt

06 Mar 2025

2597

magana.


"Wai Indo wannan wana irin girki ne haka ?tun yaushe kika ɗora abinci amma har yanzu baki gama ba ."


Rau rau Indo ta yi da ido , kana ta kalli Safina cikin kuka ta fara magana .


"Hajiya ki yi haƙuri Allah! yanzu zan gama saura kaɗan ."


"Ɗazu ma haka kika ce min saura kaɗan ,amma har yanzu baki gama ba ,


Ni na rasa wannan wana irin abinci kike dafawa haka, da har yanzu baki kammala ba.



Ke ba wani abincin kirki ma kika iya ballantana na ce wani mai daɗi sosai kike dafa mana ,dallah Malama matsa na gani ."


Safina ta faɗa haɗe da ture Indo gede kana ta ɗauki abunda suke buɗe tukunya da shi ta buɗe tukunyar dake kan gass.



Shinkafa jolof ta gani, wanda aka saka karas a gudansa ba'a yanka ba ba'a kum kankare bayansa ba ,sai kokonba da aka yanka aka ɗora akan shinkafan ,baki Safina ta buɗe da niyar yin magana sai kuma takaici ya hanata yi ,babban chokalin zuya abinci ta miƙa hannu ta d'auka ,



Abincin ta ɗiba kaɗan a cikin chokalin ta ɗanɗana ,ai tana zuba abakinta ba shiri ta tofar da shi ƙasa , kana ta ajiye chokalin gede, ta daga hannu ta s'aukewar Indo lafiyayyan mari akan kuncinta.


Wani irin ihu Indo ta kurma .


"Wayyooo Hajiya."


Haka kake ji da karfi .


Har Baba Maigadi dake zaune a bakin gate ma sai da ya ji ihun na ta .


Ba shiri Baba Maigadi ya miƙe ya yi cikin gidan da sauri don zuwa duba me ke faruwa .


"Ke! dan wulakanci za ki saka mana kokonba a cikin abinci ,haka ma karas, yanzu dan wukanci duk lokacin da kika ɓata kina kirki ashe wannan banzan jolof ɗin kike dafa mana ?"


Bata tsaya jiran amsar Indo ba, ta cigaba da faɗin.


"Ai kuwa in sha Allah! Yau ke ƙad'ai za ki cinye wannan jagwalgwalen da kika dafa ,dan ba zan yi asarar kayan miya da shinkafa ba .




Tana kaiwa nan ta juya fuuu ta fita ta bar kitchen, a palo suka ci karo da Baba Maigadi ,tsayawa ta yi ta karewa Baba Maigadi kallo saf ,kana ta buɗe baki ta ce .


"Kai kuma Baba lafiya? na ganka cikin palo ba sallama ."



"Wallahi Hajiya ihun wannan ƴar aikin naki na ji , shi ya sa na zo gani ko lafiya ,dan na ga ihun ya yi yawa ."


"Toh sannu ɗan sa ido ,toh ni ce nan na mare ta ,ko za ka rama mata ne .?"



"A'a Hajiya ."


"Ohhh! Na d'auka zaka rama mata , tunda ba rama mata ka zo yi ba, sai ka juya ka koma wajan zamanka ."


"Toh Hajiya."


Baba Maigadi ya kuma faɗi, haɗe da juyowa .


Yana koƙarin barin palon ya ji Safina ta kira shi.


"Baba! ."


Dakatar da fitan ya yi ya juya ya amsa da " Na'am ."


"Yauwa , yau ba abinci a gidan nan ,dan wannan yarinyar babu wani abincin kirki ta dafa , shirmenta kawai ta yi ,in kuma zaka ci a haka in ta gama ta kawo maka ."



Cikin sanyin murya Baba Maigadi ya buɗe baki ya ce.


"Toh Hajiya, a ɗan kawo min a haka zan ci dan wallahi yinwa nake ji ."

Taɓe baki Safina ta yi haɗe da cewa .


"Shi ke nan, za ta kawo maka in ta gama ."


Ta faɗa ,tana kaiwa nan ta juya ta bar palon ta nufi ɗakinta don zuwa ta shirya ta fita ta je ta samowa kanta abunda za ta ci.



