Showing 21001 words to 24000 words out of 63190 words
falaƙi, yana ta maimaitawa, ya buɗe wannan ruwan ya
tsiyaya a marfin ya watsa wajen bishiyar kukar, wata irin kururuwa da su Liman suka ɗauka sai
da Sheik ya ja baya kamar zai fita da gudu, sai kuma ya tuna ashe shi ne jagaba a garin. Ya
daɗe yana ta karatun nan sai uban gumi yake sharɓawa, ruwan maganin na kuwa sau uku ya
watsa, cikin taimakon Allah sai Liman da Mai Gari suka fara atishawa, kawai sai ga su an sakko
da su ƙasa, mai fardaɗiyar ce aka sakko ta kamar wanda aka jefo ta, ta zo da rubda ciki,
gabaɗaya wajen ya kaure da faɗin
"Allahu akbar! Allahu akbar".Wani daɗi ya rufe Sheik yana jin kawai ya warke, shi dai da talauci
sai ko ya ga ana yi amma kam sun yi hannun riga da shi da talauci, tun da ga shi har ta ci
nasarar warkar da yaro da kuma su Mai Gari, duk da ya san cewa da alama aljanin jikin yaron
nan wahala ce ta tsinkon da ya masa ta sanya ya fita.
Mai Gari da Malam Liman sai washe baki suke, su kuma jama'a maza da mata sun dunƙule
hannu suna jinjinawa Sheik suna faɗin Allahu akbar!.
Sun san ba ƙaramin aiki ne a sakko da mutane daga saman kukar bulukiya ba, matar nan
wasu mata biyu aka sa suka kinkime ta aka ce a kaita gidan ta.
Mai Gari da Liman faɗi suke
"Jajirtaccen balaraben malami, garin Ƙundu ya yi babban kamu, sai inda ƙarfinmu ya ƙare dole
gari ya kyautatawa Malam kai jama'a ku ce Allahu akbar!" Gabaɗaya wuri ya kaure da kabbara
a tare. Sheik bakinsa ya ƙi rufuwa, sai jin kansa yake yana ƙara girma, har ya fara hango yadda
zai yi kuɗi a saya kadarori. Yana shafo gemunsa ya ce
"Kar ku damu, mu dama taimako ne muke yi, indai aljannu ne ko ido biyu za mu fafata da su
bare kuma a jikin ɗan adam, ai na gani duk aljannu ne suka baibaye kukar amma yanzu sun
tarwatse" Ya faɗa yana ɗan murmushi, a take mutanen gari suka fara kawo kuɗi suna ba Sheik
tun yana zubawa a aljihu har dai aka ara masa fanteka yake sakawa, mutane suna murnar
ceton su Liman da ya yi da kuma murnar garin su zai yi lafiya za su rayu babu tsoro.
A cikin kunnesa iska take kawo masa maganganun matan sa suke wajen wata tana cewa
"Ai mun samu wajen zuwa, mun huta kaiwa malamai da bokaye kuɗaɗenmu suna bamu
maganin mallakar miji, da wanda ake yi wa kishiya, shikenan yanzu a wajen balaraben malami
za muke baje haja" Wata ta ce
"Ai na faɗa miki yanzu malamin nan sai ya rasa lokacin kansa in aka ringa tururuwa"
Duk abin da suke faɗa Sheik yana ji har ya fara hango yadda zai ke tsula musu kuɗin aiki.
Ana cikin haka kamar an ce Sheik ya ɗaga kai, sai kuwa ya sauke idanunsa a kan kukar
bulukiya. Wani kan ƙwarangwal ya hango ajiye a saman kukar, sai ƙaho a jiki, da sauri ya
sunkuyar da kansa, yana haɗiye wani yawu muduk. Carbinsa ya shiga ja da sauri-sauri dama
robar ruwan maganin tana cikin fantekar kuɗin, gabansa ne ya shiga faɗuwa ya tuno furucinsa
da yake cewa ko ido da ido za su fafata.
Liman ne ya ce
"Ya Sheik ya dai?" Ya faɗa ganin duk ya diririce yana ta faman haɗa gumi" Ya san babu wanda
ya lura da abin da ya gani, bai sani ba dai ma ko shi kaɗai aljannun suka buɗewa ido yake
ganin kan ƙwarangwal ɗin. Yaƙe ya yi ya ce
"Ah babu komai fa dama"Ya faɗa yana ɗan ɗaga kai kaɗan ya hangi saman kukar, dariya ya ga
kan yana masa, kafin ka ce kwabo sai aka ga an fara sama da Sheik alamar ƙafafunsa sun fara
barin kan ƙasa, idanu ya zare don kafin ƙiftawar ido har ya wuce saman kan mutane shi kaɗai
yana shawagi a saman ba tare da ya riƙe ko ina ba, yana riƙe da fantekar kuɗi.
