Showing 15001 words to 18000 words out of 52064 words
Chapter 6 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt
Allah dai ya sa lafiya tun jiya na tura miki saƙo na ga baki buɗe ba har yanzu.
Sorry ni ce na wahalar dake ko? wallahi ke ɗin ce ta musamman, faɗa min please yaushe zamu sake haɗuwa dan wallahi tun jiya da muka rabu nake cikin wani yanayi,ki taimaka mu haɗu please.
Bayan ta kammata karanta duka saƙon nin na sa ta shiga yi masa reply kamar haka.
Sorry jiya na gaji ka wahalar da ni sosai, shi ya sa ban hau online ba na kwanta,dan ban jima da tashi ba ma wallahi,
Maganar haɗuwa kuma ka bari zan gaya maka sanda zamu haɗu.
Tana gama rubuta masa haka ta tura masa.
Bayan ta fita daga cikin chat d'insu da Nas ne ta shiga na Suraj.
Shi ma dai hoton da ta tura masa ya yaba, haɗe da cewa ya yi missing d'inta sosai,lafiya tun jiya bai jita ba, Allah ya sa ba ciwon maran da take fama da shi ba ne ya tashi.
Murmushi ta saki haɗe da yi masa reply shi ma.
*Naila*
Bayan na fito daga wanka shiryawa na yi cikin wata jan a tamfa supa ɗinkin riga da sket,bayan na taje kaina na nannaɗe shi ya yi kamar donut,kana na d'auko dankwalin atamfan na yi d'aurin ture ka gasiya da shi powder kawai na shafa,sai turaruka dana fesawa jikina,bayan na kammla na ɗ'auki farin mayafi na yafa,kasancewa kayan nawa akwai fari a jiki.
Takalmi da jaka su ma duƙ fari ne,
Ina gamawa na ɗ'auki wayata da key ɗin motata na fita na bar ɗakin na nufi palo,dan shan tea,dan tun dana fito nake zuba idon ganin Asiya ta kawo min tea amma shiru har na kammala shiryawa.
A baƙin kofar ɗakina na haɗu da ita zata kai min tea ɗin,kallon ta na yi kana na ce "Ki kai min dinning kawai na sha acan."
Kai ta geɗa min kana ta juya ta nufi dinning.
Tea da bread na zauna na ci bayan na kammla na yi wa Momma sallama na wuce.
Parking lot na nufa bayan na amsa gaisuwan security's ɗin da kuma Lado mai wankin motoci na shiga motata bayan mai gadi ya buɗe min gate na ja ta na nufi makaranta.
Security's guda biyu na cikin wani mota za su min rakiya dan Daddyna baya so na fita wani waje ni kaɗai,tun lokacin da wannan abun ya faru da zu a hanyar Gombe.
Kullun ina jin haushin rakiyan da suke min,amma yau normal na ji,ko dan Mommana ta bani labrin abunda ya faru ne oho ?
*Maher*
Bai wani jima a gidan Isham ba ya fito,dan bai fi mintuna 15 ya yi a ciki ba,a hakan ma don an kawo masa abinci ne shi ya sa.
Kasan cewa bai yi breakfast ba ne ya sa da aka kawo masa abincin bai yi musu ba ya zauna ya ɗan ci kafin su fita suka fita da Isham suka nufi masallaci don yin sallan jumma'a,don yau jumma'a ne.
Da motarsa suka tafi shi Isham ya bar tasa motar a gida.
Bayan sun bar gidan Isham, ya hau titin da zai kaisu masallacin ne ya zo sallaka dayan titi,wata mota ta taho a guje ta zo ta bugi tasa motar,ba shiri ya taka burki.
Ni kuwa ina sauri na karasa makaranta don naga ɗaya ta yi bana so a sauko daga sallar jumma'a cinkoso ya yi yawa a hanya ne shi ya sa nake duƙi cikin sauri.
Ina cikin duƙi aka kirani a waya garin duba wanda ya kira ɗin ne na budi wata mota ba shiri na taka burki haɗe da dafa kirji,amma na kasa fitowa daga cikin motar,ballanta na ga wanda na buge din.
