Showing 18001 words to 21000 words out of 52064 words

Chapter 7 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt

06 Mar 2025

2589

ina faɗin.


"Wayyo kafaɗa zafi wallahi ciwo yake min sosai a kai ni gida bazan iya yin lecture ba, Allah ji nake kamar zazzabi zai rufe ni."


Maher na jin haka ya karasa kusa da ni haɗe da zama gefena ya ɗago fararen kafafuwan tawa ya tire takalmin dana saka kana ya ɗora kafar saman cinyarsa ya buɗe jakata ya d'auko man zafin da aka bani a kemis aka ce na dinga shafawa ,ya shiga shafa min a kan kafar.


Cikin shogoɓa na ce.


"Washhhhh! Da zafi fa ka yi min a hankali."


Yanda ya ga na yi maganar ba karamin burgeshi na yi ba,


Dan Maher na mugun son mace mai shogoɓa,amma bai samu ba, dan Safina babu abunda ta iya.


Dan haka shi ma biye min ya yi ya ce " Ya ce I'm sorry dear bari na hura miki."


Bai tsaya jiran mai zan ce ba ya shiga hura min wajan a hankali.


Wani irin iska mai sanyi yake fitowa daga bakinsa kamar AC da aka kunna yanzu ya fara sanyi.


Lumshe idona na yi,sanyin na ratsa kafafuna.



Gaba ɗaya mun manta a cikin aji muke sosai ya maida hankali wajan shafamin man zafin da hura min iskan bakinsa.



Sir Junaid ne ya yi gyaran murya,sai a lokacin muka dawo cikin hayyacinmu.


Ta gefen ido na kalli 'yan matan d'azu,sai na ga jikinsu duk ya yi sanyi.



Tattausan murmushi na sakar musu haɗe da yi musu gwalo.


Ina cikin yi musu gwalo na ji Maher na cewa " Sir bari mu je gida kawai saboda na ji jikinta ya ɗan fara zafi."


"Okay,ba damuwa Allah ya kara sauƙi."



"Ameen ya Allah."

Maker ya amsa.

Kana ya ɗauki jakata ya rataya a kafaɗa ya kara cincibata muka bar cikin ajin.



Mota ya wuce da ni,wannan karon a gaba ya saka ni ba a baya ba,


Sai da ya ajiye ni a ciki tukun, kafin ya miƙa min jakata haɗe da cewa.



"Na gaji da zama drevanki a gaba za ki zauna."


Ya kare maganar yana mai rufe min mota.


Kana shi ma ya zaga ya shiga mazaunin dreve ya kunna motar ya ja muka bar harabar makarantar.



Sai da ya ɗauki hanya kana ya juya ya kalle ni ya ce.


"Ki dinga nuna min hanyar gidan naku dan ni ban sani ba."


Kai na geɗa mai kana na shiga nuna masa hanya.


Wani irin miskilin Murmushi ya saki sanda ya hango su Mahmud a bayansa suna binsu.



Ummm! ashe bayanmu ku ka bi baku koma gida ba,ya yi maganar a cikin ransa,haɗe da samo waje ya yi parking.


Ina ganin ya yi parking na juya na kalle shi kana na ce .


"Ya Maher bamu fa zo ba."


A maimakon ya bani amsa sai ma buɗe mirfin kofar da ya yi ya fito ya saida motar Naila da Mahmud yake ciki.


Tsayawa Mahmud ya yi haɗe da sauke glass ɗin motar,suna hada ido da Maher ya sosa kai haɗe da faɗin.


"Sorry yellabaï wallahi in na je gida da wannan motar babu Hajiya karama in Hajiya babba ta tambayeni bansan irin amsar da zan bata ba."


"Okay, buɗe min bayan mota na sa maka ita."


Sauka Mahmud ya yi haɗe da buɗe murfin kofa.


Ina nan ina zaune,ta cikin mirror motar nake ganin sa da Mahmud,


Ina cikin kallonsu ban ankara ba har ya zo inda nake kafin na yi magana har ya cinciboni ya wuce dani cikin motata ya sakani a baya ya sake komawa ya dauko min jakata da takalmina da ledan bagungunan da aka butuna min ya dawo gaban motar ya ajiye min su akan cinyata.


