Showing 72001 words to 75000 words out of 97338 words

Chapter 25 - YARO DA KUDI Book Complete by Binta Umar Abbale .pdf

10 Jul 2025

4306

abinda nayi mata, wai mai yasa
zuciyarki take wasiwasi a kai na ne , Momy mai zanyi da wannan zabiyar yarinya, ok tunda abin
ya zama haka, kar ki kara turo ta tayi min gyara a dakina"
[30/05/2019 11:35 PM] ®Binta Umar Abbale: Momy tace"a kwai abinda ya faru tsakanika da ita
myson ni ba Yarinya bace"


Dariya ce ta kashi sosai ya rika yi ganin yadda Momy ta dage tana tuhumarsa

Yace"ok toum Momy tunda kince haka sai kije kiyi mata ruwan zaki kawai"

Kunya ce ta kama Momyn ta kai masa duka a kanshi tace"baka da kunya ko Myson "

"To Momy kin dage sai tuhuma ta kikeyi wai mai nayi mata, ai in nayi mata wani abu daga
lokacin da ta fita zaki ga alamu ko ta wurin tafiyarta ne"


Momy tace"to mubar naganar ma daga yau na daina sata tayi maka aiki yafi alkairi"

Tabe baki yayi kawai ya koma ya kwanta ,tace" ka fasa fita yanzu ne"

"Yanzu zan fita Momy ina hutawa ne"

"Ok sai ka fito"

Ya fi miti goma a kwance bayan fitar Momy din sai mutsu-mutsu yakeyi duk ya rasa inda zai sa
kanshi da kyar dai ya mike ya nufi toleit ya sake yin wani wankan tun kafin ya gama yafara jin
wani sanyi-sanyi yana ratsa shi a daddafe ya fito cikin karfin hali yake kimtsawa zazzabi ne
yake so ya rufeshi ,haka dai ya daure ya gama kimtsawa ya fito cikin shirin fita
Momy ta kalli agogo tace"baka yi yamma ba kuwa myson dubi time"


"Momy karki damu Hospital kawai zan shiga daga nan babu inda zan je"

"To Allah ya tsare"
Momy tafada


Yana fita Giss dama yana tsaye ,sai kawai ya rufa masa baya Tony ya bude masa mota ya
shiga yayi saurin zagayawa ya zauna gurinshi, Giss ya shiga Tony ya ja motar suka fita daga
gidan.
[06/06, 01:48] +234 808 996 5176: [31/05/2019 8:53 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*99*

Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin, Maryam ta rika kiyaye haduwarta da Nasir sabida wata
irin kunyarsa take ji sosai kuma har yanzu soyyayrsa tana nan daram a cikin zuciyarta

Yau misalin Tara Na dare suna zaune ita da Abdul a harabar gidan suna hira cikin nishadi
,shima yau kwanansa biyu da dawowa sosai Maryam tayi kwalliya tana cikin atamfa "yar
Ghana anyi mata duguwar riga mai babban hannu sosai tayi kyau ta yafa mayafi kalar kayan
fuskarta ta sha kwalliya suna zaune a cikin wasu kujeru farare masu kyau

Abdul yace"insha Allahu a satinan za'akawo komai na aure za'a sa sati hudu daurin aure, in
naje nadawo"


Maryam ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya tace"to Allah ya kaimu"

Yace" maganar aikinki kuma zan samu Nasir da takkadunki nasan bazai ki daukirki ba tunda
tunda takkadunki sunyi
kyau

Da sauri ta dago kai tana kallonsa jin abinda yace


Tace" Kana ganin zai dauke ni kuwa kasan bama shiri dashi"


Dariya Abdul yayi yace"karki damu nasan yadda zanyi dashi"


Sai wajan karfe goma da rabi Abdul ya mike da niyar tafiya bayan ya aje wasu manya manyan
ledoji


Maryam ta mike ta biyo bayanshi suna tafiya suna hira har ya karaso kusa da motarshi, ya
shiga yana kokarin fita , Mai gadi ya bude get din Nasir motar Nasir ta shigo cikin gidan