Jama'aka shiga faɗin
"Subhanallahi!" Ana ta maimaitawa kowa yana ganin ikon Allah, Sheik gabaɗaya ya tsure sai
hannu yake miƙawa alamar a kawo masa ɗauki, tun da aka fara sama da shi yake faɗin
"Yauma tublar sara'ir, jama'a taimako" Kowa jin Sheik da kansa yana ambatar taimako sai suka
fara ja baya, jar su Mai Gari kowa ya koma can nesa, sai da aka kai Sheik saman kuka, wuyan
jallabiyarsa da shi aka rataye shi a jikin kuka, yana ji yana gani kan wanann ya ciro hirami daga
wuyan Sheik ya masa ɗaurin ɗankwali gwaggwaro a kansa, babu wanda yake ganin kan sai
Sheik...
MAMAN AFRAH
09025576222
*TALLAH TALLAH TALLAH*
????????????
*KIN KARANTA*
??????????????
*Shin kin karanta littafin nan? Kin ji cakwakiyar da ake yi a ciki? Ta kamu da mugun son sa
wanda da shi ta raini zuciyarta tun tana ƙarama, tun bata san mene ne so ba, sai dai tana daf
da sanar da shi aka saka aurensa da yayarta da yake ƴan uwa ne, ta ji takaici a hakan take
fafutukar jan hankalinsa duk da yana mijin yayarta, mutuwar yayarta shi ya bata damar cin
karenta babu babbaka, ta shiga ta fita ta aure shi tun dafin mutuwar matarsa bai barshi ba, sai
dai shegen kishin ta, ya sa ta raba mijinta da kowa ciki kwa har da uwar da ta kawo shi duniya,
hatta ƙawayenta mararsa aure sai da ta daina hulɗa da su dk don kar a aure mata miji, mai zai
faru? Aminiyarta da ta yarda da ita take faɗa mata sirrinta ita ce mafarin komai, kwatsam mijin
ya tashi ƙara aure, da aminiyarta suke fafutuka wajen toshe ɓarakar auren da mijin ya ɗakko,
ashe dai ita ce ta yi wufff da mijin nata sai a washe garin ranar da ta tare suka yi ido huɗu, shin
ya zaman zai kasance? Kin taɓa jin inda kishiya take yin asiri ta rufewa kishiyarta HQ a toshe
wurin gabaɗaya a gefe guda a fito mata da mazantakar namiji? To a buk ɗin nan an yi wannan
badaƙalar, da 500 kawai zan baki book ɗin har ƙarshe* .
09025576222
[7/5, 6:08 PM] Mom mashkr & Afrah: https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1
Mums & mums-to-be!
Adashen washing machinebby & kids’ clothes + accessories ya dawo!
Easy payment, zero stress!
Ki shiga kafin a gama!
+234 707 753 2253
♂️ *MALAMIN BOGI*♂️
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1️⃣
PAGE 6
*MA'ARUF*
Yana dafe da kuncin yana jin zafi da kuma haushin abin da Hajiya ta masa.
Daddy ya ce
"Haba Hajiya yanzu abin da ya yi har ya ci hukuncin mari haka?" Ya tambaya yana kallon ta
Rahma ce ta taɓe baki ta ce
"Haba Daddy ko duka aka masa ai hukuncin ya yi kalli fa yadda ya ɓata mini kaya" Shiru Daddy
ya yi duk da bai ji daɗin abin da aka yi wa Ma'aruf ɗin ba, amma sai dai son ƴarsa ya rufe maaa
ido. Hajiya ce ta ce
"Alhaji kai kake sangarta wannan yaron, in ba haka ba har ya ɓatawa tilon ƴar tamu jikinta kake
tambayar dalilin dukan da aka masa, kuma har kana ganin hukuncin da aka masa ya yi tsauri"
Daddy iska ya furzar mai zafi ya ce
"Bai kyauta ba kam amma dai da baki mare shi ba" Ma 'aruf ya danne takaicin da ya ji yana mai
sauke hannunsa daga fuskarsa ya ce
"Ba komai Daddy ai ita ma mahaifiya ce a gareni, duk abin da ta yi daidai ne... Kafin ya ƙarasa
maganar Hajiya ta katse shi da faɗin
"Ai indai tsara magana ne kai dai sai ko a samu na biyunka amma babu na ɗayanka, ka iya
kalallame mutane wannan da mace ne kai kishiyarka ta shiga uku saboda kissa" Bai ce komai
ba ya juya jiki a sanyaye zai fita, Daddy ne ya ce
"Ina kuma za ka je" Ya ce
"Zan je in ɗan watsa ruwa ne" Amsa masa Daddy ya yi shi kuma ya fita.