Kai Maigadi shi ma ya geɗa, kana ya juya ya bar palon .



Cikin kitchen kuwa , Indo tana nan dafe da kuncinta har yanzu ,bata motsa daga wurin da Safina ta bar ta ba .


Ta daɗe a haka ,sai da ta ji abincin da ta ɗora ta fara kamawa kafin ta tire hannunta daga kan kuncinta ta karaso gaban gass d'in ta kashe .



Bayan ta kashe, kula ta d'auko da niyar zubawa Safina, sai ta tuna ta ce ba za ta ci ba ,mai da kulan ta yi ta rufe haɗe da d'auko plate ta zuba nata ,kana ta zubawa Baba Maigadi shi ma .




*Safina*


Bayan ta shiga ɗakinta, shiryawa ta yi cikin doguwar riga, ta ɗauki mayafinta ta yafa ,kana ta ɗauki jakarta da kuma ATM card dinta da wayarta, kana ta bar ɗakin ,tana fita ba ta tsaya ko ina ba sai wajan motarta ,


Baba Maigadi yau tun kafin Safina ta yi magana ya miƙe ya wangale mata gate,


Guntun murmushi Safina ta saki ,kana ta kunna motarta ta ja ta bar gidan.




Restaurant ta je ta siyo lafiyayyan abinci ta ci ta ƙoshi ,sai bayan sallahr magrib da tawo gidan.



Bayan mai gadi ya bude mata ƙofa ta shigar da motarta ,ta fito ta rufe motar ,har zata wuce cikin gida sai ta hanko plate d'in abinci a gaban bencin Baba Maigadi .



Bayan ta gama kallon plate d'in maida dubanta ta yi kan Baba Maigadi da ya gama rufe gate ya kamo bencinsa da niyar zama ya ji Safina na magana .



" Baba ya na ga baka ci abincin ba ?"



Cikin sanyin murya Baba ya ɗago ya kalli Safina kana ya ce .



" Wallahi Hajiya na kasa ci ."



Kai kawai Safina ta girgiza kana ta juya ,da niyar shiga ciki ,ko me ta tuna ta ja ta tsaya haɗe ta kallo ledan dake hanninta kana ta kalli Baba Maigadi shi ma, kana ta ce .



"Zo ka karba ,ba dan halinka ba ."


Safina ta faɗa, tana mai zura hannunta cikin ledan dake hannunta ,wanda bayan ta gama cin abinci a restaurant ta gama ne ta ce a yi mata take away ,shi ne aka mata .


Da yake take away guda biyu ne ,ya sa ta tire ɗaya wanda shinkafa da miya da salak yake ciki ta bar wanda kayan snacks take ciki ,



"Ungu ka karbi wannan kaci , abinci ba dan halinka ba ."



Ta faɗa tana mai hararan Baba Maigadi.


Baba Maigadi kuwa ,bai damu da irin hararan da Safina ta yi masa ba, shi dai matsalarsa abinci ne kawai kuma ya samu .


Cikin sauri ya karaso wajan da Safina take tsaye ya saka hannu ya amshi abincin , haɗe da yi mata godiya .


Bata tsaya amsa godiyan da yake masa ba , ta juya ta shiga ciki .



Baba Maigadi kuwa ,da kallo ya bi bayan Safina , yana mai faɗin .


" Lallai yau waca rana Hajiya ta bani abincin da ta siyo ,ba ma wanda ta dafa da kanta ba ."


Ya yi maganar haɗe da juyowa ya koma kan bencinsa ,ya zauna ya soma cin abinci .



Safina kuwa ,tana shiga cikin palon har za ta wuce ciki sai ta juya ta kalli eriyan da kitchen yake kana ta juya ta nufi kitchen ɗin ,tana zuwa bata tarar da Indo a cikin kitchen ɗin ba , tukunyar abinci ta buɗe ta ga abinci tuli a ciki ,kofa ta yi ta mai da tukunyar ta rufe , haɗe da juyowa ta bar kitchen ɗin.


Tana fita ɗakin da Indo take ta nufa tana zuwa ta tura ƙofar ta shiga .



