Showing 15001 words to 18000 words out of 97338 words
Chapter 6 - YARO DA KUDI Book Complete by Binta Umar Abbale .pdf
yana mata wulakantacan kallo ,ya tsare kofar dakin ,"yace get Out" joya
wa tayi da nufin tafiya Abdul ya dakatar da ita ,ya kalli Nasir da rai a bace yace wallahi baza ta
fita a haka na mahaifinta na waje a zaune Sam bai dace ba hakan"
Tsaki Nasir yaja ya shige dakinsa
Anwar yace"wai kai ina ruwanka da yarinyar ne malam naga fa kana min shishshigi a kanta wai
ko son ta kake yi ne iyi ,Wallahi tunda na kwadaita da ita sai na biyawa kaina bukata ko ta halin
yaya ne kai dai kafi kowa sanin halina"
Karaf! A kunne Nasir lokacin da yake fitowa daga dakin sa hijab din Maryam a qasa yana ja wai
bazai dauko da hannunshi ba,
Gabanshi ne yafadi jin Furucin Anwar yariga yasan halin sa ciki da waje tamkar maye yake
gurin mace zai iyayin komai a kanta Dan ta wani fanni na yafishi son mata tunda shi ba kowace
mace yake kwanciya da'ita bah'
Ba Dan komai ya hana Anwar cika burin sa ba a yanzu sai Dan in ya tuno da hallacin da Uwar
yarinyar tayi masa ,bazai taba cutar da jinin Aunty shi ba zai bari a cuceta ba yarinyar taci
darajar malam Ya'u da Aunty shi ,Amma da badan haka ba a gabanshi zai sa Anwar ya
yagalgala masa ita wallahi sabida tsabar haushin da take bashi taqi fita daga rayuwarsa kullum
ya kwanta sai tazo masa cikin baccinsa ta ida nunta masu ban tsoro a cewar sa ,shine dalilin da
yake ganin anya Aunty shi ba mayya ta haifa ba ,tunda shi maye ruwansa da ita,
Da sauri Abdul yaje ya cire hijab din daga kasan kafar Nasir din ya mika mata yace"maza ki sa
kinji ko kiyi tafiyarki Allah ya saka miki"
Da sauri ta karbi hijab din hannuta na rawa ta zira tayi hanyar fita daga dakin tana Addu'ar
Neman tsari gami da godewa Allah da ya tsareta daga sharrin su Nasir
*✍,,,,,,,,*
*YARO DA KUDI*
*✍WRITTEN BY*
_*Binta Umar*_
~*Maman Abdul Wahabu*~
~*Mrs Ahamad gwadaba*~
_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATAR
CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176
~*DEDIGATED TO MY FAN'S*~
*30*
Abdul latif ya daura idonsa kan Nasir bayan fitar Maryam Ransa A mugun bace yac" yanzu kai
Nasir da kai za'a hada baki gurin cutar yarinyar can hakan da kukeyi yayi daidai kenan Abinda
kuke a waje shine za kuzo gida kuyi mai Maryam tayi maka ? Yarinyar da take bala'in tsoranka
wane irin Abu Aunty tayi maka zaka saka mata da haka"? Ya karashe ya Maganar yana sauke
ajiyar zuciya cikin tsantsan bacin rai!!
Wani kallon banza Nasir yayi masa yana ya mutse fuska cikin izgili yace" kai karfa ka kawo min
maganar banza mana ,Kai meye ruwanka da ita lokacin da kashigo A kai na kaga yarinyar da
zaka daura min jakar tsaba ,mai zanyi da'ita ,Aba sai kace zabiya Mtssss! Sam Sam Allah ya
tsareni ita Dan Uwarta mai yakawo ta dakina anan fa naganta har da tube hijab tamkar tana
dakin Uwarta" ya karashe maganar yana wani zakuda kafada Alamar babu Abinda ya dameshi,
Dauke kansa yayi daga kan Nasir din cikin bacin rai har ila yau jin irin Furucin da yakeyi Lallai
Nasir yayi Nisa!
