Showing 84001 words to 87000 words out of 97338 words

Chapter 29 - YARO DA KUDI Book Complete by Binta Umar Abbale .pdf

10 Jul 2025

4305



Sai data ga ficewarsu sannan ta koma ciki




To ban garan su Maryam kuwa lokacin da labari iskesu, kasa katabus sukayi jikinsu yayi sanyi,
Aunty tafi minti ashirin tana jajanta abun , Nasir ne ya auri diyarta Maryam anya wannan Abu ya
hadu

Sai ta dinga tuhumar Nafi'u yadda a kaiyi haka tafaru, nan ya warware mata dukkanin abinda ya
faru

Maryam kamar ta mutu Dan bakin ciki kuka takeyi wiwi, babu Abinda zata cewa Anwar sai dai
tace "Allah yayi mata sakayya wannan tozarcin da yayi mata cikin jama'a
[08/06/2019 7:42 PM] ®Binta Umar Abbale: Shi kuma Abdul, ta barshi da Allah yadda yaci

amanarta bazata taba yafe masa ba, in ta tuno wai ita matar aure ce kuma matar Nasir sai
gabanta yayi ta mugun faduwa, Ya Rabi tayi tayi da ita tayi shiru abin ya gagara ,




Malam ya shigo yana sa6e babbar riga kana ganinshi kasan yana cikin tsantsan farin ciki



Kawai ya taddasu sunyi jingum jingum sai kace gidan makoki, ya bisu da kallo daya bayan daya
kana ya mayar kan Maryam wacce ke rakube gefan kujera tana shirgar kuka kamar wacce a kai
ma mutuwa



Ranshi ya baci ya daka mata tsawa gami da cewa"kukan mai kikeyi Maryamu"?




Ya Rabi tace"wallahi kuka take tun da taji labarin abinda ya faru, anyi anyi tayi shiru taki yi"



Zama yayi cikin kujera yana fuskantar ta yace" wani irin kuka zakiyi Maryamu ke da Allah ya
rufawa Asiri lokacin da a kaso a tona miki, tabbas nasan a kwai abinda Allah ya boye a wannan
al'amarin,
Abinda nakeso dake shine ki kwantar da hankalinki kina tare da albarkamu insha Allahu zakiga
alkairi a rayuwarki mutukar kika yimana biyyaya, nine mahaifinki na kuma karbi sadakinki na
kuma bawa Nasiru Auranki a madadin Abdul"
Malam ya karashe maganar gami da zira hannu cikin aljihun malin malin din dake jikinshi ya ciro
kudi yace"ga kudin sadakin ki Maryamu Allah yayi miki albarka ya baki zuri'a tagari tare da "yar
uwarki abokinyar zamanki"

Maryam tana kuka ta sanya hannu bibbiyu ta karbi kudin dake hannun mahaifinta
[09/06, 19:26] +234 808 996 5176: [09/06/2019 2:23 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*113*
Da kyar Ya Rabi ta rarrashi Maryam ta bar kukan da takeyi ta sanyata tayi Wanka ta fito mata
da wani uban les blue colour yayi mugun yi mata kyau abinka da farar fata ta sata tayi kwalliya
dai-dai misali dama Maryam bata da matsalar gashi kullum cikin gyarashi take, dan haka Ya
Rabi ta kara gyara matashi sosai ta fito mata da mayafi pink colour hade da yari da sarka

fashion munti colour set din Takalmi da jaka iri daya masu bala'in kyau da tsada,kan kace
kwabo Maryam tafito Amarya sosai tayi kyau, haka "yan uwan mahaifiyarta suka sanya ta a
gaba suna ta bata baki kan ta godewa Allah akan sauyin da yayi mata, dama haka shi yafi
alkairi a rayuwarta



Lokacin da Mubina taji labarin abinda ya faru sai da takusa yin dan Karamin hauka, kamar ita
ace zatayi kishi da wannan yarinyar tasan tafita komai na rayuwa ilimi kudi wayewa nasaba uwa
uba kyau ita a ganinta tafi Maryam komai da komai sabida haka taci alwashin akan sai dai Nasir
ya zaba ita ko Maryam din domin bazata taba yin kishi da wannan jahilar ba.