Sai ya kashe motar kawai ya fito yana jiranshi Maryam na tsaye a gefanshi kanta a kasa,Sam
bataso ta hada ido da Nasir din



Giss ya bude masa kofa ya fito ,fuskarshi babu yabo ballasa ya mikawa Abdul hannu suka
gaisa


Abdul yace" yanzu nake zan can kada ma"

Fuskarshi ya saki yace" yaushe kadawo ne Alhaji"


"Yau kwana biyu da dawowa wallahi, nazo ganin amarya na"

"Ok andawo lafiya ya aiki"?
Nasir yafada yana binshi da wani kallo jin abinda yace

"Alhmdullhi wallahi komai normal"


Nasir ya zare hannunshi cikin gajiya yace"zan shiga ciki Abdul nima Na gaji ,gashi gobe nake
saran zan wuce america amma bazan dade ba"


"Allah ya kaimu da jirgin safe zaka bi ko na yamma"?

"Na yamma"
Nasir yafada yana kokarin barin gurin

Abdul yace "zan shigo da wuri insha Allahu a kwai alfarmar da nake nema a gurinka"


"Allah ya kaimu lafia"
Yafada yana wucewa Giss ya na take masa baya

Duk wannan abinda yake faruwa Maryam kanta a kasa tana jin duk irin share-sharen da Nasir
yakeyi shi kuma Abdul din sai wani binshi yakeyi lallai ta yadda Farin jini da daukaka a jininsa
take
[31/05/2019 9:17 AM] ®Binta Umar Abbale: Ita yanzu ta daina shiga sabgarsa ma kwata-kwata
sabida ta lura ba karamin dan iska bane


Abdul yayi mata sallama ya wuce ita kuma jiki a sanyaye ta wuce bangarqnsu



Momy na zaune cikin kujera tana kallo kuma tana jiran shigowar Nasir din sabida bayan fitarshi
dazu Alh Salisu yazo ya kare mata rashin mutumci wai itace take zigashi yakeyin duk abinda
yakeyi cikinsu babu Wanda yake gani da gashi ,sabida haka lallai in ya dawo ta ce masa yaje
yana naimanshi ,aura shi da Mubina babu fashi, tunda haka Mahaifinshi yace kafin rasuwarshi.

Momy ranta ya baci domin har kuka sai da tayi tunda take babu mutumin da ya taba tsayawa a
kanta yayi mata cin nutumcin da Alh Salisu yayi mata yau, sabida haka mutukar ita ta haifi Nasir
dole ne ya auri Mubina inyaso daga baya sai ya auri zabinshi.



Yayi Sallama ya shigo Momy ta bishi da kallo har ya karaso kusa da ita ya zauna, ita kanta
tausayinsa takeji ganin yadda girma ya hau kanshi da kananun shekarunshi amma da yake

*Yaron* yana da ilimi cikin nutsuwa yake tafi da komai


Yace"Momy na gaji wallahi"

Cikin tausayi ta kalleshi ,ta kasa cewa komai ma


Sai ya dago kai yana kallonta jin har ya shigo yayi magana Momy bata tanka mashi
Lallai akwai wani Abu


Ya gyara zamanshi sosai yace"Momy menene,? Bafa nasan in ganki cikin damuwa, uhmm
lafiya lau Na fita na barki"



"Myson lafia ba lafiya ba"
Momy tafada tana gyara zama sosai tana fuskartansa


"Tell me"
"Momy fada min ko manene kinji"


"Dazu bayan fitarka Kawunka yazo har cikin falon nan ya karemin zagi sosai wai lallai sai ka
auri diyarshi ,sabida haka mutukar nice Na haifeka dole ne ka aureta domin mu samu kwanciyar
hankali"


Ranshi ya baci mutuka jin abinda Momy take fada masa


Yace"Momy kikace "uncle Salisu yazo gida ya zage ki to akan me"?


