Showing 1 words to 3000 words out of 63190 words

Chapter 1 - MALAMIN BOGI COMPLET BOOK by Ameera Adam.pdf

18 Jul 2025

5263

[6/25, 4:05 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J

‍♂️ *MALAMIN BOGI*‍♂️


NA

MAMAN AFRAH


First Class Writer's Asso.�

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga

Da sauran su.
*09025576222*


BOOK1️⃣

PAGE 1

Mashin ne yake tafiya a hankali, mutane biyu ne a kan mashin ɗin, mai tuƙawa sai kuma
wani farin mutumi wanda yake sanye da jallabiyar fara tas da hular larabawa sai hirami rataye
a wuyansa.

Tun da suka shigo cikin ƙauyen Ƙundu, mutane suka zubawa mashin ɗin ido ba komai suke
kallo ba sai wanda yake goye a bayan mashin ɗin. A tsakiyar garin mashin ɗin ya tsaya kusa da
wata majalisa da mutane suke zazzaune. Sakkowa mutumin ya yi yana rataye da wata jaka a
kafaɗarsa inda mai mashin ɗin yake miƙo masa jakar da ya ɗora masa a gaban mashin wacce
da alama kayansa ne a ciki. Cikin wata murya mai taushi da yake furta hausa kamar ɗan koyo
amma cikin furucin akwai ƙalƙala na larabci ya ce

"Nawa ne kuɗin" Mai mashin ɗin ya faɗa masa, amma maimakon ya bashi abin da ya faɗa sai
ya fito da kuɗi mai yawa daga aljihun ya miƙa masa ya ce ya ɗauki kuɗinsa, yana mai cewa

"Wannan kuɗin ma sai da na iso nigeri'a na yi canji, ban san ya lissafin kuɗin yake ba" Ya faɗa
yana ɗan shafa lallausan gashin kansa wanda yake haɗe da saje suna sheƙi kana gani ka ga
balarabe usul.

Bayan mai mashin ya ɗauki kuɗinsa ya miƙa masa sauran, ɗauke da jakarsa ya nufi wajen
majalissar nan cikin hausar mai kamar larabci ya ce

"Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh ya ahlu hazihil ƙarya" Ya faɗa yana ɗaga
musu hannunsa da yake saƙale da carbi yana ja. Duk suka mayar da hankali kansa, suna amsa
masa a tare, hannu ya shiga miƙa musu suna musabiha kowa yana jin daɗin gaisawa da
balarabe farar fata.
Cike da ɗan girmamawa ya ce yana son a kai shi gidan shugaban garin, nan wani ya masa
jagora yana cewa gidan mai gari. Balaraben nan yana faɗin

"Ayyuwa, mafi mushkila" Da haka suka kama hanyar gidan mai gari, kasancewar yammaci ne,
sai suka samu majalisar mai gari a cike da jama,a ana fadanci, mai gari yana zaune ya ƙwame
a kan kujera. Ganin farin mutumin nan yana biye da ɗaya daga cikin mutanen ƙauyen sai kowa
ya zubo masa idanu, amma bai karaya da kallon ba, ya maje yana ɗan murmushi mai bayyana
haƙoransa wanda suke ɗauke da haƙorin makka guda biyu.

Mai gari kuwa ya saki baki da idanu yana bin mutumin da kallo, shi in ba a waya ba idan ana
nuna hoton ka'aba da yake ganin fararen fata, sai ya ce bai taɓa ganin farin mutum kamar
wannan ba. Tun kan su yi magana, mai gari ya yi ƙarfin halin faɗin

"Audu daga una ka samo balaraben mutum?" Ya faɗa yana kallon wanda ya rako baƙon. Audu
ya hau masa bayanin cewa yanzu aka sauke shi a mashin, kuma wajen mai garin ya buƙaci a
kawo shi. Mai gari ya hau faɗin cewa jama'a su matsa su ba mutumin waje, haka Audu ya ajiye
jakar a gefe ya koma gefe ya tsaya, suka zubawa baƙo na mujiya.

Mai gari ya kalli baƙo ya ce

"Barka da zuwa Malam, daga ina kuma wajen wa ka zo" Ya faɗa yana kallonsa, har mai gari ya
fara tunanin ya fara yi wa baƙon maganar bebaye, don sai ya yi tunanin ko ba ya jin hausa,
amma dai ya san tun da har Audu ya ce ya faɗa musu wajen mai garin zai zo to tabbas yana jin
hausa.
Har ya ɗauke tsammani sai ya ji baƙo ya yi gyaran murya, ya ciro jakarsa ya ta rataye,

Shek ya ɗan sunkuya kaɗan, yana murmushi da kamun kai ya ce
“Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu

“Ni sunana Sheikh Abu Abdurrahman Al-Yamanini ɗan Yemen ne daga Al-Mukalla. An turo ni
nan Najeriya domin taimakawa al’umma wajen magance matsalolin da suka shafi ruƙiyya ta
shaiɗanun aljannu, da cututtuka na zuciya da jiki.”