Kwayenta sai zugata sukeyi kan in taje kar ta saurarwa Maryam kuma kar ta sake ta yadda su
zauna gida daya da ita domin babu aji.

Hanifa kuwa dariya take tana farin ciki a fili tafito tace"wallahi haukan bazan kike domin ko
makawo ne ya sha fa ki ya shafa kishiyarki yasan tafiki kyau, nesa ba kusa ba sabida haka ki
daina wani hura hanci"



Mubina ta rika zaginta kamar "yar maguzawa a kan me zatace Maryam tafita ita irin matan nan
ne masu San kansu komai sun fi kowa iyawa



A waya ta kira Nasir din tace masa ita Sam bazata zauna gida daya da wata wallahi kuma sai
dai ya zaba Ita ko Maryam




Lokacin yana tare da Momynsa kuma duk taji abinda Mubina tace hankalinta ya tashi, tun ba'aje
ko ina ba Mubina tafara shigo da tsirfa dama kwata kwata ita tasan Maryam ba zata damu ba
Mubina ce abin ji


Ganin Nasir din bai bata amsa ba ya kashe wayarsa tace"My son wane mataki zaka dauka ne
nifa banason rigima kuma ba nasan abinda zai daga maka hankali"

[09/06/2019 2:42 PM] ®Binta Umar Abbale: Tsaki yaja yace"Momy karki damu babu macan da
ta isa tasa na sauka daga kan ra'ayina , mutukar Mubina tana San zama dani dole tabi
umarnina, Momy bani da ra'ayin raba gida kuma bazan raba ba tare zasu zauna da juna
shikkean nagama magana"


"Myson ina ganin ka raba musu gidan kawai zaifi alkairi"


"Momy ki kyaleni Dan Allah wallahi Momy Mubina bata isa tasa ni nayi abinda banyi niyya ba,
kawai ki bar maganar,ke dai kawai ki cigaba da min addu'a"



"Toum shikkenan My son Allah ya taya riko ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu"



"Ameen Momyna abinda nake so inji kenan"

"Yanzu cikin Estet din zaka zauna ko zaka fita"?




A jiyar zuciya ta sauke gami da cewa "gidan Dady dake Tarauni nan nasa a gyara dazu munyi
waya da mai akin za'a mishi fanti ko wane part kowa zai dau daya tunda uku ne shikkenan
naraba gaddama babu wacce zata ga "yar uwarta sai taso"




"Kayi dabara Myson"
Momy tafada ta cigaba da cewa "yanzu ni kadai zaka bari a gidan nan ko"


Dariya yayi yace"Momy ko kinaso in zauna nan din"?


Itama dariya tasa tace"A'a babu ruwana ni bana son zama da sirika, Myson ina nan ina maku
fatan alkairi

Murmushi kawai yayi yana girgiza kai
Ya mike tsaye gami da cewa "zan shiga inyi Wanka in fito yanzu zan Dan fita a kwai wasu baki
da za muyi daga Fatkwat abinda ya hana Abbas halarta daurin auran kenan, gashi na kashe
wayoyina dole nasan zasu nemeni"




Momy tace" Yau dai daya su yi maka uziri yau ranar auranka ma sai ka fita My son"


Murmushi yayi yace"Momy kenan"
[11/06, 11:02] +234 808 996 5176: [10/06/2019 6:00 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*114*

Wanka yayi ya sanya wata shadda mai uban tsada wagambari fara kal ya sanya hula fara
takalmi mai gidan dan tsaya baki sai a goganshi na silver mai mugun tsada sosai dressing din
yayi mishi kyau kana ganinshi kasan ango ne hannushi rike da farin glass ya fito sai zabga
kamshi yake Momy na zaune tana waya da mutananta tana fada musu yadda al'amarin ya kasance,
yace"Momy zan fita ni sai bayan isha'i zan dawo"



Momy ta mike ta biyo bayanshi tace"yanzu yaushe zasu tare iyalin naka"?