Kana ya kalleni ya ce.


" Allah ya kara sauƙi."

Baki na buɗe daniyar yi masa magana ya juya ya bar wajan.


Ya nufi motarsa ya shiga ya yi revas ya bar wajan ya nufi restored,don samowa kansa abunda zai ci.


Da kallo na bi motarsa da shi har ya bar wajan.


Kana na maida dubana kan Mahmud, cikin ɗaga murya na ce.


"Kai kuma mai kake jira ba za ka shiga ka ja motar mu tafi ba.?"


Cikin mamaki Mahmud ya kalleni,dan tunda nake ban taba daga masa murya ba sai yau.



Kamar na san abunda yake tunani na ce.


"Sorry Mahmud."


Murmushi Mahmud ya saki yana karantar yanayin da nake ciki, kana ya ce.


"Ni ya kamata na baki hakuri Hajiya ba ke ba,dan haka dan Allah ki yi haƙuri."


Kai kawai na geɗa masa,kana na ce.


"Please ka shiga ka ja motan nan mu tafi gida Mahmud."


Da toh ya amsa kana ya shiga mota ya ja muka karasa gida.


Bayan ya danna honn bai gadi ya buɗe masa ya shiga da motar ciki,ya yi parking ya fita, kana ya zaga ya buɗe min ni ma,na fita a hankali dan in na danna kafar zafi take min.


Bayan na fita Mahmud ya daukar min jakata da ledan bagunguna na.


Ta gefen bango na dinga bi ina dingishi har na karasa cikin palon namu, bayan Mahmud ya buɗe na shiga.


Zaune na samu Momma a palon tana kallo.


Jin shigowarmu ne ya sata dagowa ta kalli wajan.


Tana ganina cikin sauri ta miƙe ta karasa inda muke ta rikoni ta karasar da ni sakiyar palon ta zaunar da ni kan kujera,kana ta kalli Mahmud ta ce.


"Mahmud lafiya, meye samu Mamana a ƙafa na.ga tana dingishi.?"


"Wallahi Hajiya wani ne ya..


Mahmud bai kasara magana ba,na kartse shi ta hanyar faɗin.


"Wallahi Momma driving nake aka kira ni a waya na dauko ina cikin duba mai kiran sai na bugi wata mota,da yake ashe ban rufe murfin motata bata rufu sosai ba ne ya shi ya sa a take kofar motar ta buɗu mijin Safina ƙawata ya zo wucewa da wani abokinsa a mota za su je masallaci sai ya ga abunda yake faruwa da sauri ya fara motarsa ya fito ya zo ya shiga motata ya kashe motar ya taimaka min na fito,


Shine ya kai ni kemins aka dubamin kafar tawa aka bani magunguna,ga magunguna ma a hannun Mahmud,bata maganin Mahmud."


Na yi magana ina mai kallon Mahmud da yake min kallon mamaki.


Saboda karyan da na ɗan yiwa Mommana.



Hannu Mommana ta miƙa ta karbi magungunan da Mahmud yake miƙa mata.


Bayan Mahmud ya mika wa Mommana magani da key din motata ya yi mana sallama da kuma Allah kara sauki ya tafi.



Taimaka min Mommana ta yi ta kai ni ɗakina,ta kira ƴar aikinmu ta ce ta kawo min abinci .




Da daɗɗare zazzabi mai zafi ya rife ni daƙer na yi bacci.



*Maher*


Bayan ya je restored ya ci abincinsa ya koshi ya miƙe ya nufi gidan iyayensa don yi musu sallama.



Ba shi ya fito daga can ba sai da aka kira sallar la'asar sannan ya bar gidan.


Sai da ya tsaya ya yi sallah a hanya tukun kafin ya koma gida.


Bayan ya koma babu kowa a palon,palon kaca-kaca a haka ya girgiza kai ya nufi saman shi.



