Showing 96001 words to 97338 words out of 97338 words

Chapter 33 - YARO DA KUDI Book Complete by Binta Umar Abbale .pdf

10 Jul 2025

4288

sai aukin tunani ko na meye oho maka ni dai nafada maka
akwai jama'a suna jiranka kuma tun jiya suka zo daga ghana sabida haka sai kafito"




kashe wayar yayi yana jan tsaki babu abinda yace da Abbas din kawai ya cigaba da shirinshi




tsaf ya shirya ya dauki wata karamar jaka irin ta mata fiya





kai tsaye part din Mubina ya nufa sai zabga wani mugun kamshi yake



Mubina na zaune a falo tana kallo tana braekfarst tana sanye da kayan bacci bata cire ba,yayi
sallama gami da shiga ciki
[6/20, 09:56] Binta Umar Abbale: Gabanta ne yafadi lokacin da ta ji kamshin turarashi kafin ta
ankara ya shigo falon cikin sallama fuskarsa babu yabo babu fallasa



tunda ya shigo take binshi da wani kallon wanda ita kadai tasan ma'anarshi yau yayi mata wani
kwarjini ga wani uban kyau da yayi, fuskara take bi da kallo yana tsaye yana kallonta ji take
tamkar ta je tai tata shafa kwantacan gashin da yabi kewayayyiyar fuskarshi ya kwanta yai sosai
sai kyalli yakeyi abinka da farin mutum.



kallonta yake yana jira yaga zata gai dashi koko har yanzu girman kan yana nan

kamar tasan tunanin da yake kenan tace"kanina sai ina kuma da alama zakayi tafiya ne"




"Eh zan je America zamu ni jirgin 12:00 pm ni da Abbas , zamu dawo ranar ita yau so ki kula da
kanki ,babu ruwanki da waccan yarinyar ko wacce ta zauna ma tsayinta"




"Ok shikkenan sai kadawo da kake min maganar babu ruwana da waccan " yar talakawan yo ni
dama meye runawa na da ita,ita kanta tasan cewar ruwa ba sa'an kwando bane"




"Oho miki"
yafada yana kokarin fita,sai yai saurin dakatawa gami da juyowa ya wani sha kunu sosai
yace"wato bani da matsayin da zagi gai dani ko a matsayina na mijinki sabida kin rai nani"





diriricwa tayi tana kallonshi har zatace masa kai ne ai zaka gaidani tunda kasa kake dani,sai
wata zuciyar ta kwabeta sabida tuno karanta dashi sati daya da ya huce




Tace"to ka shigo ka tsaya a tsaye ko zama kakiyi ta yaya zan gai daka"


kallonta yayi yace"ok shikkenan na lura har yanzu baki dauke ni a matsayin miji ba,amma insha
Allahu in na dawo zan nuna miki matsayinki"

yana gama fadar maganarsa ya sa kai ya fice daga falon,


kai tsaye part din Maryam ya nufa.
[20/06, 20:55] +234 808 996 5176: .[6/20, 12:06] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*

*125*



Shiru falon nata tamkar babu wani mahalukin da yake rayuwa ciki tana cikin bedroom dinta a
kwance wani irin zazzabi ta tashi dashi mai shiga kashi gabobinta duk ciwo suke mata,tana
kwance kan bed ta kudundune jikinta cikin bargo sai rawar dari take,ta rika jin motsi kamar
anshigo falon,



yunkurawa tayi tana kokarin mikewa zaune,shikuma ya sako kai dakin.




saurin dauke kanta tayi gabanta yana dukan uku-uku kwata-kwata bata tsammaci zuwanshi ba




idanshi a kanta har ya karaso kusa da ita



babu zato taga ya dago kanta dake kasa yana karewa fuskarta kallo

lokaci guda yayi kicin-kicin da fuska gabanshi na wata irin faduwa, Allah yasa kar zarginsa ya
tabbata


sakin fuskar tata yayi gami da cewa"zanyi tafiya zuwa America sai rana ita yau zan dawo ki kula
da kanki, bayan haka kuma na lura da abinda kike kunshewa kallo guda da nai miki sabida kafin
in dawo ki ki samawa kanki mafita sabida kin san bazan taba karbar dan da ba nawa ba"
bai saurari abinda zatace ba kawai ya sakai ya fice daga dakin.