"Gobe insha Allahu
Za'ayi komai a gama"

"To Allah ya kaimu lafiya"
Momy tafada cikin farin ciki


Sai da ta ga fitarshi daga gidan sannan ta koma ciki


Ban garansu Mubina kuwa buki suke sosai da sosai babu yadda bata dayi da Nasir ba a kan ta
shirya party tanaso ya hallata amma yace mata babu inda zashi dan bashi ya sata ba, haka dai
tayi hidimar bikin ita da kawayenta

Wata kawar Ya Rabi ce tazo ta dauki Maryam ta kaita gidanta ta dauko mai mai kunshi gami da
gyaran jiki, kunshi yayi kyau sosai baki da ja daki guda ta sata ta turara mata jiki gami da
gyaran fata sai da fatar Maryam tayi mulmul sosai Hajiya Aisha ta shirya Maryam sosai sannan
ta dauketa a motarta suka nufi wani hadaddan boutique ta dinga jidar mata kananun kaya masu
kyau da tsada.



Hajiya Aisha tana dreving ta kalli Maryam dake kusa da ita tace"kinga wannan kananun kayan
da na sai mai ki in kinje gidan mijinki su zaki riqa amfani dasu, kar ki tsaya kunya kinji ko tunda
kinga kina da kishiya




Kiyi kokari ki kama mijinki a hannu tunda dai Allah ya qaddara wannan yaron Mijikin ne sai ki
godewa Allah, yanzu sauran yaki yana gareki
[10/06/2019 8:00 PM] Binta Umar Abbale: Hajiya Aisha ta dage tana koyar da Maryam dabarun
zama da miji da yadda a ke kula dashi tace "su mazan wannan zamani da kike ganinsu sai da
rarrashi da siyasa, sabida haka sai in zage damtse gurin ganin kin kama mijinki a hannu"



Maryam kuwa sunkuyar da kanta tayi tana jin kunya Hajiya Aisha jin irin abinda take fada ita
kam kunya take ji tana ganin bazata iya amfani da wadan nan kananun kayan ba




Sai daf da magariba suka shiga gida,

Ya Rabi taji dadin abinda kawarta kuma aminiyarta tayi mata ganin yadda Diyarta Maryam take
walwali ga wani mugun kamshi tana zabgawa duk inda ta gifta





Bayan sallah magariba Ya Rabi tace ai ya kamata su shiga bangaran Momy domin su gaisheta
kuma suyi mata godiya da fatan alkairi

Duk su ukun suka shiga gurin Momy ta karbe su cikin mutumci gami da kyautatawa


Ya Rabi tace" Hajiya sai mukaji wannan abin alkairi kuma"



Momy tayi dariya tace"ai haka Allah ya tsara dukkanin abinda Allah ya tsara babu mahalukin da
ya isa ya hana, Allah yayi Maryam matar Nasir ce"




"Wannan abu haka yake hajiya, Ubangiji Allah ya sanya alkairi ya basu zaman lafiya Allah ya
bashi ikon kyautata adalci a tsakaninsu"


"Ameen ya rabbi nagode sosai"
Momy tafada tana kallonsu cike da murmushi




Ta cigaba da cewa gobe insha Allahu zasu tare a gidanshi dake tarauni kar ku wahalar da
kanku komai an tanada a gidan, Maryam kadai muke bukata,insha Allah kayan lefanta ma
zataje ta tadda a can"





"Hajiya Allah ya saka da alkairi ubangiji Allah ya kara arzuqi da wata mukan babu Cabinda
zamuce daku wallahi"
Aunty tafada tana sunkuyar da kanta