Kasan cewa ya dan gaji ne shi ya sa yana hawa ya rage kayan jikinsa ya shiga ya watsa ruwa ya fito ya saka riga mara nauyi ya kwanta,


Bai dade da kwanciya ba bacci ya yi awan gaba da shi.



Ba shi ya farka ba sai gaf da magrib.


Sake shiga toilet ya yi ya kara wasa ruwa sannan ya fito ya shirya shaf -shaf cikin jallabiya da dogon wango kana ya wuce masallaci.



Da aka idar da sallah bai bar masallacin ba har sai da aka kira sallar i'sha ya yi tukun kafin ya dawo gida.


A palo ya sameta zaune ta dora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jiran shi ya dawo,dan yinwa take ji kuma bazata iya cin indomi yanzu ba saboda ta gashi da shi.



Kallo ɗaya ya yi mata ya dauke kai ya juya ya yi hanyar sama.


Yana cikin taka matattakalar ya ji tana faɗin.


"Maher yinwa nake ji abinci zan ci dan Allah ka je ka yi min takeaway,ko kuma mu tafi tare na ci acan."


Dagakar da tafiyan ya yi kana ya juya ya kalleta a fusace ya ce.



"Ni ban ce miki yinwa nake ji ba Safina sai ke ?


"Wai tukun na ma bari na tabbayeki Safina,wai ina ne gidan iyayenki yake.?"



Wani irin miƙewa Safina ta yi cikin jin haushin tambayar da Maher ya yi mata ta buɗe baki ta ce.


"Yanzu Maher cin fuska zaka min ?


Dan kawai iyayena ba masu kuɗi ba ne ban?


Ka sani duk da iyayena ba masu kuɗi ba,amma a cikin shiga mai kyau ka ganni ka ce kana so na."








*Fulalin Jajirtattu ce ✍️*







*More comment more typing ✍️*





*Share fisabilillah 👏*
[29/01, 15:05] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V

________________________________________________


Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ


________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*


*Gargaɗi*

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️1️⃣2️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*



Murmushin takaici Maher ya yi,kana ya juya ya ci gaba da taka matattakalar,


"Maher ina magana shine ka share ni ko?"



Banza Maher ya yi da ita.

Dan ko juyowa bai sake yi ba, ballantana ta sa rai zai yi mata magana.


Kofa ta yi ta juya ta nufi ɗaki a fusace.


Shi kuwa Maher kasan cewa da ya shiga palon ya kullene ya sa bai kara saukowa ba, ɗuk da bai cika barin fitilun palon a kunne ba,amma yau ya gwanmaci ya kwanta,a haka akan ya sauka Safina ya kara bata masa rai.


Kayansa ya shirya saf!dan gobe da wuri zai koma (Abuj),kuma jibi akwai basinjojin da za su ɗiba su kai gasar (Saudiya) dan an kusa babban Sallah an fara tafiyar aikin haji.


Bayan ya kammala shirya kayansa, toilet ya kara shiga ya kara watsa ruwa ya fito ya shirya cikin kayan bacci mara nauyi ya kashe fitilun ɗakin haɗe da kara gudun AC ya hau lafiyayyan gadonsa bayan ya yi addu'ar bacci ya kwanta.


Har bacci ya fara daukarsa sai ya tina da ita.


Saurin buɗe ido ya yi haɗe da zura hannunsa akan bedsheet drowe din,ya shiga lalubar wayarsa,ya dauka kana ya kunna hasken wayan ya tashi ya zauna akan gadon ya jingina bayansa da pillow kana ya shiga neman number ta da ya ɗ'auka dazu da ya ɗauko mata jakarta.


Bayan ya ga number har zai danna mata kira sai kuma ya fasa, ya ajiye wayan gefen gadon.


Tunani ya shiga yi kamar haka.


Yanzu ko ya take? Ko ta ji sauƙi oho,


Allah dai ya sa zazzabi bai kamata ba.


Ya faɗa haɗe da zamewa ya kwanta.


Har ya rufe ido sai ya ji bazai iya kwanciya ba tare da ya kira ta ya ji ya take ba,tunda shine mai laifi, ɗuk da ita ce ta jawa kanta amma yafi ta laifi.


