Showing 18001 words to 21000 words out of 97338 words
Chapter 7 - YARO DA KUDI Book Complete by Binta Umar Abbale .pdf
ni zai keta min haddi ni back"yar
iska bace"
Kafin ta rufe bakinta suka fadi rigib! Ita da Anwar din sakamakon bude kofar da Nasir yayi babu
zato ,
Tana kan ruwan cikin Anwar din tana kokarin tashi daga kansa yayi da shi kuma ya sanya duk
hannuwanshi biyun ya ruqunqume ta kam!
Tamkar wani Dan dambe haka Nasir yayi kansu a hautsi ne ya daki kafar Anwar da wani
mitsayacin takalmi mai ta yoyi da yasanya a kafarshi yanzu domin Wanka ya sakeyi gami da
sake wani dressing din domin sake fita,
Ya San ya hannusa guda ya dauke Maryam daga kan Anwar din yana zaginta da turanci ya
fidda hannu ya dinga gaura mata tafi tamkar Wanda Allah ya Aiko shi,
A kasalance Anwar ya mike yana kokarin kwatar maryam daga Hanunsa, Ya kai masa wani
kutofo,yayi taga taga zai fadi ya tsaya da kafaunsa
Da sauri Abbas da Abdul latif wadanda kecan falo suka karasa gurin domin hayaniyar da sukaji
kadan daga can bedroom din Nasir Dan a zatonsu ma ko fada ne ya hautsine a tsakaninsu su
biyun.
Ya kara daga hannunsa zai kara kai mata mari Abdul latif ya riqe hannun yana masa wani irin
kallo,
Bai ce komai ba ya mai da idonshi kan Maryam dake takure idon ta na zubar da hawaye,
Fizge hannusa yayi yace da Allah malam sakar min hannu wannan "yar iskar yarinyar ni zata
nuna wa iskanci Dan Ubanta a dakina za ta kwanta a jikin wannan Dan iskan yafada yana nuna
Anwar dake zaune da jiki a mace domin ya Riga yagama kwadaituwa da yarinyar,
Cikin mamaki Abdul ya maida idonshi kan maryam a karo na biyu ,yace" Maryam mai yakawo
ki dakin nan ina kuma hijab din ki?
Cikin kuka tace Momy ce tace nazo na sharewa Ancle dakinshi nayi masa gyaragare wallahi,
Ajiyar zuciya ya sauke yace "zo ki wuce ki tafi kin ji ko" dakin Nasir din tayi niyar komawa domin
dauko hijab din ta,
A zabure! Yayi kan ta yana mata wulakantacan kallo ,ya tsare kofar dakin ,"yace get Out" joya
wa tayi da nufin tafiya Abdul ya dakatar da ita ,ya kalli Nasir da rai a bace yace wallahi baza ta
fita a haka na mahaifinta na waje a zaune Sam bai dace ba hakan"
Tsaki Nasir yaja ya shige dakinsa
Anwar yace"wai kai ina ruwanka da yarinyar ne malam naga fa kana min shishshigi a kanta wai
ko son ta kake yi ne iyi ,Wallahi tunda na kwadaita da ita sai na biyawa kaina bukata ko ta halin
yaya ne kai dai kafi kowa sanin halina"
Karaf! A kunne Nasir lokacin da yake fitowa daga dakin sa hijab din Maryam a qasa yana ja wai
bazai dauko da hannunshi ba,
Gabanshi ne yafadi jin Furucin Anwar yariga yasan halin sa ciki da waje tamkar maye yake
gurin mace zai iyayin komai a kanta Dan ta wani fanni na yafishi son mata tunda shi ba kowace
mace yake kwanciya da'ita bah'
Ba Dan komai ya hana Anwar cika burin sa ba a yanzu sai Dan in ya tuno da hallacin da Uwar
yarinyar tayi masa ,bazai taba cutar da jinin Aunty shi ba zai bari a cuceta ba yarinyar taci
darajar malam Ya'u da Aunty shi ,Amma da badan haka ba a gabanshi zai sa Anwar ya
yagalgala masa ita wallahi sabida tsabar haushin da take bashi taqi fita daga rayuwarsa kullum
ya kwanta sai tazo masa cikin baccinsa ta ida nunta masu ban tsoro a cewar sa ,shine dalilin da