Momy tace "nasan dai Dota bata da matsala yarinyar tana da nutsuwa amma dai sai a kara ja
mata kunne sabida ba ita kadai zasu zauna ba a kwai "yar uwarta duk abinda zata gani ta

kauda kanta wataran sai labari






"Insha Allahu za'a yi mata fada Hajiya duk da cewar Maryam bata da kwarfinaya da yawa,
amma yau da gobe ta wuce wasa
Hajiya Aisha tafada cikin nutsuwa da dattako


Hira suka cigaba da yi cikin fahimta gami da wayewa dake Hajiya Aisha wayayyiyar Mace ce
kuma "yar boko shine dalilin da yasa Momy ta ji hankalinta ya kwanta da ita
[11/06, 13:58] +234 808 996 5176: [10/06/2019 10:17 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*115*
Nan sukayi sallahr isha'i Momy ta sanya mai aikinta Uwani ta hada musu abinci dole babu
yadda suka iya suka zauna suna ci suna mamakin karamcin Momy





Karfe takwas na daran rabar Lahadi Maryam ce durkushe gaban mahaifinta tana kuka sosai shi
kuma yana mata fada kan ta kula da auranta kuma tayiwa mijinta biyyaya da dukkanin abunda
ya umarce ta.




Aunty ma tayi mata addu'a sosai sannan tayi mata nasiha irin tama ta mata yi nayi bari na bari


Yaya Rabi daman ita kullum Cokin yiwa Maryam din nasiha


Dake babu jama'a sosai sabida basu wuce su biyar ba sai Momy tacewa drevar ya dauki
babbar mota kawai ta isa


Haka Ya Rabi ta sanya Maryam cikin mota tana gursheken kuka kamar ranta zai fita wai yau ita
ce ta auri Wanda bataso Wanda yayi mata muguwar tsana a rayuwarshi

[11/06/2019 7:09 AM] Binta Umar Abbale: Momy ta rungume ta a jikinta tace "kiyi hakuri Dota ki
zauna da mijinki lafiya da "yar uwarki nice mahaifiyar Nasir nafi kowa sanin halinshi duk wani
abu da kike tunani zai faru babu shi sai alkairi, ni da kaina zan damka masa amanarki shine ki
kwantar da hankalinki in kika iya zama da Nasir zaki ji dadinshi sabida yana da saukin kai duk
ranar da kika ga ya tashi yana muskilanci to mybe da akwai abinda yake damunshi ke zaki
dinga bibibyarshi tunda shi zurfin ciki gareshi, dan Allah Maryam ga amanar Nasir nan Na
damkata a hannunki kamar yadda ba bashi taki amanar ki lura da cinsha da shansa domin Sam
baya son cin abinci sai na tsaya a kanshi sannan"




Wani irin tausayin Momy ne ya kama Maryam babu abinda Momy zata nema ta Gaza yi mata
shi a rayuwarta sabida haka tayi alkawarin ko da Nasiru zai yankata gunduwa gunduwa za ta
tsaya ta rike amanar da ta karba



Wani irin gida ne mai bala'in kyau da tsari plate ne mai dauke da part uku sai katowar haraba
gurin ajiye motaci ma na mussaman ne can gefe lambu ne an kewaye shi da wasu karafuna
sun sha ado gurin gress kafet ne a ko ina na gurin yanayin gidan kamar irin gina ginen
kasashan waje ko ina tsaf tsaf Ma'aikatan gidan sai kaiwa suke suna kawowa ko wanne da
aikinshi




Nura tayi parking din mota Momy ta fito hannuta rike da Maryam Ya Rabi da sauran jama'a suka
fito suna bin gidan da kallo cike da kauyanci sabida kalar faint gidan ma abin kallo ne Momy ta
fito da waya tana neman Nasir ta kira ya kai sau uku ba'a daga ba, gashi tana ring sai ta kashe
wayar tana tuna in wane part din ne na Maryam tana tsaka da tunani motoci suka fara shigowa
gidan dauke da amarya Mubina da ta wagarta, motoci sun kai goma






Kan kace kwabo gurin ya cika da hayaniya dangin Mubina suka dinga fitowa daga mota kamar
bazasu kare ba.

