Showing 24001 words to 27000 words out of 52064 words
Chapter 9 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt
yi ba,tunda in ina yi bana maida hankali.
Ganin ta ƙi amincewa ne ya sa kawai na haƙura na kyaleta.
*Safina*
Washe gari
Ta saɓa sanda Nadia tana nan in ta tashi daga bacci ta tarar da breakfast akan dinning na jiranta,amma yau tana fitowa taga wayam ba komai akan dinning,haka ma sharan palo ba'a yi ba.
Kitchen ta nufa dan a tunaninta ko bata gama ba ne,amma sai dai tana zuwa kitchen nan ma babu kowa,a fusace ta juya ta nufi daƙin da Indo take ciki,
Tana zuwa ta shiga buga kofa.
Indo dake ta faman bacci,dan saboda tsabar laushin katifan da ta samu ko sallar asuba yau makara ta yi,duk da kuwa a gidan su ta saba yin sallah da wuri amma yau sai da ta makara.
Tana saka da bacci mai dadi ta ji ana buga kofar ɗakin,wani irin zabura ta yi ta tashi zaune kan katifar,kana ta shiga murza ido haɗe da duba ɗakin,sai a lokacin ta tuna a inda take,da ma abunda ta zo yi a gidan.
Tana cikin tunani ta ji Safina ta kara buga kofar wanda tafi ta ɗazu karfi ,haɗe da faɗin.
"Wallahi Indo in baki buɗe kofar nan har kika bari na je na d'auko key na zo na buɗe da kaina na sameki a ciki ranki sai ya....
Bata karasa magana ba Indo ta buɗe kofar.
Tana buɗe kofa ta zube a kasa ta shiga gaida ta, haɗe da bata hakuri.
"Hajiya ina kwana ?dan Allah dan annabi ki yi haƙuri laushin katifa ne ya hanani tashi da wuri,dan Allah ki tireta ki shimfiɗa min tabarma,dan wallahi laushinta ta yi yawa."
Da ran Safina a ɓace yake,amma jin maganar da Indo take faɗi ne ya sata sass'auta firkarta, haɗe da buɗe baki ta fara magana.
"Na ji maza tashi Malama ki je ki dora min abincin safe."
Cikin rawar jiki Indo ta miƙe ta nufi kitchen.
Bayanta Safina ta bi,ta je ta kunna bata gass,dan da ma mantawa ta yi bata iya kunna gass d'in ba,saboda jiya ma ita ta kunna mata.
Gass din ta kunna mata kana ta juya ta kalleta ta ce.
"Maza debo ruwa ki zo ki dora,kafin ya tafasa ki fereye doya,in ya tafasa sai ki saka ki zuba gishiri da shuga gakan."
Da toh Indo ta amsa kana ta ɗebo ruwa ta zo ta ɗora ta koma da ɗauki doya da kwano da kuma wuƙa ta shiga fereyewa.
Sai da ta tabbatar ta fara fereye doyan tukun kafin ta juya ta bar kitchen ɗin.
*Bayan kwana uku*
Yanzu kam Indo ta iya anfani da kayan kitchen ɗin, har ma da sauran abubuwan dake cikin gidan, shi ya sa Safina ta kyaleta yanzu kam ko tana kitchen ba ta zuwa, saɓanin lokacin da ta zo in har za ta yi aiki a kitchen sai ta leƙa.
*Abuja Nigeria*
Ranar da suka je suka ajiye pasinjoji a ƙasar Saudia ranar suka kara juyowa suka sake dawowa dan kwashe wasu.
Yau ba shi ne da aiki ba,shi ya sa yake a gida bai fita ba tun safe yake wutawa,dan kwana biyu da ya yi yana tuƙa jirgi ba karamin gajiya ya yi ba,kuma har yau bai kira Safina ba,sai kuɗin da zata bukata wajan siyan abubuwa bukata kadai ya tura mata,,duk da kuwa ya bar komai amma sai da ya tura mata 100k
Lolacin da Safina ta ga kuɗin kiransa ta yi amma still ya ƙi daukan wayarta.