yake ganin anya Aunty shi ba mayya ta haifa ba ,tunda shi maye ruwansa da ita,
Da sauri Abdul yaje ya cire hijab din daga kasan kafar Nasir din ya mika mata yace"maza ki sa
kinji ko kiyi tafiyarki Allah ya saka miki"
Da sauri ta karbi hijab din hannuta na rawa ta zira tayi hanyar fita daga dakin tana Addu'ar
Neman tsari gami da godewa Allah da ya tsareta daga sharrin su Nasir
*✍,,,,,,,,*
[18/03, 13:49] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*YARO DA KUDI*
*✍WRITTEN BY*
_*Binta Umar*_
~*Maman Abdul Wahabu*~
~*Mrs Ahamad gwadaba*~
_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATAR
CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176
~*DEDIGATED TO MY FAN'S*~
*30*
Abdul latif ya daura idonsa kan Nasir bayan fitar Maryam Ransa A mugun bace yac" yanzu kai
Nasir da kai za'a hada baki gurin cutar yarinyar can hakan da kukeyi yayi daidai kenan Abinda
kuke a waje shine za kuzo gida kuyi mai Maryam tayi maka ? Yarinyar da take bala'in tsoranka
wane irin Abu Aunty tayi maka zaka saka mata da haka"? Ya karashe ya Maganar yana sauke
ajiyar zuciya cikin tsantsan bacin rai!!
Wani kallon banza Nasir yayi masa yana ya mutse fuska cikin izgili yace" kai karfa ka kawo min
maganar banza mana ,Kai meye ruwanka da ita lokacin da kashigo A kai na kaga yarinyar da
zaka daura min jakar tsaba ,mai zanyi da'ita ,Aba sai kace zabiya Mtssss! Sam Sam Allah ya
tsareni ita Dan Uwarta mai yakawo ta dakina anan fa naganta har da tube hijab tamkar tana
dakin Uwarta" ya karashe maganar yana wani zakuda kafada Alamar babu Abinda ya dameshi,
Dauke kansa yayi daga kan Nasir din cikin bacin rai har ila yau jin irin Furucin da yakeyi Lallai
Nasir yayi Nisa!
Ya kalli su Anwar yana girgiza kai yace "Wallahi mutukar Wani Abu ya samu yarinyar nan ta
dalilinku sai nayi Shara'a da Ku A kanta , kai ne mai furucin ko ta halin kaka sai ka kauda
kwadayinka a kan ta ,yafada yana kallon Anwar,yaci gaba da cewa Wallahi duk in da zanshiga
in fita zan shiga a kan in Daukar mata fansa.
Wani kallon banza Anwar yayiwa Abdul din yace"Kai ka isa ka hanani ae kata Abinda nayi niyya
A kan waccan yarinyar Mara galihu "yar mai gadi da har kak e wani tada jijiyar wuya a kai kai a
suwa Kai din banza" ya karashe maganar yana furzar da wani huci mai daci Aba kinshi,
Girgiza kai Abdul yayi yana binsu da kallo daya bayan daya ,ya kalli Anwar din A karo na biyu
ganin yadda ya zaqe da yawa har yake wani rantse rantse gami da cin Alwashi a kan Maryam
din Tabbas idan wani Abu ya same ta Wallahi Anwar sai ya gane bashi da wayo
Yace"OK toum tunda ka rantse ae ga fili nan ga mai doki sai ka bada himma tanan ni kuma
zaka San ka tabowa kanka Abinda baza ka iya ba kana maganar Maryam bata da gata to tana
da gatan Allah dani in sha'Allahu Allah zai tsareta daga sharrinku ,kai kuma Nasir ya fada yana
nunashi da hannu yace "wallahi duk Abinda ya samu Maryam ka tabbata babu rufin Asiri dady
sai yaji domin kanajin furucin wannan Mara mutuncin a kanta kayi shiru wato kabashi goyan
baya kenan ko mai yarinyar nan tayi maka da kayi mata wannan tsanar da har zaka bada hadin
kai gurin cutar da ita, nafada na kara maimaitawa kar Ku batawa yarinyar nan rayuw.....
