Showing 21001 words to 24000 words out of 52064 words

Chapter 8 - SANADIN RABUWAR book1 by Sakina Isma'il-WPS Office.txt

06 Mar 2025

2587

da sallah ta shi ta yi ta naɗe sallayar da hijab din ta aniye,kana ta juya za fita ta nufi kitchen don samar wa kanta abunda zata ci.


Ruwan tea kawai ta ɗora,bayan ya yi zafi ta sauke ta hada tea mai kauri ta juya ta bar kitchen ɗin da dawo ta zauna palo,kana ta shiga shan tea ɗin.


Bayan ta gama shanye tea ɗin ta shi ta yi ta koma ɗakinta ta dauko wayarta ta kira Hajiya don jin in an samu mata ƴar aikin.


Misscall biyu ta yi mata bata dauka ba,sai ana uku ta d'auka,bata tsaya amsa gaisuwar Safina ba ta ce.


"Kinga Safina ina sane da ke ,gashi yanzu za'a kawo miki ,tana kaiwa nan ta kashe kiran.



Bayan ta kashe kiran ta ja dogon tsaki haɗe da cewa .

" Yarinya sai shegen damu,ki sani fa ba dan kina min abunda nake so ba da babu abunda zai sa na sauraranki Safina, sabada kwata -kwata bana hulɗa da talakawa."


Ta kare maganar haɗe da miƙewa ta fita ta bar ɗakin ta mufi palo dan zuwa ganin matar da ta kawo mata ƴar aikin da za'a kaiwa Safina,dan tun d'azu aka zo aka sanar mata da zuwan su amma ta kasa tashi sai yanzu.


Tana shiga palon matar ta zame ta zauna a kasar carpet ɗin,kana ta buɗe baki ta ce.


"Hajiya barka da fitowa."


"Yauwa barkan ka dai."


Ta faɗi tana mai karasa wa gaban kujeran ta zauna ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya.



Bayan ta zauna ta kalli yarinyar da aka kawowa Safina,bata wuce shekaru 12 biyu ba rakube a bayan kujera dan tun da suka zo gidan ta kasa sakewa saboda kyan da gidan ya yi ,ya sata jin tsoron zama a ciki.



Sai da ta karewa yarinyar kallo saf kana ta maida dubanta kan Lantana kana ta ce.


"Wannan ce ƴar aikin.?"


"Eh ita ce Hajiya."


"Amma wannan yarinyar kamar ta yi kankanta bazata iya wannan aikin dana lissafo maki ita kadai ba."



Murmushi Lantana ta yi kana ta juya ta kall Indo kana ta ce.



"Ke! Indo baki gaida Hajiya ba?"



"Hajiya ina wuni ?"


"Indo ta faɗa."


Murmushi Hajiya Nafisa ta yi kana ta amsa da.

"Lafiya lau."


Kana ta kara maida dubanta kan Lantana ta ce.


"Lantana ya na ganta dun afirgice.?"



"Wallahi Hajiya bata taɓa ganin irin wadennan gidajan ba,ballantana ta shiga ciki,shi ya sa,kika ganta duk a tsoroce amma na tabbata in an kwana ɓiyu za ta saɓa."


"Lantana ta faɗa."


"Okay,shi ke nan ba damuwa,tashi ki lega sakar gidan ki kiran mun Habu ,ku zo tare."



"Hajiya Nafisa ta faɗa."


Da toh Lantana ta amsa haɗe da miƙewa,ai Indo na ganin haka ita ma ta miƙe,kallonta Lantana ta yi kana ta ce.


"Indo ya dai.?"


"Zan biki."


Cewar Indo.


"Dallah Malama koma ki zauna ba tafiya na yi ba."


Mai Hajiya zata yi in ba dariya ba,sai da ta yi mai isarta kana ta sagaita,



Kallon Lantana ta yi kana ta ce.


"Barta ta biki d'in,mana Lantana."


"Toh Hajiya."


Cewar Lantana,kana ta kalli Indo ta ce.


"Mu je toh."


Tana gama fadar haka ta juya ta bar wajan.


Indo ta bi bayanta suka fita.


Babu jimawa suka dawo da Habu dreva.



"Sannu da hutawa Hajiya,gani ance kina kirana."


"Yauwa sannu Habu,ka ɗauke su ka kai su wajan matar Maher,in ku ka shiga ku ce ni na turo ku."



"Toh Hajiya."


Habu ya amsa.