Tarar da Indo ta yi ta i'dar da sallah , tana kwance akan sallar da ta yi Sallan da shi, shigowar Safina ɗakin ne ya sa ta tashi zaune , haɗe da cewa .


"Hajiya sannu da zuwa ."


Safina bata amsa mata ba ,sai ma jefa mata tambaya da ta yi .


" Wa kika ajiye wa wancan jagwalgwalen da kika dafa kika bari a cikin tukunya ?"



Cikin sanyin murya Indo ta buɗe baki ta ce .



" Ba kowa ."


Indo ta bawa Safina amsa .


"Okay ,toh maza tashi ki je ki cinye wannan abincin in ba haka ba ranki ya ɓaci ."


Cikin sanyin murya Indo ta kallon Safina haɗe da cewa .


" Hajiya na ci na ƙoshi ."



" Wallahi Indo baki isa ba ,bazan taɓa zubar da wannan uban abincin ba ,dole ke da kika dafa ke za ki cinye ."



Kuka Indo ta fashe da shi .


Cikin kuka take faɗin .


"Dan Allah! Hajiya ki yi haƙuri ,wallahi na ƙoshi ,amma zan ci anjima ."


"Shi ke nan ,na baki nan da zuwa anjiman ki tabbatar kin cinye abincin nan ."


Kai kawai Indo ta geɗawa Safina , Safina ta juya ta bar ɗakin ,ta wuce ɗakinta .



*Saudia Arabia*


*Bayan kwana biyu*


Yana nan kwance ɗuk 'yan ɗakinsu ba sa nan sun fita ,shi ƙad'ai ,shirun din ne ya yi mai yawa ya sa shi tashi haɗe da d'auko wayarsa ,ya fita bayan ya kulle ɗakin ya wuce hotel ɗinsu Suraj dake kusa da nasu .



Yana zuwa ya murɗa kofar ya tarar da ƙofar a buɗe ,dan haka shiga kawai ya yi ya maida kofar ya rufe ya nufi ciki .


Kwance yake rufda ciki ya saka waya a hasfree yana waya da masoyiyarsa Safina.


Bai ji shigowar Maher ɗakin ba ,saboda ya lula duniyar masoya .



"My love albishinki."


Safina da ita ma tare kwance akan gadonta ta ce.

" Goro."


" In sha Allah, muna gama aikin Haji zan zo Nigeria ,dan haka ki shirya tarbar masoyiyarki.


"Farin ciki da bai kai zuci ba Safina ta yi , haɗe da cewa ."


"Woww! My love gaskiya na ji daɗin da jin wannan labarin ."


"Amma ba ki kai ni farin ciki ba ."


"Waye gaya maka ? Na fika nesa ba kusa ba ,kai dai Allah ya kawo ka lafiya ."


Suraj ya amsa da ameeen .


Haɗe da kallon Maher da yake zama gefensa ,dan sai yanzu ya lura da shi .


Maher kuwa wani irin bugawa kirjinsa ya ji a lokacin da ya ɗan ji muryar Safina ya doki dodon kunnuwansa .



A lokacin da ya ji muryar ya daɗe yana tunanin.


Safina ,ya faɗa , kai ina ba ita ba ce ba gaskiya dan Suraj da ko aurana ma bai je ba ,ta ina ya san Safina?


Kai! Gaskiya ba ita ba ce ba .


Ya sake faɗi a cikin ransa, kana ya nemi waje ya zauna kusa da Siraj ɗin.



Suraj kuwa ganin Maher ya zo ne ya sa shi faɗin.


"Yauwa my love ga Bro ɗina bari na baki shi ku gaisa ."


Ta can bangaren Safina ta amsa da .

" Okay ,ba shi ."



Miƙawa Maher waya Suraj ya yi, haɗe da faɗin.


"Bro ga budurwata da nake baka labari ,ku gaisa ."



Kamar Maher bazai karɓi wayar ba ,sai kuma ya karɓa ya kara a kunne haɗe da faɗin .


" Hello ."



*Safina*


Sai faman cewa hello take amma ta ji shiru ,tana dubawa ta ga kuma wayan na yi amma ba ta jin abunda ake faɗa.