Kai! Arrama da kata mana Dan Allah ya isa haka" Abbas yafada Wanda tun zamansa a gurin
bai ce uffan ba ,sai yanzu
Ya gyara zama gami da zakuda kafada ,yaci gaba dacewa,Ubanmu ne kai wai da zaka titsiye
mu kana zagi ina Ruwanka da duk Abinda zamuyi Rayuwarka ko tamu ,Malam kar kasake kawo
mana maganar banza yarinyar daka ke wani tada jijiyar Wuya A kanta kana da Alaqa da ita ne
kai idan baza kayi ba sai ka hanamu kai baka isa ba Wallahi Kaii!! Kauce Malam!! Yafada A Fusace!
Tsaki Nasir yaja yana duba Wani Dan kareren agogo a daure a hannunshi bakwai shaura na
Magariba Ya kalli su Abbas din yace "guys Ku tashi mu ware Ku rabuda wancan Komai Allah
yace Annabi yace ko wa zai gayawa sanin Allah oho,"
Cikin Mutukar bacin rai Abdul ya fuce daga dakin yana Allah wadai da tur da wannan dabi'ar da
Abokannanshi "yan Uwanshi suka jefa rayuwarsu ciki
Yana fita suka Kwashe da dariya gami da tafawa ,Nasir yace"ni narasa gane kan wancan
gayan wallahi A kwai shiga Abinda babu ruwanka ko mai ya shafeshi da Lamarin yari yar oho"
Dariya Abbas yasa yace"mybe ko son ta yakeyi Dan ga Alamu nan sun bayyana"
Tabe baki Nasir yayi yace"tabbas da ya cika Dan Asara Wallahi yarasa wa zai so sai wancan
yarinyar mai kama da ru66a66an tomatiri Allah ya sawaqe mai!!"
Dariya sukayi dukkaninsu gami da mikewa domin fita,Shima dariyar yasa yace"Wallahi nake
gaya maka Ae irin su babu Abinda zakaji sunayi sai qarni in ka kusancesu Sam Sam yarinyar
batayi ba yafada yana tabe baki,
Anwar yace"komai me takeyi sai na biya bukata ta a kanta Wallahi idan Uwar qarni ma takeyi
bai da meni ba"
Gabanshi ne yafadi kadan ya Dan kalli Anwar din ta gefen ido ,jin Furucinsa har yanzu a kan
Maryam din ,bai qara cewa komai ba har suka fice daga shashen gaba daya
Wata sabuwar mota suka shiga Nasir ya ware kida kamar yadda ya saba suka five daga gidan
*✍,,,,,,,,,,*
[20/03, 02:30] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*YARO DA KUDI*
*✍WRITTEN BY*
~*Binta Umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~
~*MRS AHAMAD GWADABE*~
_*WANNAN BOOK DIN NASIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI
SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176
*DEDIGATED TO:MY FAN'S*
*31*
Lokacin da Maryam ta fita daga dakin Nasir kai tsaye part din Mom ta nufa cikin Nutsuwarta
tamkar babu Abinda ya faru.
Mom na kokarin hawa sama domin gabatar da sallah magariba ,sai ta dakata ganin shigowar
Maryan din.
Cikin sakin Fuska tace" Maryam Kin gama ko?
Cikin Nutsuwarta kamar ko da yaushe tace"Eh Momy na nagama Farlour ne ban gyara ba sai
gasu sunshigo game lokacin Sallar Magarb yayi zanje nayi Sallah".
Mom din ta gyara tsayuwarta tana kallon ta tace"ina fatan bai miki komai ba nasan Halin
kayana"
Murmushi tayi kadan"tace Momy na kenan Mai zaiyi min Ancle din yace ne kawai in tafi tunda
sun shigo "
"Daga haka fa" Momy tafada tana mata kallon tuhuma.