"Ga dalili nan na fada maka"
Momy tafada


"Ouk sabida a auri "yarshi yazo har gida ya zageki"
Yafada a zafafe sai huci yakeyi"

"Cam down My son, ban fada maka wannan magana ba fa domin ta daga maka hankali, kuma
bance in kaje kayi mishi rashin kirki ba, ni dai kawai ga umarnin da na baka"



Shiru yayi kawai ya koma ya kwanta hade da rimtse idonsa lallai dole yayiwa tufkar hanci domin
kuwa babu shegan da ya'isa yazo ya runka tadaga mahaifiyarshi hankali wallahi ,sabida a halin
yanzu ita kadai ce ta rage masa
[31/05/2019 9:28 AM] ®Binta Umar Abbale: Momy tace"kayi shiru ba kace komai ba My son don
Allah ka fitar dani kunya, wallahi nagaji da wannan cin mutumci"


Da kyar ya dago kanshi ya zuba mata idonshi wadanda suka sauya kala yace"Momy kinaso in
auri Mubina ko"?


"Inaso mai My son"

"Ki kwantar da hankalinki insha Allahu zan aureta tunda kinaso"


Momy ta saki fuska sosai tace"Allah yayi maka Albarka My son Ubangiji ya shiga al'amarinka,
yadda kake bina kaima In sha Allahu naka yaran zasu bika"


Mikewa tsaye yayi yace"Momy nagode da addu'a, zan shiga ciki"


"Ba zakaci abinci ba ne"?
Momy ta tambayeshi


Shiru yayi yana Dan murmushi

Itama Murmushin tayi tace"OK zakayi halin naka ko"

Sai ya saki dariya kawai yace" Momy ni tun a motana na cika cikina,in kinason saura in dauko
miki"


"A'a rabani da kayan zaqi nan"
Momy tafada tana tabe baki
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [31/05/2019 4:58 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA

KUDI*
*100*

Murmushi yayi kawai ya wuce dakinsa, zuciyarsa sai zafi take yi, shi yarasa mai yasa mutane
sukeyin haka, amma dole zai tari Uncle dinsa, ya kiyaye zuwa gurin Momynshi yana bata mata
rai duk abinda ya dameshi yafi mutumci ya tunkareshi da maganar
Amma Sam! Bazai yadda da bacin ran Momynshi ba.



Karfe goma shaura Abdul latif ya shigo gidan yayi parking din motarshi Nasir din ya kira a waya
"hello Abdul din yafada bayan yaji andauki wayar

"Kashigo ne"?
Nasir din ya fada

"Eh kana part dinka ko kana gurin Momy"?

"Kashigo gurin Momy kawai"

"Ok"
Abdul yafada ya kashe wayar


Momy Na zaune cikin kwalliya kamar ko da yaushe, suka gaisa da Abdul cikin sakin fuska tana
tambayarshi mutan gida

"Lafiya kalau Momy"

"To masha Allahu"

Nasir yana zaune kan kujera cin abinci ,hannunshi rike da waya yana latsawa Abdul ya karasa
inda yake ya zauna kujara guda, gami da mika masa hannu
"Ya a kayi ne Alhaji"
Nasir yafada hannushi rike da hannun Abdul din


"Normal Alhaji"
Abdul yafada yana dariya


Yace"ya shirye-shirye"?

"Na kammala sai tafiya kawai"

"OK kasan abinda ya kawoni gurin ka"?

"Sai kafada"
Nasir ya fada yana danna waya


"Zan kawo maka takkadun Maryam ka duba don Allah ka dauke ta aiki a hospital dinka ,kasan a
nan zan barta cikin Estet din mu Na family kafin in kammala ginina ,in kuma nasamu gurin zama
zan dauketa mu tafi tare"


Ba tare da ya kalleshi ba yace"wacece Maryam"?