Haka ma bangaren Maher , jin shiru da ya ji ne ya sa shi jan gajeran tsaki , haɗe da tiro wayan daga cikin kunnensa ,ganin wayar na yi ba'a magana ne ya sa shi kallon Suraj haɗe da miƙa masa wayar .


Karɓa Suraj ya yi ,kana ya kalli Maher ya ce .



" Bro ya baka yi magana ba.?"



Ni zan yi magana ko budurwar taka za ta yi magana ?"



"Kana nufin hello ɗin da na ji ka yi ma bata amsa ba ?"



"Ni ban ji komai ba ."


Maher ya sake faɗin .



Duba wayan Suraj ya yi ,ya ga har yanzu ba'a kashe kiran ba .


" Hello my love ,kina jina ?


"Hello ."

Shiru.

Katse kiran ya yi ya, ya sake kira ,nan ma dai yana ta cewa hello , Safina ma tana ta cewa hello amma shiru ,ba wanda yake jin dan uwansa .



Katse kiran Suraj ya yi , ya dubi Maher kana ya ce .


" Wallahi network, bata jin abunda take cewa ."


Taɓe baki Maher ya yi , haɗe da miƙewa .


Kallonsa Suraj ya yi kana ya ce.


" Ina kuma za ka ?"


"Zan koma hotel dinmu ne ."


"Zaka koma ,yanzu fa ka zo ? Ko hira ba mu yi ba ."


" Ta ina za mu yi hira bayan kana soyayya ."


"Haba Bro wai me ye sa kake min haka ne ? Tunda muka zo bamu yi wani hira ba ,


"Washa rabu da mu haɗu dan Allah !"


" Ni ka ga tafiya ta ."


Maher ya faɗi .


Bai tsaya jiran me Suraj zai ce ba , ya juya ya bar ɗakin ,ya koma hotel d'insu .







*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*




*More comment more typing ✍️*




Share fisabilillah 👏 my lovely fan's 🥰




07049322735
[23/02, 12:23] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________


Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/FpkwDV3VSsHAei7kZz518c

________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V


________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*


*Gargaɗi*

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️2️⃣7️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*



*Bayan komawar Maher hotel d'insu*


Zaune yake ya yi shiru yana tunanin wannan muryar da ya ji ɗazu ,ya so ya kara jin muryar amma network ya hana .



Ya daɗe yana tunanin ,ganin tunanin abunda yake ba zai taɓa faruwa ba ne ya sa ya ajiye tunanin a gefe ,kana ya tiro wayarsa daga cikin aljihu ya shiga neman number Safina ,yana gani number d'in ,ya yi dealing number .


Zaune take wannan karo tana kallon wani film ɗin India ta ji wayarta na ringing .


Ba tare da ta duba mai kiran ba ta ɗaga wayan ta kara a kunne kana ta ce.

"My love network na ta damu ko .?"


Ta can bangaren Maher ya yi magana kamar haka .


" Yau kuma wana abu kike kullawa ne kika kira ni da my love Safina ?"



Ta ji Maher ya jefa mata da tambaya .


Taɓe baki ta yi ,kana ta saita kanta ta ƙirƙiro murmushi ,kana ta ce.


"Haba Maher wai me ye sa kake min haka ? Yanzu a matsayinka na mijina ban isa na kira ka da sunan my love ba sai in ina kulla wani abu ?
Wana irin abu nake kullawa toh .?"


" Ohooo ! Wannan kuma ke kika sani ni ban sani ba , ni yanzu dai ba wannan ba ma ,ina so na sani shin kin dawo da Nadia da na ce ki dawo da ita ko kin yi taurin kan da kika tsaba .?"


Guntun murmushi Safina ta saki ,kana ta buɗe baki ta ce .


"In dai wannan maganar ne ya sa ka kira ni toh ka kashe kiran bana so ."


"Anƙi a kashe kiran ,ki amsa min tambayata Malama kin dawo da ita ko baki dawo da ita ba ?"


"Ban dawo da ita ba ,sai ma zuwa gidansu da na yi, na yi mata shegen duka haɗe da ja mata kunne a kan kar ta kara kiran min miji ."