“Na karanci ilimin hadisi da ruƙiyya tun ina ɗan shekara 9, kuma Alhamdulillah, na yi aiki a
masallacin Umar bin Khattab a can ƙasarmu.”

“Ban zo nan domin neman duniya ba, sai dai in taimaka da abin da Allah ya bani. Na riga na
shirya tsari na musamman da za a gudanar da ruƙiyya ta jama’a kowace da kuma maganin
mantuwa, ruɗu da zalunci" Ya faɗa yana ɗorawa da faɗin

“Na riga na fara shirya ruwan da aka karanta masa ayatul kursiyyu da suratul jinn sau 70. Da
yardar Allah, wannan ƙauye zai zama mai kwanciyar hankali, dama na samu labarin matsalolin
garin nan ne a wajen wani bawan Allah, a inda ya mini kwatance aka sako ni a hanya don na zo
na taimaka"
“Wannan hidima kyauta ce, sai dai idan wanda aka warkar ya ga dama ya kawo sadaka...
kamar yadda ake yi a Yemen!”

Yana sunkuyar da kai, jama’ar wurin suna cewa "Allahu Akbar!"


Mai Gari yana gyara rawani da kallon mutanensa ya ce
“Wallahi wannan ba ƙaramin bako bane, jama'a ku kalli yanda yake fari kamar an wanke shi da
ruwan zamzam!”

Ya cigaba da faɗin
“Ka ce Yemen? To wannan kauyen namu na Ƙundu bai taɓa samun baƙo daga ƙasar larabawa
ba. Kai ne farko, to tabbas alheri ya shigo ƙauyen Ƙundu da yammacun nan!” Ya ce ba tare da
ya jira cewar kowa ba ya ɗora da faɗin

“Mun dade muna fama da matsaloli, mazajen da suka daina kataɓus a wajen matansu, matan
da suke magana da kansu, kawai ka ga zabgegiyar mace ta dage tana zance ita kaɗai, yaran
da suke kuka ba dalili ba dare ba rana sy damu jama'a muna ta zargin shaiɗanun aljannun nan
ne suke buɗe musu maganai(Idanu) Amma yanzu Allah ya kawo mana ƙare kukan ka muna yi
wa Allah godiya" Ya kai ƙarshen jawabin yana juyawa ga mutanen da suke kewaye da shi,
wanda dama asali a wajen suke zaune da wanda suka zo daga baya.

Ya ce daga yau, Sheikh Al-Yamani zai zauna da mu, za a bashi ɗakin baƙi na gidan baƙina da
sannan za a riƙa kai masa tuwo da dare da ɗumamen safe, da rana za a kai masa dambu ko
fura ni a matsayina na Mai Gari na ɗauki wannan nauyin” Ya ce yana gyaran zaman rawaninsa,
don a nasa ganin ya ƙure iya ƙurewa.
A ɓangaren mutanen wajen suna jinjinawa Mai Gari bisa namijin ƙoƙarin da ya yi, amma a
zucuyar Sheik ba haka bane, ransa ne ya ɓaci jin an ambaci tuwo da dambu, saboda ba zai
lamunta ba, ya baro tuwo a ƙauyensu sannan yanzu ma yake fama da tuwo da dambu.

Kai ya ɗago yana faɗin

"Ma sha Allah, Alhamdulillahi hamdan-hamdan, sakallahu bil kairi" Mai Gari ya washe baki don
furucin balaraben kaɗai ya masa nuna da cewa baƙon ya jinjina masa.

Don haka cike da ƙarfin gwiwa ya dubi jama'a ya ce kun ji sai larabceni yake yana mini addu'a
wataƙila har da addu'ar zuwa makkah ya mini" Jama'ar garin kasancewar jahilci ya musu katutu
suka hau gyaɗa kai, balarabe kuwa a ransa ya ce

'Tashin hankali gobarar gemu, wallahi in na yarda da wannan wawancin in nutse a wajen nan,
dole in nemawa kaina mafitar cin daɗi ko na murmure, a kan me zan zo in ke ruƙiyya da ƙarfin
tuwo da dambu, wallahi dole na samarwa kaina ƴanci daga cin tuwo da dambu' A fili kuma ya ce

"Liy su'alun(Ina da tambaya) Ya faɗa yana ɗaga yatsa, duk da basu san mai ya ce ba, don shi
ma kansa ba wai ya ƙware bane a larabcin, larabci ne na ƙarfin hali da ya zauna yake koya a
wajen wani saurayi, sannan a ƙamus na larabci mai fassarar hausa yake ƙara samun ƙwarewa.