Kana ya miƙe ya kalli su Lantana ta Indo ya ce.


"Ku tashi mu tafi toh."


Miƙewa Lantana ta yi,kana ta kalli Indo ta ce.


"Ɗauki jakar kayanki mu tafi."



Kai Indo ya geɗa kana ta cincibi jakar kayanta,bayan Lantana ta yiwa Hajiya Nafisa sallama suka bar palon.



Suna fita sakar gida Habu ya kunna mota, kana ya buɗe bayan motar ya kalli Lantana ya ce.


"Ku zo ku shiga baya."


Kai suka geɗa haɗe da zuwa suka shiga baya,ya rufe musu kofa.


Shi ma ya zaga mazaunin dreve ya shiga baba mai gadi ya wangale musu gate ya fita ya bar gidan ya nufi unguwar su Maher.



Habu dreva kuwa ba dan komai ya sa ya ce su shiga bayan ba sai don tsamin da ya ji Indo na yi, Lantana kuma babbace bazai yu ya ce mata ta shiga gaban mota ba, shi ya sa dukan su ya ce su shiga baya .




Suna zuwa unguwar su Maher,a waje ya yi parking ya fito,kana ya zaga ya buɗe musu murfin motar ya ce.


"Ku sauko mun zo."


Fitowa Lantana ta yi,ita ma Indo ta fito,ya maida murfin motar ya rufe,


Kana ya nufi ɗan karamin gate ɗin,suna binsa a baya.


Nocking ya yi mai gadi ya zo ya buɗe.


"Ah Mala Habu kai ne ka sake dawowa.?"


"Eh wallahi ni ne baba."


"Toh sannu da zuwa, Allah dai ya sa lafiya.?"



"Lafiya lau Baba wajan Hajiya muka zo, Allah ya sa tana nan.?"


"Eh tana ciki,ku shiga."


Kai Habu ya geɗa kana ya kalli su Lantana ya ce.


"Ku zo mu shiga."


Kai suka geɗa kana suka bi bayansa suka nufi cikin gidan.



A bakin kofar shiga palon Habu ya tsaya ya yi nocking,sai da aka dau kusan mintuna ɓiyar kafin a zo a buɗe.


Kallon su ta shiga yi daga sama har kasa.



Sai da ta karewa su Lantana kallo saf kafin ta juya ta kalli Habu,


Kasan cewa Habu ya gana mai take nufi ne ya sa shi buɗe baki ya fara magana.



"Hajiya Nafisa ce ta ce na kawo su wajan ki."


"Okay, ka jira mu a waje in mun gama magana zata sameka."


Da toh Malam Habu ya amsa kana ya juya ya bar wajan su kuma suka shiga ciki.



Magana suka yi akan kuɗin da za'a dinga biya su ɗuk wata,sai Lantana ta ce dubu uku ma ya yi, Safina ta kara mata dubu biyu ya zama dubu biyar,


Godiya sosai Lantana ta yi, bayan ta gama da su ta miƙe ta nufi sama dan faɗawa Maher,sai dai,tana zuwa ta tarar da kofar Maher a kulle,


"Kai! kar fa a ce mutumin nan komawa ya yi bai gaya min ba,dan na ga motarsa dazu dana buɗewa su Habu ƙofa."


Ta yi magana.


"Tabbas ya koma,dan in dai bai koma ba, ba zai taɓa fita babu mota ba,kuma in yana gari baya kulle kofarsa."


Ta sake faɗi.


Kafa ta yi ta juya ta koma kasa.



Ɗakinta ta nufa ta je ta d'auko dubu goma ta fito ta bawa Lantana,


Godiya Lantana ta yi kana ta juya ta kalli Indo ta ce.


"Yauwa Indo ni zan koma, ki wa Hajiya biyayya,ki mata ɗuk abunda ta saki,kuma ki nitsu ki yi aiki da kyau,kin ji Indo.?"


Maimakon Indo ta amsa sai ma cewa da ta yi.


"Tafiya za ki yi, ki bar ni a gidan yankan kai Hajiya.?"


Mai Safina zata yi in ba dariya ba,sai da ta yi dariya sosai kana ta ce.


"Ke! Nan burni ne,kuma yawancin gidajen burni haka suke kin ji nan ba gidan yankan kai ba ne,ko kin taɓa ganin mace ta yanka mutun .?"


Kai Indo ta girgiza alamar a'a.


"Yauwa toh kin ga ni,maza yi mata sallama sai na kai ki ɗakin ki da za ki dinga kwana."