"Duka fa kika ce Safina ?"


Babu tsoro Safina ta kara faɗin.


" Eh duka nake nufi ,da fa Hausa nake magana ba da wani yare ba ,da za ka kara tambayata ."


" Ahhh! Lallai sai yanzu na tabbatar ke mahaukaciya ce."


"Maher ni kake kira da mahaukaciya .?"


" An kira ki da mahaukaciyan ki yi ɗuk abunda za ki yi ,jaka kawai ."


"Yana kai wa nan ya katse kiran kitt!"



Kofa Safina ta yi haɗe da miƙewa fuuuuuu, ta nufi ɗakinta .


Bata wani d'au lokaci da shiga ɗakin ba, ta fito riƙe da hijab a hannunta da key ɗin mota da wayarta ,ta nufi waje ,tana zuwa ta ce wa Baba Maigadi ta buɗe mata gate ,da s'auri Baba Maigadi ya miƙe ya wangale mata gate ta cilla hancin motarta waje ,ta ja motar ta mufi gidansu Nadia .



Da yake unguwarsu Nadia ba nesa sosai da na su unguwar ne ,ya sa cikin lokacin ƙanƙani ta karasa unguwar ,bayan ta yi parking ta fito ta nufi cikin lungun ,da sauri take tafiya har tana tuntubi .


*Saudia Arabia*


Maher kuwa bayan ya katse kiran da yake yi da Safina ne , ya dannawa Yayan Nadia kira ,amma sai dai kasss! Kiran taƙi shiga ,saboda matsalar network da ake ɗan fama da shi .



Bayan mintuna goma ya sake goda number ,ai kuwa ya ci sa'a number ta shiga wannan karon .


Zaune yake a kofar gidansu tare da wani abikinsa suna hira ya ji wayarsa na ringing ,yana dubawa ya ga bakuwar number ce ,kamar bazai dauka ba , sai wani abu kuma ya ce masa ya ɗ'auka ,dan haka babu ɓata lokaci ya d'auka ya kara a kunne , haɗe da yin sallama .


Ta can bangaren Maher ya amsa mai sallamarsa , haɗe da faɗa masa shi waye .


A take fara'ar fuskarsa ya faɗaɗa,


Gaishesa ya yi Maher ya amsa, kana ya shiga faɗa masa dalilin kiran na sa da ya yi .



"Yauwa, Sufyanu da ma ba dan komai ya sa na kira ka ba, sai don ina son na ji shin da gaske ne matata ta zo gidanku ta ɗaki ƙanwarka ko ɓata zo ba .?"


Ajiyar zuciya Sufyanu ya s'auke kana ya kwashe komai ya gayawa Maher .



" Ohhhh my good! Yanzu abunda Safina ta zo ta aikata kenan ?"


"Eh yellabai ."


Sufyanu ya bawa Maher amsa.


Bai rufe baki ba ,ya hango ta tana doso ƙofar gidansu ,dan ya santa, ya daɓa ganinta sau ɗaya , a lokacin da ya je wajan ƙanwarsa ,lokacin ne ya ga ta shigo da motarta ta dawo daga unguwa a lokacin , shi ya sa ya gane ta yanzu da ya ganta .



"Sufyanu ya na ji ka yi shiru kuma ?"



"Yellabai ita na hango tana zuwa ne ."



"Wa kenan ?"


"Ita matar taka mana yellabai ."


"Ita ce ta kara dawowa gidan naku ?"


"Eh ita ce ."


"Okay ,kana ji na ? karka kashe wayan ka bari ta karaso mu ji da me ta zo yau kuma , ka sauke wayan daga kan kunnenka ,kar a fahimci waya kake ."


"Toh yellabai ."


Sufyanu ya amsa haɗe da tiro wayan daga kan kunnansa .



Kara sowa Safina ta yi ,ba tare da ta kalli inda su Sufyanu da abokinsa ya ke ba ,ta yi cikin gidan .


Da sauri Sufyanu ya miƙe ya sha gabanta ,kana ya ce.


"Hajiya ina za ki .?"



Kallon saba da k'asa Safina ta yi wa Sufyanu kana ta ture shi gefe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login