Showing 48001 words to 51000 words out of 97338 words

Chapter 17 - YARO DA KUDI Book Complete by Binta Umar Abbale .pdf

10 Jul 2025

4310


Duk wannan abinda yake faruwa Dady ya naji ,ranshi yana mugun zafi,da irin rashin kunyar da
Nasir yakeyi,anrasa mai tsawatar masa ,a cikin "yan uwanshi,sabida sunajin tsoransa,wanan
yana nuna cewar ko mutuwa yayi haka zasu wofintar da jininsa,tabbas zumunci bai ce haka ba
tunda shi ba haka ya musu ba

[15/05/2019 2:18 PM] Binta U Abble: Tari! ne ya sarqe shi ya riqayi babu kakkautawa ,nan da
nan suka mayar dashi suka kwantar,Nasir ya nufi frji da sauri ya ciro ruwa mara sanyi sosai
yazo ya na sama a baki,


Dady ya ki karba ,idanunshi tsaye kan Malam Ya'u, yana kallonshi ,da kyar ya daga hannunshi
da yayi masa bala'in nauyi yayi masa alama yazo gareshi ,Malam Ya'u ya karasa kusa dashi
jikinshi a sanyaye,yace "sannu Alh Allah ya baka lafiya"


Dady ya bude baki da kyar yace"Malam Ya'u ko bayan babu raina ban amunce ka bar gidanan
ba ,shashen da kake ciki na mallaka maka shi ,halak malak, sannan , inaso kayi min wannan
alfarma ga amanar Nasir nan na damka maka ita a hannunka kar ka wofintar da shi,ka cigaba
da yi mishi addu'a Nasir naka ne dama can "
Malam Ya'u yace"na karbi Amana Alh ko da ranka ko babu jinnika ba abin gudu bane a
gareni,in sha Allahu zaka tashi ka cigaba da rayuwa, nagode da karamchin ka a gareni ubangiji
Allah ya biyaka da aljanar fiddausi"


Cikin zuciyarsa yace ameen,sannan ya kamo hannun mahaifin Abdul latif ya ruke gam! Yace"ni
Hussen in dai na isa da kai da abinda ka haifa ,ina so ko bayan babu raina ,ka daura auran
Abdul da Maryam,domin ina sha'awar hada zuri'a da ta Ya'u, da naso Nasir ne ya samu wannan
garabasa domin auran kamilar mace irin Yarinyar dace,dukkaninku baza Ku fahimchi haka ba
sai nan gaba, Nasir ya fadamin qeqe da qeqe ban isa dashi ba ,kuma bazai bi umarnina ba,
sabida haka da wannan bakin cikin zanmu a rayuwata ,Nasir nagode nagode, nagode, tari ya
rurnikeshi,!!


Hankalin Nasir yayi mugun tashi, kaddai ,dady ya sauki maganar su ta dazu da zafi haka,har ta
janyo masa tashin ciwonsa,shifa yafadi hakane kawai dan ya bata masa rai, amma
kwata-kwata-ba gaskiyar abinda yake zuciyarshi ba kenan,

Kafin ya dawo daga tunanin nashi,yaji Momy ta rusa ihu,yayi da Mahaifin Mubina,yake Fadin
*innalillahi wa'inna ilayi raji'un*
Dady ya amsa kiran Ubangiji
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [16/05/2019 9:26 AM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*


*74*


Nasir ya fasa wani ihu yayi kan dadynsa ya ruqunqume shi,kuka ya kece masa ,cikin dimuwa da

fitar hayyaci ,yake fadin *innalillahi wa'ina ilayi raji'un*
Dady kar ka mutu, bakace ka yafe min ba, dady ka tashi in fada maka abinda yake zuciyata duk
kanin abinda nafada maka abaya ,karya nakeyi wallahi,dady ina mutukar kaunarta ,har a cikin
zuciyata,dady in kayi min haka ina zan sanya rayuwata pls dady karka yimin haka rayuwata
nima tazo karshe ban da amfani a duniyar nan,kafadamin mai kake bukata nayi maka shi
yanzu!!! Nasir kuka yake sosai da sosai ,duk ya gigice yafita hayyacinsa, in banda gumi babu
abinda yake zuba a jikinsa,yabi ya rungume gawar dady ya hana kowa ya kusance shi,da kyar!
Malam Ya'u ya karaso gurin gami da dafa kafadar Nasir din cikin dauriya da jajircewa ya ce"kayi
hakuri Nasiru Allah Ubangiji ya amshi Alh cikin aminci da yaddarsa, ya mutu yana kalamar
shahada,yanzu babu abinda yafi bukata da kai sai addu'a kaji"



Nasir ihu! Yakeyi yana sambatu da'alama kwakwalwarsa a lokacin ta daina aiki,domin kwata
kwata bai ji abinda Ya'u yake fada ba.