Sallama Indo ta yi wa Lantana kana Lantana ta kara yi wa Safina godiya ta fita ta bar palon.


A bakin gate ta tarar da Habu zaune yana hira da baba mai gadi.


Ganin Lantana ta fito ne ya sa Habu yi wa baba mai gadi sallama,kana suka bar gidan.


A ciki kuwa.


Kallon Indo Safina ta yi kana ta ce.

"Yauwa Indo maza ta shi mu je na nuna miki dakin ki."


Kai Indo ta geɗa haɗe da miƙewa,ta bi bayan Safina da ta riga da ta yi gaba.


Ɗakin da Nadia ta ke kwana ta buɗe da key ta shiga Indo na binta a baya.



K'atuwar katifa ce shimfiɗe a saƙiyar ɗakin,sai wata ƴar karamar wardrobe dake can gefe,da kuma karamin carpet a kasa.


Juyowa Safina ta yi ta kalli Indo kana ta ce.


"Yauwa Indo nan ne ɗakin ki,nan za ki dinga kwana."



"Hajiya kina nufin wannan ɗakina ne."


Indo ta tambaya ,tana mai karewa ɗakin kallo.


"Eh ɗakin ki ne Indo."


"Yeeee! Ni ma na zama ƴar burni."


Indo ta faɗa tana mai washe baki.


Kai kawai Safina ta girgiza,kana ta ce.


"Zo mu je na nuna miki banɗaki."



Kai Indo ta geɗa tana mai ci gaba da washe bakinta.


Toilet dake cikin ɗakin ta nufa ta buɗe ta shiga nuna wa Indo.


"Yauwa Indo ga banɗaki nan wancan abun a ciki za ki dinga fitsari sa karashi,in kika gama sai ki dannan wannan abun kashin zai tafi,wannan kuma nan za ki kunna in kina son yin wanka,ga kuma famfo in za ki yi alwala."


"Kin fahimta.?"


Safina ta tambayi Indo a lokacin da ta gama nuna mata yanda ake anfani da kayan toilet ɗin.


"Eh Hajiya na fahimta ba ri ma na nuna miki."


Indo ta faɗa tana mai matsowa ta danna wajan yin floshin in angama kashi.


Haka ma sauran duƙ ta nuna mata.



Mamaki sosai Safina ta yi da a lokaci ɗaya Indo ta fahimci komai.


Indo,ba dai iya rik'e abu ba.


Dan sau ɗaya in ka nuna mata abu take haddacewa.



"Ma sha Allah, Indo yanzu ki ajiye kayanki ki zo ki share min palo."


Kai Indo ta geɗa kana ta ajiye kayanta suka fito palo.







*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*





*More comment more typing ✍️*





Share fisabilillah 👏
[01/02, 10:32] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V

________________________________________________


Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ


________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*


*Gargaɗi*

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️1️⃣4️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*


*Abuja Nigeria*


Tunda suka sauka ya zo gidansa dake cikin Abuja yake bacci,ba shi ya farka daga bacci ba, sai wajan biyun rana,tashi ya yi ya zauna kan gadon haɗe da yin miƙa kana ya zare bargon da ya yi lullubi da shi ya ajiye ta a gefe,kana ya zira fararen kafafuwansa kasan carpet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin.




Sauka ya yi ya miƙe ya nufi toilet,ruwa ya watsa,ya yi alwala ya fito ya zo ya shimfiɗa sallaya ya tada sallah azahar.


Bayan ya i'dar da sallah ya miƙe ya naɗe abun sallan ya koma gaban gado ya zauna ya ɗauki wayarsa da yake a kashe tunda ya zo ya kunna.


Wayar kamar jira take a kunnata ta d'au ringing,yana dubawa ya ga sunan Safina ce take yawo akan screen ɗin wayar gajeran tsaki ya ja haɗe da ajiye wayan ya miƙe ya nufi baƙin kofar fita,yana jin wayan na ringing a karo ba biyu amma ko waiwayowa bai yi ba,ballantana ya dawo ya ɗauki wayan.


Palo ya nufa yana zuwa bai tsaya ko ina ba sai kan dinning table,yana yuwa ya ja kujera ya zauna,ya shiga buɗe kulolin abincin.


Jolof din shinkafa ce ya ga ni a cikin kular,


Buɗe dayan ma ya yi yaga pepper chicken din kaza.