Maher ne ya juya ya kalli Isham cikin ɓacin rai ya ce.
"Ka ga ƴar iska ko taƙi fitowa ta ban haƙuri."
"Yi haƙuri, amma ta ya ya kasan mace ce a ciki.?"
"Haba Isham kai ma kasan da na miji ne da tuni ya s'auke glass ɗin motarsa yana bani haƙuri."
"Haka ne kuma,toh ka yi haƙuri kawai ka ja motar mu tafi."
"Ta buga min mota ka ce na ja mu tafi ?bayan ban je na duba inda ta buda din ba.?"
Bai jira amsar da Isham zai bashi ba ya buɗe murfin motar ya fita.
Inda motarta take ya nufa,ya yi nocking na sauke glass ɗin motata,
Ido cikin ido muka yi da shi.
*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*
*More comment more typing ✍️*
Sharen fisabilillah 👏
[22/01, 13:44] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭
Story & Written ✍️
By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)
________________________________________________
Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V
________________________________________________
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ
________________________________________________
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
________________________________________________
*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝♀️🧝♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Book one free*
*Gargaɗi*
Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.
Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.
Page ▶️🔟
*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*
Yana gadin ita ce ya s'auke ajiyar zuciya,dan har ga Allah ya ji daɗin ganinta,lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai kana ya soma magana "Ohhh ashe ke ce,na tabbata kina sane kika buga min mota."
Ni ma dai har ga Allah na ji daɗin ganinsa dan rabun da na gansa tun bikin Safina.
Kasan cewa ni ma ina da nawa miskilanci ne ya sa na haɗe rai ni ma ,haɗe da cewa "Kamar ka sani kuwa na gane motarka shi ya sa ina ganin ka taho zaka sallaka titi na yi sauri na bugi motarka,kama ci sa'a da bata yi komai ba,dan ni na so a ce wani abu ya sameta, muga yanda zaka yi ka tafi masallaci."
Ina kai wa nan na kunna motata da sunan barin wajan ya yi saurin shan gabana ya tsaya haɗe da ziro hannu cikin aljihu wangonsa ,idonsa ƙur a kaina babu alamar matsawa.
Security's ɗin da ke bayana a wani mota daban ne suka fito suka ƙarasa inda yake tsaye suka saka hannu da sunan masar da shi,suna haɗa ido da shi ba shiri suka suke hannun su ƙasa haɗe da juyowa suka koma cikin motar su.
Ni kuwa ɗuk abunda ya faru a gaban idona ya faru.
Wani irin haushin Security's din na ji,a zuciyata kuwa faɗi na ke 'yan iska kawai matsorata wai a haka suke gadi na,a fili kuwa kunna motata na yi nayo kansa ba shiri Maher ya matsa cikin ɓacin rai ya nufi motarsa da s'auri haɗe da fizkarta a guje ya bi bayana.
Kallonsa Isham ya yi, kana ya ce.
"Wai Maher ina zamu je ne na ga ba hanyar masallaci muka nufa ba."
Ci kanka bai ce da Isham ba,
Kafin ka ce me ya karasa kusa da motata,ya buɗe ta shi ma,amma bai kai bugun da na yi wa nasa motar dazu.
Kasan cewa ni mace ce,gani da shegen tsoro,
Ina da tsiwa sosai amma tsoro kam ba'a magana.
Yana buga min mota, murfin motar ta buɗe,iska ya dinga kaɗawa da karfi ba shiri na saki stearing motar kafin ka ce me na fasa ihu haɗe da kwanciya kan kujera hannuna na waje,
Maher na ganin haka ya yi parking da sauri ya fito ,cikin sauri ya karasa inda motata take ya afka ciki,bai bi ta kaina ba sai da ya shiga ya saka hannu ya kashe motar tukun kafin ya juya ya kalli inda make,
Ganin ba abunda ya sameni ne ya sa shi s'auke ajiyar zuciya haɗe da tallafo kaina kana ya soma magana.