*Bangarensu Boɗejo*
Kamar yanda Baffa ya yi alkawari akan cewa washe gari zai je ya saida shanunsa,hakan kuwa ta kasan ce,dan kuwa washe ya je ya siyar da shanun ya zo suka shirya washe gari suka yi garin Adamawa,dan sun taɓa zuwa Gombe basu same su ba,shi ya sa suka yanke shawara zuwa (Adamawa)
Bayan sun je Adamawa,da taimak'on wani bawan Allah suka samu suka kama hotel,ranar kwana suka yi ba su yi bacci ba, tunda ba su saba da kwana cikin wadennan ɗakunan ba,
Amma ga mamakinsu,sai suka ga Boɗejo ta yi bacci sosai,dan da asuba ma daƙer suka tashe ta,dan taƙi tashi.
Washe gari suka shiga zaga garin Adamawa ,ko Allah zai sa su ga iyayen Boɗejo,amma ina har yamma ta yi ba su ga ko mai kama da su ba, ballantana su.
A haka dai jiki babu ƙwari suka koma hotel din da suka sauka,washe gari suka tattara nasu eh na su suka koma rugarsu.
*Safina*
Kwance take kan gadonta tana aikin chat da ta tsaɓa yi kullun.
Tana yi tana tsakin Murmushi.
"Na yi missing dinki my love bari na kira ki video call sai na ganki ya faɗa,bai tsaya jiran amsar da zata bayar ba ya danna mata video call.
Tana cikin yi mai reply ta ga kiransa ya shigo wayarta,gyara kwanciyarta ta yi haɗe da ɗaga wayan.
Ganinsa ta yi zaune idonsa manne da glass ka laptop a gabansa da alama aiki yake a ciki.
Rufe laptop ɗin ya yi ya ajiye ta a gefe kana ya kalleta ya tsaki murmushi.
Ita ma murmushi ta yi mai daga kwancen da take.
"My love gaskiya kin gara kyau,wai me sirrin ne ? Ni anya ma kina tunani na ma kuwa,dan na ganki bulbul da ke,ko da yake nafi son na ganki a haka."
Ya karashe magana yana mai cigaba da tsareta da ido.
Ajiyar zuciya ta sauke,kana ta buɗe baki ta ce.
"Ɗuk kai kaɗai dear?
Ka ce na yi ƙiba ba na tunaninka,ka ce gwara ma da na yi baka son gani na a rame,duk kai kaɗai.?"
"Eh mana ɗuk ni kaɗai."
"Awwwnnn, i love you."
Ta faɗa.
"Me too,my love."
Shi ma Suraj ya faɗa da wani irin murya dake nuna tsantsar so da kaunarta da yake yi,
"My love."
Ya kira Safina.
"Na'am."
"Wallahi ina sonki sosai na matsu na zo ( Nigeria ) na ganki gani gaki,na faɗa miki irin yanda nake sonki a zahiri."
"Wallahi ni ma burina kenan, Allah dai ya nuna min ranar da zan ganka gani ga ka a batsayin mata da miji."
"Ameen matata."
"Suraj ya faɗa."
"Har an d'aura ma kenan.?"
"Eh tuni an d'aura baki sani ba.?"
Ya faɗa yana mai sakin murmushi.
"Ohhh, haka ne fa na tuna ashe an d'aura, amma yaushe zaka zo ka ɗauki matar taka.?"
Ita ma ta faɗa cikin zulaya tana mai yin dariya.
Ɗan dakatar da murmushin da yake yi ya yi,kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa maganar da yake son yi mai mahimmanci ne,kuma babu wasa a ciki
Baki ya buɗe kana ya ce.
Bayan babban sallah da sati ɗaya zan zo in sha Allah,saboda zan tafi aikin hajji nan da sati biyu,ina so in na dawo ayi komai a gama nan da wata biyu zuwa uku a aura mana aure."
Ya yi magana.
"Wai da gaske kake.?"
Safina ta tambaye shi.
"Sosai ma kuwa da gaske nake, ko ke ba kya so a yi yanzu ne baki gaji da soyayyar wajan ba.?"
"A'a ina so mana."
"Zan zo, da gaske,kuma kallo ɗaya zaka wa fuskata ka fahimci hakan ai."
"Haka ne, Allah ya kaimu."
Ya amsa da ameen.
"Bari na kwanta kaina ya fara ciwo ma karasa magana gobe da safe in Allah ya kaimu."