Plate ya ɗ'auka ya zuba jolof da pepper chicken ,yana gama zubawa ya maida murfin ya rufe kana ya ɗauki spoon ya soma cin abincin dan wani irin yinwa yake ji.


Ya ɗan ci ba laifi, bayan ya gama ya tura plate d'in gefe ya ɗauki glass cup ya zuba lemon da aka yi da zallan kankana,shi ma ya shanye,yana gamawa ya miƙe yana ƙwallawa mai aikinsa kira.


"Janson! Janson!!



Babu jimawa wanda ya kira da Janson ya fito daga wani ɗakin,


Wani matashin saurayi ne,wanda bazai wuce shekaru 24 ba,fari ne,amma kallo ɗaya zaka masa ka fahimci shi ɗin yare ne,sanye yake da gajeran wando wanda ya tsaya mai iya gwiwa.


Sai riga mai gajeran hannu.


Karasowa ya yi inda Maher yake ya rusuna kaɗan kana ya buɗe baki ya ce.


"Sir ganu ina burci na ji ya kira ni."


Ya yi maganar da wannan hausan na shi da ba ta fitowa sosai.



Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya nuna masa dinning table da 'yan yatsun hannunsa.


Kana ya juya ya koma bedroom ya barsa a wurin.


Da kallo Janson ya bi Maher da shi kana ya wuce dinning ɗin ya shiga kwashe kayan dinning.




Ba dan komai ya sa Maher ya ɗauki mai aiki namiji ba sai don baya son takusa,kuma baya son ya zauna da mace gida ɗaya wanda ba muwarraminsa ba, shi ya sa ya nemi da a nema sa mai aiki namiji,kuma mai safta sabada baya son kazanta.


Wannan ne dalilin da ya sa aka kawo mai Janson,


Janson akwan safta ga iya girki kamar mace.


Saboda ya taɓa yin aiki a wani hotel.



*Maganda rugar fulali*



Zaune take a gaban bukkan na su ,ta yi shiru.



Wata mata fara kyakkyawa sosai,sanye take da kayan fulani ta fito daga cikin bukkan ta karaso inda take,har ta zauna Layla bata sani ba,sai da ta ji bafulanar matar na magana sannan ta dawowa daga duniyar tunanin da ta lula.


Ɗago fararen idanuwanta take a sunkuye ta yi ta d'ora su akan bafulatan matar da ta yi magana.



"Sannu moɗon Innawuro."


Maimakon matar ta amsa,sai ma je fa wa Layla tambaya da ta yi.



"Doɗejo wai me yake damu ehmo kin zauna kina ta tunani ne.?"


Ta yi maganar irin nasu na fulanin daji.



"Innawuro yau ma na yi wannan mafarkin, Innawuro bansan wacece wannan mai kama da ni ɗin ba."


"Yau kam zan faɗa miki komai Boɗejo ."


Ta yi maganar tana mai gyara zamanta sosai akan tabarmar da suke kai,kana ta soma magana.



"Tabbas wacca kike mafarkinta ƴar uwarki ce,ku biyu mahafiyarku ta haifa.


Kwashe komai ta yi ta faɗawa Layla,na yanda ta haɗu da Hajiya Sumayya da ma Naila,har da bata ita da ta yi ta rik'e mata ta bawa Naila nono,har 'yan fashin da suka gani suka gudu,duk ta faɗa mata, babu abunda ta boyewa mata,bayan ta gama faɗa mata ta ɗago ta kalli Layla dake hawaye.


"Yi haƙuri Boɗejo ban faɗa miki ba,ba mu ne iyayenki ba,iyayenki suna burni kuma daga ganinsu masu kuɗi ne sosai,


Sanda suka gudu suka barki washe gari ba inda bamu je neman su da ni da Baffanki ba, amma bamu gan su ba, ɗuk bayan kwana biyu ni da Baffanki muna zuwa neman su amma bamu gansu ba,shi ya sa muka barwa Allah komai muka hakura muka cigaba da rainon ki har i'zuwa wannan lokacin da kike a gabana,



Wannan sunan Baɗejon ma ,mu ne muka sa miki,dan ba mu san sunan da iyayenki suka sa miki ba."


Innawuro ta karashe magana cikin sanyin murya.


Haɗe da saka hannu akan fuskar Boɗejo ta shiga share mata hawayenta.


Sai da ta kammala share mata tass,kana ta jawota cikinta ta rungume ta,kana ta ci gaba da faɗin.