Sai ta duburburce tana tsoran kar Momyn ta Fahimci Abinda yafaru,yanzu gashi ita kuma qarya
ba dabi'ar ta bace,
Kallon zargi Momyn take mata race"kifada min gaskiya daughter kinji ko"?
"Ok zo nan Muje sama Muyi sallah a nutse sai ki fada min"
Momyn tafada gami da karasowa inda take tsaye ta kama hannunta suka haura Sama inda
dakunan su suke.
Bayan sun idar da sallahr ne Cikin Nutsuwa Mom din ta kalli Maryam tace"kifada min idan ya
dake ki kamar yadda ya saba kinji doughater"
Shiru Maryam tayi tana wasa da hannunta.
Sai da Mom din takara Maimaita tambayar,sannan tace"Allah Momy babu Abinda yayi tafada A
fili a zuciyarta tana Jan Istigifari.
Taci gaba da cewa ,Dama Dama Wannan Abokin nashi ne,sai tayi shiru takasa karasawa,
Ina jinki ya kikayi Shiru Momyn tafada"
Shine Yake kulani Momy nikuma bana so tafada kanta a kasa,
Momyn tace"To ae kina da gaskiya Mutuncin "ya mace tsare kanta babu ruwanki dashi ko ya
kulaki ,gaisuwa kawai na lamunce kiyi dashi kinji ko kuma zanyiwa Nasir magana tunda ba
kyaso tayi masa magana duk inda ya ganki Kar yakara shiga lamarinki"
Gabanta yafadi jin Abinda Momyn take fada,
Da sauri ta dago kai tace"A,a Momy ba sai kin yiwa Ancle maganar ba Dan Allah"
Harararta Momyn tayi kadan tace"ae dole in yi mishi magana yajawa Abokinshi kunne domin a
kanki zan iya batawa dashi"
Sunkuyar da kai tayi tana Murmushi kadan tace"Dan Allah Momy mubar maganar bana so ki
batawa Uncle rai"
Dariya Momyn tayi gami da Mikewa daga kan daddumar da sukayi sallah A kanta tace" in dai a
kanki ne ran Nasir zai baci kuwa ,
Mikewa tayi ita ma tabi bayan Momyn suka sauka kasa ,a tare Maryam din na kokarin fita da
niyar tafiya bangaransu Momyn ta dakatar da ita,tace Lallai sai ta tsaya sunci Abinci tare ,ba
yadda ta iya haka ta bi bayan Momyn can dainnig in da kayan Abinci ke jere iri iri na haduwa na
Alfarma,
Momyn ta hada Mata komai tsaf ,Cikin nutsuwa Maryam tafara cin Abincin suna hira da Momyn
kadan kadan ,sai da Momy ta tabbatar da Maryam ta koshi sannan ta kyaleta ta tafi
bangaransu.
Lokacin da tashiga shashin nasu Ana sallahr isha'i Aunty da su Nafi'u duk sallah suke ,sabida
haka Alwala ta daura ita ma tabi sawun su.
Aunty na idarwa tafara hidimar Zubawa yara Abinci ,ta kalli Maryam dake zaune kan dadduma
bayan ta idar da sallah tana Addu'a ,"kefa a zuba miki ? Nasan dai kinci gurin Momynki ko?
Daga kai Maryam tayi A nutse tace wallahi kuwa Aunty a koshe nake Amma da safe naci
dumame dama yafi dadi"
Tabe baki Aunty tace Allah ya kaimu . mai kika tsaya yi a ne a can?
*✍,,,,,,,*
[23/03, 00:15] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*YARO DA KUDI*
*✍writing By*
~*Binta Umar*~
~*Maman Abdul Wahabu*~
*MRS AHAMAD GWADABE*
_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR
CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176
_INA MIKA SAKON TA'AZIYATA GA "YAN UWA DA IYALAN ALHJI RUFA'I GWADABE ,MUNA
ADDU'AR ALLAH YAJI KANSHI YA GAFARTA MASA ALLAH YA YAFE MASA ALLAH YA
KYAUTA TAMU BAYAN TASU_
*32*
Aunty Momy ce ta Sani gyaran dakin Ancle Maryam tafada cikin Nutsuwa.