Maryam ko yanke jiki tayi tafadi, ta suma!!!


Kafin kace kwabo gidan ya hautsine da hayaniya, tuni Nura ya fita ya sanar da Sucurty da ke
waje abinda ke faruwa a cikin gida,



Aunty ko tana bangaransu duk wannan abin da yake faruwa bata sani ba tana kchin tana
hidimar Dora abincin rana,taga Malam ya shigo mata da yarinya ranga ranga,

Salati ta tafka tana tambayarsa abinda ya faru ,sabida dama tasan da batan da Maryam din tayi
na awanni biyar da suka wuce,Malam Ya'u yace"babu lafiya Suwaibah ,muna cikin tashin
hankali,Allah yayiwa Alh rasuwa


Gigicewa aunty tayi domin duk a zatonta mahaifinta yake nufi ,sabida tasan shima ba shi da
koshin lafiya.


Kuka ta fashe dashi tace "shikkenan baba wahala ta kare"


Ganin bata fahimci abinda yake nufi ba,yasa ya tsaya yayi mata bayanin komai,aunty ta rika
salati tana sanar da ubangiji,da gudu tayi dakin ta zaro hijab tana ,nanata innalilahi a fili,take

tambayar mai ya sameshi,shiru Malam yayi mata shi dai yana ta tasbihi cikin zuciyarsa, tare
suka shiga farlou, har yanzu Nasir na rungume da gawar Mahaifinshi ,yanzu. Ya dai na zubar da
hawayen sai kukan zuci yakeyi kwata kwata ya hana kowa kusantar gawar ,har Momy dinsa,
dake kusa dashi ,ita kuma a lokacin Allah ya sanya mata juriya,kwata kwata idanunta sun bushe
,babu hawaye ko days,amma kana kallonta kasan tana cikin dimuwa! Da tashin hankali
[16/05/2019 9:43 AM] Binta U Abble: Tace"My Son shiyasa kullum nake fada maka ka kiyaye
bacin ransa ,sabida kasan yana da lalura,kaki ji ,ko ka gani yanzu yazo ya tafi ya barmu mai
zakace min ,my son ,mai zakace min!!
Momy tafada muryar ta tana karkarwa,


Aunty tazo ta dafa kafadar Momy tana zubda hawaye tace"Hajiya Kiyi hakuri kinji,dama Allah ya
kaddara lokacin Alh yayi yanzu bawa bai ta kashe wani ba face sai lokacin sa yayi, kiyi hakuri
,kiyi mishi addu'a Allah ya jikanshi Hajiya Allah ya sanya mana hakurin jure rashinsa da mukayi.



Sai lokacin hawaye ya kecewa Momy ,tafadi a gurin ragwajb ,tana kuka, cikin tashin hankali da
damuwa take fad in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un



Aunty tazo ta dafa kafadar Nasir tace"dan gidan aunty kayi hakuri kaji ko ka fawwalawa Allah
kowa na hakane,don Allah ka saki kyale Alh ayi masa suttura ,duk wannan abinda kakeyi bazai
sa dawo mana dashi ba"


Nasir ya zubawa aunty ido yana kallonta ,bakinsa dai motsi yakeyi ,da kyar ya samu ya finciko
maganar ,yace"aunty dady ya mutu,!! Wancan yarinyar ,ce tayi sanadi ni babu ruwana,sabida
lafiya kalau na tafi na barshi da'ita,sabida haka ,duk yadda zanyi sai nayi gurin ganin na
wulakantata ,tunda tayi sanadin kashe min mahaifi.

Aunty Sam!! Bata fahimchi maganarsa ba ,ta lura kwata kwata baya cikin hankalinshi,tace"eh
nima Na amince Auncle ka dauki mataki kan wanda ya zalunce ka,amma yanzu abinda nakeso
dakai ka saki Alh ayi mishi suttura kaji ko"



Nasir yayi zakwado!! Yana bin dady dake rungume a jikinshi da kallo vakinshi sai motsi
yakeyi,yanzu wai da gaske ne dady shi ya mutu !! Ina karya ne!
Abinda ya fada kenan da karfi!! Sai ya fara Jan numfahi!! Da karfi ,kan kace kwabo ya afka kan
dady din nasa ya suma!!!