Wata yar Momynta ce ta hangi Momy tsaye jingene da mota ,abin ya bata mamaki yanzu yanzu
sukaje can gidanta domin su mikamata Mubina a matsayinta uwar miji ba ta nan abin mamaki
sai gata anan ko mai ya kawota oho




Har kusa da Momy ta karasa inda Momy take tace"Hajiya Aminatu ashe kina nan, yanzu yanzu
mukaje domin mu mika miki amarya kamar yadda al'ada ta gadar ba mu same ki ba"





Cikin nutsuwa da sakin fuska Momy tace"wallahi kuwa ai sabani mukayi domin bamu Dade da
fitowa daga gida ba nayi tunanin zan sameku anan, ai babu matsala ga "yar uwar tata ma yanzu
zan hadasu in yi musu nasiha"
Momy tafada tana kara damqe hannun Maryam






Hajiya Abu wato yayar Momyn Mubina ta dago kanta cikin mamaki tana kallon Momy kana ta
mayar da kallonta kan Maryam wacce sukayi kafada da kafada da Momy cikin zuciyarta tace
wato ita ce ta dauko ta ma lallai yarinyar tana da fada a gurin Momy




Sai ta hau yaqen karya tana danne abinda yake zuciyarta kamar gaske tace"Masha Allahu haka
yayi, bari mu bude part din Mubina sai mu shiga ciki tunda dai ita ce uwargida"




"To babu matsala"
Momy tafada cikin nutsuwa da dattako

Hajiya Abu ta kauce daga gurin cikin dinbun mamaki dole sai sun zage damtse kan Hajiya
Aminatu in ba haka ba burinsu baxai cika ba a kan Nasiru dole ne su ci arzigi su bar arziqi a
mazauninsa.
[11/06/2019 7:49 AM] Binta Umar Abbale: Momy taja tsaki abinda ba halinta ba tace"wallahi
wasu mutanen suna bani mamaki wai sai mutum yazo ya tadda mutane a guri ya kasa gaidashi
sabida girman kai Allah ya kyauta"




Ya Rabi tayi murmushi tace"Hajiya kenan aiko mutane kowa da irinshi sai hakuri"



"Allah ya sawaqe ameen"
Momy tafada tana kara kiran wayar Nasir din a karo na biyu
Gashi tana ring bai daga ba Momy jikinta ya bata babu lafiya amma ta barwa zuciyarta addu'a
kawai take masa




Hajiya Abu ta dawo gurin a karo na biyu tace"Hajiya Bisimilah"
Dukkaninsu suka rufa mata baya




Farlo a cike sai hayaniya suke Momy ta nufi wani bedrom dake falon tace"a shigo mata da
Mubina




Nan Hajiya Abu ta kamo Hannun Mubina wacce ke cikin kawayenta sai shewa sukeyi

Kwata-kwata babu kunya irin ta amare a tare da ita fuskarta tasha kwalliya kamar me ga wani
uban gashin ido da tsa in ta kalleka tamkar wata aljana mayafin dake jikinta ma figigi ne sai
taunar jingam takeyi abun dai babu arziqi

Cikin nutsuwa Momy take binta da kallo tana nazarinta tabbas Mubina bata da da'a ko kadan
tana zaune kan kujera har da Dora kafada daya kan daya babu abinda ya dameta





Momy ta sauke ajiyar zuciya tace"Mubina sauko kasa ki zauna kusa da "yar uwarki"




Sai da ta bata lokaci sannan ta sakko kasa tana wani ya mutse-ya mutse





"Alhmdullhi Allah kai ne abin godiya daka nuna min wannan rana da raina da lafiyata"
Momy tafada tana sauke ajiyar zuciya ta cigaba da cewa "Mubina ga kanwarki Maryam a
matsayinki na babba wacce kika darata shekaru da hankali ga amanarta na baki a matsayinta
na "yar uwarki domin bazan kirata kishiyar ki ba sabida banason kuyi zaman kishi ke da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login