"Ayya sorry my love,ba komai ki kwanta sai mun yi magana gobe,ina sonki sosai ,ki kularmin da kanki."
"Ni ma haka,bye."
"Ta faɗa tana mai kashe kiran."
Ajiye wayan ta yi,ta yi shiru kamar mai tunani.
Sai na ga ruwan comment zan kara yawan typing,akasin haka kuma,kara rage yawanshi zan yi.
*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*
*More comment more typing ✍️*
*Share fisabilillah 👏*
[05/02, 12:34] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭
Story & Written ✍️
By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)
________________________________________________
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/LkKggQHADe9IjmqxpteXaO
________________________________________________
Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V
________________________________________________
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
________________________________________________
*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝♀️🧝♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Book one free*
*Gargaɗi*
Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.
Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.
Page ▶️1️⃣6️⃣
*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*
"Toh ni yanzu in ya zo ina zamu haɗu? Kuma in ya ce zai turo iyayensa su zo su yi maganar aure wana gida zan kai su ?
Ina, hakan ma bazai taɓa yuwa ba dole na nemo hanyar da zai sa ya fasa zuwa,ko kuma in ya zo muka haɗu a wani waje na ganshi ya gan ni na samu karyan da zan faɗa masa ya fasa zuwa."
Ta yi magana tana kallon wayarta da ta fara ringing yanzu.
Kallon wayan ta yi ta ga sunan Nasir ne yake yawo akan screen ɗin wayan.
Kamar ba za ta ɗaga ba,sai kuma ta ɗaga ta kara kunne haɗe da cewa.
"Hello."
Ta cikin wayan Nas ya ce.
"My dear kin manta da ni yau shiru baki neme ni ba."
"Sorry na yi busy ne shi ya sa."
"Okay,ya kike toh."
"Lafiya lau."
Safina ta amsa.
"Me aka ajiye min na zo na karɓa."
Nas ya sake faɗin.
"Kaina."
Safina ta bashi amsa.
"Woww!toh na zo na karba kenan.?"
"Me zaka karba?"
"Kan na ki da kika ajiye min mana."
"Toh ai adana maka na yi."
"Noo, ban yedda ba sai kin ban kayana."
"Toh zan baka kayanka,in lokaci ya yi."
"Yaushe,ni dai kawai mu haɗu gobe."
"Gaskiya ba lallai ne na fita ba."
"Me ye sa ?"
"Kawai bana jin fitar ne."
"Anya Safina baki daina so na ba kuwa."
"Haba ina,soyayyarka sai ma karuwa da ya yi a cikin zuciyata."
"Toh in har abunda kika faɗa gaskiya ne ki yanda kawai mu haɗu gobe."
"Shi ke nan zan zo na same ka a wancan gidan naka ba sai ka zo ka ɗauke ni ba."
"Okay,zan jiraki wajan 2 rana haka."
"Okay ba damuwa."
Hira suka ɗan taɓa kana suka yi sallama kowa ya kwanta,dan har 12 na dare ta ɗan wuce a lokacin.
Har za ta ajiye wayan sai ta tuna da Maher,cikin contact ta shiga ta nemo number sa kana ta danna masa kira.
Yana saka da bacci ya ji wayarsa na ringing,tsaki ya ja haɗe da saka hannu ya shiga lalubar wayar.
Dan idonsa a rufe suke har yanzu bai buɗe su ba.
Jin bai ji wayan ba ne ya sa shi buɗe ido sai a lokacin ya ga hasken wayan.
D'aukar wayar ya yi ya duba mai kiran,sunan My dear ya gani na yawo akan screen ɗin wayar,tsaki ya kara ja kana ya daga wayar a fusace ya fara magana.
"Wai Safina baki da hankali ne ? Ta ya ya za ki kira ni a wannan lokacin."
Safina kuwa har ta fudda rai zai amsa sai ta ji muryarsa da yake nuna alamun bacci yake ya tashi.
Uffam bata ce masa ba har sai da ya kammala masifarsa tukun kana ta buɗe baki ta ce.
" Wai Maher me ka ɗauke ni ne ? Ta ya ya ina matsayin matarka zaka koma ba za ka gaya min ba,sai dai na hau sama na tarar ta ƙofa a rufe,wannan ai wulanci ne,shi ne yanzu dan na kiraka a wannan lokacin zaka yi magana sabada kana tare da budurwarka kuna sheƙe ayar ku na katse muku, shi ne zaka min faɗa wallahi a....