Guri ya hargitse da salati,Ya'u yazo ya janye Nasir ,daga kan dady,yayinda "yan Uwan dady din
suka samu damar janye dan uwansu,domin sutur tashi,
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [16/05/2019 8:45 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*


*75*

Momy ta kidime tayi kan Nasir din tana kuka sosai ,tamkar wacce tasamu tabin hankali take
cewa "My son kai ma zaka tafi ka bar ni ne, ta kamashi sai jijjigashi takeyi tana kuka da sauri
Malam Ya'u yazo da ruwa mai sanyi cikin gora ya bude ya watsa wa Nasir din ,cikin zuciyarsa
yana ta nanata Kalmar innalilahi
Nasir ya mike a zabure!! yana dube dube babu dadynshi a gurin ya mike da sauri ,jiri! ya
debeshi ya yar kan kujere ,sai ya dafe kanshi da hannunshi guda,ya na furta,kalame "Ya Allah!!

Momy da aunty sai tausarsa sukeyi,kar ma dai aunty taji labari,shidai idanunshi suna
rufe,kwata-kwata hankalinshi da tunanunshi baya kansu,zuciyarsa take fada masa kayi rashin
mahaifinka har abada Nasir,sai ya karyar da wuyanshi jikin kujera ,hawaye yana zirarowa daga
idanunshi da suke rufe,


Kankace kwabo mutuwar Alh Huseen ta karade birni da kewaye sabida dukkanin wanda ya
kwana ya tashi a garin kano da kewaye babu Wanda bai sanshi ba idan ma baka taba ganinshi
ido da ido ba to za ka ganshi a jarida ko gidajan TV ko tashoshin yada labarai,sabida yadda
yayi suna gurin taimakon marayu da nakassasu gami da taimakon talakawa ,Sam dukiyarshi
bata rufe masa ido ba sabida haka ,kofar gidan damqam! Take da jama'a duk suna jira a fito
dashi domin suyi masa rakiya zuwa ma kwancinsa na gaskiya ,sai jaje sukewa juna suna ta
fadar alkairinsa, dayawa daga cikinsu hawaye suke sharewa domin sun gaza daurewa sabida
sunsan ba karamin rashi sukayi ba,



Addu'oi Ya'u ya dukkufa yana ta tofawa Nasir ,duk domin ya samu zuciyarsa ta sanyaya, cikin
hukumcin ubangiji ya bude idonshi ,ya na binsu da kallo daya bayan daya, kimanin minti biyu,ya
mike tsaye cikin nutsuwa ,aunty tayi saurin riko hannunshi,sai Malam Ya dakatar da ita ,yayi
mata alamar ta rabu dashi, kai tsaye dakinshi dake farlo ya nufa ,ya bude ya shiga gami da rufo
kofar,Momy tabishi da kallo zuciyarta ,tana tsinkewa

Toleit ya bude ya shiga ya dauro alwala ya fito ya kwabe kayan jikinshi, ta cire sarkokin da suke
wuyanshi,hade da barimar dake manne a fatar kunnenshi,ya bude katuwar siff dinshi,ya ciro
wata jallabiya fara kar da ita ya sanya a jikinshi bayan ya sanya gajeran wando,ya dauki carbi
mai ma dan nai

Lokacin da ya fito anfito da dady,"yan uwa suna ta yi mishi addu'a Momynshi na gurfane gaban
gawar tana kuka sosai da sosai, cikin jarumta yazo ya janyeta ya zaunar da ita kan kujera, bai
cewa kowa komai ba,yafara kokarin daukar dady,ganin haka yasa jama'ar da suke gurin suka
mike dama shi suke jira ya fito yayi masa addu'a ,sai suka kama masa makarar ya Dora a
kafarshi, suka fita bakinshi dauke da addu'oi iri-iri yana nai mawa dadynshi rahamar Allah.
[16/05/2019 9:05 PM] Binta U Abble: Nan Aunty ta zauna ita da saura jama'a suna ta tausar
Momy,kwata-kwata ta manta da Maryam da a ka kai mata ita ranga ranga,sai ganinta sukayi
tafado farlo din tamkar zautacciya sai zare ido takeyi dama ga su tubarkallah,


Ta rika bin ilahirin farlou n da kallo, cikin zuciyarta take fadin Allah mafarki takeyi ba gaske bane
abinda ta gani cikin mafarkin ta.