Ya kalli su Anwar yana girgiza kai yace "Wallahi mutukar Wani Abu ya samu yarinyar nan ta
dalilinku sai nayi Shara'a da Ku A kanta , kai ne mai furucin ko ta halin kaka sai ka kauda
kwadayinka a kan ta ,yafada yana kallon Anwar,yaci gaba da cewa Wallahi duk in da zanshiga
in fita zan shiga a kan in Daukar mata fansa
Wani kallon banza Anwar yayiwa Abdul din yace"Kai ka isa ka hanani ae kata Abinda nayi niyya
A kan waccan yarinyar Mara galihu "yar mai gadi da har kake wani tada jijiyar wuya a kai kai a
suwa Kai din banza" ya karashe maganar yana furzar da wani huci mai daci Aba kinshi,
Girgiza kai Abdul yayi yana binsu da kallo daya bayan daya ,ya kalli Anwar din A karo na biyu
ganin yadda ya zaqe da yawa har yake wani rantse rantse gami da cin Alwashi a kan Maryam
din Tabbas idan wani Abu ya same ta Wallahi Anwar sai ya gane bashi da wayo
Yace"OK toum tunda ka rantse ae ga fili nan ga mai doki sai ka bada himma tanan ni kuma
zaka San ka tabowa kanka Abinda baza ka iya ba kana maganar Maryam bata da gata to tana
da gatan Allah dani in sha'Allahu Allah zai tsareta daga sharrinku ,kai kuma Nasir ya fada yana
nunashi da hannu yace "wallahi duk Abinda ya samu Maryam ka tabbata babu rufin Asiri dady
sai yaji domin kanajin furucin wannan Mara mutuncin a kanta kayi shiru wato kabashi goyan
baya kenan ko mai yarinyar nan tayi maka da kayi mata wannan tsanar da har zaka bada hadin
kai gurin cutar da ita, nafada na kara maimaitawa kar Ku batawa yarinyar nan rayuw.....
Kai! Arrama da kata mana Dan Allah ya isa haka" Abbas yafada Wanda tun zamansa a gurin
bai ce uffan ba ,sai yanzu
Ya gyara zama gami da zakuda kafada ,yaci gaba dacewa,Ubanmu ne kai wai da zaka titsiye
mu kana zagi ina Ruwanka da duk Abinda zamuyi Rayuwarka ko tamu ,Malam kar kasake kawo
mana maganar banza yarinyar daka ke wani tada jijiyar Wuya A kanta kana da Alaqa da ita ne
kai idan baza kayi ba sai ka hanamu kai baka isa ba Wallahi Kaii!! Kauce Malam!! Yafada A Fusace!
Tsaki Nasir yaja yana duba Wani Dan kareren agogo a daure a hannunshi bakwai shaura na
Magariba Ya kalli su Abbas din yace "guys Ku tashi mu ware Ku rabuda wancan Komai Allah
yace Annabi yace ko wa zai gayawa sanin Allah oho,"
Cikin Mutukar bacin rai Abdul ya fuce daga dakin yana Allah wadai da tur da wannan dabi'ar da
Abokannanshi "yan Uwanshi suka jefa rayuwarsu ciki
Yana fita suka Kwashe da dariya gami da tafawa ,Nasir yace"ni narasa gane kan wancan
gayan wallahi A kwai shiga Abinda babu ruwanka ko mai ya shafeshi da Lamarin yari yar oho"
Dariya Abbas yasa yace"mybe ko son ta yakeyi Dan ga Alamu nan sun bayyana"
Tabe baki Nasir yayi yace"tabbas da ya cika Dan Asara Wallahi yarasa wa zai so sai wancan
yarinyar mai kama da ru66a66an tomatiri Allah ya sawaqe mai!!"