Hajiya ta taɓe baki tana cewa
"Wannan uztazun yaron miskilin gaske yana abu kamar dai bai san me duniya take ciki ba" Ta
faɗa tana kama hannun Rahma. Daddy bai ce komai ba ya mayar da hankalinsa ga danna
waya.
Sai shagwaɓa take zubawa a haka suka haura sama wai za ta yi wanka ta sauya kayan
wanann na jikinta.
Ma'aruf yana zuwa ɗakinsa ya mayar da ƙofa ya rufe tare da jinginuwa a jikin ƙofar, ya sauke
wata nannauyar ajiyar zuciya yana tuna irin yadda Hajiya da Rahma suka ɗora masa karan
tsana, ya san kuma ba komai ba ne dalili illa kasancewarsa ɗan ƙauye kai ba ma ƙauyancin
kaɗai ba babban abun shi ne bashi da masu gidan rana, ya san da a ce yana da kuɗi ko da
kasancewarsa ɗan ƙauyen ne to zai samu sassauci da salama, sai dai ba sa ganin ilimin da
yake da shi na addini a nasa ganin da tunanin ilimin addini kamar shi ne zai zama ginshiƙin da
za a ƙauna ce ka, ko yaya dai ka fi ƙarfin jahili, amma a hakan suke masa kallon bagidaje
saboda addininsa.
Goshi ya dafe jin yanayin da ya fara ziyartarsa a ƴan kwanakin nan, wato wasu sababbin
abubuwa da suke son ɓullowa daga zuciyarsa, wanda a halin yanzu shi kansa yake yaƙi da
xuciyarsa, saboda ya san tabbas tana son ta kai shi ta baro ne, to in ba tsautsayin takaba auren
shiɗaɗɗe ba, mene ne yake jin zuciyarsa tana son ta kai shi ta baro shi?.
Ya san tabbas ba ya son halayyar Rahma, ko kaɗan baya damu da sallah ba, ga raini da ɓaci
a gaban iyaye saboda an sangarta ta, sai dai yanzu yana jin wasu ƴan canje-canje a game da
ita, wanda ba ya raba ɗayan biyu wannan kalmar ce da ake kira SO, wannan kalmar dai da bata
duba cancanta ko matsayi, tun da ya san so babu ruwansa da ɗaukaka, matsayi, ƙanƙanci,
talauci mulki kyau ko muni, idan ba zuciyarsa tana son yaudararsa ba mai ya kaita take son
faɗawa tarkon son Rahma. A fili ya furta
"Zuciyata karki mini haka, kar ki yaudare ni, kar ki ja mini abin da zai zama da na sani, kar ki
saba da abin da ba za ki taɓa samu ba, idan mafarki kike yi ki falka, Rahma ta masu kuɗi da
ƴaƴan masu faɗa a ji ne"Ya ƙarasa faɗa yana faɗawa kan katifarsa ya yi rubda ciki. Ya ci gaba
da faɗa a zuciyarsa cewa
'Ta yaya ina baƙauye, sannan ni da albarkacin zumunci na zo gidan nan cin arziƙi amma kike
ɗakko mini dala ba gammo haba zuciyata ki mini lamuni, ki rufa ni ki saya, ki rufa mini asiri kar
ki ja mini tozarci, don abin da kike so ba za ki samu ba ni na sani' Ya ƙarasa faɗa a zuciyarsa
yana fito da wayarsa, number mahaifinsa Mai Garin Ƙundu wanda yake ɗan uwa ne na jini ga
Daddy, ya shiga kiransa, amma bai ɗauka ba, sai da ya kira sau uku ba a ɗauka ba sannan ya
mayar da wayar ya akiye a kan katifar yana mai kifa kansa a jikin katifar yana jin yadda son
Rahma yake fara huda zuciyarsa a hankali.
*LAMI*
Kallon Sheƙeƙe ta yi wa Tunde tana riƙe da ƙugu ta ce
"Tunde na faɗa maka ba ya nan, ni nan da ka ganni da haushin kuɗin da ya guje mini na kwana,
amma in kana ganin kamar yana nan na hana shi fitows ga ƙofa ka zo ka shiga ku fafata, ka ga
sai a yi ko a kai ko a shi" Idanu yake zarowa jin furucinta shi dama ya tsani bayar da bashi
saboda ba yadda zai yi ne ya ba Ibra amma gashi cibi yana neman zama ƙari.