Tana kwance tana binshi da kallo har ya kari maganarshi ya fice tana mamakin furucinsa

itama tafara zargin wani abu gabanya ya dinga dukan uku-uku da sauri ta diro daga bed din ta
nufi toliet ta dauko pt ta dauki fitsarinta ta fara kokarin gwadawa,Addu'a take Allah yasa kar
zarginta ya zama gaskiya





Aikuwa Allah bai amsa mata ba domin positive ya nuna mata,zaman dirshan tayi a toilet din
jikinta na kyarma,ranar da aka kawota gidan nan ranar tagama al'ada aranar tai wanka,kuma
ranar ta dauki ciki,innalillahi wa inna ilayi raji'un




Kuka ne ya kufce mata tanayi tana mai-mai ta innalilahi dama rabo ne ya kawota gidan Nasir
gashi ya fahimci ciki ne da ita tun ba aje ko ina ba, tasan sarai baya kaunar haihuwa ita kam ko
zama da kasa zata hade baza ta yadda ya zubar mata da ciki ba




nan ta karaci kuke kukenta ta mike tayi wanka tafito ta shirya tsaf, ta dauki aniyar yaqi da Nasir
duk abinda zai biyo baya zata dauka domin bazata yadda ya zubar mata da ciki ba.
[6/20, 16:21] Binta Umar Abbale: Tunda Nasir ya tafi basu hadu da Mubina ba ko wacce na
gurinta, yau kwananshi biyar saura kwana biyu ya dawo kenan,




Mubina suna waya dashi kullum in bai kirata ba ita zata kirashi wani lokacin in "yan
wulakancinsa suna kusa sai yaqi dagawa ku kuma yafara neman fada babu arziqi take masa
sallama,ta aje wayar.




Maryam ko jikinta yaqi dadi kullum cikin zazzabi take ga jiri babu damar ta dade a zaune in ta
mike tsaye sai jiri ya kusa kada ita, haka dai take daddafawa ta sha magunguna abin sai a
hankali

Misalin karfe hudu na safe na yamma jirginsu Nasir ya sauka a filin saukar jirage na Malam
Aminu dake kano,



Yaranshi Tony da giss suna hango fitowarshi daga jirgi suka nufeshi da sauri ko wanne fuskarsa
dauke da murmushi na murnar dawowar oga




rungumeshi sukai suna dariya,shima dariyar yake sannan suka nufi inda motarsu take,




Giss yace" Boss ina Abokinka ne,naga tare kuka tafi"


"yana can na barshi yana hado mana kaya mybe gobe ko jibi ka ganshi"



Tony yace"Boss ina muka nufa ne"



hutawa yake so yayi yasan in ya je gida yanzu Momy bazata barshi ba,kai tsaye yace mu wuce
can gest house dina idan na huta sai muje gurin Momy"


"Ok Boss"


lumshe idanshi yayi yana jin wani irin a jikinshi tsigar jikinshi sai tashi takeyi in ya tuno da wani
abu wanda shi kadai yasan ko menene shi

Tony da Giss ne suke ta faman yi masa hira wani ya amsa wani ya share shi kadai ya san
abinda yake damunshi tsawon kwanaki bakwai din nan da yayi dauriya kawai yake,amma bazai
je ya kashe kanshi ba,tunda shi dai ga yadda Allah ya halliceshi




"Boss mun karaso"
Giss yafada bayan ya bude mashi kofa




a hankali ya bude idanshi wadanda suka kada sukayi jajazir dasu ya fito daga cikin motar,Giss
yayi saurin yin gaba yaje ya bude mashi kofa yana jiran karasowarshi,
sai da ya shiga sannan ya bi bayanshi hannunshi rike da karamar jakarshi da ya tafi da ita
bayan ya aje jakar sai ya fito ya barshi domin yaji dadin hutawa




yana zama gefan gado wayarshi ta fara kara

wayar ya kalla ganin Momynshi ce yasa ya dauki wayar yana sauke ajiyar zuciya,

"Momah"
yafada muryarshi kasa-kasa



Itama ajiyar zuciyar ta sauke tace"Myson ya naji muryar ka kamar na mara lafiya,uhum? ina nan
zaune ina jiran karasowarka, kace karfe hudu zaku sauka ko"?




Gyara murya yayi ya san halin Momynshi yanzun nan sai ta tada hankalinta, yace"Momy mun
sauka, yanzu haka ina gesthouse dina,ina hutawa bayan sallahr magariba zan shigo"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login