Dariya sukayi dukkaninsu gami da mikewa domin fita,Shima dariyar yasa yace"Wallahi nake
gaya maka Ae irin su babu Abinda zakaji sunayi sai qarni in ka kusancesu Sam Sam yarinyar
batayi ba yafada yana tabe baki,
Anwar yace"komai me takeyi sai na biya bukata ta a kanta Wallahi idan Uwar qarni ma takeyi
bai da meni ba"
Gabanshi ne yafadi kadan ya Dan kalli Anwar din ta gefen ido ,jin Furucinsa har yanzu a kan
Maryam din ,bai qara cewa komai ba har suka fice daga shashen gaba daya
Wata sabuwar mota suka shiga Nasir ya ware kida kamar yadda ya saba suka five daga gidan
*✍,,,,,,,,,,*
*YARO DA KUDI*
*✍WRITTEN BY*
~*Binta Umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~
~*MRS AHAMAD GWADABE*~
_*WANNAN BOOK DIN NASIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI
SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176
*DEDIGATED TO:MY FAN'S*
*31*
Lokacin da Maryam ta fita daga dakin Nasir kai tsaye part din Mom ta nufa cikin Nutsuwarta
tamkar babu Abinda ya faru.
Mom na kokarin hawa sama domin gabatar da sallah magariba ,sai ta dakata ganin shigowar
Maryan din.
Cikin sakin Fuska tace" Maryam Kin gama ko?
Cikin Nutsuwarta kamar ko da yaushe tace"Eh Momy na nagama Farlour ne ban gyara ba sai
gasu sunshigo game lokacin Sallar Magarb yayi zanje nayi Sallah".
Mom din ta gyara tsayuwarta tana kallon ta tace"ina fatan bai miki komai ba nasan Halin
kayana"
Murmushi tayi kadan"tace Momy na kenan Mai zaiyi min Ancle din yace ne kawai in tafi tunda
sun shigo "
"Daga haka fa" Momy tafada tana mata kallon tuhuma.
Sai ta duburburce tana tsoran kar Momyn ta Fahimci Abinda yafaru,yanzu gashi ita kuma qarya
ba dabi'ar ta bace,
Kallon zargi Momyn take mata race"kifada min gaskiya daughter kinji ko"?
"Ok zo nan Muje sama Muyi sallah a nutse sai ki fada min"
Momyn tafada gami da karasowa inda take tsaye ta kama hannunta suka haura Sama inda
dakunan su suke.
Bayan sun idar da sallahr ne Cikin Nutsuwa Mom din ta kalli Maryam tace"kifada min idan ya
dake ki kamar yadda ya saba kinji doughater"
Shiru Maryam tayi tana wasa da hannunta.
Sai da Mom din takara Maimaita tambayar,sannan tace"Allah Momy babu Abinda yayi tafada A
fili a zuciyarta tana Jan Istigifari.
Taci gaba da cewa ,Dama Dama Wannan Abokin nashi ne,sai tayi shiru takasa karasawa,
Ina jinki ya kikayi Shiru Momyn tafada"
Shine Yake kulani Momy nikuma bana so tafada kanta a kasa,
Momyn tace"To ae kina da gaskiya Mutuncin "ya mace tsare kanta babu ruwanki dashi ko ya
kulaki ,gaisuwa kawai na lamunce kiyi dashi kinji ko kuma zanyiwa Nasir magana tunda ba
kyaso tayi masa magana duk inda ya ganki Kar yakara shiga lamarinki"
Gabanta yafadi jin Abinda Momyn take fada,
Da sauri ta dago kai tace"A,a Momy ba sai kin yiwa Ancle maganar ba Dan Allah"
Harararta Momyn tayi kadan tace"ae dole in yi mishi magana yajawa Abokinshi kunne domin a
kanki zan iya batawa dashi"
Sunkuyar da kai tayi tana Murmushi kadan tace"Dan Allah Momy mubar maganar bana so ki
batawa Uncle rai"
Dariya Momyn tayi gami da Mikewa daga kan daddumar da sukayi sallah A kanta tace" in dai a
kanki ne ran Nasir zai baci kuwa ,
Mikewa tayi ita ma tabi bayan Momyn suka sauka kasa ,a tare Maryam din na kokarin fita da
niyar tafiya bangaransu Momyn ta dakatar da ita,tace Lallai sai ta tsaya sunci Abinci tare ,ba
yadda ta iya haka ta bi bayan Momyn can dainnig in da kayan Abinci ke jere iri iri na haduwa na
Alfarma,
Momyn ta hada Mata komai tsaf ,Cikin nutsuwa Maryam tafara cin Abincin suna hira da Momyn
kadan kadan ,sai da Momy ta tabbatar da Maryam ta koshi sannan ta kyaleta ta tafi
bangaransu.