Mata tagani zazzaune ko wacce cikin hijabi ga carbi a hannu,da kyar! Ta samu ta furta,kalarmar
da ta fito daga bakinta, Tace"aunty wai da gaske dady ya mutu,wani mummunan mafarki nayi,


Kafin aunty tace komai,Momyn Mubina ta daka mata tsawa ,cikin tsantsan kyama tace" waye
sa'anki a gurin nan da zakizo kina mana maganar banza da wofi ko an fada miki ana wasa da
mutuwa ne,shegu mayu! Kun kasheshi kun huta ,mutsiyata, kawai masu mugun abu, sarakan
surkulle, Allah wadaran talaka Wanda zaka dauko shi daga rana kai ya mai da kai cikinta,
dukiyar Alh kukewa to Baku da gado da ita ,ehe!!



Maryam tayi tsaye bakin kofa tana ji da kallon ikon Allah, ita kwata kwata magangan nun Momy
Mubina sam basu dameta ba,illah jin ciwon rashin dady da radadin yadda takasa bin umarninsa
na auran tilon danshi wato ancle din ta,har ya koma ga ubangiji ,yanzu ita yaya zatayi da
rayuwarta,gashi tanaji a gabanta dady ya bar wasiyar cewar a daura mata aure da Abdul latif
duk da tasan ,ba haka yaso ba a zuciyarsa ya mutu ne da burin ganin ya aura Mata Uncle

Hajiya Rakiya wato mahaifiyar Abdul kenan ta rika watsa aunty mugun kallo na tsana, sai tabe
baki takeyi,sabida dama can ita macace mai mutukar izza gami da taqama,ta tsani talaka Sam!
A rayuwarta shiyasa ko inuwa bataso ta hada dashi, macace "yar mulki ko shi Mahaifin Abdul
din hakuri yake da'ita.

[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [17/05/2019 4:00 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*


*76*


Maryam ta zube nan bakin kofar kuka ya kufce! Mata sosai take yi har da majina,a nan Nasir ya
cimma ta, da ya lura ita ce a gurin ka wai ya sanya kafarsa yayi ball da ita,ya yi shigewarsa ciki
batare da ya waiwayo ba, ihu ta kurma lokacin da kanta,ya bugu da bango ,ta dafe gurin
hawaye wani na bin wani ,dakinsa ya shiga ya fito rike da dadduma ,babu Wanda ya kula a cikin
mutanen da suke farlo din ya sakai ya fice Maryam tayi sauri ta bashi hanya ganin yadda ya
taho gadan gadan ,

Haka dai akayi zaman makokin dady Auntt da Maryam suna kunsar Bakin ciki gurin mutane
domin kowa ya daura mutuwar dady din a wuyansu,gefa guda kuma ga wasiyar da dady ya bari
cewar kar su bar gidan,


Nasir kuwa wani irin ya dawo mai shiru shiru sai ya yini ya kwana bai kula kowa ba har Momyn
sa tare da "yan uwanta da suke kara kaina a gidan tun safe yake shiryawa ya fice ,kwata kwata
yanzu ya dai na saka kananun kaya kullum cikin doguwar Riga yake"yar saudia kanshi da hula
irin ta Larabawa sai ya dawo tamkar wani balarabe,kullum zaka Ganshi a masalaci ,nan yake
zama yayiwa dadynshi addu'o yana zubar da hawaye, yau tsawon kwanaki goma shabiyar da
rasuwar dady din Momy bata ga ko da murmushin sa ba ko magana zai mata ,bata wuce kalma
biyar ko kasa da haka ,kwata-kwata baya yin doguwar magana kullum fuskarshi a murtuke
abokanshi sunzo mai ta'aziyya mussaman Abbas da Anwar sunji mutuwar dady sosai kadai
Anwar in ya tuno rashin kunyar da yayiwa dady din sai jikinshi yayi sanyi,to ko su kansu in sun
zo Nasir din baya sakar musu fuska haka zasu karaci shirmensu su tafi,