"Safinaaaaa!ya kira sunanta cikin wata iriyar murya dake nuna tsantsar ɓacin rai,dan sosai ransa ya ɓaci akan maganar Safina ta karshe.
"Ko da wasa,kar ki kara ce min ina zina,sanda bani da aure ma ban yi zina ba ballantana yanzu da aure na, ɗuk da kuwa auren da shi da babu ɗuk ɗaya ne a wajena,amma Allah ya kiyaye na nemi matan banza."
Yana kaiwa nan ya katse kiran.
Ganin ya katse kiran ne ya sa Safina bin wayar da kallo haɗe da taɓe baki kana ta ajiye wayar ta kwanta.
Maher kuwa saboda tsabar ɓacin rai da yake ciki har ya ƙasa komawa bacci yi,sai juye yake akan gado yana tunanin ta inda zai fara nemawa kansa mafita,dan har ka Allah,ya gaji da irin abubuwan da Safina yake masa.
Yana cikin wannan tunanin ne ta faɗo masa a rai wayarsa ya ɗauka ya shiga contact ya nemo number d'inta yana gani ya yi dealing ɗinsa ya saka a kunne.
Ina saka da bacci na ji wayata na ringing,gyara kwanciyata na yi kana na cigaba da baccina hankali kwance,dan yau ƙafata ya yi sauƙi sosai yanzu kam,
Har wayar ta tsinƙe ban ɗaga ba,
Ɓangaren Maher kuwa har zai haƙura sai wani abu kuma ya ce sake gwadawa Maher ƙila za ta ɗaga.
Anfani ya yi da shawaran da zuciyarsa ta bashi.
Ƙara dealing number nata ya kara yi.
Ƙarar wayar na ji a karo na ɓiyu.
Gajeran tsaki na ja kana na buɗe idona na ɗora su akan wayata dake ta faban ringing.
Jawota na yi na duba mai kiran,na ga ba suna.
Tsaki na kara ja haɗe da faɗin.
"Wallahi ko waye kai sai na yi maka rashin mutunci haka kawai ina tsaka da bacci zaka tashe ni.?"
Kofa na yi haɗe da ɗaga wayan.
Ban jira an yi magana ba na fara masifa da wannan muryar nawa da baya fitowa sosai saboda baccin dana yi.
" Wai kai waye? Da zaka takura min ina tsaka da baccina mai daɗi,haka jiya ma ka yi min,dan na gane karshen number ka,ka dena takura min Malam tunda ka iya kiran mutun ,ba ka iya magana ba,ko kai kurma ne ban sani ba."
Ɗuk na yi maganar a lokaci ɗaya kuma cikin daga murya.
Maher kuwa jin yanda take masifa ne ya sa shi gyara kwanciyarsa haɗe da sakin guntun murmushi kana ya tire wayar daga kan kunnensa ya kashe kiran haɗe da maida wayan ya ajiye inda yake ajiyewa.
Jin shiru ba'a yi magana ba ne ya sa ni tire wayar daga kan kunnena na duba,ina dubawa na ga ya katse.
"Kai wai kashe min waya ya yi? Ina magana zaka kashe min waya saboda ka raina ni ,ka maida ni mahaukaciya zan yi maganninka,sai na sa an nemo min kai ɗuk inda kake an kama min kai."
Na yi maganar ina mai ajiye wayan haɗe da kwanciya.
Maher kuwa lokaci ɗaya ya nemi ƙuncin da yake ciki ya rasa,cikin nitsuwa da kwanciyar hankali ya yi baccin sa.
*Washe gari*
Kamar yanda Safina da Nas suka tsara akan haɗuwar su hakan kuwa ta kasan ce,dan kuwa bayan ta tashi daga bacci wajan 11:30 wanka ta shiga ta cuɗe cikinta sosai,ta wanke ko ina lungu da saƙo,ta d'au lokaci mai tsawo a toilet ɗin kafin ta fito bayan ta yi alwala.
Mai ta shafa da turaruka ta fesa.