Lokacin da tashiga shashin nasu Ana sallahr isha'i Aunty da su Nafi'u duk sallah suke ,sabida
haka Alwala ta daura ita ma tabi sawun su.
Aunty na idarwa tafara hidimar Zubawa yara Abinci ,ta kalli Maryam dake zaune kan dadduma
bayan ta idar da sallah tana Addu'a ,"kefa a zuba miki ? Nasan dai kinci gurin Momynki ko?
Daga kai Maryam tayi A nutse tace wallahi kuwa Aunty a koshe nake Amma da safe naci
dumame dama yafi dadi"
Tabe baki Aunty tace Allah ya kaimu . mai kika tsaya yi a ne a can?
*✍,,,,,,,*
[14/03, 12:41] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*YARO DA KUDI*
*✍WRITTEN BY*
~*Binta Umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~
*28*
To masha Allah Mom tace dama ae ni haka nakeso duk da nasan ba laifin ki bane dama nashi
ne.
Bata ce komai ba ta karbi key din kanta a qasa ta kama hanyar fita daga farlour n Nom tace kiyi
sauri ki gama mybe yanzu ki kanshi domin Lokacin shigowar ne yanzu mussaman yafita tun
safe nasan dole zai dawo ko Dan yin Wanka ,sannan
Cikin nutsuwa tace in sha Allahu zan yi sauri Momy ,
Yawwa Allah yayi miki Albarka Maryam
Amin tace ta kama hanyar fita daga Farlour nan
To ko da Maryam ta bude shashin Uncle din Abin yayi mugun bata mamaki ganin yadda ko ina
yake a hargitse babu gyara A fili tace gayu an sanku ba'a San makwancinku ba ta6! Yanzu shi
duk gayunshi dakinshin haka yake lallai
Bata kara tsinkewa da Abin ba ma sai da ta shiga bedroom dinshi taga kaca kaca komai a
hautsine kayanshi barbaje kan bed dinshi wasu a qasa wasu a kan kujera takalma a haushine
duk da gurin ajiyarsu suke mirrow dinshi kaca kaca turarurruka ne masu Dan karan tsada a
zube a gurin gami da mayuka sun fi kala a shirin wasu har sun fado kasa,
Toilet din tabude ta shiga ,Wai Abin sai a hankali da'alama tunda ya tafi Momy ba sosai take
sawa a gyara dakin ba domin bacin da yayi,, yayi yawa gajerun wando nane sunfi kala goma
gasu Nan a zube cikin Abin Tara wanki da'Alama kullum sai ya balle sabo ganin ledodinsu a
gurin ,
Nan da Nan ta Tara ruwa tafara Aikin toilet din tsaf ta'hada kayan wanki dasuke gurin ,kananun
kayan kuwa ta zuba su cikin ijin wanki ta kunna shi ,sannan ta ciga da Aikinta ,duk wasu
tarkacan su gwangwanin turarurrukan Wanka gami da kwalayen sabulai da sauransu sai da
takwashe tsaf cikin wani katon duzbin' tafito dashi can harabar gidan,
Ta koma ta matse kayan da ta zuba cikin Abin wanki ta shanyasu tsaff jikin hangar dake manne
a toilet din ,takashe injin,gami da qara wanke toilet din tas sai da ta tabbatar da yayi mata yadda
take so sannan tafito tafara Aikin bedroom din cikin Nutsuwar ta
Hijab din jikinta ta cire ganin yana hana ya Aiki kafin ta Ankara tafara jin kiran sallah magariba
Cikin sauri ta karasa shimfida bed shirt din ta jera fililon kan tsaff ta karasa kan Mirrow din
tafara gyara ka yayyakin dake Kai tsaf ta jere su gwanin sha'awa ta share dakin Tass tafitar da
duk wani Abu Mara muhimanci gurin takalmanshi ma tsaff ta gyara masa dakin sai fitar da wani