Bayan sadakar arba'in yafara aiki a asibitinshi domin shine burin dadynshi,yanzu duk abinda
yasan dady yana so kafin rasuwarshi shi yakeyi ta mai da gidan fursuna da gidan marayu gurin
zuwa bayayin sati daya batare da yaje ba tsakaninshi da Malam Ya'u kuwa gaisuwa ce itama
sama sama baya taba yadda wata doguwar hira ta shiga tsakaninsu shi kuwa Malam Ya'u yayi
ta janshi da magana wani sa'in yana jinsa yake shareshi Allah sarki Malam baya gajiya da
hidima dashi
[17/05/2019 5:14 PM] Binta U Abble: Tun ranar da dady ya mutu rabon da ya sanya Maryam a
idonsa, kwata-kwata baya son su hada hanya sabida yadda ya tsane ta tsanar da yake mata ta
yanzu taci uwar ta da, shiyasa yake gudun haduwarsu domin yana ganin zai iya kasheta a
yadda yake jin zafinta a zuciyarsa,shi gani yakeyi itace silar mutawar dadynshi

Allah sarki Momy duk tayi sanyi itama zuwa yanzu ta fawwala wa Allah komai su Nafi'u da

miftahu kullum suna gurin ta suna de mata kewa duk ranar da basu shiga bangaran nata sai ta
aika Uwani mai aikinta ko lafiya, wani lokacin kuma suna makaranta,


Auntt ta dauki zafi da Maryam sosai lokacin da mijinta ya warware mata dukkanin abinda ya
faru kafin rasuwar dady ,ta dinga yi mata fada sosai da sosai tunda ga ranar Maryam ta dai na
ganin dariyarta


Maryam duk jin ta takeyi a takure kullum tana dakinta tayi kuka har ta gode Allah kullum cikin
bawa auntt ta hakuri takeyi,aunty tace indai kika ga na hakura to sai kinje kin bawa uncle dinki
hakuri,sannan nima zan yafe miki,


Maryam taci alwashin baza ta taba zuwa tabawa uncle hakuri ba sabida ai bai fita jin radadin
mutuwar dady ba ,yadda takejin dady a ranta ,gani takeyi tafishi son sa da kaunarsa ,sabida
haka ita a ganinta ita ce ya cancanci a bawa hakuri bashi ba
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [18/05/2019 10:31 AM] Bint U Abbale 💜: *YARO DA KUDI*

*77*



Yanzu duk wasu abubuwa da yakeyi a da marasa kyau ya rage yi ,sallah cikin jam'i bata wuce
shi , duk abinda yakeyi lokaci nayi zai nufi masjid ya rage saka kananun kaya, sosai yana saka
kayanmu na hausawa, askin da yake kanshi yasa an gyara masa Sosai yanzu ya dawo
cikkaken mutum amma duk da haka akidarshi tananan ,ta turawa yana yawan sauraron
wakokinsu ,zuwa club ma ya rage ba sosai yake zuwa ba, duk dai wani abinda yasan dady
dinshi yanaso kafin rasuwarshi yana kokari ya yi abin , Son matanshi kuma wannan ma tun
daga mutuwar dady din bai kara kwanciya da wata yarinya ba,sabida yanzu duk "yan matan
nashi tsoro yake basu yadda kullum suka tunkareshi zasu ga fuskarshi babu Rahama ko ta
kwabo ,baby ce kamar mayya kullum sai ta bishi asibiti taje ta isheshi da iyayi ,baya ko
sauraronta



Yau ta kasance ranar Sunday ce , yana part dinshi a kwance bacci yakeyi Momy ta shiga tana
tashinshi , tashi yayi yana dan ya mutse fuska Momy ta karaso ta zauna bakin gadon tana
kallon Dan nata tace"My son wannan baccin naka fa yayi yawa dubi time yanzu daya shaura
,ina ta zuba ido shiru baka shigo ba"

Mika yayi yana kallon agogo yace "Wallahi Mom gajiya ce a jikin nan nawa ,kin san tunda

nafara aiki bani da lokacin kai na wallahi , yau din ma dole zan fita a kwai wasu mata da nayiwa
aiki zan je na dubasu duk da cewar Dr Sofia na kula min dasu amma zuwan nawa yana da
muhimanci"


"Hakane Son ai ladanka na gurin Allah, duk Wanda yazo ka taimakama sa ko da kudi ko babu
,kasan wannan shine burin dadynka dama"


Taci gaba da cewa yanzu ma aikin lada zakayi ,Baban gida ne gashi can ciwonshi ya tashi
,muje ka dubashi



Kallon Momy yayi yana murtuke fuska yace"waye baban gida"?



Cikin Mamaki Mom din tace "banason rainin hankalin ka fa my son Baban gidan kake tambayar
wanene"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login