Kara d'auko wayar ya yi a karo na biyu kana ya danna mata kira,lokacin sha ɗaya da zabi na dare har ta wuce.



Cikin baccin da ta samu ya ɗauke ni daƙer ne sabada zazzabin da nake ji, na ji wayata na ringing.



Kasan cewa bani da nauyin bacci ne ya sa kiran na shiga na farka.


Ja wayar tawa na yi,na daga,cikin magagin bacci na ce.


"Hello."


Bai amsa ba ,sai ajiyar zuciya da ya sauke kawai,haɗe da kashe kiran .


Shiru da na ji ba'a yi magana ba ne ya sa ni buɗe idona sosai na kalli screen ɗin wayar,


Idona ne ya sauka a wata number wanda bansan ko na waya ba.


Ganin babu suna ne ya sani jan gajeran tsaki haɗe da ajiye waya na kara zamewa na kwanta ina mai faɗin.


"Gaskiya ko waye ya kira ni a wannan lokacin kuma ya ki magana ban yafe ba,haka kawai za'a tashi mutun ni da daƙer na samu bacci ya ɗauke ni".Na kare maganar haɗe da rufe ido ,babu mata lokaci bacci ya kara dauka ta.


Abunda ban sani ba shine a lokacin da na tashi ajiye wayata ban sani ba na taɓa wajan kira na kara kira number Maher,har Maher zai share,sai kuma ya ce bari ya daga.


Dagawa ya yi ya kara a kunne ya yi shiru.


Yana jin baganar da take faɗa nan ne ya fahimci ban san na kira shi ba.


Murmushi ya yi haɗe da gyara kwanciyarsa sosai,ya cigaba da saurarona,


Ba shi ya kashe wayan ba sai da ya ji ina sauke numfashi alamun na yi bacci sannan ya katse ya kwanta shi ma babu jimawa bacci mai daɗi ya yi awan gaba da shi.



*Safina*


Ganin bata da mafitan da ta wuce ta kara zuwa ta dafa indomin ne ya sata miƙewa daga kwance da take akan gado, haɗe da ajiye wayar hannunta da take chat da samarinta,kana ta fita ta nufi kitchen.


Indomie da kwai ta soya kana ta dauko lemo mai sanyi ta fita ta bar Kitchen ɗin ,ta zauna palon ta ci kayanta ta koshi ta sha lamon da ta d'auko kana ta yi wata uban gyatsa haɗe da miƙewa ta koma ɗakinta ta bar plate d'in da jarkar lemon a palo.



*Gidan iyayen Maher*


Nihilah ce kwance akan gadonta ,ta kalli Nihal da ita ma take a kwace a nata gon kana ta ce.


" Nihal gaskiya dazu da na ga yaya Maher ya zo gidan nan na ɗ'auka hukun tamu zai yi akan abunda muka zo muka faɗawa grandpa ."


Cikin sanyin murya Nihal ta buɗe baki ta ce.

Ni da na gansa babu wani tsoro da na ji,tunda ni ba ni ce na je na gayawa grandpa d'in ba,kuma ko shi ma Bro Maher ɗin shaida ne,tunda ba halina ba ne."



Cikin rashin hakurin irin na Nihilah tashi zaune cikin daga murya ta ce.


"Nihal me bangane mai kike nufi ba ?"



Nihal bata kula Nihilah,sai ma juya mata baya da ta yi ta ja bargo ta rufe har kanta.



Kofa Nihilah ta yi kana ita ma ta kwanta.



*Safina*


Ba ita ta yi bacci ba sai wajan karfe 1 na dare Sannan ta yi bacci.


Dan har video call ta sha da Suraj,sai daga baya suka yi sallama kana ta kwanta.


*Washe gari*


Tunda ya dawo daga masallaci bai koma ba,dan sai wajan 6 da rabi na safe ya dawo gidan,yana shiga palon idonsa ya sauka akan plate d'in abinci da jarkar lemo a kasar carpet da Safina ta ci ta bari a palon.