Mai Gari cike da ɗan razana yake kallon baƙon balaraben nasu, don bai san wannan larabcin
da ya yi ba cike da ƙarfin hali ya yi namijin ƙoƙarin faɗin

"Ya Sheik, mene ne sussu,aliy(Liy su'alun yake nufi).

Balarabe ya ce

"Ina nufin ina da tambaya" Murmushi ya yi ya ce a zuciyarsa

'Allah sa dai ba wata tambayar ƴar ƙure zai mini ba, ni da ko bihim ban sani ba a yaren larabci,
kai ko cewa aka yi zo in kashe ka Mai Gari ba sani na yi ba' A fili kuma sai ya ce

"Allah sarki mene ne tambayar?" Baƙo ya ce

"Na ji ka ce za a ke bani tiwi da dimbo(Tuwo da dambu yake nufi, amma cikin ƙalƙalar larabcin
rainin hankalinsa ya ce tiwi da dimbo shi a dole bai san tuwo ba.

Shiru Mai Gari ya yi don bai fahimci komai ba, sai da Audu wanda ya rako baƙon da yake ya
fahimci manufar Sheik sai ya ce

"Yana tambayar tuwo da dambu" Mamaki ya so kama Mai Gari amma kuma da ya yi tunanin
baƙon daga ƙasar waje yake ta larabawa sai ya ce

"Ikon Allah na kwance ya faɗi, wallahi an samu akasin lissafi Malam abincinmu ne na hausawa,
mu nan duk wanda bai san tuwo ba sai muke ganin kamar saɓo ma ya yi, don shi muka ci muka
girma kuma shi muke ci har yanzu"

Ya Sheik ya ɗan yatsina fuska ya ce

" La a'alamu hazihil ism(Ban san wannan sunan ba) Shiru Mai Gari ya yi yana tunanin kar
baƙon ya ɓaro masa wani gagarumin abu tun da shi ya ce zai ke ciyar da shi saboda bajinta.

Sheik ya ce

"Mu a namu ƙasa dajaja wato kaza safe da rana dare sai mutum ya ci, kuma muna shan shayi
mai kauri wanda madara ta isa sosai, bama cin komai bayan wannan sai shimkafa ƴar
gwamnati ta buhu" Ya faɗa yana ɗago carbi ya shiga ja.

Mai Gari gumi ya shiga haɗawa, kasancewar duk kiwon da ake a gidansa ba a ci ko tattabara
ba a ci bare kaza, idan har an yi yanja a shekara ne ake layya da sallah, shi ma gudun jama'ar
gari su yi da shi, suke ganin yana shugaba bai yanka ba.

Kamar ya yi kuka haka ya amsa da ceww za a yi bakin ƙoƙari don ganin an ciyar da Sheik ɗin
da abincin da ya saba ci, duk da yanzu ya musu bayanin cewa ya yi wata guda a wani gari
yana koyan harshen hausa dakyar ya samu ya ɗan iya, a can garin ne ma ya ji labarin halin da
garin Ƙundun yake ciki shi ne ya zo.
Sheik ya ga ikon Allah, Mai Gari duk ya rikice saboda tunanin ciyar da wannan baƙo, dan dai
babu yadda zai yi tun da yanzu yana yin wani furuci mutanen gari za su ji babu daɗi tun da suna
ganin waraka ta zo.

Haka mutane suka yi ta tittiɗowa daga gidajensu suna fitowa tamkar wanda ake rabon
buhhunan shinkafa, aka kewaye fadar Mai Gari maza da mata da yara, ana ta kallon baƙon
balarabe.

Sai daf da magriba, Mai Gari ya umarci jama'a da su tafi, haka suka tafi shi kuma ya sa aka
ɗauki jakunkunan Malam, Mai Gari da kansa ya taso ya kama hannun Malam domin bai taɓa
riƙe ko da rigar balarabe ba, bare kuma hannunsa.

Wani irin laushi ya ji hannun Sheik, tunaninsa tsabar zaman ƙasar larabawa ne da rashin aikin

wahala, bai san cewa tsabagen shafa mayukan bilicin ne da Sheik ya yi ba da mayuka masu
sanya laushin fata duk don cim ma manufarsa ta zama MALAMIN BOGI.

Suna tafiya wasu ƙamshin turaruka suna tashi daga jikin Sheik, wanda wannan ƙamshi shi ne
yake ƙara tabbatarwa da Mai Gari cewa yana tare da balarabe ɗan larabawa.


Suna gaba masu ɗauke da jaka suna biye da su, gidan saukar baƙin Mai Gari suka nufa, gida
ne na jar ƙasa aka shafe da siminti, ɗakuna uku ne gidan a share ƙal, kasancewar ba a daɗe da
wasu baƙi suka zauna a gidan ba.

Ledar tsakar ɗaki ce shimfiɗe a ɗakon, sai katifa mai tudu, nan ne ɗakin da Sheik zai sauka.