Bayan ta kammala ta miƙe ta je gaban wardrobe ta buɗe ta tiro atamfa mai kyau wanda aka yi mata dinkin dogowar riga ta shirya ta kara komawa gaban mirror ta shafa powder da turare ta kara fesawa,sai zuba kamshi take yi yau.
Bayan ta kammala ta ɗauki mayafinta da jakarta da talalminta ta yi palo,
Bayan ta fito gaban dinning ta karasa ta zauna ta ɗan sha kunun geɗa da ƙosai da Indo ta yi ,ta miƙe tana tuba agogon dake hannunta,ta ga karfe ɗaya saura,
Biyun ba ta yi ba amma ai kafin na karasa za ta kusa yi bari kawai na tafi."
Ta faɗa tana mai kwallawa Indo kira.
"Indo! Indo!!"
Fitowa indo ta yi daga ɗaki tana cewa.
"Gani Aunty,na shirya unguwa zamu tafi.?"
Indo ta faɗa tana washe baki.
Ba ta tsaya jiran amsar da Safina za ta bata ba ta juya za ta koma ciki Safina ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata tsawa.
"Mahaukaciyar banza mahaukaciyar wofi,ban son rawar kai, da wa za ki je unguwa,aiki kika zo yi min ko unguwa.?"
Wani irin tsoro Indo ta ji,ba shiri ta rube ƙasa ta tire dankwalinta tana fifita, haɗe da buɗe baki ta shiga bawa Safina hakuri.
"Dan Allah! dan annabi Aunty ki yi haƙuri bazan kara ba."
"Na ji maza tashi ki tafi ku ma ki tattabar kin yi girki kin gyara ko ina kafin na dawo."
Indo na jin haka ta geɗa kai haɗe da miƙewa a guje ta bar palon ta koma ɗakinta har tana tuntubi.
Da kallon takaici Safina ta bi Indo da shi,har ta ɓace mata,kana ta girgiza kai ta juya ita ma ta yi waje.
Bayan ta amsa gaisuwar da maigadi yake mata ta ce.
"Baba buɗe min gate zan je kasuwa."
"Toh Hajiya a dawo lafiya."
Safina ta amsa da Allah ya sa.
Kana baba maigadi ya buɗe mata gate,ta shiga motarta ta ja ta bar gidan.
Tana zuwa unguwar ta d'au waya ta kira Nas, yana ɗagawa ta ce masa tana baƙin gate
"Okay, ki yi home maigadi zai buɗe miki gate na sanar masa da zuwanki,in kin shi ga ki sameni a part ɗin rannan da muka zo tare ."
"Okay."
Safina ta faɗa tana mai danna home babu bata lokaci maigadi ya wangale mata gate ɗin gidan ta cilla hancin motarta cikin,bayan ta shiga ciki parking ta yi ta amsa gaisuwar maigadi ta juya ta nufi part ɗin da Nas yake ciki,
Tana zuwa ta tura kofar ta tarar ta shi a buɗe ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
Ba ta rufe baki ba ya zo ya rungumota ta baya ya shiga shinshina wuyanta.
*Fulalin Jajirtattu ce ✍️*
*More comment more typing ✍️*
Share fisabilillah 👏
[05/02, 16:10] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭
Story & Written ✍️
By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)
________________________________________________
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/LkKggQHADe9IjmqxpteXaO
________________________________________________
Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V
________________________________________________
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
________________________________________________
*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝♀️🧝♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Book one free*
*Gargaɗi*
Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.
Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.
Page ▶️1️⃣7️⃣
*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*
Sakinta ya yi ya rufe ƙofar da key kana ya ja hannunta suka nufi ciki.
Bayan sun karasa tsakiyar palon kara rungumarta ya yi ya cigaba da shinshinar wuyanta.
"Haba Nas ka bari mu gaisa mana."
Safina ta yi magana, haɗe da zame jikinta daga na Nas d'in.
Cikin marairaice fuska Nas ya kalli Safina kana ya ce.
"Haba my love, waca irin gaisuwa zamu yi da ta wuce wannan?ni wannan abunda nake yi miki shi ne gaisuwar masoya,wancan gaisuwar sai dai a waya,kuma ni ban ma ɗauke shi da mahimmanci ba."
Ya karashe magana, haɗe da saka hannu ya tallafo duka kumatunta duga biyu,ya haɗa bakinsu waje guda ya shiga yi musu wani irin