"Naila dama ke matsorociya ce bansani ba ?"
Ci kansa ban ce masa ba sai harara da na dalla masa.
Dan har yanzu a sorace nake.
Ganin ban saƙe yin magana ba ne, ya sa shi sake faɗin "Sauko mu je motata na ajiye ki inda za ki je na wuce masallaci an kusa tada sallah."
Kasan cewa a sorace nake har yanzu bazan iya tuka mota ba ne ya sa ban yi mai musu ba na geɗa mai kai,kana na shiga koƙarin fitowa.
Ƙara na saki a lokacin da na ɗaga kafata na ji ya na min zafi.
"Sorry Hajiya bari na taimaka miki ki samu ki sauko."
Dayza daga Security's ɗin ya faɗi yana mai chuso kansa cikin motar.
"Karka kuskura ka taɓa ta."
Ya ji an faɗi a bayansa.
Juyowa ya yi ya ga Maher ne tsaye a bayansa fuska a haɗe.
Yanayin yanda ya ga fuskarsa ne ya sa ba shiri Mahmud ya fito da kansa daga cikin motar.
"Matsa gefe na fito da ita, in na fito da ita sai ka ɗauki mortar ka maida ita gida."
Kai Mahmud ya geɗa kana ya matsa gefe ya bawa Maher hanya ya kara shiga cikin mota,dan dama fita ya yi ya bata hanya ta fito sai ta kasa.
Yana shiga ya tayata fitowa daga ciki, haɗe da d'auko mata jakarta da talalminta kana ya cincibota ya nufi motarsa da ita.
Kallonsa kawai nake sai yau na kare masa kallo,lokaci ɗaya abunda ya faru a baya suka shiga dawo min lokaci ɗaya naji haushin kaina,akan abunda na yi masa a baya.
Shi kuwa Maher har ya karaso gaban motarsa Isham dake kallon dramar su tun d'azu yaƙi fitowa ne ya fito yanzu ya buɗe masa murfin motar ya sakata a baya ya mika mata jakarta da takalmanta,sai a lokacin ya kalleta kana ya ce "Sorry kin ji matsorociya."
Yanzu ma ban amsa masa ba sai ma harara da na kara aika masa da shi.
Guntun murmushi ya saki haɗe da rufo min kofar ya koma gaban mota ya ja motar a guje ya nufi masallaci,
Ina ganin inda ya kawo ni na kalli keyarsa dake kusa da kujeran da nake kai,kana na ce " Me zan yi a masallaci kuma? Ni fa makaranta zan je muna da lecture 2 am please ka kai ni."
"Abunda ake a masallaci shi zamu yi,kika kara magana kuma sai na yi miki abunda yafi wanda na yi miki yanzu."
Ba shiri na ja bakina na yi shiru.
Juyowa ya yi ya kalli Isham kana ya ce.
"Sauko muje Isham."
Baki Isham ya buɗe da niyar yin magana Maher ya haɗe rai, dariya Isham ya ɗan yi haɗe da buɗe murfin motar ya fita.
Shi ma fita wa ya yi,ina ganin haka na ce " Wai ni kuma fa.?"
Ki zauna ki jira mu yanzu zamu fito,bai tsaya jiran mai zan ce ba ya buɗe murfin motar ya fita ya kulleni ya yi cikin masallaci.
"Kutumelesi wai rufe ni fa ya yi.?"
Na yi magana cikin takaici,da kuma haushin abunda ya yi min.
Bangaren su Mahmud kuwa ƙin komawa gida suka yi dan in suka ce za su koma gida ba su san mai za su gayawa Hajiya Sumayya ba in ta tambaye su inda Naila take,shi ya sa suka bi bayan su,ganin masallaci suka zo ne ya sa hankalin su kwanciya, haɗe da sauko wa su ma daga cikin motar dan yin sallah.
Amma ba su shiga cikin masallaci ba nan waje suka yi sallah,saboda kar su shiga ciki su tafi shi ya sa suka tsaya inda za su gansu idan sun tashi tafiya.