irin qamshi yake mai dadi ,Cikin sauri tafito farlaur din hannunta riqe da wata katuwar Leda da
ta zuba tarkacan da ta sharo a dakin ,shaf ta manta da hijab din ta a dakin sabida yadda take
sauri kar ta rasa Sallahr magari ba Dan gaskiya maryam bata qara'i Lokacin sallah nayi take
gabatar da ita Allah ya huwace mata wannan,
*Allah kasamu a danshinta*
Turus tayi gabanta yana wani mugun duka ,ganin su da tayi a zaune su hudu da Alama
shigowarsu kenan Dan ko Alama bataji shigowarsu ba,Nasir ya na kokarin bude dakin suka
buga karo,da'ita da sauri ya dago kai hannunshi dafe da goshin Cikin Mamaki yaga Maryam
tsaye ta zuba masa idanunta Wanda ya tsana a rayuwarshi,
Da mugun sauri ya koma da baya yana sakin ajiyar zuciya domin ya zata mafarki yakeyi Wanda
ya sabayi nata duk daran duniya,yafara nunata da hannu bakinshi na rawa yaga za furta ko
kalma daya,
Ganin Abinda yakeyi yasa tace Auncle nice Maryam fa Momy CE tace in zo in gyara maka
shashinka yanzu na gyara maka ciki nan nakeso in gyara a nutse take maganar,
Anwar!! Anwar!! Ya kwala masa kira Cikin mugun bacin rai!!
Da sauri Anwar ya karaso gurin ,yace kai A boy wannan kira haka kaifa dadi na dakai a kwai
takurawa wallah.... Kafin ya karasa idonshi yayi tozali da Maryam tsaye jikin kofar dakin nasir
kanta a sunkuye tana wasa da hannuta ,bata son kallon Nasir ganin irin wulakantancan kallon
da yakeyi mata, Gashi babu hijab a jikinta a takure ta ke jinta,sai maqe jikinta takeyi jikin kofar,
Wani murmushi Anwar ya saki yana Sosa Kanshi sai wani kallon kurrula yakewa Maryam
tamkar ya lasheta
Tsaki Nasir yaja ,yace ga tsuntsu daga sama ga tanan dama kana nemanta kaga ba sai kasha
wahala ba yafada tana yi mata wani Dan iskan kallon raini ,cikin wata muguwar tsawa gami da
kyara yace kauce min anan Fockyou mother fourkar!! yafada yana wani tsale tamkar zai kai
mata duka,da sauri Maryam ta kauce ta bashi hanya jikinta yana kyarma ,ya zo ya wuce yana
wani ya mutse fuska tamkar yaga kashi ,ya kakalo yawo ya taufa mata ajiki ya shige dakin gami
da banko kofa,
Jikin kofar ta makale tana takure jikinta ganin yadda Anwar ya ke kusantar ta yana kokarin
Rungumeta,
*✍,,,,,,,*
[16/03, 07:01] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*YARO DA KUDI*
*✍WRITTEN BY*
~*Binta umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~
~*MRS AHAMAD GWADABE*~
~*DEDIGATED TO: MY FAN'S*~
*29*
Ya karaso daf da ita yana mata wani kallo irin nasu na "yan duniya sai lasar baki yake yi tamkar
wani tsuhon maye,
Hannunta ya kama ya riqe cikin nashi yace baby kin hadu fa wallahi babu karya ina son ki kina
so na kema? Yafada yana kanne mata ido daya,
Kauda kan ta tariqa yai ganin fuskarsa dab da tata ,tayi shiru bata ce komai kokarin ta kawai
yadda zata gudu daga hannun waddanan Azzaliman,
Sai yafara hade ta da jikin kofar dakin Nasir din da take makale ya sanya hannuwanshi duk
biyun yana lalubarta, Bige hannun tayi tana kokarin fashewa da kuka,ya kara mai da hannunshi
jikinta a karo na biyu
Sai tafashe da kuka cikin kuka" tace Uncle ka fito ka tai make