Kamar zai yi kuka ya ce
"Ba zan yarda ba sai kin biya ni kuɗin da nake bin mijinki" Wani uban tsaki ta yi ta ce
"Da na san lokacin da kuka yi, to ko biyar ba zan bayar ba idan rigima kake ji na dame ka na
shanye, ni na fi inyamuri iskanci dan ka ji in faɗa maka" Ta faɗa tana wani zazzare ido. Haushi
da takaici ya cika shi ya ce
"Ko za ka daure ki ranta masa" Hanci ta yatsina ta ce
"Ko naira biyar ɗita ba za ta yi ciwon kai ba, ka kama hanya ka je gidan kakarsa wataƙila tana
da abin biyanka" Tana gama faɗar haka ta juya ta bar shi a tsaye yana riƙe da takarda yana
sababi cikin gurɓatacciyar Hausar sa .
Yana fita bai zame ko ina ba sai gidan Inna Tasallah kafin ya ƙarasa can ya haɗu da wani
wanda jiya yana zaune a fadar Mai Gari aka yi wa su Lamu shari'a. Ganin Tunde yana tafiya
yana ɗaga takarda yana masifa ya masa magana, bayan sun gaisa da shegen tsegumi sai
cewa ya yi
"Ah, ah Oga Tunde sai ina kake sauri" ,Kamar jira yake ya ce
"Tsausayi mana ya sa na ba wannan Ibra bashi, ya ce zai dawo daga kasuwa jiya ya mini
blance amma yanzu na je gidanaa wai ba ya gari yanzu sai cewa ta yi matarsa wai sai dai in je
gidan Kakarsa ta biya ni" Buɗar bakin mutumin sai cewa ya yi
"To ai kai faɗuwa ta zo daidai da zama" Tunde ya saki baki cike da jin haushin wancan ɗin yace
"Wannan wulaƙanci ne, ashe kana mini baƙincikin kasuwancina in ba haka ba ni kake wa fatan
faɗuwa?" Ya faɗa yana nuna kansa.
Da sauri wancan ɗin ya ce
"Haba Oga Tunda ya za a yi in maka fatan faɗuwa a sana'a Hausa ce fa na maka wato karin
magana, abin da ya sa ma na faɗa saboda ina sp in jaddada maka cewa wannan Kakar tasa
kuɗi gare ta jiyan nan a fadar Mai Gari muna zaune sai da ta biya kuɗin saniyar Jummai... Tun
bai gama bashi labarin ba Oga Tunda ya yi gaba yana sauri yana zabga masa godiya, saboda
so yake ya je kar kuɗin ya ƙare.
Inna Tasallah ce zaune a bakin gadonta ta sha ɗaurin ɗankwali gwaggwaro, tana zaune robar
kayan miyarta a ƙasa a gabanta, hannunta kuɗi ne naira ɗari da saba'in dama da safe ta yi
cinikin naira ɗari ya zamana tana da 200 shi ne ta saya koko na talatin ta sha a haka ko suga
bata saka ba, duk don kar ta saya sugan tun da ita bata ƙaunar abin da zai taɓa mata kuɗi sai
dole.
Sai maimaita irgen kuɗin take tana ta washe baki a fili ta ce
"Kai jama'a wato a jikin kuɗi akwai wani maganaɗisu wanda idan kana irgawa duk ɓacin ran da
kake ciki sai ka ji ya washe, Allah ka ƙarawa kuɗi daraja" Ta faɗa yana gyara naira ashirin ɗin,
da yake ɗari ce guda, sai hamsin sai ashirin ɗin.
Tana cikin wannan yanayi na nishaɗi kamar daga sama ta fara jin ana rafka mata sallama,
abin mamakin ma yadda ta ji muryar ba ta bahaushe ba ce, da sauri ta ɗaga filo ta cusa kuɗin a
cikin rigar filon ta gyarawa rigar filon wajen ta gyara ta ja robar kayan miyarta ta tura ƙasan
gado a zuciyata tana faɗin
"Yanzu na shirya ko tashin bob(Bomb) Za a yi na ɓoye kayan sana'a ta kadarata, haka kawai ka
ji inyamuri yana rafka sallama, har ta buɗe baki za ta amsa sai ta fasa, fitowa ta yi daga ɗakin,
wani tsohon gatari ta ɗauka ta nufi ƙofae gidan a ganinta koyaushe gwara ka zauna cikin shirin
kar kana zaune a zo a cika da yaƙi" Ta faɗa