"Ki yi hakuri kin ji Boɗejo ? Wallahi ina sonki, kuma son da nake miji ko da ace ina da ɗa wanda na haifa a cikin cikina ma ,iya kacin abunda zan nuna masa kenan,


Ɗuk da a cikin wannan rugar mace tana yin shekara 12 ake mata aure,amma kasan cewa bakiya son hakan ne ya sa na kyaleki har kin kai wannan shekarun baki aure ba,



Ɗuk da maganganun da nake ji a bakin mutane na rashin auren ki,amma na toshe kunne na yi kamar ban san suna yi ba,


Kuma ba dan komai ya sa nake hakan ba,sai don irin son da nake miki,da kuma gudun ɓacin ranki."



Tunda ta fara magana Boɗejo take kallon ta har ta kai aya.
Ajiyar zuciya Boɗejo ta s'auke kana ta buɗe baki ta soma magana.


"Innawurona na san kina so na,kuma na san ko iyayena da suka haifeni iya kacin son da zasu min kenan in ina tare da su,



In sha Allah, Innawuro na yi miki alkawari ko na ga iyayena bazan taɓa rabuwa da ke ba,saboda kin mun ɗuk abunda ɗa yake bukatar samu a wajan mahaifiyarsa."


Shafa kanta Innawuro ta yi kana ta ce.


"Na gode sosai Boɗejona,kuma in sha Allah daga gobe zamu fara zuwa garurukan masu kuɗi ko Allah zai sa muga iyayenki."



Cikin fara'a Boɗejo ta ce.


"Allah! Innawuro.?"


Kai Innawuro ta geɗa mata alamar tabbar mata da gaske take.



Da haka dai ta ce in Baffan Boɗejo ya dawo daga wajan kiwo zata faɗa masa.



Bayan dawowar Baffa daga wajan kiwo Innawuro ta faɗa mai maganar nemo iyayen Boɗejo da ma faɗa mata da ta yi,akan cewa ba su ne iyayenta ba,saboda yawan mafarka-mafarkai da take yi.



Sosai Baffa ya goyi bayan da hakan.



Dan haka ya ce in sha Allah! Gobe zai je cikin gari ya saida shanunsa ɗaya su zo su fara shirin tafiya burni nemon iyayen Boɗejo.



Da wannan suka bar maganar suka shiga wata hira daban.


Bangaren Boɗejo kuwa cikin farin ciki ta yi bacci ranar, haɗe da addu'a Allah ya sa,taga iyayenta da ƴar uwarta.


Dan ita farin cikin ganin ƴar uwarta da suka kwanta ciki ɗaya kuma suka fito rana daya kuma lokaci ɗaya ma yafi yawa akan na iyayenta da suka haifeta.



Da wannan tunanin har baccin barawo ya yi awan gaba da ita bata sani ba.



*Kaduna State*


*Gidan Maher*



Ranar da Indo ta fara aiki a gidan Safina sosai ta sha aiki ranar,shi ya sa da daɗɗare da ta kwanta babu jimawa bacci ya d'auketa.







Maher kuwa kuwanan sa biyu a Abuja,ya ɗauki pasinjojin suka nufi (Saudia Arabia)da su,dan gabatar da aikin haji.






*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*






*More comment more typing ✍️*




Share fisabilillah 👏
[02/02, 17:29] null: 😭😭SANADIN RABUWARMU 😭😭



Story & Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)


________________________________________________


Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/LkKggQHADe9IjmqxpteXaO

________________________________________________


Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V

________________________________________________


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________



*Diamond 💎 Star 🌟 Ladies 🧝‍♀️🧝‍♂️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝



*Book one free*


*Gargaɗi*

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba,ta ko wace siga,sannan ban amince a daura min shi a YouTube ba tare da izini na ba,a kiyaye please,dan in anyi min haka zan ɗauki mataki tunda hakkina ne.

Wannan labarin ƙirƙirarra ne,in ya yi kama da labarin ka/ke,ku yi haƙuri akasi aka samu.




Page ▶️1️⃣5️⃣



*💫Bismillahi rahmani rahim 🙏💫*



*Nailah*


Da na tashi da safe kafata ya yi sauƙi sosai,sai dai kaɗan -kadan yake min ciwo,


Na so na je school amma Mommana ta hana ni zuwa ta ce sai na kara jin sauƙi sosai,kuma ta ce bazan kara yin tuƙi da kaina ba sai dai dreva ya dinga kai ni ya dawo da ni,babu irin rok'on da man mata ba ,akan ta barni na tuka ta ce bazan kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login