Ni kuwa ina cikin mota na fito da wayata ina dannawa,lokaci zuwa lokaci nake jan tsaki.
Ga gumin da nake yi,saboda rashin kunna AC da bai yi ba.
"Gaskiya kai mugu ne Maher,saboda sabar mugunta ka rufe ni ka fita ka bar ni cikin mota ko AC baka kunna min ba."
Na faɗi idona na taruwa da kwalla,dan ni ina da s'aurin kuka in abu ya ban haushi,
Ɗuk da akwai ni da tsiwa amma kwata -kwata in abu ya bata min rai nan da nan zaka ga hawayena,dan ina da rauni sosai.
"Allah ya isa Maher da abunda kamin."
Na faɗa ina mai sharen ƴar kwallan da ya zubo min.
"Ni ban ce miki Allah! ya isa ba,sai ke za ki ce min Allah ya isa.?"
Na ji ya faɗi a lokacin da yake saita zamansa sosai kan kujerar motar alamar yanzu ya shigo.
Ɗagowa na yi na kalli inda yake zaune na banƙa masa harara.
"Karki kara min harara kika kara min abunda ya fi na ɗazu zan yi miki mara kunya."
"Ai mara kunya na gidan ka."
Na faɗa can ƙasar maƙoshina,
Ya jita tsarai ya share ta.
Tada motar ya yi ya juya hancinsa ya bar masallacin.
Su Mahmud ba su bi bayan su ba,sai da suka tabbatar sun fita tukun kafin shi ma ya ja motar Naila da yake ciki shi ma Ahmad ya ja suka bar harabar masallacin.
Bayan sun hau titi ya kalleta ta cikin mirror motar ta yi mai masifar kyau da kayan dake cikinta sosai,a zuciyarsa ya ce.
Safina kam bata iya irin wannan kwalliyar ba,ko wanda take yi in zata je unguwa ma ba ta kai wannan ba,
Ta dayan bangaren kuma ya ce.
Ta ya ya zata iya kwalliyar kirki tunda ƴar talakawace bata saba saka kayan masu sada ba, ballantana ta san darajar su.
Can ƙasar maƙoshisa ya ce.
Gaskiya Naila baki kyauta min ba,har yanzu na kasa tire ki a cikin zuciyata.
Ɗuk da irin wulancin da kika min amma kina nan a cikin zuciyata Naila.
"Abokina lafiyarka kalau kuwa?"
Ɗan haɗe rai ya yi ya ce.
"Me ka ga ni.?"
"Na ga sai magana kake kai kaɗai."
"Kana nufin ka ji abunda na faɗa ?"
"Eh na ji."
Isham ya bashi amsa.
Share sa Isham Maher ya yi kana ya kalli Naila ta cikin mirror motar ya ga tana murmushi.
Shi ma sai ya sinci kansa da yin murmushi.
Kana ya juya ya ci gaba da tuƙin da yake yi.
Kemis ya kai ni aka duba kafar akata aka bani magani da zan dinga shafawa a kafar,da wasu magunguna na sha,kana muka fita wajan rike da hannunna ina dingishi.
Ganin ina ɓata masa lokaci ne ya sa shi dauka ta cak ya karasa gaban mota ya saka ni haɗe da rufo min murfin motar.
Kana shi ma ya zaka ya shiga.
Kallon Isham da yake tsaye bai shiga ba ya yi kana ya ce.
"Kai kuma sayuwar me kake yi ba za ka shiga mu tafi ba.?"
"Ku je gida zan tafi na gaji da yawon zan nemi abun hawa na tafi gida."
Isham ya yi maganar yana mai saida mai napep d'in da ya zo wucewa,kana ya faɗa masa inda za shi ya shiga mai napep ya ja napep d'insa suka bar wajan.
Kafaɗa Maher ya ɗaga kana ya ja motarsa ya bar wajan.
Sai da suka bar wajan kana ya ce.
"Bari na kai ki gida."
"A'a makaranta zan je ina da lecture yanzu ma lokaci ya kusa saura 8 minut mu shiga,dan Allah ka taimaka ka kara gudun motar ,dan in ban je da wuri ba wannan Malamin ba barina zai yi na shiga ba."