Ayya to ae kin kyauta Aunty tafada.
Ancle din ma ya kwana biyu bai shigo min ba Aunty tafada tundai ranar da yadawo"
Ita dai Maryam bata ce komai ba domin Aunty bata son Laifin sa ko kadan.
****************
Karfe takwas saura na safiyar Litinin Maryam tsaf cikin Unporm dinta na Makaranta, Tana zaune
gefen Babanta suna karyawa a gurguje ,ta kalli su Naf'iu tace "kuyi sauri Wallahi idan ba
hakaba in tafiyata"
Ya Maryam ni dai naga Mutafi kawai Mubarshi tunda kullum sai yasa munmakara,
Duka Nafi'u ya kaiwa Miftahu jin Abinda yake cewa yace "bana hana yimin Rashin kunya ba"
Maryam tayi sauri ta riqe hannunsa tace "ai ba karya yayi maka ba ka dakeshi sai na rama
masa"
Dariya Babansu yake musu yace"kai Miftahu kafiye tsokana kai kuma Nafiu sangirma kamar
gyambo"
Aunty tace "Haka sukeyi si tayin koka ye kokayen shashanci"
Mikewa Maryam tayi tana gyara books din hannuta gamida da gyara jakarta tace"ai sai Ku tashi
Mutafi ko"
Duk suka miqe a tare suna yiwa iyayen nasu Sallama.
Mi kewa Malam Ya'u yayi shima ya biyo bayansu Dan haka yake musu haka yake rakasu har
kusa da makarantar sannan ya dawo gida dake makarantar babu nisa da gidan Alhji Huseen
din.
Suna fitowa harabar gidan sosai Nasir ya fito daga part dinshi jikinshi sanye da kayan motsa jiki
jikinshi a Murmurde ,sakin Fuska yayi lokacin da Idonshi yayi tozali dasu Nafi'u Yace "Morning
My boys gami da dumqule hannusa kamar yadda yake musu ,Da sauri Nafi'u ya karaso yana
dariya ya daki hannun Sosai yace"Morning Ancle katashi Lafiya"
Kalau Aboki na Nasir din yafada yana Jawo hannun Miftahu suna gaisawa,
Farin ciki ne ya Lullube Malam Ya'u yana tsaye Fuskarshi tamkar gonar auduga Dan dadi.
Nasir ya Mika masa hannu kamar ko da yaushe yace "Arrama Barka da Asubah"
"Barka kadai Nasiru katashi Lafiya"
"Lafiya Alhmdilahi"
Yace "kuzo in aje Ku a Skull din ko"
Yayi can inda motarshi take a je.
Ayya ai da ka barsu ma Nan makarantar tasu take bakin hanya"Malam Ya'u yafada
Ai fita zanyi Arrama Kawai su shigo na sauke su Nasir din yafada,
Ko gama rufe baki bai yi ba Miftahu yayi gaba dama yana kwadayin shiga Motar Ancle din.
Cikin sanyi Murya Maryam tace"Ancle ina kwana"?
Yanajin ta ya share ta,bata daddara ba ta kara maimaitawa,
Shiru yayi a karo na biyu yana kokarin bude mota Malam Ya'u yace' Maryam na gaishe da kai
Nasir"
"Ok ya joyo Ya Dan kalli inda take yace" Lafiya Maryam yaya kike?
Dadi taji ganin yadda Ancle din ya Amsa gaisuwarta.
Tace"lafiya lau Ancle ,banza yayi da ita ya tada motar bayansu Nafiu sun shiga ko sauraron ta
bai yi ba yafara kokarin tafiya.
Tace "Ancle ban shiga ba fa"
Wata harara yayi mata yaja tsaki kadan Dan ganin Malam Ya'u na gurin ya daka ta tashiga
tukkuna sannan yaja motar
Malam Ya'u ya karasa bakin get din yana kokarin bude masa kofa,
Ya fice daga gidan.
Yana fita ya tsayar da Motar ya waigo yana kallonta A wulakance ,yace ke saukar