Mai Gari ya kalli Sheik ya ce

"Ya Sheik wannan ɗakin ne za ka sauka a ciki" Sheik da ya ga ɗakin a ransa ya ji daɗi, amma
a fili sai ya ce

"Wannan ɗakin babu shara!" Haka Mai Gari ya sa samarin da suka ruƙo jakunkunan Sheik suka
share tas aka goge, sannan Sheik ya shiga yana faɗin

"Alhamdulillah, ma sha Allah" Yake faɗa cikin muryar lanƙwasar harshen larabci.

Bayan su Mai Gari sun tafi don Mai Gari ya ce zai kawo mutane biyu da za su zauna a sauran
ɗakunan biyu suke taya Sheik zama, amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama ya ce kar a
kawo komai ya riƙe ayar Allah ba ya jin tsoron komai.

Ɗakin ya rufe ya garƙama mukulli tamkar dai marar gaskiya duk da dama marar gaskiyar ne
wanda ko a ruwa sai ya yi gumi. Hular gashin nan nan ya cire kasancewar zafi yake ji, kansa da
babu ɗigon ko gashi ya bayyana wanda yake ƙwalƙwal, hatta fuskar babu wani gashin saje da
gemu duk ya ɗaye.
Jakar kayansa ya buɗe gabaɗaya kayan jallabiyoyi da turaruka masu ƙamshi ne da hulana
carbuna, da sauran su, wani zip ya buɗe a cikin jakar kuɗi ya fito da shi ƴan dubu dubu rafa
uku, wani murmushi ya saki a fili cikin yin ƙasa da murya da hausa raɗau ya shiga faɗin

"Allah sarki Lami uwar ƴan jaraba ana can ana baloƙoƙo ko ya suka ƙare da mai zubin adashe"
Ya faɗa yana tuno cewa matarsa uwar gidan ita ce ta shiga adashe ɗauka dubu ɗari biyu sai da
ɗaukanta ya zo mai adashe take mata hanya-hanya Lami da ta gaji ta je gidan mai adashe
ranar bata nan ta tafi wani ƙauye sai kishiyarta a gidan, tana ganin Lami ta since saniyar mai
zubin adashe, tana fitowa riƙe da igiya bata zame ko ina ba sai wajen mijinta Ibra dama cin
kasuwa zai tafi haka ta damƙa masa saniyar ta ce ya kai kasuwa ya karɓo kuɗin ta ɗauki dubu
ɗari biyun ta, ta ba mai zubin adashe sauran kuɗin ko mai za a yi sai dai a yi ko ta mutu ko ta yi

rai bata tsoro. Ibra ya karɓi saniya bayan ya je ya siyar daga kasuwar ma bai hau motar garin
Mai mangoro ba, wato can garinsu, sai ya hau wata motar da bai san garin da ,a ta je ba,
wannan ne silar barowarsa gida, da kuɗin ya sayi komai da komai na kayan larabawan da
kayan magungunan ƙaryar da ya zo da su.
Kuɗin ya mayar yana ƴar dariya, yana cewa sai ya zama maloniya a harkar maluntar bogin
nan, yadda zai wuce raini idan ya koma ya biya kuɗin saniyar don yana ganin lokacin ko jirgin
sama zai iya saya a yadda ya tsara in komai ya tafi daidai kenan, in ba a samu mushkila ba.


Mayukan bilicin ɗinsa wanda su ne taimakon farar fatarsa, da ƙwayoyi da yake saya na
bilicin har allura ake masa ta sanya fari, duk don ya yi ɓadda kama a cikin fatarsa ta asali.

Yanan nan zaune har aka kira sallar magriba, bai ankara ba sai ya ji ana ƙoƙarin turo ƙofa, a
kiɗime ya lanƙwasa muryarsa zuwa maganarsa da hausa bata gama kama bakinsa ba ya ce

"Waye?" Mai Gari da suke tare da limamin garin ya ce

"Ya Sheik buɗe mana mun zo mu tafi da kai, za a yi jam'in sallar magriba" Hannu Sheik ya kai
ya taɓo tsakiyae kansa da yake salle babu gashi, ya mayar da kallonsa kan hular gashinsa mai
haɗe da gemo da saje tana yashe a ƙasa, ba na wannan ba, magungunan bilicin ɗinsa da ya
fito da su ya yi ɗai-ɗai da su.
Jin suna ƙara turo ƙofar da ƙoƙarin buɗewa ya mie tsaye babu shiri yana muzurai, a zuciyarsa
yana faɗin

'Allah kar ka bari asirina ya tonu ban cika burina ba, wayyo Allah, yau na san matsawar suka
gane waye ni ba lallai in fita daga garin nan da ƙafafu ba' Ya faɗa jikinsa yana karkarwa duk ya
ruɗe...

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login