Abdul ya sha kunu yace"bana son iskanci fa"


Fuskarshi ya hade yace"ban fahimci wace Maryam kake nufi ba,ai shiyasa na tambayeka"

"Ok My wife dina yarinyar gidan nan"
Abdul yafada babu wasa a fuskarshi


Nasir ya dago kanshi yana kallonsa tsawon minti uku bai ce komai ba, ya saki Murmushi gami
da cewa "a yanzu dai bama bukatar ma'aikata, in ma muna bukata to batayi ilimin da zata yi aiki
a wannan asibitin ba"


"Mai kake nufi"?
Abdul yafada rai a bace


"Bana nufin komai"
Yafada hankalinshi Na kan wayarshi


"Look Nasir ka tsaya kayi min maganar da zan fahimta bafa na son wulakancin ka Wanda ka
saba"
Abdul yafada ranshi a mugun bace

Momy ta waiwayo da sauri ganin yadda Abdul din yake daga murya tace"lafiya wai naji kuna
magana Sama-sama"?
[31/05/2019 5:21 PM] ®Binta Umar Abbale: "Momy wai sabida yaron nan bai da kirki nace
masa, ya dauki yarinyar nan aiki a asibitinsa, shine yake fada min magana"


Momy ta kalleshi tana murmushi tace"duk abin ai ba Na zafi bane Abdul wace yarinya kake
magana a kai"


"Momy Maryam nake miki magana fa"


"Ok Dota wai"?

"Eh Momy"?
Abdul ya fada yana mikewa tsaye ranshi a bace


Momy ta kalli Nasir yana zaune har'ila yau hankalinshi na kan wayarshi


Tace"Myson Dan Allah ina Neman alfarma nima ka dauketa aiki,wai maiye duniyar ne ,tunda dai
Abdul din ya amince tayi ai shikkenan , Wanda ya taimaki wani shima Allah zai tai makeshi"


"Momy ki rabu dashi don Allah kar Allah yasa ya dauketa zan cigaba da nema mata"


"A'a duk baza ayi haka ba , ka koma ka zauna mu kashe magana"
Momy tafada tana kallon Abdul din

A gogo ya kalla yace"Momy wucewa zanyi wallahi banason abin bacin rai , zamu iya rigima
dashi yanzu"


Cikin mamaki Momy tace"akan mace zakuyi rigima da Dan uwanka Abdul"?


Kunya ta kamashi sai ya sunkuyar da kanshi kawai


Momy tace"koma ka zauna"

Ya koma ya zauna kawai gami da dauke kanshi yaki yadda ya kalli Nasir din

Shi kuwa babu abinda ya dameshi


Momy tace"Myson "mai kace a kan maganar"?


Tafi minti biyu kafin yayi magana, daga bisani yace"Momy ni a yanzu bani da lokaci amma zata
iya zuwa gurin Dr Sofia tayi mata intervio shikkenan sai ta ajeta a matsayin da ya dace"



"To ai babu matsala sai taje din"
Momy tafada,ta cigaba da cewa kai Abdul kaji abinda yace"


"Momy babu komai ai sai taje tunda naima takeyi,Allah ya rufa asiri"


"Ameen ameen"
Momy tafada ta cigaba da cewa dan Allah kar Ku yadda wata mace ta farraqa tsakaninku kunji
ko"


"Momy kar kidamu insha'Allah"
Abdul din yafada yana mikewa da niyyar tafiya yayiwa Momy sallama




Bayan fitarshi Momy tace"don Allah my son ka rage girman kan nan gami da izza domin babu
inda zata kai ka"



Dariya yayi sosai har sai da habarshi ta lo6a yana kallon Momy din yace" Momy yaya ake
girman kai don Allah mutane da dama suna fadin haka a gareni , basu San cewar ni haka
nuture dina ne ba"

"E ai duk da haka my son kana karawa da wani ni dai nace ka daina"


"Insha Allahu Momy kiyi min addu'a"


Momy ta zauna suka cigaba da hira cikin so da kaunar juna.
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [01/06/2019 5:11 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*101*
Nasir bai tafi America ba sai da yaje gurin kawunshi Salisu, sabida yadda yaga Hankalin Momy
shi ya tashi a kan al'amari, nan uncle Salisu ya rika kwantar da kanshi yana rarrashinsa, da yayi
hakuri ya auri Mubina, Nasir yayi mamaki ganin yadda yake kwantar masa da kai sai kawai ya
basar , yace" magana ta wuce amma don Allah kar ka kara tayarmin da hankalin Momy domin
abinda kayi mata ya daga mata hankali, zan wuce america, sati biyu zanyi zan dawo in yaso sai
muyi maganar, Abin mamaki Dadyn Mubina ya dinga washe baki yana shi wa Nasir albarka nan
Nasir ya tafi ya barshi sai mamakinshi yake,lallai mutane basu da kirki, wato in kana da kudi
komai kafada dai-dai ne ,shi kanshi yasan ba don Allah uncle din nashi yakeso ya hadashi aure
da diyarshi ba.