Ci kanta bai ce da ita ba.
Kuma bai kara gudun motar ba,sai ma kara rage dugun da ya yi.
"Haba Ya Maher dan Allah ka taimaka min ka yi s'auri please kar na yi late."
Nan ma dai bai kula ta ba.
A tak'aice dai sai wajan 2:5 Am suka isa makarantar na su.
Parking ya yi kana ya fito,zan fita kenan ya ce.
"Koma ki zauna ina zuwa."
Banza na yi masa.
Abun mamaki sai na ga ya nufi class ɗinmu.
"Wai da ma ya san class ɗin da nake ne.?"
Na tambayi kaina.
Ga mamaki fal a raina.
Shiga cikin class ɗin ya yi bayan ƴan mintuna kaɗan na ga ya fito da Malamin mu, kana ya dawo gaban motar ya bude bangaren da nake kana ya cinciboni.
"Ɗan Allah ka sauke ni zan iya karka min haka a gaban Sir Junaid ."
"Ko saurayinki ne.?"
Ya yi maganar yana tsareni da ido.
Kauda kaina na yi gefe har muka karasa class ɗinmu.
Bai direni a ko ina ba sai kan kujerar,yana ajiye ni ya ɗan ronkofo da kansa kana ya matso da bakinsa daidai kunnena kana ya ce.
"Ina jiranki a waje."
Daga nan ya juya ya fita.
*Fulalin Jajirtattu ce ✍️*
*More comments more typing ✍️*
Share fisabilillah 👏
[27/01, 14:57] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭
Story & Written ✍️
By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)
________________________________________________
Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V
________________________________________________
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ
________________________________________________
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
________________________________________________
*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝♀️🧝♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Book one free*
*Gargaɗi*
Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.
Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.
Page ▶️1️⃣1️⃣
*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*
Bayan fitar Maher Fauziya ƙawata wacca ɗuk cikin class ɗinmu ita kaɗai nake kulawa,saboda ita ma bata da hayaniya sosai shi ya sa tamu ta zo ɗaya.
"Kawata gaskiya wannan saurayin naki ya haɗu yaushe kika samo shi babu labari.?"
Tsaki na ja kana na ce.
Ni ba saurayina ba ne,mijin ƙawata Safina ce,kawai kaɗe ni aka yi a mota dazu da zan zo school shi ne ya taimaka min."
Ɗan guntun murmushi Fauziya ta yi kana ta ce.
"Gaskiya ban yedda ba,ko da kuwa mijin kawarki ce amma na tabbata yana sonki,saboda yanyin yanda na ga yana kallonki kaɗai ya isa ya tabbatarwa da mutun hakan."
"Wannan kuma ni ba matsala ta bane tunda ni ba son sa nake ba."
'Yan class ɗinmu kuwa da kallo suka bi Maher da shi,'yan mata sai faɗi suke wow,gaskiya wannan gayen ya haɗu,wata ta ce.
"Ni wallahi ko ta halin ƙaƙa sai na samu numbersa na fara soyayya da shi,dan bazan taba haƙura da wannan handsome din nan ba."
Wani irin dogon tsaki na ja kana na juyo a fusace na ce.
"Haba kun ishemu da surutu,ku tashi ku bisa ku je can ku karata ,
Ku ko kunya ma bakuwa ji,
In banda subar da mutunci da kuma aji ba, saurayi bai ce yana sonku ba ? Bai kuma neme ku ba ɗuk ku bi ku damu mutane a kansa."
Na yi maganar cikin daga murya.
Dariya 'yan matan da suke zaune a bayan namu suka yi, kana dayan ta kalle ni ta ce.
"Ke dai ki ce kishi kike yi saboda mun ce muna son saurayinki."
Ina jin haka na kurma uban ƙara ba shiri Sir Junaid da yake magana sa Maher a waje suka shigo a tare.
Ina ganin shigowar su na ɗaga kafata na dora kan teburin dake gabana na shiga kuka