Kansa kawai ya girgiza haɗe da karasa wajan ya d'auke plate d'in da jarkar lemon ya kai kitchen kana ya dawo ya nufi sama.


Yana zuwa sama har zai koma bacci kafin 8 ta yi sai ya fasa ya dau akwatinsa ya bude ya karasa shirya kayansa ya saka abubuwan da bai saka ba kana ya maida akwatin ya rufe


Bayan ya kammala, duba agogon dake manne a bangon ɗakin ya yi gaya 7pm har da minti sha biyu, toilet ya shiga,sai daya ɗauki kusan mintuna 15 kafin ya fito ya shirya cikin kayansu na matuƙan jirki,bayan ya kammala ya sake duba agogo ya ga 7 harda mintuna 42 waya ya dauka ya dannawa drevan gidansu kira,bugu biyu ya daga,sai da ya amsa gaisuwan sa tukun kafin ya ce.



"Habu kana ina ne.?"


Ta cikin wayan Habu dreva ya amsa kamar haka.


"Gani ina hanya yanzu zan karaso ranka ya daɗe ."


"Okay".


Kawai ya faɗa haɗe da kashe kiran.


Kana ya ja akwatinsa ya fita ya rufe part dinsa ya sauka k'asa.


"Sannu Alhaji za'a koma.?"


"Eh Baba zan koma sai mun dawo."


"Toh Alhaji Allah ya tsare."


Ameen Maher ya amsa kana ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya tire dubu goma ya miƙawa mai gadi.


"Alhaji na ga wata bai kare ba kana bani albashi kuma."


Karba Baba ai albashin ka yafi dubu goma wannan kawai baka na yi ka dinga siyan abinci kana ci kafin Nadia ta dawo, amma dan Allah in ka tashi fita siyan abincin ka tabbata ka rufe min ko ina kafin ka tafi."


Karba Baba mai gadi ya yi ya shiga yin godiya,kana ya ce.


"In sha Allah Alhaji zan yi yanda ka ce, Allah ya tsare hanya ya sauke ka lafiya ya kuma tsare gabanka da bayanka."




"Ameen."

Maher ya amsa.


Nocking suka ji ana yi baba mai gadi ya buɗe.


Habu dreva ne ya shigo haɗe da durkusa har kasa ya gaida Maher kana suka gaisa da baba mai gadi kana ya ja akwatin Maher ya yi waje da shi.


Shi ma Maher ya kara yin sallama da baba mai gadi kana ya bi bayan Habu.


Yana fita Habu dreva ya buɗe masa bayan mota ya shiga ya rufe masa kana shi ma ya zaga mazaunin dreve ya shiga ya ja motar suka nufi airport.



Suna zuwa airport,bayan Habu ya ajiye shi suka yi sallama ya tafi shi kuma Maher ya nufi ciki.


Mutanan wajan sai gaisheshi suke yi hannu kawai yake daga musu 'yan matan wajan kuma sai binsa suke da kallo suna hadiye yawu.


Bangaren Maher kam bai ma san suna yi ba,a haka dai har ya karasa wajan.


Bayan mintuna talatin kowa ya shiga jirgi,sai da suka daidaita komai na jirgin kana ya ja jirgin suka lula sararin samaniya,suka nufi (Abuja)






*Funanin Jajirtattu ce ✍️*




*More comment more typing ✍️*




Share fisabilillah 👏
[29/01, 15:05] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DEXGcEbLae77lzVJ1DsF0a

________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V


________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*


*Gargaɗi*

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️1️⃣3️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*


*Safina*



Ba ita ta farka daga bacci ba sai wajan sha biyun rana, tashi ta yi ta zauna kan gadon haɗe da yin wata miƙa da wata doguwar hamma,da ɗuk wanda yake zaune a kusa da ita zai himci cewa yinwa take ji.


Bayan ta gama hamma da miƙa ,sauka ta yi daga kan gadon ta nufi toilet ta yi brosh da alwala kana ta fito ta shimfiɗa sallaya ta yi sallar asuba da bata yi ba,sai yanzu.


Bayan ta i'dar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login