****
Yau satin daya da tafiyar Nasir ,Abdul ma ya tafi bayan ya kammala komai na maganar aure
rana kawai ake jira,cikin so da kaunar juna sukayi sallama da Maryam.


Momy kadaici duk ya dameta sai ta fito harbar gidan ta zauna kan kujera kawai nan su Nafi'u
suke zama da'ita suna hira Maryam ma sai ta samu gurin zuwa , siyi ta hira cikin fahimta



Ranar Momy ta tashi ta shiga ciki sai ta bar wayarta kan kujera Maryam na zaune suna chating
da Abdul sai Murmushi takeyi kawai da'alama hirar tana mata dadi


Wayar Momy tafara kara da sauri ta kalli fuskar wayar, Myson ta gani yana yawo a fuskar
wayar.


Gabanta ya fadi tayi kamar ta dauka wata zuciyar tace kar ki dauka, wayar ta katse kafin ta
farga wani kiran ya kara shigowa,

Sai da takusa katsewa sannan ta daga batare da tace uffan ba


Ajiyar zuciya taji yana saukewa kafin taji wani irin voice da ya kusa sumar da ita a zaune
Momynahhh"
Taji ya fada yana ajiye numfashi



Shiru babu magana

"Please Momy kiyi min magana mana yinin yau banji muryarki ba ayyuka sun dame ni"


Maryam tana ta kokawa da zuciyarta, jikinta yayi bala'in daukar dumi domin Nasir ya gama
kashe mata gangar jiki, gaskiya tana bala'in kaunar Nasir



"Momy"
Maryam taji yafada da ainihin muryarsa ,sai taji kamar ma acikin damuwa yake

Sai tayi saurin kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya daki-dai
[01/06/2019 5:38 PM] ®Binta Umar Abbale: Momy ta dawo gurin, ta kalli Maryam dake zaune
tace"Dota na barki ke kadai ko"


Maryam tayi murmushi tace"A'a Momy chating nakeyi ma"



Wani kiran ne ya kara shigowa wayar Momy a karo na uku


Momy tayi saurin daukar wayar tana dariya


Tace"Myson yau nayi fushi ,nayi ta tsammanin kiranka tun da safe naji shiru nace Allah yasa
lafiya"


Ajiyar zuciya ya sauke yace"Momy ina ta magana shine kika shareni ko"

Cikin mamaki tace"yaushe akayi haka, My son"?


"Yanzu Momy na kira sau biyu ina ta magana naji shiru"


Momy tayi murmushi tana kallon Maryam tace"ba nice na daga wayar ba Myson Dota ce wallahi
ni Na shiga cikin gida"


Shiru yayi na minti biyu sannan yace"Momy mun gama magana da uncle ,in nadawo za mu
tsayar da magana ina fatan haka yayi miki"


"Yayi dai-dai Allah yayi maka albarka"


"Ameen ameen Momyna"

Sukayi shira sama-sama sannan yayi mata sallama dama a cikin busy yake yanzu ma free ya
samu shiyasa ya kirata sabida duk abinda yakeyi hankalinshi na kanta.



Bayan Momy ta aje waya ta kalli Maryam cikin murmushi tace"Dota Son'ya kira waya kinki
magana mai yasa"?



Maryam tayi murmushi tana tunanin abinda zata ce ,da kyar dai tace "Momy kafin inyi magana
ya kashe wayar shiyasa"


Dariya tayi tace"ina fatan dai kinje anyi miki intarvio kamar yadda ya fada"


"Momy ban je ba"


"Mai yasa Dota"

Shiru tayi kanta a kasa domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login